← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 98

Sashe 4

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk abinda Junaid keyi akan idon yarannan ne... Sosai Junaid ya basu tausayi musamman da sukaga halin da yake ciki a haka har mahaifinsu ya k'araso ya taddasu, nan suke nuna masa abinda suke kalla, d'an babban cikin yace "Daddy yunwa yakeji."

Mutumin da ya ambata da Daddy shiru yayi tamkar mai nazari basu ankara ba sai gani sukayi babu Daddyn su a wajen, suka ci gaba da kallon Junaid yanda ya komawa Azeeza babu abinci sai faman kuka take masa yana lallashi....

Yaran har suna rige-rige wajen d'aukan sauran abincinsu suka kaiwa Azeeza, ta macen wacce bazatafi shekara biyar ba harda gogewa Azeeza hawaye tana fad'in "Aunty ki daina kuka you can eat our food kinji, tunda Momy ta tafi ta barmu Daddy ya hanamu kuka yace mai kuka tears d'insa zai k'are...."

Daga Azeeza har Junaid cikeda mamaki suke duban yarinyar, d'ago kai da zasuyi suka Kalli mutum tsaye akansu hannunsa rik'eda farin takarda wanda yake a nad'e basai ance maka snacks bane ciki... Jikin mutumin yayi sanyi sosai jin abinda 'yar tasa take fad'i

Shiko namijin mai kimanin shekaru 6 kallon mahaifinsa yayi yaga yanda yayi sakare yana duban k'anwarsa sannan ya dubi su Junaid da Azeeza yaga yanda suma suke kallon mahaifinsa da k'anwarsa cikin wani irin yanayi...

Cikin sauri yaron ya k'arasa ya shiga janyo k'anwarsa daga jikin Azeeza yana fad'in "Taheera what do you think you're doing, unhand her... Didn't Dad warn us about strangers?.."

Cikeda damuwa yarinyar tace "But Hammad look she's crying and hungry... I only want to help..."

Cikin sauri mahaifin nasu ya durk'usa had'i da dafa kan yaran kana yace "Hey kids go back to your seat now okay...."

Babu musu yaran suka jinjina kai , Taheera ganin abinci hannun mahaifinta harda d'anyin tsallen murna kana ta juyo da dubanta ga Azeeza tace "Aunty Daddy bought some.... Ki daina kuka kinji....."

Azeeza da murmushi ya cika fuskarta don sosai yarinyar ta burgeta batasan sanda ta shiga jinjina mata kai ba tana share hawayenta...

Bayan su Taheera sun koma wajen zamansu sai kuma aka shiga kallon-kallo takanin mutumin dasu Junaid.....

Saurin saita kansa mutumin yayi kana ya mik'awa Junaid hannu donyin musabaha....

Junaid bai mik'a masa hannu ba sai kallon da ya bisa dashi...

K'ak'aro murmushi mutumin yayi yana d'an satan kallon gefen da Azeeza take kana yace "Am.... am.... Kuyi hak'uri da surutun Taheera, haka yarinyar take da son taimako,...." Ya maido da dubansa ga Azeeza wacce ta kafesa da idanu uwa ta sami TV... Gaba ya d'aya ya tsargu da kallon da take masa, cikin sauri ya ajiye abinda ke hannunsa a gefenta kana yace "If you don't mind miss...."

"Bazataci ba..."

Kalaman da ya jiyo kenan tana fitowa daga bakin Junaid....

Mutumin ya bisa da kallo cikeda mamaki...

Azeeza da tuni har tasa hannu zata d'auka Junaid ya finciko takardan yayi wurgi da ita...

Cikeda mamaki mutumin ke kallon Junaid sai sannan ya tuna yayi shisshigi ta yuwu wannan yarinya matan gurgun nan ne dole abin ya zafesa idan yayi mata kyauta...

Saida ya daidaita tsayuwansa had'i da gyaran murya kafin yace "Kayi hak'uri bawan Allah taimako nayi niyyan yi kaman yanda naga yarana sun buk'aci hakan, sannan ni ba mugu bane bazan cutar daku ba kuma ni d'an uwanku musulmi ne....."

"Malam naci bazataci ba... Bamu sanka ba bamusan daga ina kake ba kawai ka baiwa 'yar uwata abinci.. A ina ka tab'ajin anyi haka...?"

Saida ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya jin Azeeza ba matar Junaid bace kafin ya d'an murmusa yace "Toh ni sunana Barrister Nasaar Gumau, kuma ni d'an asalin garin Gumau ne dake jihar Bauchi sannan mazauni garin Abuja.... wad'ancan yarana ne Hammad and Taheera, yanzu haka mun fito garin Maiduguri ne domin duba dangin mahaifiyarsu..... Kuyi hak'uri nayi abinda baku umarceni ba, a yanayin aikina kullum ina zama ne cikin shirin had'uwa da sabbin mutane...."

Tunda ya soma magana suke dubansa cikeda mamakin yanda ya zak'e sai basu labari yake uwa wanda suka tambaya....

A dai-dai lokacin jirgi ta iso ba tareda sun sami zarafin amsa masa maganganun tasa ba, iyakaci abinda suka fahimta shine gari d'aya suka nufa....

Junaid bai kuma cewa komai ba sai tura wheelchair d'insa da ya shigayi had'i da tura jakan kayansu...

Azeeza kuwa tuni ta d'au snacks d'inta ta soma ci tana alamu wa Barr Nasaar da hannu alamun godiya....

Kallonta ya dingayi yana murmushi har yaransa suka k'araso suka rik'e hannayensa, cikin sauri ya isa yanda luggage d'insu yake shima ya shiga janyowa suka nufi jirgin.....

***

*Misau*

A k'ofar makarantar allonsu ta hangi Lado ya kasa ya tsare hasken farin wata tal ya haske mata d'an duk'uninin fuskarsa.....

Jikinta ya d'auki kyarma don duk yanda taga Lado haka takeji, Lado ya zame mata kaman dodo a garin...

Sunkuyar da kanta tayi had'i da damk'e allonta sosai ta soma tafiya tamkar wacce zata auka k'asa....

Tana isowa yanda suke shida abokansa bugun k'irjinta ya k'aru ga uwar warin kayan maye da ya gauraye wajen, musamman suka maida wajen dabansu sabida hanyar wucewar Deejo ne....

Aiko kaman jira suke ta k'araso suka mik'e suka nufota, bata ankaraba duk saurin da take sai ganin Lado tayi tsaye k'ik'am a gabanta yana hura hayak'in sigari...

K'iris ya rage Deejo bata saki fitsari a wando ba sabida tsoro, ta yunk'ura zata sa gudu tayi d'aya hanyar sai ganin Tanimu tayi a wannan gefen, d'aya gefen ma Muntala ya tsare.....

Deejo ta soma kuka tana k'ok'arin duk'awa take fad'in "Dan Allah kuji k'aina kumin rai wllhi makarantar Allo na nufa...."

Bud'an bakin Muntala sai cewa yayi "Allah yasa tawada kika nufa gaba d'aya, banza kucaka ke kin tab'a ganin Lado ya kira budurwa d'akinsa a garin nan tak'i zuwa... Ke wacece??"

"Kaima ka tsaya kake tambayanta wllhi tunda nayi niyya ko babu kaji sai na d'ana shegiya ku nad'o min ita....."

Lado ya fad'i cikeda umarni wa sauran abokan nasa...

Deejo ko dukda k'arancin shekarunta ta fahimci cutar da ita suke sonyi, tana ganin Muntala ya kai mata sura ta saita allonta ta sauk'e masa a gefen kunnensa saida yaji jinsa ya d'auke ya saki k'aran azaba.... Bata jira ba tasa gudu, zaninta sai filfilawa kake, 'yan k'afafun kawai kake hangowa....

Lado da Tanimu suka bi bayanta a guje, abinka da wad'anda suke buge sai gani suke tana zille masu, idan wannan yakai mata wawusa sai ta zille ta k'asan k'afarsa har saida ta had'asu gware, ta dumbuzi k'asa ta watsa masu aiko nan suka soma ihu suna lalumen hanya....

Ai Deejo tunda ta samu hanya take gudu bata zarce ko ina ba sai gidan Innah Balki...

Innah da Malam na zaune tsakar gida suna sauraren radio abokin hiransu zab'en dare kawai sai ji sukayi an banko k'ofa an shigo... Ai a tamanin suka mik'e suna salati, k'afafuwan Deejo kawai suka hango ta d'age labulen Innah Bilki tana fad'in "Baffah a kule k'yauren zasu shigo...."

"Ke Deejo lafiyarki? Su waye zasu shigon....." Innah ta tambaya cikeda tashin hankali, Baffah kuwa cikin sauri ya fice ya nufi wajen gidan ganin su waye suka biyo Deejo amma wayam baiga kowa ba....

***

Wajajen 12am suka iso Abuja, kowa sai watsewa ake amma su Junaid basu san yanda suka nufa ba, Allah yasa Barr da yaransa basu tafi ba don dama Azeeza da yaran sosai suka sha hiransu cikin jirgin, Taheera kam ma jikin Azeeza tayi bacci...

Barr baiji d'ar d'in tambayansu unguwar da suka nufa ba, ganin Junaid bai basa k'wakk'waran amsa ba yasa ya nemi alfarman da su wuce gidansa gaba d'aya, da farko Junaid k'in amimcewa yayi saida Azeeza tayita masa magiya don lokaci guda soyayyan Taheera ya shiga zuciyarta...

Ba don Junaid yaso ba suka d'unguma gaba d'aya suka nufi gidan Barrister Nasaar

****

Belt d'insa ya ida d'aurawa had'i da karkata hularsa ta 'yansanda ya zauna cif akansa kafin ya feshe jikinsa da turaruka masu k'amshi...

Sai faman binsa da kallo take daga yanda take zaune saman gadon k'afafu d'aya bisa d'aya har lokacin cikin kayan baccinta take....

"Sweet kayi kyau....."

Ta fad'i tana juya idanu....

Gajeren murmushi yayi kafin ya k'araso ya manna mata peck gefen kumatunta yace "I'm off to work.... Idan bak'uwar taki tazo ki gaisheta...."

Ta kuma murmusawa tanai masa wasu salo da yasan k'arshe sai yayi lattin fita, cikin dabara ya zame ya fice ko breakfast baiyi ba, idan da sabo fita babu breakfast yabi jikinsa....

Yana ficewa ta koma gado tayi kwanciyarta... Kwanciyarta da kaman minti ashirin taji doorbell na k'ara.....

Saurin mik'ewa tayi tana mamakin har Nadiya ta iso....

Abinka da jik'ekk'iyar 'yar bariki d'an mayanin rigar baccin nata kawai ta yafa ta nufi k'ofan....

Da murmushinta ta hangame k'ofar tana fad'in "Thanks for accepting my invitation in such a short ti....."

Had'iye maganar nata tayi ganin wanda ke tsaye gabanta.....

Tun daga sama har k'asa yake faman binta da kallo shu'umar murmushi kwance saman fuskar sa....

Tsaki tayi had'i da juyawa cikin gidan tana fad'in "So tell me, what the hell brought you here.... Bance maka ina expecting bak'uwa ba...."

"Come on darling, no even good morning kisses sai masifa....."

Ya k'arashe yana rik'ota lokaci guda ta fad'o cikin jikinsa....

K'ok'arin turesa take duk yanda yake sumbatan ta tana fad'in "Lamid'o stop all this, and kindly get yourself outta here.... You can't be seen here.... Dan Allah ka tafi kafin Nadiya tazo...."

"Oh really darling, korata kike... So tell me mai kike shiryawa akan Nadiya....?"

Ya k'arashe yana k'ek'ashe idanu....

Shu'umin murmushi tayi had'i da dafa bayan kujera kana ta soma fad'in "I'll win her trust and then.... Move to the next step, besides no need to rush things...."

Murmushi Lamid'o yayi had'i da shafa sumarsa data sha low-cut kana yace "I trust you darling... So tell me, do you need my help....?"

Murmushi ta kumayi kana tace "Not really..... Ka gane kawai ka tafi we talk later...."

"Haka zan tafi babu komai...."

"Ka tafi before I hate you....."

Ware hannayensa yayi alamun surrender kana yace "Alright fine, zan tafi.... If you need anything just call or text OK...."

Gira kawai ta d'aga masa had'i da binsa da kallo har ya isa k'ofa.... Saida yakai dai-dai k'ofa kafin ya juyo had'i da huro mata kiss saman hannunsa sannan ya fice...
Chapter 4 · 0% Book details