← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 98

Sashe 40

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Luf ta kwanta cikin jikinsa tana maida ajiyan zuciya, lokaci guda ya yaye d'ankwalin kanta kyakkyawan sumarta wanda bai faye tsawo sosai ba ya bayyana....

Murya can k'asan mak'oshi yaci gaba da fad'in "Deee I'm your husband, you're my wife... Ko a islamiyar taku ba'a sanar daku matsayin miji ba...?"

Saurin girgiza masa kai tayi kana tace "Nidai kawai don ina son binka Habuja ne shiyasa idan kace na zauna kusa da kai nake zama, amma idan su Innah suka lek'o suka ganmu haka ai ce mana zasuyi mu 'yan iska ne, nidai kawai ka daina min irin wannan wasan idan kana so nasa na matsawa Baffah da batun tafiyarmu don ni wllhi ba 'yar iska bace, ko su Lado ma Allah bai basu nasara akaina ba..."

Gashi dai maganganun nata abin dariya ne amma kalamanta na k'arshe sunyi mugun d'aga masa hankali... Wani irin zabura yayi ya mik'e yana mata wani irin duba wanda ita kanta saida taji tsoronsa kana yace "Waye Lado, meye had'inki dashi....?" Idanuwarsa a waje ya mata tambayar ga wasu jijiyoyi da suka taso lokaci guda daga goshinsa....

Idanun Deejoh sukayi rau-rau ganin yanayin Ahidjo, tsoro sosai ya wanzu a fuskarta, cikin sauri ta shiga girgiza kai tana dubansa hawaye na zubowa daga idanunta....

Cikin tsawan gaske yace "Ba kuka nace ki min ba, ki sanar dani waye Lado or whatever...!!!"

Deejoh ta kuma zabura kukanta ya k'aru lokaci guda ta soma fad'in "Wllhi wllhi D'angayu ni ba 'yar iska bace, ...."

Take Deejoh ta sanar dashi komai gamedasu Lado, har tareta da suka shayi a hanyar makarantar allo....

Duk sanyin dake kad'awa a garin saida Ahidjo yaji wani gumi na tsartsafo masa.... Ji yake da zaiga su Lado yanzu haka a gabansa babu abinda zai hanasa harbesu har lahira.... Lokaci guda tausayin Deejoh ya kuma rufesa.... He couldn't believe she went through all this.... Ganin kukan nata na k'aruwa tana kuma fad'in ita ba 'yar iska bace ya sanya Ahidjo saurin rungumota ya manneta cikin jikinsa suna jin bugun k'irjin juna, a hankali yake furta "Ki daina kuka Dee, it hurts.... I do believe you kinji koh, na yarda ke ba 'yar iska bace, na sani... Ki daina kuka kinji...." Ya k'arashe yana mai k'urama waje guda idanu, shi kad'ai yake imagining kalan azaban da zai baiwa su Lado, fuskokinsu kawai yake kamantawa a idanun zucinsa dukda ba sanin su yayi ba...

Deejoh kuwa jinjina masa kai kurum tayi had'ida yin lamo cikin k'irjinsa.... Ta jima a hakan har bacci ya soma d'aukarta....

***

Kishingid'e yake a parlorn nasa TV da AC na faman aiki, kasancewar daga aiki ya dawo inners ne kawai jikinsa sabida zafi da akeyi a garin Abuja..

Fuskar Azeeza yake hangowa shi kad'ai sai murmushi yake, hannunsa rik'eda k'aramar bracelet d'inta da shakka babu yasan a hannunta ya zame, domin cikin motarsa ya tsinta.... Lokaci guda yake tuna k'arfin hali irin na Azeeza.... Murmusawa ya kumayi, a hankali ya furta "She's crazy...."

Daga bakin k'ofar ta tsaya tana dubansa, soyayyarsa na ratsa b'argo da tsokarta, kallonsa takeyi yanda yake murmushi yana juya bracelet d'in hannunsa, tausayin kanta ya kamata, wai duk tsarewa da take da hana rab'an Uncle Siraj da take bazata tab'a mallakansa ba... Meyasa meyasa Uncle bai fito cousin d'inta ba ya fito k'anin mahaifinta, shin wannan wane irin musiba ce.... Lokaci guda tasa hannu ta goge hawayen da ya gangaro mata, zuciyarta taci gaba da raya mata har abada bazata tab'a barin wata mace ta rab'i Uncle ba koda ita bazata tab'a mallakansa ba amma kam tabbas zata mutu da k'aunarsa cikin ranta....

K'ok'arin saita kanta tayi kafin ta d'anyi knocking k'ofar glass d'in...

Saurin mik'ewa yayi daga kishingid'en da yake kafin ya mik'a hannu ya janyo jallabiyarsa ya zura....

Mik'ewa yayi ya isa k'ofar had'i da bud'e mata murmushi saman fuskarsa.... Ganin yanayin fuskar nata babu walwala tamkar ma kuka tayi ya sanya jikinsa yin sanyi.... Aiko kaman jira take yana bud'e k'ofar ta fad'a k'irjinsa tana kuka....

Jikin Siraj ya kuma yin sanyin, k'ok'arin janyeta yake daga jikinsa amma tak'i sakinsa, saima dad'a k'ank'amesa da tayi.....

Hankali tashe Siraj ke tambayarta meke faruwa....

Juyin duniyar nan Siraj yayi Nana H ta sanar dashi meke faruwa ta kasa sai faman kuka take....

Da k'yar ya samu ya masu mazauni saman kujera yana mai ci gaba da fad'in "Nana H sweetheart wai meke faruwa, waye babu lafia cikin gidan, ko ciwon Ammah ne ya tashi....?" A tare ya jero mata tambayoyin da shike dawowarsa kenan baiko lek'a sashen Ammahn ba....

Da k'yar Nana H ta tsagaita da kukan nata kafin ta soma fad'in "Uncle do you really love me...?"

Kallon mamaki Siraj ke binta dashi kana ya jinjina kai a hankali had'i da furta "Of course I do love you.... So much...."

Nana H ta kuma goge hawayenta kana taci gaba da fad'in "Uncle zaka iya auren macen da zata wulak'antani taci mutuncina ta zageni...?"

Cikin sauri ya shiga girgiza kai alamun a'a kana yace "Bazan bar wata mace da sunan matata ba taci zarafin 'yan uwana and especially you my sweetheart...." Ya k'arashe yana rik'o hannayenta

K'aunar Siraj ya kuma ratsa cikin zuciyarta, duk duniya babu wanda ke treating d'inta da kulawa kaman yanda Siraj keyi....

"Uncle budurwarka sakatariyarka tacimin mutunci yau cin mutunci da ba'a tab'a min irinsa ba, ta kirani da sunaye marassa kyau.... She even called me your watchdog....." Ta k'arashe murya na rawa...

Ga tsananin mamakinta dariya taga Siraj nayi, ta shiga tambayar kanta cikin zuciyarta kodai baiji abinda tace bane.... Muryarsa ya katseta cikin d'an sautin dariya yake fad'in "I thought wani abin ne ya faru.... Ki kwantar da hankalinki sweetheart, idan dai Azeeza ce haka take, ni kaina na soma sabo da halinta, and waye yace maki Azeeza budurwata ce....?"

Ita haushi ma ya bata tama rasa mai zatace masa, da a baya ne da yabi bayanta kuma da ya rabu da budurwar rabuwa ta har abada, toh mai yake nufi... Anya wannan tsinanniyar yarinyar haka nan tabar Uncle....? K'irjinta ya shiga mata zogi da rad'ad'i....

"Naga tana shige maka da yawa ne...."

Ta basa amsa kai tsaye baki a ture....

Murmusawa Siraj yayi don har cikin ransa dad'i yaji da akace Azeeza budurwarsa ce kana ya girgiza kai yace "No she's not my girlfriend, she's just.... My sectary kin fahimta....."

A hankali ta jinjina masa kai had'i da sakin murmushi.... Mik'ewa yayi had'i da d'aukan remote d'in AC ya kashe ya d'au na TV ma ya kashe kana yace "Muje ban gaida Ammah ba...."

Cikin sauri ta mik'e had'i da sakalo hannunsa ta shiga zuba masa shagwab'a...

Ammah da Ayiya sun sakata tsakiya suna bata baki gameda abinda Lamid'o ya mata su Siraj sukayi sallama suka shigo.....

Sosai Nana A ke kuka tana fad'in "Ammah Uncle yayi warning d'ina banji maganarsa ba, wllhi ban zaci haka halin Uncle Lamid'o yake ba da banyi gangancin soma soyayyarsa ba....." Ta k'arashe cikin muryan kuka...

Ayiya ce ta rungumota ita d'inma idanunta yayi rau-rau take fad'in "Kiyi hak'uri 'yar Albarka ni kaina ban tab'a tsammanin haka daga Sarki ba, amma na tabbata Allah yana sane dake da sannu zai zab'a maki abinda yafi zama alkhairi....."

Ammah ta cab'i zancen da fad'in "Ni banma san mai ya kaisu gidan nasa ba...."

"Wai aike mijin Nana Hafsatu yayo mata ta hannun Lamid'on toh dai tsautsayin ganin faruwar al'amarin ya kaisu.... Ni nasan watsettsen yaro ne yaushe zan ma d'iyata sha'awarsa, napses kawai (Nonsense)..." Ayiya ta k'arashe tana hure-huren hanci....

Kasancewar basuji sallamar tasu ba yasa basu amsa ba da shikema Siraj ne kawai yayi sallaman....

Juyowa yayi yana duban Nana H fuskarsa fal alamun tambaya.... Saurin janyo hannunsa tayi suka shige study dake gefen parlorn....

"Ina saurarenki, meke faruwa, meye ya faru....?" Ya k'arashe babu alamun wasa a fuskarsa...

Bata b'oye masa komai ba duk abinda ya faru ta sanar dashi, harma da k'arin cewa ido da ido suka kama Lamid'o....

Zuciyar Siraj ta shiga bugawa, shine Lamid'o zai yaudara don jiya jiya sukayi magana da Lamid'on har ya basa goyon bayansa saidai baima sanar da Nana A d'inba don baima zauna ba tun jiyan..... Saida yayi masa kashedi kan kar ya yaudari Nana A don bazai tab'a yafe masa ba sai gashi tun ba'aje ko ina ba ya b'ata komai..... Lokaci guda ya soma huci shi kad'ansa, yana son nieces d'insa sosai baison wani abinda zai b'ata masu don su d'in amanace a hannunsa.... Cikin sauri ya fice daga gidan yana dialing layin Lamid'o....

Kallo Nana H ta bisa dashi had'i da sakin murmushi kafin ta nufi parlor yanda su Ammah ke zaune....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*29*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tunda ya fice yake dialing layin Lamid'o amma shiru baya shiga, har gidansa saida Siraj yaje bai samesa ba, hakan ya kuma tabbatarwa Siraj Lamid'o ya aikata laifin tinda gashi har kashe wayarsa yayi... Ransa ya kuma b'aci don saida yayi kashediwa Lamid'o akan Nana A yace yaji ya gani sai gashi kan aje ko ina ya nuna kansa, wani b'angare na zuciyarsa ya masa sanyi don gwara da halin Lamid'o ya bayyana kafin ya basa auren d'iyarsa, dama a cikin su ukun halin Lamid'o ya banbanta da nasu....

Gida ya koma kai tsaye yanda ya tadda Ammah da Nana H har lokacin suna parlorn yayinda Ayiya tayi rakiyawa Nana A d'aki don gaba d'aya ba jin dad'in jikinta take ba...

Da sallama ya shigo parlorn, Ammah ce kawai ta sami zarafin amsa masa Nana H kam kallo ta bisa dashi kaman ta had'iyesa.... Cikin sauri ta mik'e tamkar wacce aka zabura ta isa garesa tana faman rik'o hannunsa take fad'in "Uncle ince dai bai maka komai ba don ni banso kaje ka samesa ba.... Kasan yanzu sai ya k'aryata ko yace bashi bane...." Ta k'arashe idanunta tar kan Siraj ko kyaftasu batayi....

Zama yayi daga can gefe had'i da shafe goshinsa yana gaida Ammah... Lokaci guda ya dubi Nana H kana yace "Sweetheart bamu waje muyi magana da Ammah...."

Kallonsa tayi don tafi so ayi zancen a gabanta kana ta d'an turo baki kaman bazata tashin ba ta kuma d'aukan remote control na TV tana fad'in "Haba Uncle it's time for my reality show.... Kuma fa zan kalla ne dama...."
Chapter 40 · 0% Book details