← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 94

Sashe 58

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mijina da cikin dare" Saka yatsa yayi ya ane bakinta kafin yace "Nine kwarton ko ita?" Turo baki tayi "Oho muku nidai aka ci amana ta Allah....." bai bari ta arasa ba Ya ora bakin sa a saman nata Ji kake tai us tana amsar darasin nashi tsayin Lokuta yana hukunta tata da Kissing lips inta kafin ya auketa ya saukar da ita asan carpet ya shiga yago kazar yana saka mata abakin ta Haka ta dinga amsa tana ci tana Lumshe ido harta oshi takura mata yayi seta sha kankana A wajan shan kankanar seda tayi Kuka dan cikinta ya cika Tana gama sha ya agata Ya kaita tai Brush tare da auro alwala aikuwa tana zuwa ta haye gado se bacci Ya tattare Komai daya zube sannan ya shiga Toilet ya auro alwala Carpet ya shinfi a ya soma nafila har wajan ayan dare yana saman carpet Kafin ya tashi ya Ninke ya cire jallabiyar Jikinsa ya hau gadon bai takurata ba dan ya fahimci tana jin da in baccin janyota yayi Jikinsa ya ha eta da irjinsa yaja masu bargo arfe hu u ya farka sabida sahur dan Gobe za'a tashi da azumin watan ramadan Ba abin da ya iya ci se dabinon daya shigo akin dashi se ruwa marar sanyi sannan ya tashe ta tai sahur in itama daga falo ma yana jin su Ammi na hidimar yin sahur in farha Tsire taci da sauran Yoghurt in data rage ya an kalleta "Zaki iya azumin amman?" ta aga masa kai Ita dai tana gama sahur wani baccin ta kuma komawa shikuma jiran asubahi yayi ana kiran assalatu ya fita masallaci daga nan kuma bai Kuma dawowa ba part inshi ya wuce. Farha da yar ta iya sallah ta koma bacccin ta..........*RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 72* Ganin hasken falon Part inshi a kunne yasa ya arasa cikin falon da sassarfa Lokacin Mami ta fito daga kitchen hannunta ri e da cup da shayi aciki tana ta juyawa da spoon Jiyay gabanshi ya fa i yana addu'a Allah yasa mami bata le akin shiba dan ya manta bai saka key ba ta an kalle shi tana yi mai hararar wasa. "Shine koka tashe ni nayi sahur ko?" Ya shafa saman kanshi wanda baya barin suma ko aya tare da cewa "Ai duty in kine ni me yasa baki zo kin tashe niba, Ko abin da zanyi sahur in ma baki bani ba haka na kusan makara dan kin san bakya azumin ke" Dariya tayi tare da wucewa saman Kujera ta zauna tana shan tea in nata ajiyar zuciya Aliyu ya mayar bayan ya tabbata mami bata Je akin shi ba ya haura saman shi yayi wanka Wajan 6:00am ya fito cikin shiri ze fita ya arasa akin Mami tana kwance ta dun ule cikin Bargo ya an tsaya akanta yana duba tsadaddan agogon shi irar samfirin exporer ya an bugi pillown da mami take kai ta bu e idon ta tar akan shi kafin ta yun ura tana cewa. "Ina kwana har ka fito?" Ya saki murmushi yana cewa. "Ehh na fito mamy zani dutse yau sannan kuma zani gidan Alhaji akan case in Hanan" Mami tai masa fatan alkairi ya fita ya wuce sashin Ammi ba kowa a falon se arar Ac da fanka da suke faman yi da alamun kowa bacci yake yi Sabida dama azumi ya gaji haka akin Farha ya bu e ya shiga. Itama tana kwance kuma bacci take sosai ya zauna a gefen gadon ta ya fito da wayar shi ya kira musa akan yazo su wuce sautin maganar shice ta farkar da farha ta tashi zaune duk fuskarta a kumbure take tashi tayi daga zaunan ta sauka ban aki ta shiga ta wanko fuska ta dawo har Lokacin waya yake yi ta zauna a asa tana kallon shi ya gama wayar ta an saci kallon shi ka an tare da cewa "Ina kwana" da kulawa yace mata. "Lafiya lau yaya azumin?" tace masa "Alhamdulillahi" Shuru suka yi su dukan su kafin ya mi e tsaye. "Zan je dutse daga nan kuma zan shiga Gidan Alhaji" Bata gano me yake nufi ba tace masa "To Allah ya tsare hanya" ya zuba hannayen shi cikin aljihun shi. "Baki bu atar komai wanda zanzo Miki dashi me kike sha'awa kici idan an sha ruwa?" Tai jimm tana tunani kafin tace masa. "Ka tawo min da Nono mai tsami, se Kuma ata da Mangoro" setai shuru tana kuma tunano abin da take so can kuma tace "Yawwa da fara" dariya yayi tare da cewa "Duk zanzo dasu amman ni baza'aci fara ba" Turo baki tayi tana uni "Nidai ina so ka siyo min" Dariya ya kuma yi mata tare da cewa "Tom shikenan zan duba Miki" ya fita daga akin ta bishi da kallo wani bin yana da kirki Musamman a lokutannan ta rasa mai yasa yake lalla ata Komai tace masa yana mata batare daya dan ara mata ba ar magana kamar da ba. Bata koma bacci ba tashi tayi ta wanke Toilet inta dan yau ta tashi da arfin Jiki rahmar Allah kenan, tana azumin amman yau kuma tana jin kuzari sosai ajikinta Bayan ta wanke toilet inta Ta Cire Zanin gadon ta, takai Cikin Injin wanki ta sauya wani Gyaran akin nata tayi sosai ta tattare kayanta dasu kai datti duk ta fitar dasu Ta kunna turaren amshi a akin nata. Aliyu fita yayi akin Ammi tana bacci se kawai ya fita suka wuce dutse shida Musa. Gidan Ammi wuni akai bacci kamar babu an adam agidan Farha gajiya tayi da kwanciya ta fita sashin hajja anan tayi sallar la'asar sannan suka rankayo tare kitchen suka shiga osai suka fara soyawa sannan suka soya dankali Sannan sukai farfesu suka dafa ruwan shayi Nan da nan suka ha a dukkan abin da za'ai bu a baki dashi wajan magariba kuma akaita shigo dasu kankana gwanda lemo ayaba Hajja tasa farha Yayyanka su acikin aton Bowl ko wanne daban Farha ta gaji iya gajiya sabida a alla sunyi kayan shan ruwa kusan kala goma hajja tana tsaye da Dabino a hannunta tana wankewa Farha ta ago ta dube ta. "Wai hajja yanzu Kullum wannan aikin zamuyi har arshen ramadan gaskiya zamu sha wahala" Hajja tayi dariya tare da cewa "A,a ai nan da an lokaci ma zasu wuce saudiya umara Dukka gidan ina ga Salama ce ka ai wannan karon babu amman gaba ayan su zasu tafi" Farha ta jinjina kai cikin mamaki tace. "To Ku kuma ina zaku je?" Hajja tace. "Ni gida zan koma sauran ma'aikata ma duka gida zasu wuce se kuma ana gobe sallah zamu dawo sabida ana jibi sallah suke dawowa" Farha ta jinjina kai batare data ce Komai ba sedai taji da in wannan tafiya tasu sabida Ko banza itama tasan zata je Gida ta zauna kafin su dawo. Ana magariba suka kammala komai farha ta auki kayan bu a bakin ta taiwa hajja sallama tana shiga akinta wanka da alwala ta auro tazo tayi sallah tunda ta idar da sallah ta kwanta a asan Tiles bayan ta na e carpet akinta ruwa ka ai take ta sha dan jitayi bata sha'awar Komai haka taita malelekuwa a asa sanyin wajan yana ratsata ba aramin da i take jiba dan har wani Lumshe idanu take yi. Can bayan sallar Isha'i wanda a a'ida se Lokacin mutan gidan suke cin abinci sabida idan an sha ruwa Dabino da ruwa ka ai suke amfani dashi Safna ta shigo akin Farha tare da ce mata tazo Inji Ammi farha ta auki hajib ta saka gaba aya iyalin Gidan suna kan dining kowa yana Cin abinci Ta Tsugunna tana gaishe da Ammi wadda ta kalli Farha da kulawa tare da ce mata. "Ke kin sha ruwan naki ne?" Farha ta aga kai tana wasa da yatsun hannunta. "Yawwa to masha Allah, Nan da wajan jibi haka ko ranar sati zamu tafi umara ki ha a kayanki waje aya Idan Baba yazo zewa Musa magana seki Je gida ana jibi sallah zaki dawo kafin nan Mun dawo In sha Allah" Farha ta saki fuska sosai tana dariyar Farin ciki kafin tace. "Dama Ammi komai nawa ma a ha e yake ko yau ma zamu iya tafiya gidan Ko musa be zoba Ni zan gane hanyar Gidan Namu" Ammi tace. "To shikenan tashi kije sena neme ki" ewa tayi zata shiga akinta Bashir ya kirata. arasa gaban shi Turo mata Plate yayi tare da cewa ta zuba masa Soyayyan dankalin dake gaban shi ta auki Plate in ta zuba mai ta tura masa gaban shi ta lura daga Matar yayansu har wannan Budurwar se harararta suke ta e baki tayi zata Juya ta koma amshin farfesun da sakina keci ya doki hancin ta Wanda nan da nan cikinta ya hautsine da sauri tabar wajan tana zuwa aki ta dinga she a amai wanda shine ya galabaitar da ita a bakin Toilet ta kwanta a asan tiles tana mayar da Numfashi dan bata da Kuzari ko ka Lokacin daya shiga Gidan Alhaji Hamishi ana kiran sallar magariba...........*RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 73* Sabida haka sauka sukai daga mota suka shiga cikin wani aramin masallaci dake ofar gidan suka yi sallar magariba Ya mi awa Musa dabino Wanda ya auko daga cikin aljihun farar shaddar dake Jikinsa a tare da Musa suka shiga cikin Gidan marigayi Alhaji Hamishi a Madaidaicin Falon gidan suka tarar da Momcy a zaune tana shan Kunun Bu a baki zama sukai a asan carpet Momcy tayi juyin duniya akan su tashi su zauna a saman kujera Amman suka i tashi tayi ta shiga Kitchen tray ta fito dashi wanda ke sha e da kayan ciye ciye ta dire a gabansu tana cewa. "Nasan bakuyi bu a baki ba ga an abin Motsa baki nan" a baki sukai wajan yi mata godiya
Chapter 58 · 0% Book details