Sashe 79
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga yanda Nana H ke zaune cikin guarding tana shan hasken rana mai k'unshe da sinadarin vitamin D, fatarta sai faman shek'i da k'yalli yake, wasu kaya ne marassa nauyi a jikinta sai wani d'an gyale wanda ta d'aure sumarta ciki, kallo guda zaka mata kayi zaton ba 'yar Africa Nigeria bace, santala-santalan k'afafunta wanda babu ko k'wallin gashi jiki ta mik'esu saman kujera guda hannunta d'auke da wani glass cup wanda k'asansa yake dogo sosai, kana iya hango fruits d'in dake cikin kofin tana faman cakalan kayan lambu da wani d'an tsinke hannunta....
Gaba d'aya bazakayi zaton wai wannan d'in takaba take ba, kodashike abinka da wad'anda addini bai ishesu ba a cewarsu takaba kwana arba'in ne wai sauran kwanakin kuma iddah ne, wai a iddar mace zata iya yin komai dangi su kwalliya fita maras k'wakk'waran dalili da sauransu wani sa'in ma harda neman aure cikin iddah, Allah ka tsaremu kayi mana rahama da wayewa irinta addinin islama... Sam basusan cewa takaba bahaushe ne dai ya saka masa suna haka amma a addinance sunansa gaba d'aya iddah ne, kuma iddar macen da mijinta ya mutu wata hud'u ne da kwana goma, ita ba jini ake k'irgawa ba kaman macen da mijinta ya saketa wacce ita jini ake k'irgawa... Macen da mijinta ya mutu ya barta da juna biyu kuwa iddarta yana k'arewa ne da zaran ta haihu, ko yau mijinta ya mutu ta haihu washe gari tabbas ta gama iddarta kuma manema zasu iya nemanta zakuma tayi aure, ita haka iddar wacce ta haihu yake....
Daga yanda ta hango 'yar uwarta ta tabbata duniyar tai mata babu dad'i, wani murmushi ta saki domin ganin Nana A cikin damuwa ba k'aramin faranta mata yake ba, a hankali ta mik'e tana mai janyo yalolon doguwar rigar jikin nata ta nufi Nana A....
"Sis lafiya, what's wrong, meke damunki? Wait ya na ganki haka waye yayi dropping naki, badai wancan mayaudarin bane kika kuma basa k'ofa....?" Gaba d'aya tambayoyin a jere ta jefo mata su, Asma'u kam bata kuma iya cewa komai ba sai wani sabon kukan da ta fashe dashi lokaci guda ta fad'a jikin 'yar uwar tata tana yin mai isarta....
Nana H dai ware idanunta ta shigayi tana mai tambayar kanta toh mai ya sami musakiyar 'yar uwarta, yanzu haka bazai wuce kan namiji take wannan uban kukan ba, ita bata tab'a ganin doluwa mai kuka wa soyayyar namiji ba irin Asma'u, ta tabbata wannan kukan bazai wuce akan Lamid'o bane ko wancan musakin gold digger d'in.....
K'ok'arin d'agota tayi tana mai lallashinta had'i da rik'ota suka k'arasa saman kujerun da Nana H ke bisa suka zauna... Lokaci guda take tambayarta ta sanar da ita abinda ke damunta....
Bud'e baki Nana A tayi da niyyar magana amma ta kasa domin wani sabon kukan ne ya taso mata, Nana H ta kuma matsowa kusanta had'i da rungumeta, fuska fal damuwa take fad'in "It's okay Sis, I'm here okay, I'm here for you, ki daina kuka kinji..."
Sun d'an jima a haka Nana H na lallashinta kafin tayi k'ok'arin saita kanta, goge hawayen fuskarta tayi had'ida furta "Thank you Sis, thank you for always being here for me...."
Nana H ta girgiza kai murmushi saman fuskarta kana tace "Oh no no Sistu, you don't have to thank me for anything okay, amfanin family kenan, always support each other, so tell me meke damunki... ?"
Jinjina kai ta d'anyi tana mai kuma maida ragowar k'wallan idanunta nata take fad'in "Nana H, I'm so confused bansan meke damuna ba, and....and I'm completely lost that I don't know what to do anymore.... I'm so scared Nana H...." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya....
Kamo hannayenta Nana H ta kuma had'ida rik'esu cikin nata kana ta soma fad'in "Asma'u ban fahimceki ba, kimin bayani yanda zan fahimta may be I can help, amma yanzu kin barni cikin duhu ne, sam ban fahimci mai kike nufi ba...." Ta k'arashe idanunta k'uri kan Nana A d'in
Gingina mata kai Nana A tayi cikin murya mai tsananin rawa ta labarta mata tsaf yanda sukayi da Lamid'o da kuma Junaid.....
Juya idanunta Nana H tayi kana tace "There you go Nana A, ke yanzu kin yarda da Lamid'o ne, da idanunki kinga abinda ya aikata sannan ni ban yarda gaskiya yake fad'i ba kawai so yake ya kuma yaudarar ku daga ke har Uncle dasu Ammah, ya sanni yasan ni bazan tab'a yarda da k'aryarsa ba, haba Nana A why are you so naive, sai kace ba mace ba kike bari namiji ya maki wayo, ai mata aka sani da makirci idan ma wani makircin yake shirin had'a maki, shin dama kin yarda Lamid'o zai k'aunace ki tsakani da Allah ne, ai babu namiji mai cikekken lafiya da halitta da zai so ki tsakani da Allah a yanda kike d'in nan, mai kike tunani randa Lamid'o ya aureki kika tare gidansa yaga k'afarki ta roba muraran a zahiri babu covers da dogayen skirt dake rufe maki su, kina tunani zai soki a haka ne,...? Let me tell you this kyaun fuskarki shine kawai yake zautar da Lamid'o kuma shima d'in ba wani dalili bane illa confusing d'inki da yakeyi dani..."
Da mamaki Nana A ke dubanta kana tace "Ban gane ba, ya tab'a cewa yana sonki ne....?"
Nana H ta kuma murmusawa kana taci gaba da fad'in "Asma'u kenan, shiyasa ake saurin yi maki wayo a abubuwa da dama, shin baki tab'a kula da irin kallon da Lamid'o ke bina dashi ba idan muka had'e waje guda...? Toh waima meye dalilin da yasa sam nidashi bamu jituwa...? Ko kinsan tun kafin Heedj ya aureni Lamid'o ke sona, nice dai nak'i basa k'ofa na kuma sanar dashi Heedj nake so shi kad'ai sannan har bayan aurenmu da Heedj bai daina damuna ba yana bibiyata a bayan idon Heedj, na masa d'add'aya na sanar dashi ni ba irin wad'annan matan da yake tunani bane na kuma gargad'esa idan bai daina damuna ba zan sanar da Heedj toh kinji dalilin da yasa sam nak'i jininsa, dalilin da yasa sam bamu jituwa, shine da yaga haik'an bazai mallakeni ba bazai kuma sami goyon bayana ba ya soma nemanki.... Kuma barikiji na fad'a maki wani abu guda da namiji mai neman mata, shifa ko auren yayi ko ya aureki bazai daina bin na layi ba, kuma koda ace zai auri mata hud'u bazai daina hangen na waje ba, kina zaune a gida yana can yana holewarsa da wasu matan a hotels daban daban musamman mace irinki mai nakasa a tattareda ita,,.. Asma'u wllhi wllhi kada kiyi gangancin amincewa auren Lamid'o a banza zai saka maki ciwon zuciya ki mutu ya d'ibi dukiyarki na gado ya auro wata macen mai lafiya mai cikan halitta da dukiyar da kika bari masa, kinga kuwa ya kashe ki ya auro wata da dukiyarki....." Ta k'arashe tana mai tsare Nana A da k'wayan idanunta....
Wani irin sanyi k'alau jikin Nana A yayi, yanzu Lamid'o dama haka ya nemi 'yar uwarta da aurenta... Wa'iyazu billah, lallai dole Nana H ta tsanesa kuma dole bazata so taga wani nata dashi ba, lallaima namiji baida kunya, idan kuwa haka ne tabbas ta yarda Lamid'o ba k'aunarta yake ba kawai dai don bai sami yanda yake so da Nana H bane, wani irin hawaye masu d'umi taji suna gangaro mata, tsanar da batayiwa Lamid'o baya ba taji na taso mata, kai gaba d'aya ji tayi ta tsani duk wani namiji, zuciyarta ta karaya da yawa, rayuwar duniyar gaba d'aya taji ya kuma fita daga ranta...
A hankali ta rungume Nana H tana mai tausaya mata faman da tayida Lamid'o yanda ya dinga bibiyarta bata sanar da kowa ba ko Uncle balle Heedj, ta rufa masa asiri ta kuma tsare mutuncinta da aurenta, tabbas ta yarda Lamid'o bak'in kumurci ne mai mummunar guba.... Ta lumshe idanunta a hankali wasu hawaye masu d'umi suka gangaro mata....
Nana H kuwa murmusawa kurum tayi don ta tabbata Lamid'o ya gushe ya zama tarihi a zuciyar Nana A, ita kuma a yanzu zatayi amfani da wannan damar ta kuma mallakan Lamid'o musamman da yanzu babu Heedj, Lamid'o ne kawai zai maye mata gurbin Heedj a halin yanzu....
A tare suka shige gida bayan Nana H d'in ta kuma lallashinta da k'arfafa mata gwiwa wajen yin watsi da Lamid'o da kuma k'aryarsa, a parlor suka tarar da Ammah da alama sauk'owarta kenan, ganin su haka rungume da juna ya sanya Ammah sakin murmushi mai sanyaya zuciya, wani dad'i taji zuciyarta na mata tabbas duk randa FUSKA UKU na jikokinta suka had'e waje guda babu wanda zai kaita farin ciki, fuskar d'anta marigayi take hangowa a fuskokin nasu, Allah sarki bawa kar ya yanke tsammanin rahama daga ubanjinsa gashi dai Nana Khadija da yardar Allah zata dawo cikinsu, cikin danginta wanda batasan dasu ba sama da shekaru ashirin... A hankali ta furta "Allah ka nuna min wannan rana ranar da Khadija zata dawo cikin gidan nan kafin na bar duniya...."
Muryar Nana A ta jiyo tana mai amsawa da "Ameen Ammah, Nana K ta kusa dawowa cikinmu insha Allah, jikina yana bani tana kusa damu..." Ta k'arashe sassanyar murmushi saman kod'edd'iyar fuskarta..
Nana H kuwa dubansu kawai take tana murmushi, cikin zuciyarta take fad'in "Saidai kuyita mafarkinku amma Nana K kam ta tafi da tafiyarta, duk wata hanya da nasan zai sadata da wannan family d'in sai nabi na rufeshi, she's already in the past, I'll not allow her to ruin my present..." Muryar Ammah ce ya katse mata tunanin nata sanda ta bud'e duka hannuwarta biyu tana fad'in "Kuzo 'ya'ya na..."
Cikin sauri suka kuwa k'arasa had'ida yin hugging d'inta.....
***
Yau tinda Ma'ajura ta dawo sallah kawai tayi ko cin abinci bata tsaya yi ba ta nufi gidansu Zaliha da labari mai dad'i cewa ana nemanta gobe a foundation d'insu...