← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 98

Sashe 69

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffah yayi hamdala kana yace "D'ansanda gwara da Allah ya kawo ka na tabbata kai zaka rabamu da wannan matar...."

Gaje cikinta ya d'uri ruwa, ita kad'ai ta soma reverse tana nufan k'ofa mayafi a hannu.... Tsaban tsoro ta kasa furta koda kalma ga Sabi'u ya tsareta da ta mujiya.... Saida ta zo kusansa zata wuce ya tare hanya yana fad'in "Ina kuma zakije...?"

Gaje baki na rawa take fad'in "Yallab'ai wasan tashe nake, kaga ma rawar 'yan tashe...." Ta shiga juyi tana wani wak'e mai kama da sunbatu.... Shikam Sabi'u dariya taso basa saidai kafin ya ankare Gaje ta wawashe takalmanta da sunan rawan tashe ta arta a guje....

Sabi'u ya nufi waje zaibi bayanta Baffah ya kirasa yace ya k'yaleta bazata sake dawowa ba...

Sabi'u ya dawo cikeda risinawa yana mai gaida Baffah, Deejoh kuwa tinda ta hangesa taji wani k'atutun bak'in ciki na taso mata, bata san dalili ba amma haka kurum taji ta tsani mutumin tun ranar da yazo ya kawo masu sak'on mutuwar Yaya Ahidjo, shiko Sabi'u sosai yake kyautatawa su Baffah duk a cewarsa sabida zaman amanan da sukayi da Ahidjo ne, wani hidiman idan Baffah ya hanesa sam bai dainawa saidai yace iyakacin abinda zaiyiwa Ahidjo kenan yanzu da babu shi ya kula da iyalansa da iyayensa....

Sam Deejoh ko gaisawa bata tsaya sunyi ba ta shige d'aki abinta, tana jinsa suna gaisawa da Innah harda tambayan yaya jikinta, haushi tamkar ya kasheta, itakam sosai ta tsani wannan mutumi dukda kyautata masu da yake, ta danganta tsanar data masa sabida shine ya kawo masu sak'on mutuwar mijinta, bazata tab'a mance wannan kalamai da suka fita daga bakin wannan mutumi ba... (Deejoh kenan mai ji da k'uruciya da yarinta bata yarda mijinta ya mutu ba...)

***

*Abuja*

Yau d'in bata fice aiki ba sabida rashin jin dad'in jiki da take fama dashi, gaba d'aya foundation din sai bai masa dad'i ba, bai zaci ya shak'u da Asma'u har haka ba, mai yasa gaba d'aya ya kasa samun sukuni, shi kad'ai sai hangen k'ofan ofishinta yake yaga ko zata iso, wata zuciya tace mai yasa ka damu da ita har haka bacin kurum amfani da ita kake ka cimma burinka? Take b'angare na zuciyarsa ta basa amsa da sabo ne kurum ba wani abu ba, da zaran ka gama biyan buk'atarka ka breaking heart d'inta dana Uncle d'inta zaka cireta daga rayuwarka and that's all, tabbas babu macen da zata maye gurbin Zeenah cikin zuciyarka...

A hankali ya sauk'e ajiyan zuciya had'i da fuzar da iska.... K'ok'arin yakice tunanin cikin zuciyarsa yake amma ya kasa, koda ya kira layinta ba'a d'aga ba, hankalin Junaid ya kuma tashi, ji yayi bazai iya zaman foundation d'in ba, ji yayi yana son sanin halin da take ciki.... Tamkar wanda aka zabura ya shiga tura wheelchair d'insa ya fice, b'angare na zuciyarsa tana kuma k'arfafa masa gwiwa kan yaje ya dubata ta haka ne kurum zata kuma aminta cewa shid'in masoyinta ne, sannan ya tabbata a dai-dai wannan lokacin Siraj bai gida yana wajen aiki..Yana ficewa ya hango mai tasi kana ya saka masa hannu...

***

Wajajen k'arfe 11:00am ya shigo gidan, kana ganinsa zaka fahimci sam babu nutsuwa a tattaredashi ga wani uwar rama da yayi sai idanunsa da dogon hanci kurum kake hangowa a farar fuskar tasa....

Cikin sauri ya nufi sashen sa ya fad'a d'akinsa, kai tsaye closet ya k'arasa ya d'auki wata 'yar k'aramar jaka mai cin kaya a k'alla kala uku, cikin sauri ya shiga tura kayan ciki, waya mak'ale a kunnensa yake fad'in "Sameer I need the private jet ready right away..." Bai jira amsar Sameer d'in ba yaci gaba da abinda yake...

Tamkar ba Siraj ba haka ya fito, Shirt d'in Mango ne jikinsa mai ruwan toka sai wando black chinos, jakkar rataye a kafad'ansa ya isa parking space ya bud'e motarsa k'irar BMW ya jefa jakan cikin motar kana ya zagayo gefen matuk'i...

Kamar wacce akace ta lek'a waje tashinta kenan daga baccin asara ta hangi Uncle Siraj na jefa jakan kaya cikin mota, ta tabbata wannan tafiya ce zaiyi ta sirri wanda baiso su sani... A guje ta isa jikin window d'in ta wangale tapka-tapkan murafen window tana mai ambato sunansa take k'ok'arin fashewa da kuka tana fad'in kada ya tafi don dama ko jiya saida yasha artabo da ita da kuma Ammah, sam sun hanasa tafiyar da sunan nemo Azeeza....

A hankali ya shafi goshinsa don yasan yanzu zata taso masa Ammah.. A dole ya nufi cikin gidan kafin ta fito waje ta taddasa...

Ayiya ya tarar a k'asa ta fito kitchen hannunta rik'eda magungunan Nana A da ruwa saman k'aramar plate cikin glass cup...

Saida ta firgita da ganin yanayin Siraj... Wani irin wawan rama yayi lokaci guda... Baki bud'e take fad'in "Kai kuwa lafiya kaman wanda ya mik'e daga jinya..?"

Shafa goshinsa yayi yana duban maganin dake bisa parantin a hannunta kana yace "Badai sai yanzu Ammah zata sha maganinta ba..."

"Maganin Asma'u ce..." Ayiya ta basa amsa tana mai k'ok'arin saka kai..

"Nana A ce bata da lafiya... Since when, yaya ban sani ba...?" Ya tambaya yana mai duban Ayiyan...

"Yo ina kuwa zaka sani tunda ba 'yar gaban goshinka bace...." Ta kuma fad'i tana taka bene..

Dafe kansa yayi domin kuwa tabbas baisan batada lafiya ba, shi kansa bai zauna bane ga Al'amran da suka sha gabansa a 'yan kwanakin... Cikin sauri ya nufi upstairs aiko sukayi kicib'is da Nana H cikin kayan baccinta take ko d'aura falmaran saman batayi ba ta fad'a jikin Siraj tana kuka sosai take k'wallawa Ammah kira tana fad'in "Ammah kizo Uncle zai tafi garin yak'i ya barmu..."

Babu shiri Ammah ta fito tana fad'in "Siraj babu yanda zakaje, ince yarinyar nan ita tace bata sonka ko ana soyayya dole ne, ka k'yaleta tayi tafiyarta, ina kasan zaka sameta salon mu rasaka ko mai sanin kanka ne duniya babu yarda a yanzu....

K'ok'arin tsame jikinsa yayi daga rik'on da Nana H ta masa ya k'araso ga Ammah wacce tsananin tashin hankali ya nuna sosai a fuskarta...

Hannayenta ya kamo yake fad'in "Ammah dan Allah ki k'yaleni na nemo farin cikin rayuwata Azeeza, Ammah babu wanda yasan yanda ta tafi... Bazan iya zama bansan halin da take ciki ba, dan Allah Ammah kimin izini na tafi na rok'i arzikin ki...."

Kalamansa tamkar garwashin wuta haka Nana H take jiyosu, batasan Uncle ya kamu da soyayyar Azeeza har haka ba, ko mutuwar Zeenat Uncle bai shiga tashin hankali irin wanda yake ciki a yanzu ba.... Saurin k'arasowa tayi tana mai ci gaba da kuka take fad'in "Ammah wllhi asiri ta masa, kinga gashi wai zai bita.... Ammah shikenan ta raba...."

Tsawan da Siraj ya darara mata ne ya sanyata had'iye sauran maganarta lokaci guda kuma Ayiya da Nana A suka fito

Huci Siraj yake yana nuna Nana H da yatsa sanda yaci gaba da fad'in "You stay out of this okay... You've no right to decide for me.... Ina son Azeeza kuma zan nemota duk yanda ta shiga ta fita...." Maido da dubansa ga Ammah yayi wacce itama kallon mamakin take masa tamkar ba Siraj d'inta ba, gaba d'aya mace ta maidasa wani iri lokaci guda...

Ayiya kuwa tamkar ta taka rawa ganin Siraj ya dasa birki wa Nana H gaban kowa abinda bai tab'a yi ba duk munin kaifin da zatayi....

Siraj yaci gaba da fad'in "Ammah I'm sorry, but I really need to do this... Please understand me, Ammah zan iya kula da kaina dan Allah ki k'yalenk na nemo Azeeza..."

Ammah dake kallon wani gefen rai b'ace ta furta "Ban amince ba Siraj, ban amince maka ka fita neman yarinyar da ta sanar dakai bata k'aunarka ba..."

"Ammah please....!"

Dakatar dashi tayi ta hanyar d'aga hannu kana tace "Banson jin komai... Ka zab'a ko ni ko ita...."

Cak ya tsaya yana duban Ammah yayinda Nana H ta shiga murmusawa a hankali tana mai taune labbanta na k'asa alamun hukuncin Ammah yayi mata...

Wani irin bugawa k'irjin Siraj yayi, bai zaci Ammah zata yanke masa hukunci mai tsauri irin haka ba, shiyasa yaso ya tafi ba tareda saninsu ba... Yana nan tsaye a wajen sai ganin Nana A yayi ta k'araso cikin tafiyarta da yafi kama d'ingishi, hannayen Ammah ta kamo tana hawaye take fad'in "Ammah dan Allah ki k'yale Uncle yaje ya nemo Azeeza, Ammah Azeeza itace farin cikin Uncle kiga yanda ya rame a dalilin rashinta, Ammah dan Allah ki masa izini yaje bamu san wani hali take ciki ba.... Please...." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya...

Ganin Amman batace komai Nana A bata daina jijjiga hannunta ba alamun rok'o yasa Siraj k'arasowa ya rik'e hannun Nana A nan yaji zafin zazzab'in dake jikinta, a hankali ya soma furta "Kar ki damu sweetheart, Azeeza na cikin k'oshin lafiya a duk yanda take insha Allah, ki kwantar da hankalinki kinji I'll be fine...." Hannunta ya rik'e ya maidata d'aki, da kansa ya b'alla mata magani tasha tausayinsu ya kama Ayiya lokaci guda, for the first time da taji tausayin Siraj..

Nana H kuwa uwar harara ta raka Nana A dashi kafin ta takewa Ammah baya tana mai furta "Bak'ar munafuka a haka zaki k'are...."

Saida ya baiwa Nana A duka magungunanta kafin ya nufo downstairs zuciyarsa naci gaba da masa zafi, cikin sassarfa yake tafiyar har ya iso farfajiyan gidan....

Dai-dai sanda securities masu tsaron gate suka bud'ewa Junaid k'ofa...

Hango mutum saman wheelchair ya sanya Siraj tsayawa cak ba tareda ya kuma k'ara koda step guda bane....

Shima Junaid d'in hango Siraj da yayi tsaye a gabansa ya sanyasa daina motsa tayun wheelchair d'insa... A dai-dai kuma lokacin wayar Siraj ta soma ruri... Ga tsananin mamakin sa Sunan Lamid'o ne b'aro-b'aro ya bayyana masa saman screen d'in....

*Toh fah masu karatu ga Siraj ga kuma Junaid sun had'e, shin yaya zata kaya masu....?*

*Zuwan Junaid yayi dai-dai da bayyanar Lamid'o shin yaya wasan zata kaya.....?*

*Ku biyo alk'alman Sameena domin jin yanda wannan labari mai cikeda sarkakiya zata kaya👌🏽*

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*48*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 69 · 0% Book details