← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 98

Sashe 47

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Junaid yana katse kiran Sabi'u idanunsa suka kad'a sukayi jazir, fatarsa tayi jazir.... Cikin wata irin murya yake furta "I'm back, and I'll take my revenge on each and everyone of you... I'm gonna make you suffer much more than I suffered before...." a hankali ya lumshe idanunsa fuskar Zeenat na masa gizo cikin idanunsa, sautin k'aranta kafin ta mutu na kuma karad'a cikin kunnuwarsa da kwanyarsa....

***

Hold up ne sosai ya tareta, ko motsawa motocin basayi banda k'aran horns babu abinda kake saurare da alama ma wata k'atuwar motace ta b'aci ta tare hanyar, gaba d'aya wajen ya zama very congusted... Banda tsaki babu abinda Nana H ke bugawa, ji take tamkar tayi tsuntsuwa ta tashi sama sai buga steering wheel take tana huci, gashi ta shige tsakiya babu hali ta fice dolema ta jira ayi clearing cunk'oson.... Cikin sauri ta zaro wayarta ta soma kiran Nasaar, bugu biyu ya d'aga tamkar jira yake ta kira nan ya soma fad'in "Nana H what's taking you too long.... Ya kamata ki iso by now before that bastard uncle of yours does something to Zeeza... Wllhi ya mata wani abu zan iya kashesa...."

Bai kai aya ba ta katsesa da fad'in "Shut up you idiot.. Mai ya hanaka binsu cikin hotel d'in, isn't she your responsibility..... you know you're such a jerk... And let me remind you this, wllhi wllhi wani abu ya samu Uncle d'ina you gonna hear it from me..."

Cikin sauri ya katse kiran had'i da buga tsaki... Gyara zamansa yayi cikin mota don bai tunanin zai iya tafiya baiga fitowarsu ba....

Bayan shud'ewan awa guda ya hangi motar Siraj ya fito daga Hilton.... Cikin sauri ya tada motarsa shima ya shiga bin bayansu...

Ga mamakin sa gidansu Siraj d'in yaga sun nufa.... Zuciyarsa taci gaba da masa zogi wato bai ishesu a hotel ba sai sun tafi har gida.... Da sauri ya kuma d'aukar wayarsa ya kira Nana H ya sanar da ita ta juyo gida sun nufi gidansu....

***

Kallon Siraj Azeeza tayi a karo na biyu kana tace "Nan kuma ina ka kawoni....?"

Ba tareda ya dubeta ba yace "Gidan in-laws d'inki.... Fito muje....."

Girgiza kai ta d'anyi kana tace "Sir nifa ba girlfriend d'inka bace, I'm your secretary don't forget...."

D'an murmusawa yayi da gefen bakinsa kana yace "Nima bance ke budurwata bace, as far as I know this also part of your job.... So mu shiga kafin ki b'ata ran Boss d'inki...."

Baki sake take dubansa, itakam bata tab'a ganin mutum irinsa ba, shi kuma nasa salon kenan, wai yafi k'arfin ya fito kai tsaye ya sanar da ita yana sonta ne saidai ta gani a actions d'insa ko mai... D'an tab'e baki tayi kana tasa kai ta bisa cikin gidan ganin zai tafi ya barta.....

Ammah da Ayiya na parlor suna d'an tab'a hira kafin a shiga sallan la'asar su tashi don already anyi kira.... Lokaci guda suka tsinkayo sallaman Siraj...

A tare suka amsa yayinda suka kuma jiyo sallaman wata budurwa dake biyeda Siraj d'in....

Ammah da Ayiya dai kallo suka shiga binsu dashi lokaci guda Ammah keyiwa Siraj barka da dawowa, had'ida yiwa budurwar sannu da zuwa, Ayiya kam baki sake take dubansu...

"Ammah barka da gida.... Azeeza taho ki zauna..." Ya k'arashe yana nuni ma Azeeza data zauna bisa kujera...

Azeeza kuwa kanta a k'asa ta k'arasa tana k'ok'arin zama bisa carpet take sannu wasu Ammah....

"A'ah a'a tashi ki zauna a sama please...." Ammah ta fad'i murmushi fal saman fuskarta...

Azeeza ma murmushin take tana kuma sunne fuska had'i da gyara mayafinta, bata zauna saman kujeran ba sai cewa tayi "A'a nan ma yayi Ammah...." Kaman yanda taji Siraj ya ambaci sunan Ammah haka itama ta ambata..

Zama tayi suka soma gaisawa kafin Siraj ya mik'e yana duba agogon hannunsa don yaji ana shiga sallah masallacin k'ofar gida....

"Barinje sallah naji ana shiga.... Ammah ga Azeeza zata gaisheku.." Ya k'atashe yana ficewa cikin sauri

Ammah baki har kunne take amsa Siraj d'in lokaci guda suka soma gaisawa, Ayiya ma da sakin fuska suka gaisa, lokaci guda Ayiya ta shiga rangad'a kira wa ma'aikatan kitchen kan kace mai an cika gaban Azeeza da kayan motsa baki.....

Dai-dai nan Nana A ta sauk'o daga upstairs tana tambayar ko muryar Uncle ta jiyo don tana bayi tana alwala....

Ammah ta mik'e tana kuma murmusawa take fad'iwa Azeeza ta saki jikinta kana tace da Nana A "Eh shine ya fita sallah amma, maza kizo ku gaisa ga bak'uwa ya kawo...."

Take annurin fuskar Nana A ya k'aru cikin d'an tafiyarta mai d'ingishi ta k'araso tanaiwa Azeeza sannu da zuwa.... Azeeza ta bita da kallon mamaki ganin tsananin kamannin da suke da Nana H saidai wannan fuskarta kalan saliha ce gata da faram-faram ba kaman Nana H ba....

Nan Nana A ta k'araso tana gaida Azeeza had'i da mata introducing kanta.... Ayiya ma mik'ewa tayi ta bar Nana A da Azeeza a parlorn.....

Sosai Nana A ta sake da Azeeza lokaci guda Azeeza taji mutanen gidansu Siraj sun kwanta mata, sunada mutunci da karamci, wato dai Nana H ce kawai batayo hali irin nasu ba... Take ta soma kokonton anya Siraj zai iya kashe rai, anya Yayanta Junaid ba kuskure yayi ba.....

Muryar Nana A ya katse ta sanda take fad'in "Mu haura sama kiyi sallah..."

D'an murmusawa Azeeza tayi kana tace "Banayi ne...."

Nana A tace "OK bara naje nayi yanzu zan sauk'o kinji... Dan Allah kici abinci kisha ruwa fa kinji, Uncle bazaiji dad'i ba idan yazo yaga bakici komai ba...." ta k'arashe cikeda raha..

Murmusawa Azeeza ma tayi kana tace "Kar ki damu zan sha....."

Har Nana A ta haura sama Azeeza bata daina binta da kallo ba tana murmushi, itakam mutanen sun matuk'ar burgeta....

Tana nan zaune Siraj ya shigo yana gyara hannun rigarsa... Take ta tsuke fuska ba tareda ta dubesa ba....

Murmusawa yayi kana ya zauna gefenta ya d'auki fork yana shan yankakkiyar watermelon d'in da aka kawo mata, lokaci guda yake fad'in "Ya suka barki ke kad'ai ina Nana A..."

Ba tareda ta dubesa ba tace "Sunje sallah...."

Siraj ya kuma dubanta kana yace "Yaya baki bisu sallahn ba...."

Harara ta galla masa ba tareda tace komai ba baki a ture....

Siraj ya kuma murmusawa da gefen bakinsa kana yace "Kodai bakiyi ne...." Ya k'arashe yana kuma d'aukan wani watermelon d'in had'i da kaiwa bakinsa...

Cikeda masifa take dubansa kafin tace "Ai kasan ni arniya ce...."

Wannan karan murmushi mai sauti ya d'anyi had'i da bud'e hannayensa yace "A'a ni bance ba, nasan yanayi ne yasa bakiyi ba.... So tell me kin sanar dasu Ammah wacece ke, kinsan ya kamata ku saba kafin ki shigo gidan... Oya bud'e bakin ki...."

Ya k'arashe yana mik'a mata fruit d'in da fork d'in hannunsa....

Kallonsa kurum tayi had'i da girgiza kai don dariya ma yaso bata...

Dai dai lokacin Nana H ta sako kai cikin parlorn... Wani irin bugu da k'irjinta yayi ganin yanda Siraj da Azeeza ke murmushi wa juna tamkar masoyan asali....

Cikin sauri ta katse su sanda ta bud'e murya tana fad'in "Uncle I didn't know you home already...." Ta k'arashe tana shigowa cikin parlorn...

Murmushi Siraj ya sakar mata kana yace "Nana H sweetheart k'araso mana,..."

Takowa take tana watsa wa Azeeza wani irin muguwar kallo yayinda Azeezar ma ta bita da kallon raini

"What's this woman doing here...?" Ta fad'i tana k'arasowa kusan Siraj....

Mik'ewa Siraj yayi yana dubanta kana yace "Nana H, Azeeza is my guest..."

Lokaci guda ta shiga hura hanci tana dubansa kana tace "I was at the company, naje nemanka aka ce min kun fita, sannan da na bi bayanka sai naga hotel kuka nufa Uncle... So uncle tell what is this woman dragging you into huh...?" Tayi tambayar tana zazzare idanu tamkar wacce zata rufesa da duka....

Duban mamaki kawai Siraj yake mata kana ya kasa yarda wai d'iyarsa ke masa irin wannan tuhumar.... Azeeza kam sabida tsaban mamaki ta kasa furta komai k'arara take hango soyayyar Siraj cikin idanun Nana H....

Lokaci guda Siraj ya kamo hannunta ya shiga janyota suka nufi k'ofa yana mai fad'in "You and I need to talk...."

Harara ta watsa wa Azeeza tana biye dashi kana tace "Yes Uncle..."

Suna fita haraban gidan ya kafeta da idanu cikin tsananin fushi da b'acin rai ya soma fad'in "Nana H what exactly is wrong with you... Just why are you like this.... Look I'm sick and tired of this attitude of yours kina jina.... Don na sake maki ba yana nufin na baki k'ofa bane ki raina ni, kisan irin kalaman da zasu ringa zuwa harshenki and especially a gaban mutane....!" Ya k'arashe idanuwansa sun firfito waje...

Itama cikin tsananin fushi take fad'in "But Uncle can't you see that girl is chasing you.... She loves you Uncle... For crying out loud open your eyes and see....!"

Girgiza kai kurum yake yana dubanta cikeda mamaki kana yace "And what's so wrong with that.... Laifi ne idan tana sona... How many times do I have to tell you this... Azeeza is my secretary she's my secretary nothing more nothing less, and yes we were at the hotel... I went there to attend to some clients...."

Idanunta ne suka d'anyi rau-rau kana tace "But Uncle I'm.... I'm just trying to protect you, Uncle Nadiya bata jima da rasuwa ba, I'm afraid you might suddenly fall into a relationship with her.... Uncle ka san matsalanka and bana son ganinka cikin k'unci I love you with all my heart Uncle, It hurts seeing you broken..." Ta k'arashe tamkar mai shirin yin kuka....

K'arasowa yayi ya d'an rik'o hannunta kana yace "Na fahimceki sweetheart but you also need to understand me.... I can't live like this forever, I also need someone by my side..." Bai kai aya ba tayi saurin katsesa da fad'in "That someone is me Uncle... You have me and I'll always be here for you, I promise...." Ta k'arashe tana shafa fuskarsa hawaye na gangaro mata...

Tinda Siraj yake da Nana H bai tab'a jin jikinsa yayi sanyi da lamarinta irin na yau ba... Gabansa sai dukan tara-tara yake.... Cikin sauri ya zame hannayenta daga fuskarsa kana yace "Muje ciki....."
Chapter 47 · 0% Book details