← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 98

Sashe 23

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daddah amma bakiga lokaci ba koh.. Dare yayi ki bari da safe idan Allah ya yarda zanje da kaina na maki alk'awari kafin ki farka bacci da Mairo zan shigo maki gida, amma yanzu dare yayi ina saurayi na shiga gidan matan aure... Ko yaya kika gani Daddarmu...."

K'uri ta masa kana ta jinjina kai tace shikenan Naziru tunda kace haka, Allah shi kaimu safiyar.... Gaskiya ne kaje gida ka huce gajjiya kaima...."

Nan sukayi sallama Daddah ta komo gida cikeda kewar Maironta.... Nazir kuwa gida ya wuce yana tunanin mai ya had'a Mairo da Daddah fad'a bayan tafiyarsa, Allah sa dai ba abinda yake tunani bane, tabbas idan abinda yake tunani ne aiki ya jik'e masa, gwara yasan abin yi tun wuri, da wannan tunani ya isa gida. .....

***

*Misau*

Daga bakin k'ofar mahaifin nasa ya durk'usa saman gwiwoyinsa yanayin zaman rak'umi, kansa a k'asa yaci gaba da fad'in "Baffah ka yafe min, kayi hak'uri kada kace na fice maka a gidanka wllhi banida yanda yafi nan na sani....."

Sai sannan Baffah ya d'ago idanu yana dubansa cikeda takaici da tsananin mamaki kana yace "Ni zaka rud'a ka yaudara da kalamai Ahidjo? Shin yaushe ka d'auki hakan cikin zuciyarka? Shin yaushe ka bamu wannan matsayin,? Shin sau nawa akayi haka amma kana komawa can barikin zaka kuma mancewa damu.... Shin a haka kake so kayi albarka....? Ahidjo maike damunka a rayuwa? Mai muka maka da tsanani da kake kunyar nunawa duniya cewa mune mahaifanka? Mai ka d'auki wannan rayuwar? Mai ka d'aukemu da sai lokacin daka bushi iskanka zaka waiwayomu shin a haka kake neman albarka Aliyu? Shin a haka kake fatan gamawa da duniya lafiya? Kayi ma kanka hisabi tun a duniya.... Kuma bari kaji na fad'a maka, wllhi wllhi kaji na maka rantsuwar d'an musulmi sam rashinka a gareni bazai tab'a ragina da komai ba, damuwata d'aya tak shine mahaifiyarka.... Kayi yanda kake so da rayuwarka ni Sanda ban haifi d'an da zai sakani ciwon zuciya ba.... Maza tashi ka fice min a d'aki...." Ya k'arashe yana janyo radio d'insa...

Ko motsi mai kyau Ahidjo ya kasa kansa a k'asa yana tunanin maganganun mahaifinsa zuciyarsa bai daina masa ciwo ba, wllhi shi kansa baisan meke damunsa ba, baisan tak'amaimen dalilin da ya sanya watsar da iyayensa ba iyakaci yasan addu'a ce kawai zasuci gaba da masa.....

Yana cikin tunanin ya jiyo muryar Baffah cikin tsananin daka tsawa yana fad'in

"Ka fice min nace kafin ranka ya b'aci...!"

Sim-sim ya mik'e ya bar d'akin, rasa maike masa dad'i yayi gaba d'aya, can ya hangi Innah k'ofan fanninsa da tuni suka gina masa cikin gidan dukda ba zuwa yake ba balle zama, d'aki ciki da parlor dai-dai k'arfin talaka da kuma makewayi mai tsari... Jikinsa ya kumayin sanyi shakka babu yasan kintsa masa wajen Innah take, nauyi da k'aunar mahaifiyarsa ya cika zuciyarsa,.... Ganin wayar matarsa na shigo masa ya sanyasa ficewa daga gidan don amsa wayar, ya nufi yanda yayi parking motarsa k'ofar gidan....

***

*Abuja* 8:00am

Sanye yake cikin suit d'insa ruwan toka da alama shirin office yayi, saman stool dake ajiye gaban dressing mirror ya zauna yana gaida Ammah dake zaune saman k'aton royal bed d'inta tana afa magungunanta na safiya.....

"Baba na an fito.....?" Ammah ta tambaya tana kora maganin nata da ruwa cikin glass cup....

"Eh Ammah ya k'arfin jiki kuma?.... "

"Alhamddulillahi da sauk'i sosai kwana biyun nan bana gane ma jikin kasan k'uran hazon nan sai a hankali musamman masu ciwo irin namu...."

Siraj ya jinjina kai kana yace "Haka ne Ammah, Allah ya baki lafiya,.."

Ammah ta amsa da ameen kafin ta k'arada "Sirajo nikam nace ba yaya gaskiyar zancen da nake ji d'in nan, da gaske abokin naka yana son Nana Asma'u ne ko kuwa dai kawai hasashen su Ayiya ne....?" Ta k'arashe tana duban Siraj dake shafa wayarsa.... Lokaci ya maida wayar aljihu ya nitsa hankalinsa sosai yana duban Ammah kana ya soma fad'in "Ammah dama maganar da na shigo muyi kenan, amma naji numfashin naki kaman nason tashi, dan Allah ki dinga kiyaye k'uran nan.... Kuma inaga ya kamata ki koma checkup kwannan nan...."

"Kayya Sirajo am ni banson wani yawo a jirgin nan mutum kaman tsuntsu kaga fah yanzu ko inhaler ban amfani dashi, kaga kuwa ai Alhamdulillahi..."

Siraj ya jinjina kai kana yace "Toh Ammah Allah k'ara maki lafiya.... Kan batun Lamid'o da Nana A jiya da dare munyi maganar and he's serious, da gaske sonta yake, toh amma dai ban basa go ahead ya nemeta ba sai nayi magana da ita Asma'un....."

Ammah ta fad'ad'a murmushinta tana furta "Alhamdulillahi kai Masha Allah, ai hakan yafi, kaga duba da lalurar da Asma'u ke fama dashi gwara ta auri wanda aka sani d'in ba bare ba, kuma Lamid'o ai yaro ne mai hankali ga natsuwa, Allah sa Asma'u ta amince dashi ni sai nafi kowa farin ciki....."

Bata kai aya ba sukaji muryar Nana H da shigowarta kenan tana fad'in "Yarda kam dole Nana A tunda babu wanda ya tab'a furta mata kalman so, kuma wllhi na tabbata shima ba tsakani da Allah yake sonta ba saidon dukiyar da mahaifinmu ya bar mana...."

A tare Ammah da Siraj suka juyo suna dubanta yanda tayi maganar har zuciyarta

"Sweetheart ya zaki ce haka....?" Siraj ya tambaya yana duban Nana H wacce ke tsaye tsgege akansu hannaye hard'e a k'irji

"Uncle it's obvious.... A fili yake, no man, no man in this world will fall in love with a woman that has only one leg, haba Uncle open your eyes and see, wllhi wllhi Lamid'o ba tsakani da Allah yake son Nana A ba, ya mak'ale a company yana cin dukiya jikinsa still bai ishesa ba sai ya nemi niece d'inka... Wllhi Uncle...."

Siraj ya katseta da fad'in

"Shut up Nana H... Haba have some respect, ko kin mance Lamid'o abokina ne huh...?"

Ammah cikeda jin dad'i take jinjina kai, yau ita kanta taji dad'in tsawatarwa da Siraj yayiwa Hafsat, domin ita kanta tana son ganin Nana A a gidan miji kafin ta bar duniya...

Siraj yaci gaba da fad'in "Nasan Lamid'o abokin mijinki ne so dukda haka ban yarda ki tsoma kanki cikin alak'arsa da Asma'u ba, ki bar min komai kin fahimta koh...."

Kallon mamaki kawai take binsa dashi yanda yake ya mata fad'a, wai ita d'in Uncle love kema haka kuma Ammah na kallo bata bi bayanta ba tana shiru, duk akan wannan tsinanniyar gurguwar 'yar uwar tata, toh wllhi dole tasan abinyi, wllhi bazata tab'a bari makirci da munafuncin Nana A ya saye zukatan mutanen gidan ba, babu babban shege irin Lamid'o da ya soma kawo wannan matsala, wllhi shima sai ta shayar dashi mamaki..... Ko kallo basu isheta ba ta fice fuuu kaman zata kifa k'asa....

Siraj ya yunk'ura zaibi bayanta Ammah ta dakatar dashi tana fad'in "K'yaleta, gwara daka mata hakan, banda yarinta irinta Nana Hafsat ai Lamid'o shine dai-dai Asma'u, zata sauk'o da kanta idan ta fahimci hakan.... "

Jinjina kai kurum yayi kafin yace "Ammah kinsan hakinta idan tayi fushi bata sauk'owa da wuri...."

Ammah ta d'an murmusa kana tace "Ai haka mahaifinsu yayan ka yake idan yayi fushi sam baya sauk'owa da wuri, toh haka Nana Hafsatu take, kaga ita kuma Asma'u mai sanyin zuciya ce kaman mahaifiyar su,..." shiru ya d'an gifta sanda ta tuna 'yar uwarsu Nana Khadija... Lokaci guda taci gaba da fad'in "Allah sarki Nana Khadija ita kuma da tana raye k'ila da tayi fad'a fiyeda na Hafsat kasan masu sunan Khadija ba tayan baya ba wajen fad'a..."

Gaba d'aya suka murmusa daga ita har Siraj d'in kafin Siraj yace "Da yanzu ta girma ta zama kamansu, tabbas da mun samu FUSKA UKU iri guda a family saidai kowa da irin halinsa cikinsu... Allah ya jik'an Yaya da Aunty Zainab yasa suna Aljannah...."

Ammah ta amsa da ameen jiki a sanyaye kafin Siraj ya mik'e yana fad'in "Ammah ni zan wuce office idan na dawo zamuyi maganar insha Allah..."

"Toh Babana Allah shi taimaka koh, a dawo lafiya...." cewar Ammah dake bin d'an nata da kallon tausayi, kullum cikin masa addu'a take Allah ya yassare masa matslolinsa na rayuwa....

Kwance ya hangi Nana H saman gado sanda zai wuce k'ofar d'akin nata, girgiza kai kurum yayi ya fice ba tareda yabi takanta ba...

Tana jin k'aran takalminsa yana sauka daga bene kuma taji tsayuwansa a k'ofar d'akin, da a baya ne da Uncle Siraj bazai fita ba sai ya shigo ya lallasheta,... Duk a dalilin Nana A yanzu Uncle love ke mata haka, wllhi ta tsani Asma'u kuma bazata tab'a bari Uncle ya mata rabin soyayyar da yake mata ba...." Ta k'arashe tana huci tamkar wata kububuwa

***

Shigarsa office d'in da kad'an Nasaar ya shigo da sallama... Siraj dake faman duba wani tabloid dake hannunsa ajiywa yayi yana fad'in "Barrister barka da isowa...." Lokaci guda yake zama bisa kujeransa had'i da kurb'an coffee d'insa dake faman tururi....

Cikin sauri Nasaar ya k'araso cikeda rusunawa ya mik'awa Siraj suna gaisawa...

"Sir barka da safiya...? "

"Barka Nasaar, ya al'amra..?"

"Lafia lou Sir......"

Shiru ya d'an ratsa tsakani har Nasaar ya soma tunanin kodai Siraj ya mance appointment d'insu da k'anwar matarsa ne....

Siraj ya katse shirun da fad'in "Lafia dai koh Attorney, ka samu kaga client d'in kuwa....?"

Nasaar ya d'an shafi kansa kana yace "Sir dama zuwa 11am muke da appointment dashi.... Yanzu tafe muke da k'anwar matar nawa wacce kace zaka ganta yau....."

Saurin cire cup d'in daga bakinsa yana fad'in "Aff haka fah, I almost forgot, babu damuwa ka shigo da ita kafin na shiga wani sabgan...."

Cikeda jin dad'i Nasaar yace "OK Sir right away.... Na gode fah Sir, Allah k'ara girma..."

"Babu komai Nasaar...." Siraj ya fad'i yana kuma duba news d'in da ya tafi da hankalinsa cikin jaridar....

Tunda yaji an tab'a k'ofar yaji ya daina fahimtar komai cikin jaridar, ji yayi ya k'agu ya d'ago idanunsa yaga sabuwar sakatariyan nasa wacce yasan itace ke k'ok'arin shigowa, sallamarta da ya jiyo cikin siririyar muryarta ya kuma tafiya da wani b'angare na tunaninsa..... A hankali ya zame idanunsa daga saman jaridar ya maida idanunsa zuwa ga k'ofa, tun daga k'afafunta ya soma duba....
Chapter 23 · 0% Book details