Sashe 3
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D'ago idanunsa guda d'aya yayi had'i da kanne d'ayan kana "Na sani.... Kuma bazan bata hak'uri akan abinda Nana H tayi mata ba, wannan ita ya shafa bani ba.... Kai nifa tunda na rasa Zeenatu bana tunanin akwai macen da zan kuma rasata ya dameni ba.... Banida lokacinta ma..."
Da gefen bakinsa yake murmusawa yana duban abokin nasa kafin ya d'ago cup d'insa alamun toast yana mik'awa d'aya abokin nasu yake fad'in "To Siraj Laushi's pain in the ass behavior.... May he stay as forever bastard ...."
Kallonsa kawai Siraj yake had'i da girgiza kai kana yace "LAMID'O idan kana son Nadiya ce fah you can have her, wllhi I dont care....."
Sai sannan mai sanye da kakin ya murmusa had'i da ajiye cup d'in hanninsa saman k'aramar table d'in kana yace "Wannan shi ake kira fad'an gauraye.... Ya kamata ku ajiye iyali tsufa kuke kun sani koh...."
"Fad'a masa Detective ya ajiye Iyali dai don shine mai manyan d'iyoyi 'yanmata... Nikam I'm still young yanzu ma na soma cin tawa duniyar....."
Siraj yayi k'wafa yana watsawa Lamid'o mugun kallo kafin ya dubi matashin dake sanye cikin kakin yace "AHIDJO tashi muje naga Hafsat, I'm worried about her...."
Kallonsa sukayi gaba d'aya yanda ya mik'e a birkice kafin Lamido yace "Wannan SHAK'UWA taku tayi yawa, a dai dinga ragewa ake tunawa Hafsat ta girma ba k'aramar baby bace infact tama fika samun experience na rayuwa tunda tayi aure kai kuwa bakayi ba...."
Banda watsa wa Lamido mugun kallo babu abinda Siraj keyi... Baida lokacin tsayawa amsa masa gajeren tsaki kawai yayi had'i da d'aukan car keys d'insa ya fice daga cikin rumfar...
A tare Ahidjo da Lamid'o suka mik'e suka take bayan abokin nasu.....
Suna tafe wayar Ahidjo ta soma vibrating daga wajen aikinsu ake kiransa dole ya wuce ofishin nasu yayinda Lamido da kuma Siraj suka nufi gidan Ahidjon domin duba Nana H, 'yar gaban goshin Uncle Siraj wanda a kullum kafawa abokinsa Ahidjo sharad'ai yake akanta, ba'a b'ata ranta, donma shi kansa Ahidjon bawai lokacinta yake dashi ba yafi baiwa aikinsa mahimmanci, sam basuma faye zama tare ba sunan anyi auren ne kawai...
***
*Misau*
A guje yauma ta shigo gidan tagajan bagajan... Innah Balki tana lafiya meke faruwa... Ai kafin ta ida fitowa daga d'aki ta hangi mutum saman rijiya sai tsalle take tana kururwa...
Babu shiri zani a hannu ta fito burut daga d'akin tana sallalami...
Iya Gaje ce ta shigo cikin gidan itama a d'ari tana fad'in "'Yar k'wal uba yau yankaki zanyi shegiya mai kamada mayu...."
Aiko Gaje tayi wajen rijiyan nan da d'aurin k'irji haka nan ta fito tun daga gidan nata...
Innah Balki banda salati bata komai sai rawa da jikinta keyi kaman an d'ana mata shokin ganin yanda Gaje ta biye k'aramar yarinyar da batafi sha hud'u ba suna kokawa jikin rijiya....
Innah Balki ta maza tayi ta rik'o yarinyar ta b'oyeta a bayanta yayinda Gaje taci gaba da sababi...
"Yau zaki bar min gida ehe, munafuka mai halin uwarta, tambad'add'iya kawai...."
A hasale Innah Balki ta soma fad'in "Ke Gaje ki sauk'ak'a harshenki kan 'yar marainiyar nan, ke ko tausayi bakiji... Shin wai bakida imani ne....?"
Bata kai aya ba Gaje dake binta da kallon wulak'anci tace "Toh uwar shisshigi da iyayi, banida ita, nace banida imanin anyi rabonta ina bacci.... Yo dole ma kice d'a na kowa ne mana sabida naki d'an ya fantama bariki... Ayyiriri ni Gaje naga salo... Toh wllhi Balki ki fice a hidiman gidana idan ba haka ba billahillazi zan maidaki abin kwatance a garin nan....."
Tunda ta soma magana Innah Bilki ke kallonta, girgiza kai kurum tayi tana mai bin Gaje da addu'o'i na shiriya....
Gaje ta gyara d'aurin k'irjinta ta dubi yarinyar tace "Dan ubanki zaki dawo gidan ki sameni ne...." Daga haka fuuu tayi ficewarta daga gidan....
Innah ta maido da dubnta ga yarinyar wacce har lokacin shan zuciya take kana ta dafa kanta tace "DEEJO mai kika mata yau kuma? Ba na hanaki rashinji ba..?"
Bakin d'amaranta ta kamo tana sharen hawayenta take fad'in "Innah waifa kawai don wannan Ladon mai kid'a a dandali yace na kai mai fura d'akinsa ya saya ban kaiba shine fah tayita dukata wai na mata asara..."
Innah ta shiga sallalami tana tafe hannaye cikeda mamakin bak'in zuciya irinta Gaje, Allah sarki tausayi Deejo ya kuma cika zuciyarta, Deejo k'aramar yarinya ce wacce kamata yayi ace tana makaranta bama tallaba, amma gaba d'aya Gaje ta tauye rayuwar wannan yarinya, sannan nema ma take ta d'aurata kan wata mummunar rayuwa, tabbas d'a na kowa ne idan ta taimaki Deejo watak'ila Allah yaji k'anta ya karkato mata da hankalin nata d'an zuwa gida......
***
Sosai Nadiya taji manikin ganin Nana H a gidansu, don irin d'iban albarkan da tayi mata a while ago kan Kawunta bata tsammaci zata kuma iya mata koda kallon mutunci bane, sai gashi kuma wai hak'uri tazo bata har tana neman su zamto k'awaye....
"I'm sorry for being bit emotional.... Aunty Nadynmu kiyi hak'uri da Nana H, kowa da kika gani a gidanmu wllhi hak'uri suke dani, kinsan ina son Uncle Siraj sosai kuma inaji dashi, so duk wata mace sai naga kaman rabamu dashi zatayi....." Ta k'arashe tana sipping laccasera juice d'in da aka serving d'inta a cup, k'afafun nan kuwa d'aya bisa d'aya.... Ga wani tayani gantalin gyale wanda ake kira kafi rariya shi ta d'aura bisa kafad'anta, yatsunta kuwa kama daga na hannun zuwa na k'afa duk sunsha kwalliya da faratan roba, tamkar ba d'iyar musulmai ba balle kayi tunani wai har aure gareta....
Nadiya ta d'an murmusa kana tace "Babu komai Nana Hafsat na fahimceki kuma na hak'ura komai ya wuce insha Allah...."
Murmushi Nana H tayi had'i da matsowa kusan Nadiya tayi hugging d'inta tana mai bayyana murnanta...
Daga haka hira sosai ya b'arke tsakanin Nadiya da Nana H har saida taga kiran Uncle d'inta Siraj na shigo mata, nan ta nunawa Nadiya fuskar wayar taga mai kiran nata yanda aka rubuta _Uncle luv_
Da murnanta ta d'aga don ta sanar dashi gata gidansu Nadiya kuma ta fixing komai....
Siraj yaji dad'in hakan sosai, don yasan yanda baison b'acin ran Nana H haka itama bata k'aunar b'acin ransa.... Lamido da ya kanne idanu had'i da kafe Siraj dashi sai faman sak'awa da warwarewa yake...
Suna rabuwa da Siraj gidansa ya wuce yanda ya jera wasu pictures wanda akayi crossing d'insu da jan marker alamun an gama dasu...
Had'e kansa yayi waje guda yana wasa da zoben hannunsa saman hotunan.......
***
Ayiya da Nana A ne zaune a parlorn suna kallon tashan abin dariya cikin raha da jin dad'i.... Kaman daga sama sai ganin Hafsat da Siraj sukayi sun shigo cikin gidan mak'ale da juna...
Nan da nan Ayiya ta had'e fuskar nan tamau don itakam tak'i jinin wannan Shak'uwa mai k'arfi dake tsakanin Siraj da Nana Hafsat....
Ammah dake sauk'owa daga bene murmushi ta sakar masu sanda ta hangi Siraj da Nana H na shigowa cikin parlorn kana tace "Inyye kaga 'yar gidan Kawu an shirya kenan...."
Nana H ta kuma shigewa cikin k'irjin Siraj tana wani murmushi take fad'in "Ammah kinsan bani son fushin Uncle luv yanzu ma daga gidansu Nadiya muke mun warware komai, tama riga ta zama k'awata..."
Ammah ta fad'ad'a murmushinta kana tace "Da kyau 'yar gidan Uncle haka nake son ji maza ku k'araso nayi serving d'inku dinner...."
Ko takan Ayiya da Nana Asma'u basu bi ba suka nufi wargajejen dining area d'in...
Asma'u ta d'ago idanunta da suka d'anyi rau-rau tana duban Ayiya, domin har cikin ranta wani sa'in takanji zafin banbanci da Kakarta da kuma Kawunta da suke nuna mata k'arara tsakaninta da 'yar uwarta.....
Cikin sauri Ayiya ta kamo hannunta tana girgiza mata kai alamun kada tayi kuka... A hankali Ayiya ta kamo hannunta tace "Tashi muje lokacin hutawarki tayi, a cire k'afar nan ki huta koh...."
Babu musu Asma'u ta shiga jinjina kai tana k'ok'arin dafa kujera domin mik'ewa....
Haka suka taho zasu wuce saman bene sai sannan Siraj ya kula dasu ya d'an bud'e murya yace "Nana A , sweetheart zo mana muci abinci...."
Daga yanda yayi maganan cikin nuna kulawa har cikin ranta Nana H bata so ba, amma gimtsewa kawai tayi tana ci gaba da cakalan fruits d'in dake gabanta...
Cikin sanyin muryarta had'i da murmushi saman fuskarta ta d'an kaikaito tana dubansu kana tace "A'a Uncle na riga naci abinci... You go ahead..."
"Come on sweetheart, zo ki zauna cikin 'yan uwanki mana, kar ki koma d'aki ke kad'ai..."
Caraf kaman jira take ta tari zancen da fad'in "Uncle luv ka k'yaleta kasan ta saba da zaman d'aki, ko tazo nan ma bazata saki jikinta ba....."
Ayiya data cika tayi fam kaman jira take nan ta soma sillesu tas...
"Toh bazata zaunan ba, data zauna yanda za'a muzanta ta a b'ata ranta gwara ta zauna ita kad'ai a d'aki... Ank'i ta zauna d'in.... Wuce mu tafi 'yar Albarka...."
Ko amsarsu bata tsaya sauraro ba ta janyo hannun Nana A suka wuce..
Nana H ta rakasu da hara had'i da jan tsaki....
***
Sunfi minti talatin suna zaune a train station d'in babu alamun jirgi ga yunwa da sanyi dake azalzalanta
"Ya Junaid nifa yunwa nakeji..." Ta fad'i tana kuma kwantar da kanta saman luggage d'insu...
D'an dubanta yayi yanda take hamma babu ko k'akk'autawa cikeda tausayinta...
Hoodie d'in dake bisa kansa ya kuma janyowa ya rufe fuskarsa sosai kafin ya nufi kujeran da ya hangi dangin snacks ajiye saman kujerun.....
*SameenaAleeyou... 📚*
[12/10, 10:06 PM] +234 810 044 6653: *FUSKA UKU*🏮
*03*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Yaran sam basu kula dashi ba har ya isa yanda snacks d'in suke ajiye bisa dogon kujeran, sai faman tsalle-tsallen su suke a wajen.... Ya jima yana duban yaran kafin ya janyo hoodie d'insa ya kuma rufe fuskar shi da shi.... Cikin azama ya kwashi snacks d'in dake nannad'e cikin tissue paper ya zura cikin rigar sanyin nasa....
Har ya soma waina tayar kekensa cikin sauri don barin wajen, kaman wanda aka ce ya tsaya, cak yayi birki ya tsaya tamkar wanda ya tuna wani abin, cikin sauri ya kuma juyo kan keken ya nufi yanda ya d'au abincin, kaman yanda ya d'auka haka ya bud'e rigarsa ya maidasu ma'ajinsu...