← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 98

Sashe 14

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shafa bayan wuyarsa yayi cikeda damuwa kana yace "I.... I... I'm sorry sir, wllhi ya cire documents d'in....."

Baikai aya ba mutumin ya katsesa da fad'in "Shut up you fool... Kar ka sake min magana har sai ka sami ci gaba a aikin da na saka ka...." Daga haka katse wayar yayi yana tsaki.....

Lamid'o ya shafi naman goshinsa kafin ya shige motar yana tsaki ya bar wajen cikin sauri.....

****

*Tambuwal*

Mamaki ne ya cika Dadda jin wai shugaban Hizba ne ke sallama, Dadda ta yafa mayafi ta fice domin jin da mai yazo tunda dai tasan sun rabu lafia.....

Tana fitowa ta hangesu su biyu yau bada uniform suka zo ba shiga ta manyan kaya sukayi jampa harda hula.... Aiko suna ganinta suka k'araso cikin sauri oga sai faman sunne kai yake...

A cikin ranta tace "Wannan wage baki da yake uwa gonar auduga tasan bana lafiya gashi sai sinne kai yake uwa k'adangare... Kad'a kai kurum tayi tana jiran k'arasowarsu taji da abinda suka zo domin tana dai-dai dasu...

Ga mamakinta suna k'arasowa suka zube a k'asa suna gaisheta ai itama sai ta zube masu a k'asa ta shiga mad'e tana janyo mayafi tana gaishesu tana kwarkwasa...

A'a Oga Ayuba ya kalli abokinsa Malam Habu cikeda mamaki ganin abinda Dadda ke masu suda sukazo domin neman auren d'iyarta.....

Dadda ta mik'e tana mai ci gaba da mad'e take fad'in "Allah sarki aima baku sanar dani kuna tafe ba shiyasa tun wancan lokacin naso ka amshi lambata ko ni na amshi naka... Allah sarki ashe dai kuna tafe...."

Bakin oga Ayuba na rawa yake fad'in "A... A.. Ai Hajiya dama zamu....."

Saurin katsesa tayi da fad'in "Kar ka damu ka kirani Hindu... Eh Hindu sunan kenan... Kar ka dami kanka kirani da sunan yanka kurum....." Ta k'arashe tana wasa da yatsun hannunta sai ka rantse budurwace gaban saurayi....

Tun Malam Habu na mamaki har abin ya soma basa takaici ganin abinda wannan dattijuwan matar ke masu, wai dama wannan ce matar da abokin nasa yace ya samu.... Takaici ya ishesa jin Dadda tana fad'in bari ta kawo masu tabarma da ruwan sha....

Ai hiran da ba'a k'arasaba kenan suka ce mata zasu tafi aima basai sunsha ruwa ba a k'oshe suke.... K'afafuwan Oga Ayuba har na hard'ewa ya nufi mota Malam Habu na take masa baya....

Dadda bata bar k'ofar gidan ba bata daina masu mad'e tana d'aga masu hannu ba har saida taga wulk'awar motarsu....

Suna wucewa tayi k'wafa kana tace "'Yan cin k'aniya ni dama nasan sai ka biyo d'iyata... Toh baza'a bayar d'inba ka wani turo hula gaba uwa masinjan k'auye, yo mai Mairo zatayi da kai... Ai Mairo saifa na darje wannan koni nan nafi k'arfinka balle Mairona farin wata sha kallo hasken rana haske duniya Dustin Arfa a ganki a barki..... Gobe ku sake dawowa ni ce dai zan fito maku....." Tana ida fad'in haka ta maida k'ofar ta kulle....

Yanda ta hangi Mairo na kwance tana bacci ta k'arasa gareta ta zauna daga gefe had'ida k'urawa Mairo idanu tana tuna tun farkon had'uwarsu soyayyar yarinyar ya shiga ranta... Tana son Mairo fiye da komai na rayuwarta... Bata san soyayyar kowa ba sai na Mairo, bata jin rana tsaka akwai abinda zai iya rabata da Mairo... Zatayi komai domin kare Maironta..... Ta saki murmushi tana mai gyara mata kwanciyarta.....

****

*_Safiyar ranar Alhamis_ Abuja*

A yanda ta shigo gidan a birkice zaisa ka gane ba lafiya take ba... K'ok'arin saita kanta tayi kana ta gyara zaman mayafinta dake bisa kafad'arta ta soma takunta cikin k'walisa kaman yanda ta saba...

Hayaniyar 'yan gidan taji daga parlorn dake gefe can alamun kowa na shirin tafiya babban taron da sukedashi a family d'in.. Yau rana ce da za'a bud'e Cibiyar taimaka wa nakasassu wanda Nana Asma'u ta jajirce wajen ganin wannan abu ya tabbata, tun tana k'arama batada burin da ya wuce taga ta taimaki 'yan uwanta masu fama da lalura ta nakasa ko wace iri ce....

Nana H ta yatsina fuska ganin yanda kowa ke farin ciki a gidan, ganin bata hango Nana A a wajen ba ya tabbatar mata cewa tana d'akinta tana shiryawa... Murmushi ta saki kafin ta nufi upstairs....

Aiko tana bud'e k'ofar ta hangeta zaune gaban dressing mirror tana shafa mai....

Asma'u ta sakarwa 'yar uwarta murmushi lokaci guda Nana H ta maida mata da martanin murmushin kana tace "May I....?"

Cikeda jin dad'i Asma'u ta shiga jinjina mata kai tana fad'in "Please come in sis...."

Nana H ta k'arasa shigowa had'i da maida k'ofar d'akin ta rufe... Saman bakin gado ta samu ta zauna tana mai duban 'yar uwar tata... Nana H na karantar 'yar uwar tata take tambayarta "Sis, have you picked out your clothes for the event...?"

D'an dubanta Nana A tayi kana ta girgiza kai tace "Wllhi I haven't sis... I'm so nervous, I know there will be alot of people.... Kinsan ban saba shiga mutane da yawa ba...."

"Ya Allah Nana A what have you been doing...? Tsoron mutane ko, kar ki damu everything will fine... Trust me OK...."

Murmushi Nana A tayi kana tace "Tunda kinzo sai ki zab'a min...."

Nana H ta shiga jan kumatun Nana A tana fad'in "Goodness, what kind of sister do I have, batasan ta zab'i kaya to her own taste ba..?"

Nana A na murmishi cikeda jin dad'i take fad'in "Best in the world I guess...."

Murmushi Nana H d'inma tayi kana ta mik'e ta isa closet d'in 'yar uwar tata ta shiga zab'a mata kaya masu jida kyau... Harta covers d'in da Nana A ke sakawa sabida ruf'e k'afafunta yau Nana H ce ta zab'a mata.... Abinda zai baka mamaki yau har kwalliya Nana H tayiwa 'yar uwarta wacce sam kwalliya bai gabanta.... Ammah da shigowarta d'akin kenan don ganin ko Nana A ta shirya sai gani tayi Hafsat yau ita kewa Asma'u kwalliya sai raha da farin ciki suke, abunda suka jima basu gani ba a gidan....

Ammah da tuni farin ciki ya mamayeta batasan sanda k'walla suka ciko idanunta ba, kullum burinsu da fatansu kenan 'yan uwan su so junansu... A hankali ta silale ta bar d'akin don bataso tayi distracting nasu....

Tas Nana H ta shirya 'yar uwarta ta kuwa yi kyau sosai tayi kama da 'yar uwarta babu abinda ya rabasu don irin kwalliyar dake fuskarta Nana H tayi mata...

Nana Asma'u ta Kalli fuskarta a madubi cikeda mamaki tana shafawa take fad'in "Nana H I look different... Wannan kwalliyar tai yawa, please a rage...."

Nan da nan Nana Hafsat tayi kicin-kicin da fuska tace "Au bakison kiyi kama irin tawa sabida banida hali mai kyau koh... Idan bakison duk wani abinda zan maki fine, inma bakison ganina a taron naki ne fine.. Sai nayi tafiyata....." Ta k'arashe tana k'ok'arin barin d'akin...

Saurin rik'ota Asma'u tayi kana ta shiga girgiza kai tana fad'in "I love it sis... Kiyi hak'uri kinji.... And I look beautiful just like you.... I'm sorry kinji Sis."

Murmushi Nana Hafsat tayi kana tayi hugging 'yar uwar tata tana fad'in "Is OK... Kar kiyi kuka ki b'ata gayunki don nasan kad'an da aikin ki...." A tare suka murmusa kafin suka jera da taimakon Nana H suke sauk'owa daga matakalan benen...

Gaba d'aya suka mimmik'e suna hangosu yanda suke sauk'owa kamanninsu ya fito sosai yau.... Babu kaman Lamid'o wanda ya kasa d'auke idanunsa daga duban Asma'u, bai tab'a zaton tanada sihirtaccen kyau irin na yau ba, shi dama suka jera itada Hafsat d'in sai yake ganin tafi Hafsat kyau... Wani abu yake ji na tsargansa gameda Asma'u....

A b'angaren Ayiya kuwa tab'e baki kurum tayi zuciyarta na raya mata akwai abinda Nana Hafsat ke shiryawa tasan haka kurum bazatayi wannan kirki ba , amma koma menene tana biye da 'yar Albarka duk yanda ta sanya k'afafunta...

Siraj kam sosai yaji dad'in abinda Nana H tayi, shi dama kullum burinsa yaran su had'e kansu, abin ya birgesa sosai, har yake ji zai tsaya a gama event d'in gaba d'aya dashi dukda tulin aiki dake gabansa....

Gaba d'aya suka d'unguma suka nufi sabon cibiyar taimakawa masu nakasan, lallai Asma'u 'yar dangice kuma suna k'aunarta....

***

Kai ya d'aga yana kallon foundation d'in wanda yasha kwalliya ga guragu da dama da dai sauran masu naksa sai tururwan shiga suke ba'a hana masu nakasa shiga bakaman mai lafiya ba da sai anga invitation card d'inka...

Junaid ya janyo hular sanyinsa ya rufa a kansa cikin zuciyarsa yake furta _it is now or never_ Lokaci guda shima ya kutsa cikin masu nakasan ya shige....

*SameenaAleeyou📚*
[12/19, 12:07 AM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮

*11*

*©Sameena Aleeyou... ✍🏽*

Tunda taga Lamid'o na rawan jiki akan Nana A taji dama bata mata makeup d'in ba, abinda ya dad'a bata haushi yanda aketa zuzuta kyaun da Nana A tayi.... Koda shike babu yanda za'ayi a had'a nakshasshe da mai lafiya... Lokaci guda ta Saki murmushi sanda ta tuna hakan....

Suna isa fili ya kuma kacamewa musakai bayin Allah kowa k'ok'arinsa yaga wannan gwarzuwar macen da Allah ya mata zuciya mai kyau, mai k'aunar taga farin ciki a fuskar musakai, mai burin ta datse yawan barace-barace da musakai keyi, mai fatan taga ko wani musaki Allah ya azirtasa da sana'a domin dogaro da kai.....

Duk wani kacaniya da ake Nana A ta kasa fitowa daga mota banda bugu babu abinda k'irjinta keyi tun wayewar garin yau....

Ayiya na k'ok'arin bud'e k'ofa Nana A ta kamo hannunta ta dunk'ule sosai cikin nata idanunta sunyi rau-rau...

Murmushi Ayiya ta sakar mata kana tace "Muje 'yar Albarka yau burinki ne Allah ya cika maki shi...."

K'ak'aro murmushi tayi tana duban Ayiya kana ya soma magana cikin tsananin sanyin muryarta....

"Ayiya bansan meke shirin faruwa dani ba, bansan meyasa k'irjina ke tsananin bugu ba, bansan mai zaije yazo a taron nan ba.... Burina kenan tsawon rayuwata sai gashi yau da Allah ya cika min wannan buri nawa inajin kaman wani abu zai faru dani kaman....." Ayiya ce tayi saurin katseta ta hanyar rufe mata baki da hannunta guda tana mai girgiza mata kai alamun ta daina fad'in haka, lokaci guda take fad'in
Chapter 14 · 0% Book details