← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 98

Sashe 28

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Siraj shi ya bada order d'in nasu lokaci guda Azeeza ta saita kanta don ta lura wannan matar cikakkiyar 'yar bariki ce kuma taji ta kirawo Siraj da Uncle kenan ba matarsa bace...

Gyara zama Azeeza tayi fuskarta cikeda murmushin girma kana tace "Allah sarki gashi kuma ni bana bin doka ko wacce iri ce idan ba ta Allah bace.... Ya kenan za'ayi...?"

Siraj ya kasa furta komai sai kallon mamaki da yake binta dashi... Nana H kanta mamakin Azeeza ya hanata daina kallonta... Shiko Nasaar ganin Azeeza na neman yin b'aranb'arama ya sanya sa mik'ewa babu shiri yanai ma Azeeza idanu kafin ya furta a d'an daburce....

"Em.... Em zamu wuce Sir, yara sun dawo daga school su kad'aine a gida.... Azeeza tashi mu k'arasa gida...." Ya k'arashe murmushin yak'e saman fuskar sa....

D'an far Azeeza tayi da idanunta kana tace "Kai brother da wuri haka...?" Tayi maganar cikin sigan shagwab'a wanda ya kuma tunzura Nana H, wannan wacce irin shegiyar yarinya Uncle ya samu matsayin sakatariya,....? Muryar Azeeza ya kuma dawo da Nana H daga duniyar tunanin da ta tafi..

"Toh Sir sai mun had'u a company... Enjoy your meal...." Ta k'arashe tana wani kashe masa idanu.... Ai bata ida fita daga cikin kujeran ba Nana H ta mik'e a fusace ta shak'o mayafin Azeeza tana fad'in "Shegiya karuwa wllhi Uncle Luv yafi k'arfinki kuma wllhi sai kin kampanin tunda bana ubanki bane....!"

"Hafsaaat! " Siraj ya kirawo sunanta cikin daka tsawa kana yaci gaba da fad'in "Lafiyanki k'alau, kanki guda zaki tara mana mutane.... Meye haka kike tunanin kinayi..?"

Nasaar hankali tashe ya shiga baiwa Siraj hak'uri yana fad'iwa Azeeza su bar wajen...

Nana H taci gaba da fad'in "Uncle wllhi karuwace bakaga fari da idanun da take maka ba, Uncle bakaga felek'en da take maka ba...."

"Ya isa pls....!" Siraj ya katse ta...

Shaye da mamaki take dubansa yanda yake daka mata tsawa kan wata banzar secretary...

Azeeza kuwa murmushin cin nasara tayi had'i da cire hannun Nana H daga jikin mayafinta kana ta d'an marairaice fuska tana duban Siraj tace "Sir kayi hak'uri dukda bansan matsayinta a wajenka ba, but what she just did was an insult... A distinguished person like you bai kamata a bada kai in public irin haka ba.... I'm sorry Sir, Allah ya huci zuciyarka..." Ta maido da dubanta ga Nana H tanai mata kallon naci uwaki a bariki, bata furta mata komai ba sai murmushin da ta sakar mata kana tasa kai ta fice daga restaurant d'in..

Yanayin abubuwan da Azeeza kewa Siraj har cikin ransa yakeji dukda yasan acting ne kawai ba gaskiya ba tinda shi da gaske soyayyar Azeeza Yake... D'an gyaran murya yayi had'ida baiwa Siraj hak'uri kafin yabi bayan Azeeza cikin sauri....

Nana H baki sake tabi bayan Azeeza da kallo... Lallai wannan shegiyar yarinyar zataci uwarta ta gyara mata zama... Bata san wacece H ba, batasanta ba, tabbas da batayi gigin shiga gonarta ba... Kambala'i wai ita wannan kucakar zata nunawa bariki, wannan yarinyar a shekare ai bazata wuce sha tara ba, har ita H kaman wannan yarinyar zata taka ta zata shige.... Tayi wata silent murmushi kana taci gaba da zancen zucin nata. .. Zan koya maki hankali yarinya, aiki a Laushi Group ya zama min dole, dole na karb'i gurbin aikin da nak'i karb'a a baya ko don na saita wannan k'aramar 'yar iskar yarinyar... Barin Uncle da irin wad'annan karuwan had'ari ne.... Maido da dubanta ga Siraj tayi wanda ya had'e hannayen sa biyu alamun tun fitar su Azeeza tunani yake.. Ita gaba d'aya ta lura dashi tunda suka shigo wannan gidan cin abinci yanayin Siraj ya canza, gaba d'aya ji tayi tama k'oshi da abincin...

"Uncle....!" Shiru bai amsata ba, alamun yayi nisa duniyar tunani..

"Uncle Love...!" Ta k'ara fad'i da d'an k'arfi wannan karon...

"What Azeeza...!!" Ya fad'i a d'an harzuk'e...

Da gaske kiranta yayi da Azeeza.... Lokaci guda bak'in ciki ya kuma turnuk'eta.... A fusace ta suri handbag ta nufi k'ofa.. Waiter na tafe da tray yana fad'in "Miss here is your order....."

Cikeda masifa ta dubi waiter d'in kana tace "You know everything here is disgusting... I lost my appetite, excuse me..."

Siraj ya shafi kansa wasu irin tunani suna yawo a kwanyarsa, baiso ya sakawa ransa haka d'in ne... Cikin sauri ya mik'e yabi bayanta yana mai kiran sunanta....

***

Tak'aitaccen dariya yayi idanunsa naga kwalta yake fad'in "Kai a gaskiya kinyi k'ok'ari ban zaci zaki iya abinda kikayi ba...."

Murmushin itama tayi kana tace "Hmm wllhi Barr kar kaji bugun da k'irjina keyi, gaba d'aya tunani nake Siraj zai iya firing d'ina sai gashi ya kasa katab'us, domin daga fari na zaci matarsa ce...."

Nasaar ya d'an kuma murmusawa kana yace "D'aya daga cikin 'ya'yan marigayi Yaya ga Siraj ne, Siraj yanaji da ita sosai fiye da d'ayar niece d'in tasa...."

Shiru Azeeza tayi tana nazarin maganganun.... lokaci guda take mamakin yanda Nana H ke kishin kawun nata, abin ya zarce misali. Abin tamkar a shirin film....

Suna isowa gida, Nasaar ya d'an juyo yana dubanta had'i da kashe murya....

"Zeeza ya maganar tamu.....?" Ya k'arashe yana narkar mata da idanu.....

Lokaci guda k'irjin Azeeza ya kuma bugawa... D'an sadda kanta k'asa tayi murmushi saman fuskarta...

Ganin haka ya sanya zuciyar Nasaar yin sanyi ga dukkan alamu Azeeza ta fad'awa soyayyarsa.... Murmushi ya sakar mata kana yace "Kar ki damu I'll give you enough time to think....."

Still idanunta a k'asa ba tareda ta iya furta koda kalma ba. Isowar Taheera wajen tanai masu oyoyo ya katse shirun nasu.... Tuni Azeeza ta fice had'i da rungumar Taheera... Nasaar ya bisu da kallo zuciyarsa nai masa wani irin sanyi....

***

*Misau*

Misalin k'arfe 8:00pm ya fito rik'eda jakar kayansa don ya tabbata Baffah bai shigo gida ba yana masallaci sannan saida ya tabbata Innah ma ta soma sallah sannan ya fito....

Kallo yabi gidan dashi yana zancen zuci... Tabbas yaso zama wannan karan ya nemi albarkan iyayensa saidai bazai iya ba.... Bazai iya zama bayan aure su tilasta masa tarewa da wannan yarinyar ba.... A hankali ya furta "I'm Sorry Innah.... I'm sorry....." Lokaci guda yasa kai zai fice sai ji yayi an rik'o jakansa.... Shaye da mamaki ya juyo yana dubanta...

Hawaye kwance saman idanunta sukayi ido hud'u.... Girgiza masa kai ta shiga yi tana mai ci gaba da hawaye take fad'in

"Dan Allah kar ka tafi.... Kada ka kuma tafiya ka bar Innah... Wllhi idan ka tafi zata kuma komawa cikin damuwa da k'unci.... Ince sabida ni zaka bar gidan? Toh na maka alk'awari zan tafi, zan koma ga Iya Gaje koda zata ke yankan naman jikina ne.... Idan dai hakan zaisa ka zauna, idan hakan zaisa farin cikin Innah ya dawwama..... Innah da Baffah mutanen kirki ne dan Allah kada ka tafi ka k'yalesu kaji... Kaine farin cikin su....." Ta k'arashe murya na tsananin rawa...

Tunda ta soma magana yake duban fuskar ta, badon muryarta da yaji ba sai yace ba ita bace sabida tunda yazo gidan bai tab'a ganinta babu kwalliyan aljanai ba sai yanzu, kenan wanke kwalliyan tayi, asalin kalan fuskarta sai ya fito da kyaun tsari babu zanen gira dasu hodar nan da take shafawa.... Muryar Baffah ya katse shirun nasu...

"Khadijatu sakar masa jakarsa yayi tafiyar sa, idan sabida auren Deejoh zaka tafi... Ka tafi Aliyu dama ba yau bane fari... Kada ma ka fake da auren Deejoh... Fice min a gida....."

Dai-dai lokacin Innah ta fito casbaha a hannu tana hawaye take fad'in "Malam dan Allah kada kace haka kada kace yayi tafiyarsa, dan Allah Malam..."

Katseta Baffah yayi ta hanyar d'aga hannu kana yace "Ki k'yalesa ya tafi dama bamu muka gayyatosa ba shi ya kawo kansa... Kuma wllhi wllhi kaji na maka rantsuwan musulmi aurenka da Deejoh babu fashi tinda ba kai ka biya sadakin ba....."

Daga haka Baffah yasa kai ya shige d'akinsa....

Cikin sauri Ahidjo ya take masa baya, nan ya tarar Baffah na k'ok'arin zama ya cire hulansa... Durk'usawa yayi saman gwiwoyinsa daga can gefe, shiru ya gifta tsakani kaman babu mai cewa komai...

A hankali Ahidjo ya soma fad'in "Amma Baffah da an nemi shawarina kafin a aura min yarinyar nan.... Baffah gaskiya...."

Tsawan da Baffah ya buga masa ya hanasa ci gaba da magana...

Cikin tsananin fushi yaci gaba da fad'in "Har ni kake cewa ba'a nemi shawarinka ba... Kai wanene... Waye kai da sai an jira shawarinka... Sanda zakayi auren barikin naka shawarin wa ka nema... Sabida bakada mutunci zaka dubi tsaban idanuna kace a nemi shawarinka.... Toh ank'i a nemi shawarin naka sai ka d'auko bindiga ka harbeni tinda ban nemi shawarinka ba..... Kuma barin fad'a maka idan ka fice ka tafi ka nemi wani uban bani ba kaji na fad'a maka....." Daga haka uwar d'aki ya shige ya bar Aheedjo durk'ushe a wajen abin duniya ya damesa.....

***

*Tmbuwal*

Duban Mairo ta kumayi a karo na biyu tana mai ci gaba da tura kaya cikin jaka..... Ganin Mairo batada niyyan tashi balle ta had'a kaya ya sanya Daddah daina abinda take ta isa ga Mairo... Hannayen Mairo ta kamo tana mai duban fuskar ta.... Murya a hankali tamkar ba Daddah ba ta soma fad'in

"Mairo kiyi hak'uri wata rana komai zai zama labari, nasani a matsayina na mahaifiyarki ban kyauta maki ba, ban barki kin nemi ilimin zamani yanda kikaci buri ba, sannan ban barki kin zab'i abokin rayuwarki ba iya shekarunki.... Mairo ki sani Daddah na yin duka wad'annan abubuwa ne sabida tseratar dake da kuma mutuncin ki.... Mairo wllhi nafi k'aunarki fiye da kaina, na tabbata wata rana koda bani raye zaki fad'i hakan.... Maza tashi ki kintsa domin ficewar dare nake so muyi banso ma mutan unguwa suga fitarmu...".

Kallon mamaki kurum Mairo ke bin Daddah dashi, kafin kaga hawaye a idanun Mairo sai waje ta b'aci yau saiga k'walla suna zarya idanun Mairo....
Chapter 28 · 0% Book details