Sashe 39
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai sannan Azeeza ta d'ago had'i da sakin murmushi kana tace "Aww dama kece, kece Watchdog d'in tasa... Ya Allah wllhi bansan ke zai kira ba don ni ce min yayi zai kira watchdog d'insa don bazai barni na zaga city ni kad'ai ba.... Anyways since you here bari a firfito da kayan sai mu tafi koh...." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta kafin tayi alama wa masu kantin da su fito da kayyayakinta...
Nana H tamkar gunki haka ta tsaya cak tana duban Azeeza.... She couldn't believe it, wai ita ake kira watchdog....? kambala'in can, lallai Azeeza bata san da wacece take ba... Amma kam tabbas tayi na kud'inta watan cin uwarta ya kama, zata gane shayi ruwa ne, zata san ta tab'o Nana Hafsatou, zata san cewa no one messes with Nana Hetch.... Lokaci guda Nana H ta sakarwa Azeeza murmushi kana tace "Mu k'arasa banson holdup ya tare mu.."
Kallo Azeeza ta bita dashi had'ida yin k'wafa, murya a hankali ta furta "Da Azeeza kike zancen muje zuwa, da yanda duk kika zo min ina dai-dai dake....
Mamaki ba gama cika Nana H ba saida taga tulin kud'in da Siraj ya kashewa Azeeza.... Lallai wannan shegiyar ta tsafe Uncle amma dole tayi maganinta don ita batada boka batada Malam amma duk abinda ta saka a gaba toh fa sai tayi nasara...
Lokaci guda Nana H ta sake da Azeeza sai jefo mata fira take jifa-jifa, da sakin fuska tamkar ba Nana H ba, abun har mamaki ya baiwa Azeeza, saidai sam Azeeza bata yarda ta saki jiki da ita ba...
"Azeeza ya kamata mu zama k'awaye mu daina fad'a tinda naga da gaske Uncle love d'ina ya makance akanki...." Ta fad'i fuska d'aukeda mayaudarin murmushi, idanunta naga bisa kwalta...
Murmusawa Azeeza tayi had'ida maida komai ba komai ba kana tace "Ni dama ban k'ullaceki ba, kece dai baki fahimci wacece Azeeza ba, ni mutum ce mai sauk'in kai amma kuma maras d'aukan rainin hankali.."
Nana H ta kuma murmusawa sanda traffic light ya nuna masu koren wuta alamun an basu hannu kana taci gaba da fad'in "Ina muka nufa ne kam ban tambaya ba..."
"Citec muka nufa...." Azeeza ta bata amsa kai tsaye...
Lokaci guda Nana H ta d'auki hanyar unguwar tana mai ci gaba da jan Azeeza da fira.... Har gida Nana H ta ajiye Azeeza bayan sunyi exchanging phone number.... Nana H bata bar unguwar ba har saida taga gidan da Azeeza ta shige... Tayi murmushi tana dubanta kafin ta d'au wayarta ta shiga dialing layin Bash....
"Hello Bash wani aiki nake so ka min, mu had'u anjima banson b'ata lokaci...." Daga haka hanging wayar tayi tana mai murmusawa ita kad'ai, lokaci guda taja motarta ta bar unguwar...
Nana H na tafiya Azeeza ta lallab'a ta fito daga gidan data shiga sauri-sauri ta fice daga unguwar ta nemi cab ta shige......
***
"Hello Nazir ina jinka...." Lamid'o ya fad'i yana kuma k'asa-k'asa da murya... Nazir yaci gaba da fad'in "Ban jima da turo masa hotunan Mairo ba, kayi iyaka bincikenka da zakayi a d'akinsa na tabbata zaka samu..... Tabbas sunanta Mairo amma bansan dalilin da yasa wasu lokutan yake kiranta Nana Khadijah ba.... Na baka duk wasu information da ya kamata na baka, kayi a hankali kar Bulama yasan wannan zancen don wllhi kasheni zaiyi.... Yana son Mairo fiyeda komai na rayuwarsa...."
Lamid'o ya kuma shafa goshinsa kana yace "Kar ka damu bazai tab'a sanin komai ba... Na gode Nazir sai mun sake magana, sannan dan Allah ka sake komawa tashan mass ka ci gaba da binciken garin da su Mairo suka tafi, akwai reward mai girma da na tanadar maka..." Daga haka sallama sukayi Lamid'o ya kuma komawa cikin d'akin da sauri...
Ganin babu mahaifinsa a d'akin ya sanyasa shigewa yana ci gaba da binciken sunan da Nazir ya fad'a masa... NANA KHADIJA! sunan da yayita maimaitawa kenan yana tunanin yanda ya tab'a sanin mai sunan.... Wasu takardu ya zak'ule masu k'unshe da rubutu wanda ba sai ance maka masu mhaimmaci bane.... Lamid'o zuru yayi ma takardun yana juyasu sabida gaba d'aya a sile suke.... B'arka takardan da zaiyi yayi dai-dai da shigowar mahaifinsa, wani irin bugu k'irjinsa yayi lokaci guda ya saki takardun..... Nan suka watse k'asa.... K'irjin Lamid'o ya buga sanda yabi hotunan da suka watse k'asa da kallo... Shakka babu ta jikin hoton Fuskar Nana H da kuma Nana A ce da ita, idanma baka lura da kyau ba kai tsaye Nana H zaka ce sabida sunfi tsantsan kamanni harta murmushinsu iri d'aya ne, saidai kurum Nana H ta nunama wannan gogewar fata sabida hutu da kuma tsananin wayewa.... K'afafuwan Lamid'o suka soma karkarwa sanda ya durk'usa yana shafa hotunan, tabbas sai yanzu cikaton su Nana H ta fad'o masa, sunanta Nana Khadijah wacce suke kira da Nana K, kenan bata mutu, kenan tayi surviving accident d'in.... Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un.... Kalman dake yawo kenan cikin kwanyarsa... Mik'ewa tsaye da zaiyi yaji sauk'ar lafiyayyar mari a fuskar sa.....
Dafe da k'uncinsa ya d'ago yana duban mahaifinsa....
"Daddy.... Daddy who are you.... Tell me who you really are...!!!" maganganun da yaji bakinsa na furtawa kenan, sam baiji zafin marin ba ma.....
"Kayi kuskure Lamid'o da kayi tunanin wai zaka bincikeni ba tareda sanin ko ni waye ba.... Tabbas kaci nasaran gano wacece Mairo d'aya daga cikin 'yan uku masu fuska iri guda, amma ka sani gano Mairo bazai maka amfanin komai ba saidai ma jaza ma rayuwarka sabuwar rayuwar k'unci da ka kuma yi wanda bakayishi a baya ba..... Da sannu zaka san wanene Bulama...." Ya k'arashe kafurar murmushi saman fuskar sa...
Lamid'o na hawaye ya durk'usa saman gwiwoyinsa yana mai ci gaba da fad'in "Dan Allah Bulama ka sanar dani ko wanene kai wllhi jikina ya soma bani bakai ka haifeni ba, wllhi baka da d'igon imani da zaka raba yarinya da real family d'inta tsawon shekaru ashirin.... Dan Allah waye kai....?" Ya k'arashe hannayensa suna tsananin b'ari alamun rok'o...
Dariya Bulama ya kece dashi kafin ya buga k'ofar d'akin da sanadarsa, kan kace mai wasu k'arti majiya k'arfi sun shigo lokaci guda suka kame Lamid'o suka fice dashi... Kokawa ya shigayi dasu amma ina sarkin yawa yafi sarkin k'arfi inji hausawa, lokaci guda d'aya k'akk'arfan ya buga masa gwiwar hannunsa a k'asan wuyarsa.... Wani irin k'ara Lamid'o ya saki daga nan bai kuma sanin yanda kansa yake ba....
***
Azeeza na zaune itada Yayanta Junaid tana kora masa bayanin yanda sukayi da Siraj da kuma d'iyarsa Nana H wayar Junaid tayi k'ara ganin mai kiran ya sanyasa sakin murmushi kafin ya d'aga wayar
"Detective, kana k'ofar gidan... Shigo kawai babu matsala.."
Azeeza ta kallesa da mamaki kana tace "Yaya waye kuma Detective..?"
"Tashi ki shiga d'aki kuma kar ki fito sai ya tafi...." amsar da Junaid ya bata kenan...
A hankali ta mik'e ba tareda ta kuma cewa komai ba ta shige d'aki don tasan halin Yayan nata....
Tun daga bakin k'ofa Detective Sabi'u ke kallon Junaid idanunsa sun kad'a sunyi rau-rau.... Lokaci guda yake takowa a hankali har ya ida shigowa cikin parlorn....
Bakin sabi'u na rawa yake furta
"Junaid.... Haka suka maidaka? Junaid da gaske kaine saman wheelchair...?"
Lokaci guda idanun Junaid sukayi rau-rau, zazzafan murmushi saman fuskar Junaid ya k'arasa ya hugging k'afafun Sabi'u yana fad'in "Haka suka maidani Sab.... But I'm here... I'm here now with my vengeance...."
Sabi'u ya durk'usa suna fuskantar juna shida Junaid idanunsa sunyi jazur sanda yaci gaba da fad'in "Kar ka ragar wa ko d'aya daga cikinsu brother.... Kana tareda goyon bayana a koda yaushe...."
Junaid ya murmusa kana yace " Na gode Sab, thank you for always keeping me updated... Na gode da ka shiga rayuwar Ahidjo a dalilina...."
*SameenaAleeyou...📚**FUSKA UKU*🏮
*28*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Durk'usawa Sabi'u yayi hannayensa saman cinyoyin Junaid yake fad'in "You don't have to thank me for anything bro, kar ka mance irin abotan dake tsakaninmu kafin FUSKA UKU su bayyana cikin rayuwanka, har kullum zaka kasance d'an uwa a gareni Junaid.... So duk abinda nayi maka kaina nayiwa ka daina godiya please...." Ya k'arashe murmushi saman fuskar sa....
Junaid ya kuma murmusawa kafin suka hugging juna shida Sabi'u nan kuma suka soma firan yaushe rabo....
***
*Misau*
Kallo ya kunna masu a laptop d'insa movie d'in Avengas infinity world, lokaci guda yake mata bayani tinda yasan ba fahimtar yaren take ba.... Ga sanyi da ya kad'a sosai a garin... Ahidjo na hankalce da yanda ta tak'ure waje guda, murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarsa yake dubanta ga tsoron movie d'in da ya cikata sabida wasu irin hallittu dake ciki.... A hankali ya matso jikinta ba tareda yace da ita komai ba, lokaci guda yasa hannayensa ya kewayeta dasu had'i da shigar da ita cikin k'irjinsa.... Wani irin ajiyan zuciya ya saki shi kad'ai had'i da lumshe idanu, shi kad'ai yasan abinda yakeji gameda Deejoh....
Deejoh kam inaa bata ma san wainar da ake tuyawa ba an saki baki da hanci ana kallon movie.... Bata ankare da abinda mijin nata keyi ba saida taji wasu bak'in al'amra a tattareda ita, k'irjin Deejoh yayi wani irin bugawa hakan yayi dai-dai da wani abin tsoro da aka nuna a film d'in... K'ara ta saki had'i da k'ank'ame Ahidjo ga jikinta dake wani irin kyarma....
Shiko dad'a matseta yayi jikinsa yana fad'in "It's OK I got you.... Tsoro kike ji, na canza maki movie d'in....?" Yayi maganar cikin wata irin sakaltacciyar murya....
Girgiza masa kai Deejoh ta shiga yi k'irjinta naci gaba da bugu tama rasa yanda zatayi ta hanasa abinda yakeyi, tsoro da firgici sosai suka cikata hakan bai tab'a faruwa da ita ba.... Lokaci guda taji kuka na zuwa bakinta don tasan shine kawai abinda zata iya....
Cikin salo da dabara ya daina sabbin wasannin dake wanzuwa a tsakaninsun, A hankali ya eungumeta sosai cikin jikinsa yana lallashinta wanda tunda yake bai tab'a yin irin hakan ba, kukan da take masa sai ya kuma janyo hankalinsa sosai a gareta, bai tab'a sanin kukan mace nasa kaji wani abu gameda mace ba sai akan Deejoh, gaba d'aya sai ya wani saki jiki yana lallashinta yana sanar da ita matsayinsa a wajenta cikin dabara da salo wanda a baya idan akace zaiyi toh zai musa.... Gaba d'aya D'ansandan ya koma tamkar farar hula...