← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 94

Sashe 15

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *15* Lumshe idanunta tayi ta saki wata irin oyayyar ajiyar zuciya, Yayi mata masifaffan kyau ura masa idanu tayi babu ko iftawa sanye yake da wani irin lallausan yadi Coffee colour wanda ya haska farar fatar jikin sa sai yanzu ta kuma are masa kallo dogo ne sosai dan yadda ya mata tsaye akan ta har rumfa tsayin shi yayi mata Yana da manyan lumsassun idanuwa masu kama dana wanda yake jin bacci Yana da cikakken gemu wanda ya ha e da asumba ya cika fuskar tashi Sai aton tabon Abin sallah wanda yay ba i sosai a saman Goshin sa. Numfashin ta ne ya kusan aukewa lokacin da taji ya hura mata iskar cikin bakin shi mai amshin Mint. "Kallon fa?" Ya fa a da tattausar Muryarshi. Tsintar kanta tayi da jin matsananciyar kunyar shi. A hankali ya furta. "Do you feel what I feel when you are with me?" Ya kuma matsowa gabanta ya maimaita mata abin da yace da yaran hausa. "Kema kina jin abin da nake ji atare dani?" Matse katin asibitin dake hannunta tayi gam aranta tana cewa. Wannan Bawan Allah zai halaka ni. Jikinta ko ina rawa yake muryarta na rawa sosai tace. "To ka matsa baya sai muyi magana" Aliyu ya zira hannunshi saman nata hannun ba zato taji ya fisge katin asibitin data ri e a hannun nata. Zubawa katin idanu yayi yana gama karantawa ya saki murmushi. Bai mi a mata katin ba ya zira shi acikin aljihun shi. Hannun nashi tabi da kallo wanda yake shinfi e da wata irin ba ar suma tai luf kamar ka ta a jini ya fito. "How do you feel about your body?" Ya fa a yana arin saka wayar idanun shi cikin tata wadda ita kuma ta i yarda ta ha a idanun dashi sabida duk kunyar abin da ya gani ajikin katin tagama kamata. "Shike nan tunda baza'a min magana ba oya shiga gida" Kamar jira take da sauri ta kama ofar gidan nasu zata shiga ciki. Hannu ya zira cikin Aljihunshi tare da fesar da iska mai zafi. Tsadaddiyar wayarshi wadda bai cika amfani da ita wajan hul a da jama'arshi ba ya fito da ita ya dam a ta a hannun Farha wadda harta kai da shiga soron gidan nasu. A hankali ya rage tsayin shi ya Sunkuya daidai kunnenta ya ra a mata. "Saura ki aga wayata, zan kira ki anjima" Daga haka ya juya ya fice daga soron gidan yabar mata amshin turaren shi. Gaba aya Jikin farha rawa yake sai faman kaiwa da komowa numfashinta yake Ta kasa jan afafunta zuwa cikin Gida gefe guda ga tsoron wannan waya daya bata Ya cika mata zuciyarta. yar ta aro jarumtar jan afafunta da suka mata nauyi ta shiga cikin Gidan Duk matan gidan da an suna cikin akunan su yanayin sallamar datai ne a hankali yasa ba wanda yaji sallamar tata. aga labulan akin umma ta shiga akin da sallama, Umma ta zuba mata ido cike da tausayinta zaton umma duk jikin nata ne yasa ta koma haka. "Sannu farha ina nan ina tunanin ki Yaya arfin Jikin naki?" Ta dam e wayar tana Cewa. "Alhamdulillahi Umma" Daga haka ta nufi uwar akan su ta aje wayar a saman sif gudun kada Umma ta gani, Ta zare hijabin Jikinta Ta fita tsakar gida ban aki ta shiga ta gyara jikinta sabida priod inta daya zo mata a yanzu. Tana shigowa aki taji Muryar yaro yana cewa. "Wai ina fatima?" Umma ce ta aga murya tace. "Shigo mana menene" A lokacin Farha ta zauna a gefen tabarmar akin yaron ya shigo da atuwar leda a hannun shi fara mai yalli. "Wai wanine yace in kawowa Fatima amman ya tafi" Umma tace. "Wani yaya kamannin sa yake?" Sabida duk ta auka ko Salim ne. "Dogo ne sosai fari amman banga fuskar shi ba" Umma tai jimm dan Salim ba i ne kakkaura. "Ka mayar masa da ledar kace ba'a nan gidan take ba" Yaron yace. "Ai ya riga ya tafi tunda ya bani" Daga haka yaron ya aje ledar yayi tafiyarshi. Ikram ta bu e baki cike da aga murya tace. "Wallahi umma da gaskiyar yaron nan nima tunda kika aiken siyo suga azu na ga Mutumin a ofar gida wai yace ina Masifaffiyar yayata, Kuma Umma mutumin kamar balarabe Duk da fuskarshi a rufe take" Umma tai shuru ta zubawa Farha idanu wadda tai asa da kanta Jikinta na rawa. "Farha wanene kuma wannan Mutumin kada ki oye min gaskiya?" Farha tace "Wallahi Umma ban sanshi ba nima, Yace min wai a hanyar wajan aiki yake ganina in zan tafi, Amman umma ni ban sanshi ba Allah da gaske nake miki" Umma ta janyo ledar ta bu Magungunan da aka rubutowa farha ne masu tsada amman ba a sako katin ciki ba, Sai Kaji manya gasassu Guda Uku da Lemuka masu sanyi. "Baki san shiba ta yaya kika bashi katin maganin ki? Farha ba zaki jamin Cin mutuncin mahaifin kiba wallahi sai na tattare kayana na bar muku gidan in banda ke da Ikram da tuni na mance da barin wannan gida Salim bai cancanci haka daga gareki ba kada ki bari ru in Shai an ya shiga zuciyar ki, Maza ki tattare masa kayanshi Kisan yadda zaki ki mayar masa dasu ni babu ruwana kuma ki kuka da kanki idan mahaifinki yaji" Farha tahau kuka tana bawa Umma ha uri. "Allah umma ki yarda dani shine ya wace Katin a hannuna azu" Umma mi ewa tayi tabar mata akin. Farha tasha kukanta Daga arshe ko kallon ledar bata yi ba ta mi e ta shige aki ta kwanta. Umma ban aki ta shiga bayan ta fito Ikram tai musu shinfi a a rumfa suka kwanta dama su a rumfa suke kwanciya Farha ce ke kwanan Cikin uwar aka dan komi zafi bata fitowa. Umma ta jima batai bacci ba tsoron ta aya shine kada Allah yasa wannan Mutumi ya yaudari Farha ya rabasu da Salim dan so wani bin shu'umi ne Musamman ga zuciyar mace mai rauni. Cikin baccinta taji Nishin wayar daya bata wadda ita Fushin umma ma yasa ta mance da ita. Da sauri ta mi e ta auko wayar ta katse kiran. Can wani sabon kiran ya kuma shigowa Numbern ba suna sai dai special number ce ta urawa Numbern idanu kafin a hankali ta aga kiran. Wata irin Ajiyar zuciya Aliyu ya saki ta cikin wayar. "So kike yau na kasa bacci my princess ina ta kiranki baki aukar Min kirana ba Why?" ara dam e wayar tayi tana Zare idanu tsoronta aya kada Umma ta jiyo ta. "Dan Allah ka rufamin asiri bawan Allah kazo ka amshi Abin da ka aiko kasa ummata tana fushi dani" Ta fa i Murya can asa Kamar mai yin ra Aliyu ya Narkar da Murya kamar zai mata kuka ya soma Gaya mata mayaudaran kalamai wanda shi kanshi bai san ya iya suba Luf Farha tai tana ara nutso a saman gado Wayar kare a kunnenta wani irin Ba on lamari ke bibiyar dukkan sassan jikinta. Aliyu sai da ya tabbatar ya mata illah a zuciyarta sabida yadda yaji tana sakin Numfashi da alama kokawa take da zuciyarta Manna wa wayar Kiss yayi ya kashe kiran. Tashin Hankali Farha a zaune ta raba dare ta kasa bacci duk motsi hoton Aliyu da yadda yake mata magiya ne yake mata yawo acikin idanunta zuwa asubah wata irin Mahaukaciyar soyayyar Aliyu tai mata mugun kamu Ko Motsi tayi shi take gani bata kallon ko wani namiji a zuciyarta sai shi taji ta aminta da Salim kawai kula shi take, amman soyayya yanzu ta fara yi da bawan Allah kamar yadda ta ra a masa dan bata san sunan shiba. Aliyu kwanciyar shi yayi ranshi fes batare daya ji dukkan wasu kalamai daya yiwa yarinyar yayi tasiri a zuciyar shiba. Washegari haka ya shiga harkokin sa batare daya tuna da Farha ba Ranar Alhamis wadda ta kama rabon shi da farha kwana uku jirginsu ya aga asar chaina. Harga Allah ya mance da ita tunda ya je chaina zirga zirga yake akan yadda sabbin motocin daya siya su zo Kamfanin shi wannan tasa baya samun Lokacin kanshi bacci ma baya isarshi sosai tsayin sati aya ya auka a chaina daga nan kuma ya wuce saudiyya. Tuni soyayya da tunanin Aliyu sun huda dukkan sassan jiki da zuciyar Farha dama tun washegari da bai zoba Umma Ala dole tai amfani da Kajin ta bawa farha magungunan sai dai sam ta daina sakarwa farha fuska maganar aiki ma umma da kanta tace ita gaskiya farha ta ha ura da fita Tunda dalilin fita aikin wani ya fara biyota ita bata son Su shiga ha in salim wannan hukunci yayi wa farha da i sabida haka bata agawa kanta hankali ba suma mutan gidan duk sun auka rashin lafiyar farha ne yasa Bata koma aikin nata ba. Ba abin da Farha take sai aikin kwanciya Sai kuma zubawa wayar data oye ido kullum Tunanin ganin Kiran Bawan Allah take tun tana sanya rai har ya cika sati ba shi babu wayar shi dole tai shahadar kiran layin nashi sai dai baya tafiya haka zata ha a kai da gwiwa tana kuka ita ka ai a aki tana Allah wadai da zuciyarta data kamu da son wanda ko sunan shi bata sani ba ila ma arya yake mata yaudarar ta kawai yazo yayi. "Ni farha meke damun kine? wannan jarababban bacci da unci ke ka ai ya isheni idan ma dan na hanaki fita aiki ne to kisha Kurumin ki azu Mahaifin Salim ya turo anin sa nan da jibi zasu kawo ku in auren ki" Farha bata aga kai ta dubi Umma ba Hawaye ne ke gudu acikin Idanunta Ta kife a saman gado ranar wuni tayi kuka da magariba Salim yazo haka ta fita a zuciye duk haushin salim ya cika mata zuciyarta. Duk maganar da salim ya gaya mata ba ar magana ce take Biyo baya Cike da mamaki salim ya dube ta dan hakan bai ta a faruwa a tsakanin suba. "Farha lafiya kuwa kodai wani ya ata miki rai ne?" ago a fusace.
Chapter 15 · 0% Book details