← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 98

Sashe 77

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maido da dubansa ga Lamid'o yayi murmushi saman fuskarsa yake fad'in "I have to go... I gotta go.... We talk later ka gane...." Sauri sauri ya nufi motarsa ya bar Lamid'o tsaye wajen yana mamakin maike faruwa da abokin nasa, bai ma sami daman tambayarsa wacece Azeeza ba.... Cikin sauri ya nufi cikin foundation d'in bayan Siraj ya fice a guje kaman mai shirin barin gari....

Ya jima tsaye k'ofar office d'in nata yana tunanin ta yanda zai soma.... A hankali ya fuzar da iska kafin yasa hannunsa jikin k'ofar ya soma knocking a hankali tamkar mai tsoron kada fasa k'ofar...

Idanunta naga files d'in gabanta take fad'in "Yes who's there...?" Shiru ba'a amsata ba sai k'wank'wasawa da aka ci gaba da yi a hankali....

Lokaci guda ta daina abinda take had'ida maida dubanta da hankalinta sosai ga k'ofar.... A hankali ta mik'e ta isa ga k'ofar cikin yanayin tafiyarta....

"Ma'ajura is that you...? Wanene ne...?" Ta kuma tambaya tana mai kai hannunta jikin k'ofan, lokaci guda ta murd'a handle d'in had'ida bud'e k'ofar....

Idanu hud'u sukayi su duka biyun suna kallon juna, wani irin bugu k'irjin Nana A yayi lokaci guda zuciyar tata taci gaba da tafasa, kallon Lamid'o da tayi yanzu a gabanta ba komai ya tuna mata ba illa abubuwan da kunnuwarta suka jiyo mata sanda sukaje gidansa itada Nana H... Lokaci guda ta kasa jurema kallon nasa, saurin juyawa tayi zata rufe k'ofar saidai kafin takai ga rufewa tayi missing step sabida yanayin k'afarta...

Cikin sauri Lamid'o ya tarota ta fad'o jikinsa, hankali tashe yake tambayarta

"Are you hurt. ....?!"

Wani irin zabura ta kumayi had'ida turesa tana fad'in "Let me go... Don't you dare touch me again, ko ka d'auka nima irin 'yan matan naka ne daka saba fasik'ancinka dasu...?"

Kallon mamaki kawai Lamid'o ke binta dashi don yasan sam a baya Nana A ba haka take ba besides shi bada wani manufa ya rik'eta ba face garkuwa da yayi mata don kar ta fad'i k'asa...

Lokaci guda ya kuma sinkayo muryarta yanda taci gaba da fad'in "Mai ya kawoka nan.... Meye kazo yi nan...? I thought I made myself clear, it's over between us, ka fice min a office da kuma rayuwata....!!" Ta k'arashe tana mai nuna masa k'ofa....

Har lokacin Lamid'o bai daina dubanta ba, bai fice d'inba saima kuma shigowa cikin office d'in da yayi....

Lokaci guda hawaye suka ci gaba da zubowa daga idanunta...

Saida ya k'araso dab da ita kana ya tsaya, yana iya kallon tsakiyar kanta domin shi mutum ne mai tsawo sosai, d'an rank'wafowa yayi yana mai duban fuskarta yanda hawaye ya wanke har cikin zuciyarsa yake jin zogin zuban hawayen nata, a hankali murya can k'asan mak'oshi ya soma fad'in "I really don't have any idea what you're talking about.... Asma'u bansan mai kike nufi da cewa na d'aukeki tamkar sauran matan da na saba holewa dasu ba... Asma'u this is not you, wllhi wannan bakebace domin Asma'u na da na sani mai ganin girman mutane ne koda kuwa sun cutar da ita, amma ni bansan mai kike nufi da matan da na saba holewa dasu ba.."

Wani kallon da ta d'ago rinannun idanunsa tana watsa masa ya sanyasa d'an dakatawa da maganar nasa still idanunsa na kanta... Lokaci guda kuma ta kifa kan nata k'asa tana mai ci gaba da kuka, ba tareda ta kuma dubansa ba take fad'in "I was wrong about you, na d'auka da gaske kana k'aunata kaman yanda kace, na d'auka kai d'in mutumin kirki ne, a zatona kanada hali irin na Uncle Siraj da Uncle Heedj, but I was wrong and stupid.... Nana H was right all along, ban yarda da 'yar uwata ba na yarda dakai... Zaka k'aryata cewa baka gayyaci budurwar taka har apartment d'inka ba... Ban tab'a ganin tashin hankali a rayuwata ba irin wannan rana, idan bakaji tsoron mahalliccinka ka daina domin shi ba don me zaka daina sabida ni.... Sannan daka tabbata true identity d'inka ya bayyana mana shine ka gudu, ka b'ace gaba d'aya tsawon watanni... Do you have any idea how much it hurts..!!!?" Kuka yaci k'arfinta....

Sai yanzu Lamid'o ya fahimci mai suke nufi daga ita har Siraj, sai yanzu ya gane gadar zare aka shirya masa, bai kuma kawo kowa ba sai Nana H, yasan wannan aikinta ne, itace kawai zatayi wannan aiki don yasan since from the start bata k'aunar relationship d'insa da 'yar uwarta, ya kuma san bata k'aunar ganin farin cikin Nana A ya tabbata ita ta shirya masa wannan trap d'in idan kuma ba ita bace toh Junaid ne k'ila ya jima yana bibiyan rayuwarsa don yayi ruining d'insa ya rabasa da Nana A yayi amfani da damar wajen cutar da ita...

A hankali ya mik'e tsaye had'i da shafe fuskarsa...

Cikin sassanyar murya mai kwantar da hankalin mai sauraro ya soma fad'in "I swear it wasn't me, I've no idea wanene kika gani a gidana, sannan tun bayan da na kub'uta daga hannun kidnappers d'in nan ban koma apartment d'ina ba ina gidan mahaifina... Nana A wllhi wllhi I'm telling you the truth, na tabbata an shirya haka ne domin a rabani da ke, but whoever did that... I'm gonna find out, bazan tab'a bari wani ya cutar dake ba ko ya cutar da soyayyarmu... I'll fight for our love.... I love you Nana A... With all my heart...." Cak ta daina kuka mai sautin sai hawaye dake kwaranya mata.. Lokaci guda ta d'ago fuskarta tana dubansa

Wani irin yanayi ta hango k'wayar idanunsa ciki wanda bata isa ta k'aryata abinda ta hango ba...

Lamid'o ya kuma jinjina kai kana yace "So much Asma'u, inai maki soyayyar da bazan iya cutar dake ba komin kashinsa.... Inaso koda ace bani a raye ki ajiye wannan a zuciyarki, Lamid'o mai k'aunarki ne..." Daga haka ficewa yayi cikin sauri zuciyarsa naci gaba da masa zafi, kunnuwarsa basu daina jiyo masa sautin kukanta ba yayinda idaniyarsa basu daina hango hawaye dake kwaranya saman fuskarta ba...

Junaid dake lab'e jikin wata k'ofar yana ganin Lamid'o ya fice ya bisa da kallon tsana.... Lokaci guda ya saki murmushi domin dama bayaso Lamid'o ya mutu baiga aurensa da Nana A ba, ya tabbata daga Lamid'o har Siraj nemansa suke a halin yanzu ruwa a jallo, dole suyi tunanin ko shakka babu Shi yayi ajalin abokin fasik'ancinsu Ahidjo.... A hankali ya kuma sakin murmushi domin yanda yaga Lamid'o yayi wani irin rama uwa uba ya fice daga office d'in Nana A tamkar wanda aka masa albishir da jahannama yasan cewa duniya taimasu d'aurin goro, haka yake fatan ganinsu cikin k'unci da rashin samun kwanciyar hankali kaman yanda suka hana masa nasa......

Saita kansa yayi kafin ya nufi cikin office d'in Nana A har lokacin bata daina aikin kuka ba....

Junaid ya jima yana binta da kallo daga bakin k'ofar yanda yake zaune saman wheelchair d'insa... Badai Nana A son Lamid'o take ba har yanzu, badai sabida shi take kuka ba,.... Take yaji wani irin abu mai kama da kishi yana taso masa.... Cikin sauri yaci gaba da gungura wheelchair d'insa ya isa gareta, murya a hankali ya ambaci sunanta da irin sigan da shi kad'ai yake kiranta dashi....

"Asmah....!"

Cak ta had'iye kukanta ba tareda ta iya d'agowa ta dubesa ba....

Junaid yaci gaba da fad'in "Shin kin tab'a sanin kukanki tashin hankali ne a gareni.....?"

Har lokacin bata d'ago ba bata kuma sami zarafin amsa masa ba... Shiru ya d'an gifta tsakaninsu

"Asma'u ki d'ago ki kalleni ki sanar dani meke damunki idan har kin amince ni masoyinki ne...."

Kalmansa na k'arshe ya kuma taso mata da wani sabon kukan, ta yaya zata soma sanar dashi halin da take ciki, ta yaya zata sanar dashi Lamid'o was right there.... Ta yaya zata sanar dashi har yanzu bata daina jin k'uncin abinda Lamid'o yayi mata ba, shin idan har yanzu zata zubda hawaye kan abinda Lamid'o yayi mata mai hakan yake nufi....? Zuciyarta ta cika da k'unci da waswasi.... A hankali ta d'ago tana mai share ragowar hawayen idanunta had'ida k'ak'aro murmushi saman labb'anta...

"Barka da zuwa Brother.... Ina kwana....?"

Bai amsata ba sai kafeta da kyawawan idanunsa da yayi wanda akoda yaushe suke haifar mata da fad'uwar gaba muddin ta hangi cikinsu....

Sauk'ar da nata idanun tayi sanda ta sinkayo muryar Junaid yana ci gaba da fad'in "Baki amsa min tambayata ba Asma'u..."

Wannan karan k'ok'arin fad'ad'a murmushin nata tayi kana tace "Babu komai fah Yaya na, please kar ka tada hankalinka har yanzu jikin ne bana jin dad'insa...."

Da ace tasan yanda k'aryar data masa yayi masa zafi har cikin k'ogon zuciyarsa tabbas da bata masa ba, ta yaya zatak'i sanar dashi Lamid'o ne silan kukanta bayan yaga ficewar Lamid'on kardai hasashensa ya tabbata Nana A bata cire Lamid'o cikin zuciyarta ba.... Lokaci guda fuskarsa tayi jazir haka nan idanunsa, hakan ne take kasancewa dashi idan ransa ya b'aci, zaka iya hango korayen jijiyoyin hannayensa yanda ya rik'e wheelchair d'insa dasu, wani irin zogi zuciyarsa ke masa sabida kasa sanar dashi tsakaninta da Lamid'o da tayi....

Cikin wata irin firgitacciyar murya yake fad'in "I know you Asmah... Koda ace bamu jima tare ba nasan abubuwa da dama gameda ke, sabida ina k'aunarki, na sani idan kina b'oye min wani abu, na sani idan wani abu na damunki.... Why Asma'u ,why can't you share it with me, sabida baki sona, sabida baki aminta dani ba har yanzu, idan baki sona meyasa kika barni niketa jigilan soyayyarki.. Tell me why...!!?" Ya k'arashe wani irin ruwa na fettuwa daga idanunsa

Kukanta sosai ya k'aru, lokaci guda take girgiza masa kai alamun a'a.... Cikin muryar kuka take fad'in "Ko d'aya ba haka bane.... Bansan mai zance maka ba bansan yaya zan soma sharing dakai ba...."
Chapter 77 · 0% Book details