Sashe 55
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga d'aya b'angaren Baba Malam yace "Hafizu maza kazo gida ina nemanka, ina tsammanin Allah ya masa cikawa...."
Take Hafizu yaji jikinsa yayi sanyi k'alau lokaci guda ya jinjina kai yana mai amsawa da "Toh Baba..." Kafin ya isa Babur d'insa..
Bai ida hawa ba ya hangi Mairo tana fitowa da abin shimfid'a wanda suke zama bisa suyi karatun, tana sanye cikin dark blue hijab wanda ya fito da haskenta sosai....
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*42*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cak Hafiz ya tsaya yana duban Mairo ba tareda ya iya burka babur d'in ba, zuciyarsa tana mai ci gaba da bugu bai tab'a tsintar kansa cikin matsananciyar soyayyar wata mace ba sai akan Mairo, dama shid'in tun can mutum ne da bai shiga sabgan mutane, haka nan Allah yayisa da tsananin kunya kaman mace kai har yafi wasu matan ma, inama zai iya sanar da ita gyambon datajiwa zuciyarsa ko zai sami sassauci... Muryarta ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi...
"Malam badai tafiya zakayi ba, kayi hak'uri dan Allah abin hawa ne su Dakura basu samu da wuri ba kuma gasu nan tafe don yanzu haka da mukayi waya tace min sun samu, kayi hak'uri Malam bara na kawo maka ruwa..." Ta k'arashe tana shimfid'a darduman dake a hannunta
Tunda ta soma magana Hafiz ke dubanta, cikin sauri ya kauda idanunsa daga kanta gudun kada ta d'ago su had'a idanu ta fahimci mai yake ciki, take kuma ya tuna Baba ke kiransa da kuma abinda ya fad'i masa a waya....
D'an k'ak'aro murmushi yayi kana yace "Maryama baiwar Allah (Haka nan yake kiranta) kuyi hak'uri wllhi wani uziri ne mai girma ya taso daga gida, Baba yana buk'atata cikin gaggauwa kar ku damu yau kowa ya huta..." Ya k'arashe yana k'ok'arin yin key wa Babur d'insa...
Daddah da fitowarta kenan dama da k'yar ta mik'e donma Mairo ta b'oye tuwo tace babu mai ci sai an dawo daga karatu shiyasa ta mik'e ta fito karatun bai wai don taso ba... Ai jin Malam Hafiz yace yau babu karatu sai ta shiga washe baki tana fad'in "Yauwa Malam d'angari, wllhi yaron nan shiyasa fah kake burgeni, yo kwanya ma ai tana son hutu, jeka abinka zo na bud'e maka k'ofa..." Ta k'arashe tana tattare hijabinta had'i da hangame masa k'ofa...
Mairo dai duban Daddah kurum take tama hanata ta tambayi Hafiz ko lafiya Baba yake don taji yace wani babban uzuri ne ya taso... Kai Daddah bazata tab'a canzawa ba dai..... Yo Daddah kam ina ruwanta dad'i ya samu babu karatu harda taka rawarta...
Hafiz dai sadda kai kurum yayi ya fice cikin sauri yana mai addu'an Allah ya tashi kafad'un wannan bawa nasa....
Malam Hafiz na ficewa su Dakura suka iso, aiko ta hangi wulk'awan Babur d'insa cikin sauri ta k'araso haraban gidan ta baro Falmata na biyan mai adaidaita, nan ta tadda Mairo na linke dardumarsu ta zama...
"A'a Mairo ina Malam d'in ya tafi, kardai shid'in na gani na ficewa daga layin nan...."
Mairo ta jinjina kai sanda Daddah ke rangad'a mata kira daga cikin gida tana fad'in tazo ta basu tuwonsu idan ba horon yunwa zata masu ba...
D'an girgiza kai kurum tayi kana ta dubi Dakura tace "Wllhi wai wani uzuri ya taso masa daga gida, kinga mafa Malam na k'ok'ari k'ila d'an lokacin da yake zuwa hirarsa muke amfani da ita, wllhi yana mana k'ok'ari sosai..."
Dakura ta d'anyi jim kana tace "Amma kinaga Malam Hafiz anya nada budurwa kingafa ko kallon mata bai iyawa...."
Tak'aitaccen dariya Mairo tayi tana buge darduman bayan ta linke kana tace "Toh kodai kina ciki ne kam da har kika iya gano hakan...."
Murmusawa Dakura tayi tana mai bin Mairo da kallo kana tace "Kyaji dai dashi ni bara na k'arasa wajen Daddah ta tace min kutittiriya muyi fad'a..."
Isowar Falmata kenan take fad'in "Wllhi kuwa Mairo idan tayi tsami zamuji, kullum ko a gida zancen kenan Malam Hafiz, kinsan ma ranar ashe har recording karatunsa tayi sanda yake mana k'ari...."
Mairo mai zatayi banda dariya... Tafewa sukayi itada Falmata suna dariya suke fad'in "Ashe dai ustaz yayi kasuwa...."
"Kanku dai akeji...." Cewar Dakura kana ta shige ta barsu suna ci gaba da kwasan dariya...
***
Hafiz na shigowa d'akin ya hangi Mamarsa Yaya Azumi da kuma mahaifinsa Baba Malam kan mutumin da ya tsinta cikin kwalbati sati biyu da suka shud'e a hanyarsa ta dawowa gida...
Yaya Azumi tanakan murza wani ganye a hannunta Baba Malam na shafe goshin maras lafiyar dashi, dashike Yaya Azumi likitan gargajiya ce, Allah ya mata baiwan sanin magunguna da dama....
Cikin sauri ya k'arasa shigowa d'akin yana kai hannu jikin maras lafiyan yake fad'in "Baba da gaske ya cika....?"
Girgiza kai Baba Malam yayi kana yace "A zatona ya cika sanda naga jikinsa na mimmik'ewa amma sanda mahaifiyarka tazo ta tabbatar min da sauran ransa bai cika ba.... Hafizu idan muka bar wannan bawan Allah a nan ba tareda kulawan asibiti ba zai iya mutuwa, tabbas mahaifiyarka na iyaka k'ok'arinta amma jikin nasa tsanani yake kumayi, ace yau sati biyu idanunsa na rufe baisan yanda yake ba, inaga gwara mu nemi taimakon asibiti..."
Jinjina kai Yaya Azumi tayi kana tace "Mahaifinka yayi gaskiya Hafizu asibiti shine kawai taimakon da zamu k'arasa masa....."
Girgiza kai Hafiz yayi cikeda tashin hankali kana yace "Baba ku gane, yanzu lokacine da muke ciki na tsananin tsaro, haka kurum baza'a karb'i mutumin nan a asibiti ba sai da rahoto daga jami'an tsaro, idan muka kaisa mu kuma zamu jefa kawunanmu ne cikin had'ari don za'ace dole mu fad'i waye ya masa haka, kundai san yanda yanayin garin yake ....." Ya k'arashe damuwa fal fuskarsa...
Jinjina kai Baba Malam yayi kana yace "Kuma fah tabbas ka fad'i gaskiya Hafiz musamman idan akayi la'akari da kamala ta addini da mukedashi, tabbas wani ma ya samu hanyar mana cune.... Amma Hafizu bazamu barsa haka nan ba, wannan bawan Allah ban zaci zai kawo war haka a raye ba, tabbas Allah shi yasan dalilin da yasa ya bar wannan bawa nasa a raye.... Hafizu dole muyi wani abun, Allah kad'ai yasan dalilin da yasa mutumin nan ya fad'o hannunmu...."
Jinjina kai Hafiz yayi kana yace "Haka ne Baba...!" Shiru ya d'an ratsa tsakani ko wannensu yana tunanin mafita, lokaci guda Hafiz ya tuna da abokinsa Sahal wanda sukayi collage tare kafin Sahal ya tafi jami'ar Maiduguri ya karanti likitanci, a halin yanzu Sahal babban likita ne a babban asibitin Damaturu.....
Cikin sauri Hafiz ya soma murmushi yana hamdala yayinda Baba Malam da Yaya Azumi suka bisa da kallo suna jiran suji menene ya tuna....
"Baba Mama mun samu mafita da yardar Allah, ai kun tuna Sahal abokina da muka fara Kwaleji tare...."
A tare suka jinjina kai Mama Azumi tana fad'in "Tabbas aiko kwanaki ma yazo nan ya gaisheni...."
Hafiz yaci gaba da fad'in "Yanzu ai babban likita ne, zan kirasa yazo har gida mu tattauna matsalar idan ma shi zai kaisa asibitin kunga babu wanda zai zargemu... Ko ba haka ba...." Ya k'arashe yana dubansu gaba d'aya..
Murmusawa Baba Malam yayi had'ida bubbuga kafad'un Hafiz kana yace "Allah ya maka albarka Hafiz, hak'ika kai D'A NAGARI ne burin ko wasu iyaye, har kullum ina alfahari dakai, Allah ya maka albarka, Allah yasa ko bayan raina ka rayu akan wannan turba da kake bisa....."
Gaba d'aya murmusawa suke harda Yaya Azumi, har k'asar zuciyarta take jin dad'i idan taga tilon d'an nata da mijinta yanda mu'amala keda kyau da tsafta a tsakaninsu, tabbas iyaye masu kausasa harshe akan 'ya'ayansu suke jefa 'ya'yan nasu cikin fitintinu na rayuwa wani sa'in... Allah ka ganar damu iyaye mu zamto masu saka albarka cikin rayuwar d'iyoyinmu sabida su d'in kiwo ne Allah ya bamu kuma zaya tambayemu gameda yanda muka tarbiyantar dasu.....
Washe gari kuwa Dr Sahal ya amsa kiran Baba Malam cikeda girmamawa, Baba Malam ya masa bayanin komai da alfarmar da suke nema daga garesa....
Cikeda girmamawa Sahal yace "Haba Baba wllhi kun wuce ku nemi alfarma daga gareni, abubuwan alkhairi da kukayimin a baya a dalilin Hafiz bazan tab'a mantawa ba... Baba zanyi insha Allah, bayan haka taimako kukayi nidai d'aurawa kawai zanyi akai, Allah ya waita irinku a Al'umma...."
Ameen Baba ya amsa dashi yana murmusawa cikeda jin dad'i kana yace "Kaima Allah k'aro likitoci irinka Malam Sahal, mu shiga ka gansa....." Ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa Sahal yayi saurin taimaka masa kafin suka shiga d'akin a tare yanda wannan bawan Allah ke kwance tamkar gawa idanunsa a rufe ruf..... Cikin sauri Sahal ya k'arasa ya shiga 'yan dube-dubensa da wasu 'yan kayan aiki da yazo dasu....
Ya d'an jima yana dube duben kafin ya fito parlor ya taddasu gaba d'aya suka mik'e suna jiran ta cewar Dr Sahal...
D'an shafa goshinsa yayi kana yace "Zuciyarsa bata daina bugawa ba saidai yaji raunuka masu tsananin muni, ba iyaka wad'anda kuke gani a fili ba harda ciki wanda a turance muke kira internal injuries, sabida haka dole mu tafi asibiti sabida idan ba wani ikon Allah ba zuciyarsa tana gab da daina bugawa, zamu tafi asibiti yanzu, kar ku damu ni zanyi komai insha Allah...." Ya k'arashe yana mai kiran wani abokin aikin nasa yana mai sanar dashi a shirya d'akin tiyata.....
Godiya sosai su Baba suka dinga yima Dr Sahal, kafin Sahal da Hafiz suka ciccib'i mutumin suka fita dashi zuwa motar Sahal dake pake bakin lungun.....
***
Da sallama ya turo k'ofar office d'in nata murshi saman fuskarsa kafin ya d'an bubbuga k'ofar a hankali da zoben dake yatsar sa yana mai fad'in "May I...?"
Gyara zamanta tayi murmushi saman kyakkyawar fuskarta kana tace "Sure, please come in..."
Har ya shigo cikin office d'in murmushi bai bar saman fuskarsa ba, d'an gefe da ita ya paka wheelchair d'in nasa kana yace "Are you still working.... Haba Gorgeous ki daina stressing kanki da yawa please, ke duk wanda ya jima yana aiki kina biyansa overtime ke kuma babu mai biyanki fah, besides banson ganinki kina wahala sai naji kaman banida wani amfani....." Ya k'arashe yana mai kasheta da wani irin duba....