Sashe 12
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai haurawan da basuyiba kenan Ayiya ta dawo da baya ta nufi Nana H tana fad'in "Maimaita abinda kika ce dan uwarki... Fitsararriya shashasha wacce batasan darajan aure ba...."
Cikin sauri Nana A ta k'araso tana janye Ayiya yayinda Siraj ya mik'e cikeda b'acin rai yake duban Lamid'o kana yace "Na fad'a maka ka daina shiga sabgan wannan matar she's lunatic batada hankali....."
Baikai aya ba Ayiya ta katsesa da fad'in "Uwarka ce mahaukaciya ba niba kaji na fad'a maka, kuma na zame maku k'arfen k'afa a gidan nan zama dani dole, kuma ina numfashi baku isa k'untata 'yar Albarka ba... Asararru kawai...."
Tana kaiwa aya ta janyo Nana A dake zuban hawaye suka nufi sama...
Lamid'o dai shafa sumarsa yayi yana kallon show d'in lokaci guda yake zancen zuci shi kad'ai....
***
Suna shiga d'aki Nana A ta fincike hannunta cikin kuka take fad'in "Haba Ayiya haba meyasa zakiyi haka, kinsan banason a miki rashin kunya dan Allah idan don ni kike shiga hidiman Uncle da Nana H.. Dan Allah ki daina daga yau I beg of you please...." Ta k'arashe tana had'e hannayenta biyu waje guda alamun rok'o....
Banda harara babu abinda Ayiya ke aika mata, itakam tasha koyawa Nana A k'watan 'yanci tun tana k'arama amma abu ya faskara ta rasa wannan sanyin zuciya na Nana A tai yawa shiyasa 'yar uwar ke cutar da ita tun suna yara.... Bata tankata ba sai ficewa da tayi ta bar mata d'akin alamun itama tayi fushi.....
***
*Tambuwal*
Jin bugun k'ofa ya sanyasu tsame hannaye daga cin tuwon da suke a yanda suke d'in baje a tsakar gida....
Dadda ta mik'e tana tand'e hannu take fad'in "Kuyi zamanku barin duba wasu 'yan biyan bashin ne ke k'ok'arin karya mana k'yauren...."
*SameenaAleeyou📚*
[12/15, 12:10 PM] +234 810 044 6653: *FUSKA UKU*🏮
*09*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
"Waye...? Waye.... Waye mai buga mana k'ofa haka....?" Ta k'arashe tana tand'e ragowar miyar hannunta...
Tana bud'e k'ofar tayi arba dasu kusan biyar motarsu na pake gefe.... Baki sake Dadda ke dubansu kafin tace "Tohhhh! Ikon Allah bayin Allah lafiya...?" Ta tambaya tana gyara tsayuwarta jikin k'yauren...
"Baiwar Allah kin gane wad'annan..?" guda daga ciki ya tambaya yana nuna mata jami'ansu guda biyu wanda sukaji d'auri da bandage a jikinsu, ko ba'ace ba ta shaidasu jami'an hizbah ne da suka jibga bada jimawa ba.... Kafin Dadda tayi magana su Mairo da sukaji shiru suka k'araso d'aurin kallabi a gefen goshi suna fad'in "Wai yaya ne su waye ne....?"
Ai su Mairo suna isowa jami'an hizban nan suka b'oye bayan guda biyun....
Jami'i yace "Aiho wato kune hatsabiban kenan...."
"A'a a'a iya bakinka yaro kada ka kuma cema d'iyoyina hatsabibai ko a kotu ansan k'watan 'yanci ehe..... Dan haka kada ka kuma ce masu hatsabibai...." Dadda tace tana mai murje sauran miyar kukan hannunta da duka hannayenta biyu....
Kafin jami'in ya sami zarafin magana suka hango Oga da Mai Unguwa suna k'arasowa mai unguwa yana fad'in "Wllhi rankashi dad'e ni kaina.. Ni kaina na gaji da fitinan wad'annan mutane, ba'a sati bakaji sunyi fad'a da wani ba tun ina rabo har dai na gaji na daina nace kar wanda ya sake kawo min k'ararsu...."
Oga yace "Assha ai kaga tsiyan rik'on d'iya hannun mace kenan, haka nan zata tashi babu kwab'a...."
Oga bai kai aya ba Dadda ta katsesa da fad'in "K'aryarka wllhi ni nan da kake gani nafi maza dubu iya kula da d'iya, yo wasu shegun mazan masu guduwa su bar matan da d'awainiyar yaransu nawa ankayi hakan... Inyi..? Kawai don anga mutum na rufawa kansa asiri bai tambayi kowa a unguwa ba sai a nemi a saka masa idanu... Toh wllhi bazan d'auka ba ehe...." Ta k'arashe tana girgiza...
Mai Unguwa ya Kalli Ogan hizbah yana girgiza kai kurum alamun ka gani koh....
Oga kam tunda ya d'aura idanu kan kyakkyawar Fuskar Mairo wanda k'wan wuta ya haske ta kuma yin haske gaba d'aya ya kasa d'aga idanunsa daga kan Mairo, gaba d'aya jikin Oga sai yayi sanyi...
Mairo na girgiza take fad'in "Idan fah bazasu watse a nan ba wllhi Baba Mai Unguwa saidai kayi hak'uri don zamu watsar dasu..." Ta k'arashe tana kuma turo kallabinta gaban goshi...
Mai Unguwa zai soma masifa Oga yayi saurin dakatar dashi da fad'in "A'a a'a rankashi dad'e wato abi abun nan a sannu... Na lura akwai rashin fahimta a lamarin, kuma tunda nan ba gidan magajiya bace tabbas bai kamata a shigar masu huruminsu ba tareda sun bada izini ba, su Munkaila sune masu laifi da basuyi bincike ba kan lamarin...."
Tunda ya soma magana Dadda ke dubansa baki sake tana mamakin yanda ya d'auki b'angarensu lokaci guda....
Oga yaci gaba da fad'in "Wato ainihin Hajiya kuyi hak'uri da abinda ya faru, kuma insha Allah zamu hukunta jami'anmu sabida ni a tunanina da gaske gidan karuwai ne kuma tabbas ko Mai Unguwa da kansa yayi shaidan ba'a ganin maza a gidanki toh kinga kuwa tabbas an shiga huruminki... Kiyi hak'uri, idan nasiha sukayi niyyan maku ba ta nan zasu soma ba, tabbas anyi kuskure kiyi hak'uri Hajiya..."
Dadda ta yatsina fuska kana tace "Yauwa gara da Allah yasa kakeda fahimta, kuma kai Mai Unguwa tunda na hanaka auren d'iyata shikenan kaima ka saka mana karan tsana... Ko ba haka bane....?" Ta k'arashe tana duban Mai Unguwa da ya daburce lokaci guda yana fad'in "A'a nidai... Ni kuma....."
"Rufe mana baki har zaka wani ce goyon d'iya mace hannun mace had'ari ne... Toh Mairamu k'walelenka nan gani nan bari akwatin maye Dutsen Arfa sha kallo ehe....." Ta k'arashe tana gyara d'aurin zaninta...
Oga dai hak'uri ya kuma baiwasu Dadda sannan yace za'a d'au mataki kansu Malam Balarabe da jami'ansu da suka taka doka wacce shari'a ta kafa shiga hurumin da ba'a aikesu ba....
****
Sai wajajen 11:00pm ta dawo gidan babu ko mayafi a jikinta sai wani matsettsen skirt wanda yasha tsagu tun daga gwiwarta har k'asa, sam bazakace matar aure bace, ga uwar dogon takalmi tamkar ta kifa k'asa..
Da fallinta ta shigo gidan tana k'walla masa kira take fad'in "Sweet are you home....?"
Birki tayi ganinsa zaune a parlor ya had'e hannayensa biyu k'asar hab'arsa laptop ajiye gabansa..... K'uri ya mata yana kallon ikon Allah sam kaman ba matar aure ba tabbas abin nata ya soma damun sa....
K'arasowa tayi bayan ta kwab'e dogon takalmin nata ta zauna saman cinyarsa ta shiga zuba masa shagwab'a tana fad'in "Sweet I thought zaka joining d'inmu Dinner a gidan Ammah, ko baga text d'ina ba... And you know what...?" Ta d'anyi shiru tana dubansa yanda ya kanne idanu had'i da d'aga gira kurum sama yana dubanta.... Rungumesa tayi sosai had'i da d'ago masa car keys tana fad'in "Uncle luv ya bani motar sa.... Ka tayani godiya please...."
Ga mamakinta Ahidjo tureta yayi daga jikinsa bai tab'a mata hakan ba....
Nana H ta d'ago tana dubansa shaye da tsananin mamaki...
Babu alamun wasa a fuskarsa yake fad'in "A haka kika fita, a wannan shigar taki...?"
Girgiza kai take cikin rashin yarda da abinda kunnuwarta ke jiyo mata kana tace "Ban gane ba. Mai kake nufi....?"
Kallonta ya kuma yi had'i da tura laptop d'in dake bisa wooden table d'in gefe kana yace "No one ever told you how to dress up as a married woman.... Huh?"
Yatsina fuska tayi tana dubansa daga yanda yake zaune kafin ta sakar masa wata shu'uman murmushi tace "Oh Darling you should know by now that I don't follow rules.... Besides what's wrong with my clothes......?" Ta k'arashe tana dudduba jikinta tana juyi gabansa...
Ahidjo da abin ya kuma basa haushi mik'ewa tsaye yayi shima yana dubanta cikin b'acin rai yace "Oh really Hafsat... Are you asking me what's wrong with your clothes?... Take a look of your self.... Ki Kalli kanki wai ke matar aure a haka kika fita, mai yasa bazaki rink'a koyi da 'yar uwarki ba, itada batada aure ta fiki shiga irinta mutunci, ya kamata ki farga kisan mai kike ciki....."
Tunda ya soma magana take dubansa shaye da tsananin mamaki....
Cikin tsananin fushi itama take fad'in "Ka daina min shouting akai and yes this is me Ahidjo and therefore you have to accept me for what I am.... I don't particularly care what....."
Tsawan da ya daka mata ya sanyata had'iye maganarta.....
"Let me tell you this.... nan gidan auren ki ne ba gidanku da kika saba sangarci son ranki ba, for almost two years kin kasa banbance zamanin da bakida aure da kuma yanzun da kikeda aure, bazan kuma d'aukan iskancinki ba na fad'a maki... And you must.... You must obey my rules kin fahimta, sannan daga yau ban yarda ki kuma fita ba sai kin sanar dani.... Wawiya kawai wacce batasan meye aure ba...." Yana ida fad'in haka ya sungumi laptop d'insa ya haye sama yana watsa mata mugun aure....
Har ya haura sama Nana H bata rufe baki ba bata daina mamakin canzawan Ahidjo ba, shida a baya sabida wayewa irin nata na d'aya daga cikin abinda yasa ya fad'a soyayyarta amma wai shike cewa tayi lullub'i harma yana dangantata da wannan nakashesshiyar 'yar uwar tata,... Toh waima ta ina zata soma saka mayafi ai sai a kasa shaidata a mistaken d'inta da masakiyar 'yar uwarta... Kai ina never.. Tasan Ahidjo na masifan k'aunarta kurari kawai yake, kuma dole ta basa space na tsawon lokaci a gidan ta yanda sai ya gane kurensa ya bata hak'uri.... Ta kad'a kai had'i da d'aukan handbag d'inta ta nufi upstairs saida ta watsawa k'ofar d'akinsa harara kafin tayi shigewarta d'aki tana fad''i cikin zuciyarta... Kaine kad'aici zai kashe nikam inada irinka masu d'eben kewa.... Wani makirin dariya ta saki kafin ta turo k'ofar d'akin da k'arfin gaske ta rufe....
***
Safiyar ranar talata zaune suke cikin parlorn suna jiran fitowar Azeeza domin yauce ranar da Barr zai tafi da ita Laushi group domin nema mata gurbin aiki.....
Bugun k'irjin Barr ya k'aru sanda yayi tozali da Azeeza ta fito cikin doguwar riga 'yar Dubai kalan ruwan k'asa wanda ya amshi kalan fatarta ba fara ba sannan ba bak'a ba.... Tayi kyau har ta gaji, bai tab'a zaton Azeeza nada irin wannan kyau d'in ba sai yau....