Sashe 81
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K'aran high hill d'in dake k'afafunta ya sanya Ayiya fitowa daga kitchen tana kallon ikon Allah, baki sake take duban Nana H, da k'yar ta iya saita kanta kafin ta shiga tafe hannaye tana sallami had'ida mamakin wannan irin rayuwa
"Toh ke kuma ina kika nufa haka baiwar Allah...?"
Wani irin wulak'antaccen kallo Nana H ta watsa mata kafin ta tab'e baki taci gaba da tafiyarta....
Ayiya bata kuma furta komai ba sai addu'a da fatan shiriya da tayiwa Nana H cikin zuciyarta...
Daga bayansu suka jiyo muryar Ammah tana fad'in "A'ah Sweetheart sai ina da safen nan...?"
Nana H da tuni takai k'ofa juyowa tayi fuska babu walwala kana tace "Ammah I've an appointment with my Dr da safen nan, ko asibitin ma za'a hanani zuwa ne a tak'ureni a gida bayan nayi k'ok'ari nayi kwanaki sama da arba'in a hakan..."
Saurin girgiza mata kai Ammah tayi kana tace "A'a babu wanda zai hanaki ganin likita besides iddah kike ba takaba...."
Murmusawa Nana H tayi kafin ta d'an k'araso ta baiwa Ammah light hug.... "Thank you Ammah na, sai na dawo...."
Ammah na murmushi take furta "A dawo lafiya 'yar lele na... Allah shi baki lafiya...."
Ameen ta amsa dashi kafin ta yab'awa Ayiya wani irin wulak'antaccen kallo kana ta fice...
Ayiya ta dubi Ammah da tsananin mamaki kana tace "Mairo gaskiya da alama har yanzu baki canza d'abi'arki ta son rayuwa irinta yahudu ba...."
Yanda Ayiya tayi maganar saida ya haifarwa Ammah da fad'uwar gaba, rabon Ayiya ta kirawota da sunanta Mairo tun shekarun baya, wasu lokuta masu tsawo....
Cikin sauri Ammah ta janyo hannun Ayiya suka biya wata k'ofar k'irjinta naci gaba da bugu....
"Ayshatu kar ki mance alk'awarinmu, kar ki mance munyi alk'awarin bazamu tab'a bud'e sirrinmu ba, mai zai faru idan Nana Asma'u ko Nana Hafsta koma Siraj sukaji kin ambaceni da sunana abinda baki tab'a ba...."
K'uri Ayiya ta mata kana tace "Mairo kink'i amincewa ne amma ni a ganina da mun sanar dasu don na sani ko ba dad'e ko ba jima zasuji wata rana..."
I zuwa lokacin hawaye sun soma sauk'owa Ammah, cikin murya mai tsananin rawa take fad'in "Aishatu tsoro nake ji, ina tsoron rasa jikokina da kuma tilon d'ana da yayi saura... Bansan ta yanda zan fara ba....." Kuka yaci k'arfinta
Cikin sauri Ayiya ta rungumota itama hawayen na neman ciko idanunta, bata da kowa sai Mairo da iyalanta, ita kanta bazata so wannan ajiyayyen sirri ya bud'e ba, zata fi so ayita zama a haka don bazata tab'a so ta rasa Nana A ba, yarinyar da take so fiye da komai na rayuwarta, wacce take jinta tamkar nata tamkar ita ta haifeta..... Tabbas bud'uwar sirrin yana dai-dai ne da rasa Nana Asma'u a wajenta....
***
Tana fitowa ta nufi ma'ajiyar motar ta ma'aikatan gidan sai gaisar da ita suke suna mata barka da safiya, as usual ko kallon arziki basu isheta ba balle ta gaisar dasu, idan da sabo sun saba da wannan banzan d'abi'a na Nana H wannan dalili yasa suka fi son 'yar uwarta Nana A wacce ke ganin girma da darajan d'an Adam....
Motar ta na fitowa daga gidan Lamid'o ke k'ok'arin shigowa, dole ya koma da baya yayi parking gefen gidan yana jiran ficewarta
Murmushi ta saki masa kafin ta isa kusansa had'ida zuge gilashin motar ta...
"Good morning Handsome giant...!!" Ta fad'i tana mai masa fari da idanu
Sosai ta basa dariya amma ya gimtse a iya yawonsa na duniya bai tab'a cin karo da shed'aniya irin Nana H ba, kafeta yayi da idanu yana karantar ta, so yake ya fahimci wani abu gameda ita, meyasa sam mutuwar Heedj bai dameta, mai yasa bata k'aunar ayi maganar binciko 'yar uwarta Nana K, there must be something behind all this, he needs to find out, ya sani tun ba yau ba Nana H shed'aniya ce, amma idan yana so ya tabbatar da zarginsa dole yabi a sannu kaman yanda yake bin Bulama a sannu...
Lokaci guda Lamid'o ya sakar mata murmushi kana yace "Barka da safiya Mrs.... Aff sorry na mance ashe ke d'in widow ce, kodashike bakiyi kama da matar da mijinta ya rasu ba, kaman ma murna kike da mutuwar nasa maybe ya tare maki wani wajen yanzu kina shan iskan ki yanda ya kamata...." Ya k'arashe mayaudariyar murmushi saman fuskar sa...
Dukda kalaman Lamid'o sun mata zafi hakan bai hanata dannewa ba sabida cikan burinta kana ta kuma masa fari da idanu kafin ta soma fad'in "Tabbas wanda ya riga ya mutu toh fah ya mutu, amma Heedj miji ne da mancesa cikin zuciya da gangan jiki abu ne mai matuk'ar wuya, da ace Allah baya sakawa d'an Adam mantuwa tabbas da duniyar bata kawo haka ba, domin da zaran wani naka ya mutu tsananin tunani ka iya sawa kabi sahunsa...." Fasali ta d'anyi tana mai ci gaba da juya idanu makirin murmushi saman fuskarta sanda ta fito da kanta ta gilashin motar tana mai duban cikin idanun Lamid'o take ci gaba da fad'in "Na sani a rashi na ka d'aura idanu akanta yanzu da na zama single na tabbata zakafi kowa farin ciki, ina nan akan bakata.... Ko kana tunanin zan barka ka auri 'yar uwata na d'auke idanu kaman babu abinda ya tab'a faruwa.... Oh Darling hakan bazata tab'a kasancewa ba.... Bakada zab'i sai Nana H...." Ta k'arashe tana mai kashe masa idanu guda...
Banda tafarfasa babu abinda zuciyarsa keyi, Nana H ta gama dashi ta wannan fannin, tinda yaci amanar abokinsa yasan abun dole yayita bibiyarsa, ga Heedj baya nan balle ya nemi gafararsa ga tsananin soyayyar 'yar uwar abokiyar da sukayi tarayya wajen aikata sab'on Allah dake neman zautar dashi, Nana H bazata tab'a kaucewa daga hanyarsa ba har sai taga yanda ta rabasa da Nana A... Muryarta ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi...
"Ka shiga ka sameta tana ciki don na tabbata wajenta kazo, ta sanar dani duk abinda ya faru sannan na bata shawari irin wacce ta dace, kar ka damu da rashin Nana A kanada Nana H kyakkyawa mai cikan halitta burin ko wani namiji lafiyayye irinka, and just a piece of advice Sweetheart, make sure ka yanke alak'ar dake tsakaninku cikin gaggawa kafin na tunk'ari shirina na gaba..." Har ta soma yunk'urin jan motar da niyyan barin wajen ta kuma dakawata tana dubansa wani murmushin saman fuskarta
"It's obvious da biyu ka tura Heedj nemo Nana K don a kashesa kai kuma ka sami chance d'in kasancewa dani... Kar ka damu your little secret is safe with me, mun saba tonawa muna bisnewa dani dakai, so wannan karanma babu wanda zaiji Sweetheart...." Tana ida fad'in haka ta hura masa kiss a tafin hannunta kafin ta finciki motarta da k'arfin gaske ta barsa a wajen tana tintsirewa da dariya had'ida maka k'atoton gilashi saman fuskarta...
Dukda sanyin AC d'in motar tasa dake dukan fatarsa bai hana jikinsa tsartsafo da zufa ba, Nana H ta wuce duk wani tunaninsa, Allah kad'ai yasan jiya mai ta sanar da Nana A, fatansa dai Allah yasa bata sanar da ita laifukan da suka aikata a baya ba cikin sauri ya kuma yin horn ma securities suka bud'e masa gate d'in....
***
"Hello ina jinka, yes yes I'm on my way, what nonsense are you talking about Nasaar,.... Just cut it out, na fad'a maka gani nan zuwa kawai ka jirani...." Daga haka tsuka ta buga had'i da wurga wayar gefen seat d'in mai zaman banza tana faman huci take damk'e steering wheel d'in... Lokaci guda take furta "Imbecile...!!! Zaka sanar dani gidan uwar daka kai wancan tsinanniyar yarinyar mai zubin aljanai ba, banda asiri da tayiwa Uncle love harma mai zai hango jikinta, bak'in fatar ko me? Na tabbata wannan na fita komai da zai kwantar da hankalinsa babu abinda bazan masa ba..." Ta kuma yin tsuka ita kad'anta sanda traffic lights ke nuno mata jan wuta alamun an tsaidata...
***
A parlor Ayiya ta masa masauk'i yayinda Blessing ta masa tayin breakfast dake bisa table....
Girgiza mata kai yayi yana mai furta "No thanks Blessing I'm OK..."
Blessing ta jinjina kai cikeda risinawa kana ta furta "Alright Sir....!" had'ida barin wajen...
Kallo yabi bayan Blessing dashi zuciyarsa naci gaba da bugawa lokaci guda yake tuna sanda ya kawota gidan a matsayin mai aiki bisa umarnin mahaifinsa Alhaji Sani Bulama.... Muryar Ammah ce ta maido dashi daga duniyar tunanin da ya tafi...
"Ammah barka da safiya...." Ya fad'i sanda yake d'an zamowa daga cikin Settee d'in...
Da fari'a Ammah ke amsa masa shi kuwa gaba d'aya ba'a sake yake ba, ya k'osa yaga sauk'owar Asma'u, Allah sa dai ta fito yayi tozali da ita ko zaiji sanyi don gaba d'aya halin da jiya ya tafi ya barta ciki baiji dad'i ba....
"Nikam nace yaya labarin Nana Khadijatun, har yanzu shiru....?" Ammah ta bid'a bayan sun ida gaisawa da Lamid'on...
K'ok'arin saita kansa ya d'anyi kana ya soma fad'in "Eh toh Ammah, dama abinda ya kawoni kenan...." Jin haka ya sanya Ammah gyara zama had'ida fad'ad'a murmushinta....
"An sameta koh, matar ta amince ta negotiating.... Fad'a min nawa take buk'ata mu bata...." Ta k'arashe cikin tsananin nuna damuwa da tashin hankali...
Lamid'o yayi k'ok'arin k'ak'aro murmushi kana yace "A'a Ammah kar ki d'aga hankalinki komai zaizo da sauk'i insha Allah kaman yanda muka tsara...."
Ammah ta jinjina kai kana tace "Toh shikenan Lamid'o Allah ubangiji yasa hakan..."
Lamid'o ya amsa da Ameen kana ya k'arada "Ammah nace Siraj d'in yana gida kuwa, don naga babu motarsa kuma daga company nake bayya can sannan wayoyinsa gaba d'aya basa shiga...."
Lokaci guda Annurin dake fuskar Ammah ta d'auke...
"Yo wayasan masa yanda yajeshi, nidai kam ina numfashi bazan barsa ya auri yarinyar can ba, banda sakarci ana zancen nemo d'iyarsa yana can yana maganar wata watsettsiyar yarinya da bama k'aunarsa take ba, ni bansan uwar mai ta zuba masa yaci ba ya daburce gaba d'aya akanta... Kaga k'yale maganar Sirajo duk zancen da ake ciki kayita dani yaje can ya k'arata, burina Jikata ta dawo cikin danginta....."
Lamid'o yayi shiru yana nazarin maganganun Ammah