Sashe 1
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data Normal *RABO YA RANTSE...!!* *NA* *AUTAR MANYA* Bisimillahi Rahmanir Rahim *001* Ya zuba wa likitan jar fuskar shi yana binsa da kallo da manyan idaunshi wa anda suka rine daga farin su na asali zuwa jajir har wani ruwa ne ya kwanta acikin su gaba aya jijiyar dake kanshi ta mi e, shi kanshi likitan bai iya ha a ido dashi ba sabida yadda halittar idanun nashi ta sauya ta jirkice kai kana kallon shi kasan yana cikin tashin hankali ba an ka an ba. A hankali likitan ya auko gorar ruwa daga cikin frij in dake office in shi ya alle murfin ya mi a masa, bai musa ba ya amsa ya kafa kanshi a saman gorar wadda bai ajeta ba sai da ya shanye ruwan tas! wanda gumi ya sami damar yanko masa ta kowa ce kafa ta jikinsa tamkar babu na'urar Ac acikin office Sai dai har lokacin idanun nashi basu sauya launi ba wani aton abu ne ya zo ya tokare masa ma oshin sa zuciyar shi tai rauni a lokacin yasan kuka ma rahma ne in da zai iya da yayi sai dai taurin dake cikin zuciyar shi irin na jaruman maza sadaukai Masu tawakkali da yarda da addara shine ya bashi damar yin dakiya acikin wannan lamari da ya kuma afkuwa a gare shi. "Doctor kana nufin wannan karon ma nayi asarar Beby na a karo na Hu ALIYU ya fa a cikin Sanyi murya kamar ba tashi ba. Doctor ya dube shi. "Kayi ha uri yalla ai haka Lamarin Allah yake, Ka auka haka ya tsara maka ma a wannan karon" A hankali ya shafo tulin sumar dake kanshi wadda take a nanna e irin ta fulanin asali innan ba a irin wadda tai kamar an shafa mata relacxa bai ce komai ba har wajan mintuna goma. Kafin yace. "Muje doctor a ibi jinin nawa a ara mata ina fatan tana cikin oshin lafiya?" Likitan ya mi e yayi gaba yana cewa. "Har yanzu bacci take, bata riga ta tashi ba" ALIYU bai ce komai ba yabi Likitan zuwa akin iban jinin sai da aka ibi leda uku a jikinshi sannan likitan yace masa ya kwanta a wani an gado dake akin dan ya sami Hutu. A hankali ya mi e yana rangaji yabar akin batare daya tankawa Likitan ba, a harabar rantsatstsan asibitin Kuwa Jama'a ne Burjik mafi aka sarin su an uwan ALIYU ne na jini sai an uwan Matar tashi. Da sauri Musa Yaron shi ya taso ya kamo shi yana cewa. "Sannu oga ai da ka kirani dana zo na taimaka maka" Idanun ALIYU da suka fara rufewa ya ago ya dubi Musa murya a hankali yace masa. "Musa kaini gida please" Jikin musa na rawa ya aga murya ya kwa awa drivern ALIYU kira wanda ya taso da sauri ya shiga cikin wata ba ar jeep wadda tsayawa fa in tsadar tama ata baki ne ya araso gaban su Musa ya taimakawa ALIYU ya shiga cikin motar ya kwantar da kanshi jikin Kujerar motar ya lumshe idanun shi driver yaja motar an uwan ALIYU suna ta aga mai hannu duk jikinsu a sanyaye. Motar bata tsaya a ko ina ba sai a ofar gidan Shugaban kamfanin sayar da manyan motoci da ananu wanda ke garin kano da kuma lagos da abuja mai suna *MADAKI MOTOR'S* kuma shine mai bawa gwamnati mai ci a yanzu shawara a angaran *MATASA* Ko ina ka duba pasta ce mai hoton ALIYU tun daga farkon Titin Gidan wanda ke unguwar ofar Na'isa,har zuwa jikin ginin gidan wanda aka rubuta *HASKEN MATASA TALLAFIN MATA DA ANANUN YARA* Da gudu masu gadin gidan suka wangale aton gate in wanda motar da ALIYU ke ciki ta kutsa kai cikin aton filin adana motocin dake gidan wanda yawan motocin wajan ka ai in ka gani sai ka shiga imuwa, Masu gadin da sauran ma'aikatan gidan tuni sun zagaye motar kowa Burin shi Yaga halin da ALIYU yake ciki sannan yayi masa jaje akan abin da ya same shi Musa ne ya taimaka mashi zuwa part inshi wanda ko masu hidimar gidan basu sami Zarafin yin magana da ALIYU in ba. A hankali ya nufi ha an Parloun shi wanda ya gaji da ha uwa Ko ina amshi da sanyi ne ke tashi ga masu hidimar part in suna ta kaiwa da komowa baya amsa gaisuwar da suke masa haka yaja afafun shi da sukai masa sanyi ya haura saman shi kai tsaye bedroom inshi ya nufa ya fa aton katafaran gadon shi idanun shi ya rufe ruf yana sakin numfashi. Gaba aya masu hidimar gidan jikinsu yayi sanyi na yadda suka ga uban gidan nasu duk da bamai yawan magana bane amman sanyin shi na yau ka ai yafi na koda yaushe. aton parloun ta tana ta sintiri hannunta goye a bayanta taka sa zaune ta kasa tsaye tana ta faman kiran Numbobin ALIYU bai auka ba cikin sauri wata dattijuwa ta shigo parloun ta dubi Matar dake sintiri a parlon babbar macece sosai dan ta manyanta a shekaru sai dai a fuska da jiki zaka ga ba sosai shekarun nata suka fito ba sabida yadda take cikin hutu da jin da i Kallo aya zakai mata kasan ita ce mahaifiyar ALIYU sabida yadda kamannin nasu ya fito sosai kamar tayi kaki ta tofar haka suke da ALIYU bata da jiki sosai fara ce tas kana kallonta kaga Bafulatanar asali. "Ranki ya da e Alhaji ya dawo sai dai jikinsa duk a sanyaye yake wanda bamu san halin da hajiya aramar take ciki ba" A hankali Matar ta juyo ta kalli dattijuwar wadda tai saurin yin asa da kanta fuska babu walwala tace. "Nagode Hajja jeki kitchen ki ora mana abincin dare" Daga haka ta Nufi akinta wanda tsayawa fa in tsaruwar sa ma ata baki ne Mayafi ta auka ta fita daga Part in nata ta nufi wanda ALIYU ya shiga Tun farkon shigowar sa Duk masu hidimar sashin ALIYU sun shiga nutsuwar su sabida ratsowar Ammi mahaifiyar ALIYU angaran sai zubewa suke suna mi o mata gaisuwa bata amsawa hasali ma ko kallo basu ishe taba haka ta wuce babban parlon shi ta haura saman kanta tsaye ta shiga akin baccin sa. Ta ja ta tsaya a kanshi tana Mai zuba masa idanunta tsananin tausayin yaron nata na ratsa dukkan Jikinta. "Yanzu kai ba da ban ma'aikatan gidannan sun gayan Mami bata da lafiya ba, da ba zaka gayan ba haka kuka wuce asibiti tun safe ina matsayin mahaifiyarka amman baka gaya min ba?" Firgit! ALIYU ya mi e zaune yana zuba mata ido wanda har lokacin basu dawo daidai ba. "Allah ya baki ha uri Ammi tsananin ru ewa ce ta saka ban gaya miki ba, Suma an gidan su Mamin, ita ce ta shaida musu, Sannan Mun ha u da Khalil a asibitin shi ya fa awa cikin gidan Baba Madaki, yanzu haka duk mun baro su a asibitin" Har ALIYU, ya gama maganar Ammi bata auke idanunta daga kallon shiba inda abin da Ammi tafi tsana a duniya bai wuce gidan Baba Madaki ba wanda Yake gida ne na kakannin su ALIYU wa anda suka haifi Mahaifin su, dukkan annen mahaifin ALIYU anan cikin gidan Baba Madaki gidajen su yake wanda suke a bayan gidan su ALIYU in wajan galadanci Mahaifin ALIYU ka ai ya tsallako ya fito daga cikin gidan amman dukkan sauran an uwan shi suna cikin gidanne. Wanda Ammi sam bata shiri da an uwan mahaifin su ALIYU. "Ka kyauta min da abin da kayi" Ammi ta fa i tare da barin akin nashi. ALIYU a hankali ya koma saman gadon shi ya kwanta sai Lokacin ya tuna da wayoyinshi dake wajan Musa tuni ya kashe wayoyin sabida yasan yadda mutane zasu dame shi da waya shi kuma baya son Magana a halin da yake ciki a yanzu. Bai tashi ba sai gab da magariba ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya sanya jallabiya fara al yay arin turare mai kamshi sosai ya fita masallacin dake harabar gidan nasu ya an sami nutsuwa anan ya dinga Gaisawa da ma'aikatan gidan daga nan ya wuce part in Ammi sai dai bai same ta ba wai tana asibiti cewar annen shi ammata sajidah da safnah daya tarar suna kallo a parlo suma dawowar su daga makaranta kenan inda suke karatu a jami'ar bayero dake kano suna lavel 2 Cikin wata aramar honda civic fara ya shiga A hankali yajata yana driving kanshi bayan ya sanya p cap ya kare fuskarshi sabida gudun idanun jama'a Masu gadi suka hangame aton gate in gidan ya fita da motar dandazon matasan daya gani a ofar gidan ne ya bashi mamaki da gudu yaja motar yabar harabar gidan yana gudun kada su gane shine cikin motar. Cikin anin lokaci ya arasa asibitin yay horn aka bu e masa gate in ya shiga cikin harabar asibitin yay parking motar ya fito gudu gudu sauri sauri ya shiga angaran da aka kwantar da Mami matar shi Ya tura ofar akin ya shiga ciki tana kwance har Lokacin ga ledojin arin jinin da akai mata sun are an cire Ammi zaune ita da Maman Mami sai annen Mami in duk sun yi tagumi Kallo guda zaka ma Maman Mami kaga suna yanayin kama da Ammi kasancewar yayarta ce Mahaifin su aya. ALIYU ya tsugunna ya gaida Maman Mami wadda ta amsa mai cikin kulawa tana mai tashi ta fita daga akin Ammi data masa kallo aya itama tabi bayan maman mami sauran annen Mami ewa sukai suka fita akin yayi saura daga ALIYU sai Mami dake kwance a saman gado. *Idan kina bu atar na tallata miki kayan siyarwar ki a asan shafikan littafin nan kimin magana kai tsaye duk shafi 2 500 naira ne 09022260850* *RABO YA RANTSE...!!* *NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *002* Cikin sanyi jiki ALIYU ya arasa Bakin gadon da Mami take kwance ya zauna a gefenta, Hannun shi mai taushi ya sanya ya tallafo kanta ya ora saman jikinshi ya zuba mata ido tsananin tausayinta ne yake ratsa masa cikin zuciyarshi wanda har yake huda dukkan sassan jikin shi. Mami idanunta ta lumshe wanda ruwan