← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 98

Sashe 30

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammah ta shiga jinjina kai tana dubansa kana tace "Haka ne Siraj, abinda ka fad'i haka ne... And it breaks my heart seeing you like this babu aure.... Ka kai shekarun aure ko nace ka wuce, sannan ga girma da dukiya sun zauna maka, tabbas abinda ya ragi rayuwarka kenan iyali amma ka sani komai mukk'adari ne daga Allah. Kuma kowa da ka gani a duniyar nan da akwai ta yanda Allah zai jarabcesa... Wani ta fannin iyayensa, wani ta fannin auratayyarsa wani ta fannin kasuwancinsa... Kai ga su nan da dama... Koda za'ace kai kullum cikin farin ciki da jin dad'i kake babu tawaya ko nak'asu a duniyarka toh ka sani haka d'in ma jarabawa ce babba... Siraj wannnan jarabawarka ce a rayuwarka, kaci gaba da hak'uri har kaci jarabawarka, na tabbata addu'o'inmu bazasu fad'i k'asa banza ba.... Jikina yana bani ka kusa fita daga wannan k'angi na rayuwa.... Da izinin Allah...." Ta k'arashe murmushi kwance saman fuskarta...

Mik'ewa Siraj yayi ya isa ga mahaifiyarsa had'i da rungume kafad'unta daga yanda take zaune kana yace "I love you Ammah.... I love you so much....."

Ammah na murmushi ta mik'a hannu ta shafi sumarsa kana tace "Allah shi maka albarka.... Maza zauna ka k'arasa breakfast d'inka ka samu ka tafi aiki lokaci na k'urewa...."

Ya kuma murmusawa kana ya koma mazauninsa yana fad'in "Toh Ammah ta.... Nana A ta wuce Foundation koh....?" Ya tambaya sanda yake kai abinci bakinsa...

Ammah ma ta d'an gyara zamanta had'i da janyo plate d'inta gabanta tana fad'in "Wai ai wannan agogoce sarkin aiki, sam batako jin k'iwan fita dukda lalurarta, ai anything 7:30 ta bar gidan nan... Jiki na na bani zata zama babban jigo a rayuwan nakasassu da dama nan gaba.... Asma'u 'yar albarka ce...."

Murmushi kurum Siraj keyi kana yace "Shiyasa sai na nastu sosai na tantance irin mijin da ya kamata ya mallaketa sabida sanyin halinta da kyawawan d'abi'unta na gari bata cancanci namijin da zaizo daga baya yana goranta mata nakasun dake jikinta ba. .."

D'ago kai Ammah tayi tana dubansa kana tace "Babu wanda ya dace da ita sai Lamid'o... Sirajo, Lamido ya sami goyon bayana tinda yaron arziki ne , da zaran iyayensa sun dawo daga k'asar Amurkan kurum sai ayi bikin kuma jiya da dare munyi magana sosai da Nana A kuma na fahimci itama tana jin wani abu a tattare dashi... Dan Allah mu k'yaleta ta sami farin cikinta muddin ya tabbata shid'in ne.... Kaga babu wanda ya tab'a cewa yana sonta sai shi d'in...."

Siraj ya d'anyi shiru kana ya jinjina kai yace "Ammah bawai nak'i maki bane, na sani Lamid'o abokina ne koma nace d'an uwana ne amma ya kamata ya gane ba neman kai muke da Nana A ba... Aiko abubuwa da dama da nasan yanayi marassa kyau muddin ya tabbata min ya daina aikatasu ni daina zan d'auki Nana Asma'u na basa aurenta, amma.... Kawai dai I need more time Ammah.... Ki bar min komai a hannu na... Ni zan wuce office...." Ya k'arashe yana mai mik'ewa tsaye...

"Toh Babana Allah dai ya shige mana gaba... Baka tambayi 'yar rigimarka ba...?" Ta k'arashe cikin sigan zolaya...

Murmusawa yayi kana yace "Fushi take dani Ammah... Idan ta tashi a bacci zan kirata a waya...." Daga haka ya suri wayoyinsa da keys ya nufi k'ofa...

Ammah na murmushi ta rakasa da kallon k'auna kana tace "Toh a sauk'a lafiya Babana... Allah ya tsare...."

Ameen kurum Siraj ya amsa mata dashi yana mai k'ok'arin k'ara wayar salulansa dake faman ringing a kunnensa... Yana ficewa Ayiya ta take masa baya don taji tattaunawarsa da Ammah...

Yana k'ok'arin shiga mota ta kame marfin ta rik'e....

Cikin sauri ya dasa aya wa wayar nasa yana duban ikon Allah.. Wannan mata ta matsa masa da yawa...

"Lafiya...?" Ya tambaya yana dubanta

Ayiya ta gyara tsayuwarta kana tace "Lafiyan kenan.. Kana jina sarai naji kana son hana 'yar albarka aure sabida ku taru ku zama d'aya tinda kai ka kasa auruwa.... Kana jina... Wlhi wllhi baka isa ba, Sarki ya auri 'yar albarka an gama... Banda neman dalili ince abokin ka ne kuma da yanada wani hali mai muni da tuni ya bayyana mana, ai itama wancan 'yar gaban goshin naka abokinka ta aura mai yasa ita datace taji ta gani tana so baka hana ba sai Asma'u ce zaka hana ko? K'aramar danga mai dad'in tsallaka koh... Toh wllhi baka isa ba, idan kai aljana ta aureka ta hanaka aure toh alajni bai auri Asma'u ba... Aurenta da Sarki babu fashi ehe....!"

Tunda ta soma magana yake binta da kallon mamaki sam wannan matar fad'a bai mata wahala... Fuska a tamke ya furta "I don't have your time..." Lokaci guda ya shige motarsa ya barta nan tsaye tana ci gaba da sababi

Har ta komo cikin gidan bata daina sababiba koda Ammah ta tambayeta lafiya sai ce mata tayi Sirajo ne ya zageta tsaf da kalman nasara.... Sosai Ammah ta dinga dariya har saida taji tari na neman shak'eta kafin ta tsagaita dariyar tata abinka da asthmatic, tasan bazai wuce akan Nana A Siraj da Ayiya sukayi fad'a ba...

"Toh wai mai ya had'aku...?" Ammah ta tambaya

"Iyaka na masa kan maganar auren d'iyata da Sarki, bai isa ya hana ba... D'iyata zatayi aure insha Allahu don banida burin da ya wuce naga d'iyoyinta don nasan ita ba juya bace kaman su o'o masu Zeus asibiti a juye mahaifa wai sabida gayu...." Ta k'arashe tana gatsine da fuskarta ta b'angaren da Nana H ke sauk'owa daga bene...

Sarai Nana H tasan wannan habaicin da ita Ayiya take... Tab'e baki kawai tayi kana ta k'araso ga Ayiya tana tambayarta Uncle Siraj, ga dukkan alamun tashinta daga bacci kenan domin kuwa kayan baccin ne jikinta...

Nan Ammah ke sanar da ita ya fice.... Wani k'atutun bak'in ciki ya tokareta, yanzu duk yanda take fushi da Uncle Luv bai tsaya ya lallasheta ba yasa k'afa yayi ficewarsa... Aiko dole tabi bayansa taji dalili... Ko cin abincin batayi ba ta haura sama ta tsalo wanka ta nufi Laushi Group...

***

Ya jima mak'ale jikin k'ofar yana sauraren wayar da mahaifinsa keyi kafin ya sad'ad'o a hankali, a farfajiyan ya tarar da Ayuba ya d'an janyo hannunsa suka keb'e...

"Lafia rankashidad'e? " Ayuba ya tambaya tsoro bayyane saman fuskar sa....

"Ayuba ina fata baku sanar dashi na zo gidan nan ba...."

Jinjina kai Ayuba yayi kana yace "Rankashidad'e babu wanda ya sanar dashi kuma ko tambayarka baiyi ba, iyakaci dai ce masa mukayi an sami wayarsa cikin kujera... Domin wayar lambobi k'alilan ne cikinsu wanda nake tunanin tsirarun mutane ne yake kira.."

Lamid'o ya jinjina kai kana ya furta "Good, toh yanzu kasan abinda nake so dakai....?"

Ayuba ya jinjina kai alamun a'a "Sai ka fad'i rankashidad'e..."

Hannu Lamid'o yasa a pantpocket d'insa ya zaro kud'ad'en da bai k'irga ba 'yan d'ari biyar ya dunk'ulawa Ayuba a hannu kana yace "Wani aiki zaka min....."

Ayuba ya zaro idanu yana kallon Lamid'o da tulin kud'in da ya damk'a mar a hannu.....

***

*Laushi Group*

Da k'asaitarta ta shigo Kampanin duk yanda ta wuce kuwa sai ta kwashi gaisuwa, yau d'in a Nana H d'inta ta fito ko ita ko Azeeza, yau dole tayi sanadin aikin Azeeza kowa ya huta.....

Sai faman d'add'aga hanci take tana tafiyar izza tunda itama tanada kaso cikin kampanin.... Kai tsaye b'angaren president ta nufa wato Siraj Laushi....

Sai ka shiga wani rantsettsen parlor kafin ka tadda office d'in Siraj wanda sakatariyarsa ke zaune cikin kujeranta mai juyawa....

Tun daga cikin glass Azeeza ke hangota aiko ta saki murmushi domin kuwa tsaf ta gane ta.... A hankali ta furta "Duk wacce kika zo da ita zaki samu....

Ko sallama bataci darajanyi ba ta nufi main door d'in office d'in...

Azeeza bata ce mata k'ala ba sai murmushi da take...

Nana H taji k'ofa a gark'ame... A wulak'anci ta juyo tana duban Azeeza kana tace "Kee! Ina mai office d'in...?"

Yanda kasan tayi da dutse haka Azeeza ta mata banza taci gaba da sabganta...

Nana H tazo wuya, wai wannan yarinyar kanta guda kuwa... A fusace ta nufota had'i da buga table d'in tana fad'in "Ke are you deaf bakiji tambayar da nake maki ba...?"

Sai sannan Azeeza ta d'ago kai had'i da cire glasses fari k'al mai d'an girma wanda da gani na k'arin gayu ne kana ta d'an murmusa tace "And who are you....?"

Kambuuu ai Nana H sai ta saki baki tana kallon salon iskanci wai bata ganeta ba bayan jiya jiya suka had'u....

Murmushin rainin hankali Nana H tayi kana ta shiga nuna Azeeza da hannu tana fad'in "Bari kiji na fad'a maki you little brat, ni ba sa'arki bace kuma a yanzu naga dama wllhi aikin ki a kampanin ya zama tarihi shegiya 'yar matsiyata dama ance baku iya samun waje ba sai kun nuna yunwa, toh uncle yafi k'arfinki, k'aramar karuwa..."

Dariya mai d'an sauti Azeeza tayi kana tace "This suits you... Ai sai yanzu na ganeki da kika soma haushi... Gashi kuma kashh anyi rashin sa'a My Sir hutawa yake he already ordered me not to let anyone in... Kiyi hak'uri ki koma kya iya dawowa wani lokacin... Aww wait do you even have an appointment with him, ko kawai zuwa kikayi haka nan...?" Ta k'arashe tana maida glasses d'inta...

Nana H kasa gaskgata abinda take gani tayi, wai dai da gaske itace wata banza ke watsa wa magana a kampaninsu ofishin Uncle Love d'inta...

Tsaban b'acin rai har wani rawa jikinta keyi ta d'aga hannu zata kai wa Azeeza mari tana fad'in "How dare you....!!"

K'am Azeeza ta rik'e hannun Nana H tana wani irin murmushi take fad'in "Don't try... Don't you dare try this nonsense with me....."

Hannun Nana H bai bar b'ari ba take duban Azeeza cikin rashin yarda bata zaci shed'anan yarinyar yazo har nan ba...

Cikin sauri ta ciro wayarta daga jaka ta shiga dialing Uncle Luv, k'iris ya rage bata yarda wayar ba sabida yanda hannunta ke karkarwa... Saidai ga mamakinta ringing wayar taji a gabanta, aiko ta kai dubanta table d'in Azeeza taga wayar Siraj na faman ruri... K'walla ne kurum taji suna neman ciko idanunta saidai bazata iya kuka gaban wannan k'aramar 'yar iskar ba....
Chapter 30 · 0% Book details