← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 98

Sashe 98

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bayan kwana biyu da faruwan wannan Al'amari Ammah ta soma bud'e idanu saidai bata iya magana har yanzu sabida matsalan numfashinta da yayi tsanani, a b'abgaren su Junaid da Zaliha kuwa kullum cikin k'ok'ari suke don tuni Junaid ya sami connection da tashan mota ta can garin Tambuwal ana masa binciken wani gari ne Mairo da Daddah suka nufa, dukda basu sami wani zance mai dad'i ba hakan baisa sunyi giving up ba, a wannan 'yan kwanaki sabo mai tsanani ya shiga tsakanin Zaliha da Junaid, sun kuma rok'i Ma'ajura kan duk yanda za'ayi kada ta sanar da Nana A abinda suke k'ok'arin yi....

A can Damaturu kuwa a dole Sahal ya samarwa Ali wani therapist wanda zai dinga dubasa sabida kwanyarsa ta samu ta dawo aiki dai-dai... Dr Maji ya buk'aci da a dinga kawo masa Mairo koda sau uku a sati sabida ya gano Mairo ko mai irin kamanninta nada alak'a da past d'insa, sam basu bari Daddah tasan da wannan batu ba.... Haka Ali zai sakata gaba da ambatonta da sunan da ba nata ba, a dole take amsa sunan Deejoh idan ya kirata dashi.... A haka sabo mai tsanani ya shiga tsakanin Ali da Mairo har take jin abubuwa da dama wanda bata tab'a jinsu a baya ba gameda shi, wani sa'in har alla-alla take ranar had'uwarsu da Ali ya zagayo....

***

Yau ce ranar da Dr Maji ya yanke don gayyatar Ali zuwa asibiti sabida akwai abubuwan da dole sai a asibiti ne zai iya dubasa, Ali yaso su tafi tareda Deejoh saidai ranar d'in ba ranar zuwanta bane hakan yasa Hafiz ya masa rakiya zuwa wajen Dr Majin a babban asibitin ta garin Damaturu

***

"Hello Sadiq kana jina....."

Daga d'aya b'angaren Sadiq ya amsa da k'yar, cikin tsananin ciwo yake fad'in "Lamido they think I was dead, sunmin duka mai tsanani sun kuma k'wace hoton Mairo, amma kar ka damu yanzu haka ina nan babban asibitin garin ina receiving treatments..."

Lamid'o ya fuzar da iska had'i da shafa sumar kansa kana yace "Sadiq I'm so sorry I got you involved....."

Da k'yar Sadiq ya d'an girgiza kai kana yace "Kar ka damu bayan duka alkhairan da ka min a rayuwa this is least I can do, besides I'm still alive basu cimma burinsu ba kuma insha Allah hakan na nufin kariyarsu tazo...."

Lamid'o ya kuma jinjina kai yana mai fuzar da iska kana yace "Na gode Sadiq, make sure you keep me posted, and please you need to stay lie low har abubuwa su warware...."

Sadiq ya kuma jinjina kai kana yace "Kar ka damu Lamid'o insha Allah zan kula dakaina, I'll keep you posted, but you still need to be very careful your father might be watching you...."

"Mistake d'in da nayi a baya bazan kuma maimaitawa ba insha Allah, thank you once again bro...."

Daga haka sallama sukayi kafin Sadiq ya mik'e da k'yar zai d'an zaga ta waje sabida tsami da k'afafuwansa suka masa....

A dai-dai bakin ward d'in ya hangi wata fuska kaman fuskar da ya sani na tunk'aro yanda suke....

*SameenaAleeyou📚*
Chapter 98 · 0% Book details