Sashe 13
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka ta k'arasa ga Yayanta Junaid ta durk'usa dab jikin wheelchair d'insa.... Idanuwanta da suka ciko da k'walla ta d'ago tana dubansa dasu lokaci guda Junaid yasa hannayensa duka biyu ya kamo fuskar k'anwar tasa had'i da girgiza mata kai alamun kada tayi kuka....
Murya na rawa Azeeza ta soma fad'in "Yaya... I'm doing this for you..... And I promise I won't let you down.... Yaya bazan failing d'inka ba..... Yaya Junaid zanyi iyaka abinda ka sakani kuma na maka alk'awari the young tycoon will fall for me....and Zan kawo maka shi har yanda kake a zaune...." Tana k'arashewa hawaye ya zubo daga idanunta... Barr kuwa kasa jure sauraro yayi cikin sauri ya mik'e yana fad'in "I'll be outside.... " Daga haka ya fice cikin sauri yana k'ok'arin nitsa zuciyarsa....
Junaid da tuni shima hawaye suka ciko idanunsa sharema Azeeza nata hawayen yayi kana yace "You go with my blessings little sis.... Bazan iya gode maki ba Azeeza sabida nasan ba'a son ranki zakiyi ba... Amma ki sani ni Junaid bazan tab'a barinki ke kad'ai ba tare zamuyi..... I promise...." Ya k'arashe yana k'ak'aro murmushi saman fuskar sa...
Lokaci guda Azeeza ta rungumeshi tana kuka sosai... Saida tayi mai isarta kafin Junaid ya kuma gyara mata fuskarta ya rakota har yanda Barr yayi parking motarsa... Da kansa ya bud'e mata marfin motar ta shige... Bai bar wajen ba har saida yaga ficewarsu daga gidan....
*SameenaAleeyou📚*
[12/16, 1:12 PM] +234 810 044 6653: *FUSKA UKU*🏮
*10*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ajiye coffee mug d'in dake hannunsa yayi saman k'araman plate yana duban Barr Nasaar.... Saida ya d'an murmusa kafin ya mik'e ya shiga tafiya cikin wargajejen office d'in nasa wanda yasha wooden floor a maimakon tile.....
A dai-dai jikin aquarium ya tsaya yana kallon kifayen ciki kana ya maido da dubansa ga Barr wanda shima tuni ya kaikaito yana duban Siraj d'in...
Saida Siraj ya d'anyi gyaran murya kana yace "Attorney maiyasa kake so na canza Janet bayan I'm ok with her, she does everything on time, she knows her obligations...."
Nasaar ya mik'e tsaye yana takowa gaban Siraj kana yace "Sir as I told you, the girl really need the job... Yarinyar nan k'anwar Matata ce da ta taho daga Maiduguri... Sir kasan yanda yak'i ya maida yankinsu abin tausayi... I'm pretty sure the job will help, zata rink'a tura kud'in gida.... Yanzu haka sabida kulada yarana ta baro Maiduguri don ta zauna taredasu tunda babu mahaifiyarsu, ina fita aiki kuma su Hammad suna zuwa sch zaman nata a gidan ita kad'ai zaisa tunanin yak'in da ta gani iri da kala ya kasa barin kwanyarta... Inaso ta sami experience... Wannan na d'aya daga cikin dalilin da yasa 'yan uwan suka dage ta sami change of environment.... Sir offer her the job... Na rok'eka dan Allah...."
Tunda ya soma magana Siraj yayi shiru yana saurarensa jikinsa ya d'anyi sanyi.... Mug d'in coffee d'insa ya d'auka ya shiga kurb'a a hankali yana tunanin maganganun Barr Nasaar...
Saida ya koma mazauninsa ya zauna kana ya kuma duban Nasaar yace "Attorney kazo da Cv d'inta nan ne...?"
Gaban Nasaar ya d'an buga kafin ya saita kansa tuni wasu dabaru suka shigo kwanyarsa abinka da lawyer....
Gyara zamansa yayi had'ida daidaita suit d'insa kana ya soma fad'in "Sir Azeeza k'aramar yarinyace she's just 19 secondary school kawai ta gama sannan naso sakata a makarantar gaba da secondary saidai unfortunately takardunta sun watse dalilin tashin tashinan hanakali da suka fuskanta, shiyasa naso ta soma aikin kafin zagayowar wata shekara sai ta sake jarabawa ta koma makaranta... Sir I'm pretty sure you'll enjoy working with her... Yarinya ce mai hankali sannan a ganina Sir tafi kayita aiki da mai d'angallalen skirt kullum tana kwarkwasa gabanka, zaka iya kai Janet wani department...." Yana kaiwa aya yayiwa Siraj k'uri sabida yasan ya gama siyesa da kalamai....
A hankali Siraj yake jinjina kai kana yace "But do you think she's that literate da har zata iya aiki damu....?" Ya k'arashe fuskarsa cikeda alamun tambaya...
Cikeda jin dad'in nasarar da ya samu kan Siraj lokaci guda ya shiga jinjina kai yana fad'in "Sir kana iya interviewing d'inta and see for yourself...."
Siraj ya jinjina kai kana yace "Fine.... Babu damuwa... Skedules d'ina na yau a cike suke da na ganta a yau amma maybe a cikin week d'in nan...."
Da sauri Nasaar yace "But sir... She's here already... Please sir if possible ta shigo ka mata gwajin...."
Kallonsa Siraj yayi kana ya d'an murmusa da gefen bakinsa yace "Seems you're desperate Attorney.... Kar ka damu ni nace zan mata gwajin kuma zan mata...." Mik'ewa yayi yana duba agogon hannunsa yake fad'in "I have to attend to some clients... Kar ka damu zamuyi maganan Attorney...." Daga haka wayarsa dake faman ruri ya k'ara a kunnensa yana amsawa ya nufi private elevator d'insa wanda shi kad'ai ke bi ta cikinta a Kampanin....
D'an fuzar da iska Nasaar yayi had'i da d'an ware hannaye alamun babu matsala tinda ya amince zai d'auketa, kuma baima yi zaton zai iya shawo kan Siraj lokaci guda ba tunda yasan yanayin yanda Business men irin Siraj suke, lokacin kansu basuda shi.....
Nasaar na fitowa ya hangeta zaune tana jiransa sai d'aga kai sama take tana kalle-kallen tapkeken ginin wanda bene ne a k'alla mai hawa kusan ashirin.... A hankali Nasaar ya murmusa komai nata na birgesa musamman son yaransa da takeyi ga dukkan alamu Azeeza zata k'aunaci d'iyoyinta idan Allah ya nufa zata samu gaba idan tayi aure... Allah sarki ba kamar matarsa ba wacce tasa k'afafu ta tafi ta bar nata yaran ko oho, bikon duniya yayi tak'i amincewa ta dawo k'arshe har cewa tayi zata maka sa kotu idan bai fita hanyarta ba.... Saurin kawar da tunanin yayi ganin hankalinsa na k'ok'arin tashi... A haka ya k'araso ya tadda Azeeza tana ganinsa ta sakar masa murmushi... K'irjinta na bugu take tambayarsa feedback...
D'an k'ak'aro murmushi Nasaar yayi kana yace "Kar ki damu kin sami aikin an gama cikin satin nan Boss d'in naki zai maki interview, badon rata sosai dake tsakanin nan da gida ba da na maidaki yanzu saidai ko zaki d'anyi hak'uri tunda lokacin d'auko su Taheera a makaranta ya kusa idan yaso da zaran mun d'aukesu sai na wuce daku gida tunda nima lokacin break d'ina kenan...."
Jin zata school d'in su Taheera ya sanyata jin dad'i sosai har ta kasa b'oye farin cikinta.....
Nasaar ya bita da kallo fuskarsa cikeda murmushi don baiyi zaton zata amince ba kai tsaye office d'insa suka wuce ta kuwa shiga tayasa aiki.... Sosai Nasaar yaji dad'in hakan har lokaci yayi saurin masa, d'an zamansa da Azeeza yau ya kuma haifar da sabo tsakaninsu...
K'arfe d'aya dai-dai suka nufi school d'in su Hammad don d'aukosu... Tunda Taheera taga yau harda Aunty Zee akazo d'aukansu sai murna take hakan sai ya tuna mata sanda take k'arama sosai farkon shigarta school da Momynta Daddy ke zuwa d'aukansu watarana.... Shiko Hammad tunda ya gansu a tare ya b'ata rai sosai koma kula Azeezar baiyi ba, ya fara tsanarta baisonta kusa da Babansa bai son ganinta a gidansu, wajen Daddyn sa kawai ya nufa yayinda Taheera ta nufi wajen Azeeza sai zuba mata surutu take ita kuma Azeezar na biyeta, Nasaar na hankalce dasu sai jin dad'in shak'uwar da sukayi da juna yake.....
****
Keys d'in ta mik'a masa tana mai wasa dasu a fuskarsa.... Lokaci guda ya saki murmushi had'ida amsar keys d'in yana jujjuyawa kana yace "Wow 'yar gidan Uncle baki hawa motar k'anan mutane.... Dole Uncle yayi abinda kikeso a lokacin da kike so....."
Murmushi take kanta na kuma fashewa kana tace "Lamid'o kenan a lokacin da na fad'a wllhi Uncle Siraj zai bani motarsa a ranar ai ka zaci wasa nake amma yanzu na tabbatar maka babu abinda Uncle luv bazai min ba.... Lamid'o wllhi wllhi duk wanda ya nemi ya datse tsakanina da Uncle Luv wllhi sai naga bayansa ko shi waye....."
Lamid'o ya murmusa yana mai shafa hab'arsa yake fad'in "Kin wuce duk yanda nake tunani Nana H kuma na yarda zakiyi komai akan Siraj.... Toh yanzu mai kike ciki da batun alak'arsa da Nadiya don naga yarinyar ta dage tana son Siraj kaman ta mutu, takan masa waya a rana bila adadi.... She's into him totally..." Yayi wata murmushi kana yaci gaba da fad'in "My guy ya had'u ta yanda babu budurwar da zaice yanaso tak'isa ke kinsan da haka... And you know ina mugun tausaya maki duk randa yarinyar nan Nadiya ta auri Siraj wllhi wllhi kaman yanda kika contributing wajen datse Ahidjo da iyayensa haka itama zata datse Siraj da familyn sa ke Laushi group sai ya gagareki shiga idan bakiyi wasa ba....."
Kallonsa kawai take k'irjinta na tafarfasa tana imagining abin a gaske... Lokaci guda tayi wata murmushi kana tace "Delusional.... Kai kuma kana tunanin haka zai tab'a faruwa.... Toh ka jira kaga mai zai faru...." Ta kuma matsowa dab dashi tana shafa fuskarsa take fad'in "Just trust me sweetheart.... And remember no one messes with Nana Hafsat Laushi, the one and only Queen in the Laushi's family...." Ta k'arashe murmushi fal saman fuskarta...
Murmushi Lamid'o ma yayi kana yace "I trust you darling.... Nasan zaki iya so now za'a ara min motar ne na d'ana ko kuwa....."
Juyawa tayi ta soma tafiya ta nufi cikin gidan nasu da suka saba had'uwa.. Tana tafe ba tareda ta juyo ta kallesa ba take fad'in "Don't take too long...." Tana fad'i tana karkad'a masa yatsa cikin tafiyarta wanda tamkar da jikinta take yinsa.....
Murmushin cin nasara Lamid'o yayi kana yace "I won't darling...." Cikin sauri ya nufi motar ya kunnata ya bar wajen.....
Tafiya kad'an yayi ya d'an kutsa dajin dake gefensa kad'an ya shiga bincike a motar, duk yanda yake tunanin zai sami takardun ya bud'e bai samu ba, yasan Siraj shegen kaya ne bazai tab'a wasa da wad'annan takardu ba... Wato har ya ciresu.... Wani mugun tsaki ya buga ya shiga dukan tayun motar yana furta " Damn it.! Damn it.....!" Lokaci guda wayarsa ta shiga ruri ganin mai kiran ya sanyasa sakin wani tsaki kana ya nutsa kansa had'i da d'aga wayar....
Yana d'aga wayar daga d'aya b'angaren mai maganar yace "Ka sanar dani an sami improvement...."