Sashe 68
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nan gaba dai kar ki kuma barinta ta tafi sai taci abinci kinji koh..." Zaliha ta amsa tana mai gyad'a kai kana ta d'aurada zancen da Ma'ajuran tazo mata dashi nan suka shiga tattaunawa da Umma....
***
Shafa sumarta yake sanda tayi matashi saman k'irjinsa kana yaci gaba da fad'in "Waini yaya akayi aka barki kika fita baki gama iddan ba, mai kika ce masu...."
Tsaki ta buga don dama shi kansa Nasaar d'in maleji take yi dashi yanzu ta tabbatarwa kanta Ahidjo gwarzo ne a shimfid'a sannan samun kamansa zai mata wuya, ita sai yanzu ma take ganin tsan-tsan had'uwarsa, so tari takan tambayi kanta mai take nema ta rasa jikin Heedj da take ji sam bata k'aunarsa, wasu lokutan takan tambayi kanta amma sai ta rasa amsa, iyakacin abinda take iya tunawa shine duk sanda take kwance da Heedj bata hango fuskar kowa sai Uncle, duk duniyar nan shi kad'ai take muradin kasancewa dashi, wai shin shi baya jin haka daga gareta ne...? A duk sanda jikinta ya had'e dana Siraj takanji abubuwa masu rikirkita mata lissafi takanso shak'uwarsu ya wuce na wanda sukedashi a yanzu, wai shin duk mutumin da tun tasowarka bakada wajen zama sai jikinsa bakada wajen shagwab'a sai jikinsa wai shin haka ne ke faruwa dakai kokuwa dai itace kawai, wannan tunani sosai ya dameta, duk wasu manyan laifuka da take tapkawa ba sabida kowa bane sai don tsananin kishin Siraj da take ji bata tunanin abinda bai aikata da ita ba zata barsa ya aikata da wata macen.... Tabbas randa Uncle ya tareda wata mace zata iya rasa rayuwarta sabida tsananin kishi.... Muryar Nasaar ya kuma dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi...
"Wai bakiji mai nace maki bane... Yaya akayi suka barki kika fito...?"
Tsuka ta kuma yi a karo na biyu ta mik'e tana kiciniyar saka suturarta don ko Lamid'o ya fiye mata Nasaar babu had'i, cikin takaici take fad'in "Wai ni 'yarka ce da zaka tasa gaba kana min tambaya kaman wata k'aramar yarinya... Banson damuwa ka gane, ba matsalarka bace sanin yanda akayi na fito...."
Ganin tayi fushi ya sanyasa kuma rungumota yana bata hak'uri cikin kashe murya yana mai dad'a jadadda mata Azeeza ta fita daga rayuwar Siraj har abada...
Abinda ya d'an sanyaya zuciyarta kenan sanin cewa Azeeza bata tareda Uncle a halin yanzu wannan dalili yasa take d'an d'agawa Nasaar k'afafu don tasan ya mata k'ok'ari, na farko kawar da Ahidjo da yayi na biyu kuwa kawar mata da Azeeza da yayi wannan dalili kad'ai yasa bazata watsar da Nasaar ba.....
*Toh gareku masu sakewa da yayye kawunai da sauransu, ansan cewa muharram tab'a jikinsa ba haramun bane, amma komai yanada limit, don Allah musan yanda muke mu'amala da wad'anda suke a sunan muharamman mu, shi d'an Adam dama kad'an zai samu shed'an ya sami hanyar shigowa rayuwarsa yana mai raya masa wasu abubuwa, kar mu mance ibilis mak'iyinmu yayi alk'awarin zuwa mana ta sama ta k'asa ta gaba ta baya da kuma ko wace b'angare ba don komai ba sai don son ya b'atar damu... Wllhi wllhi mu kiyaye mu dinga kula da yaranmu da Ubangiji ya bamu amana, da yawa yayunsu ke lalata masu rayuwa, da yawa kawunansu ke lalalata masu rayuwa duk don dama guda da aka bada, mu kiyaye musan irin rayuwa mai tsafta da ya kamata mu gina iyalanmu bisa, kar muyi tunanin wayewa ne kaga k'atuwar budurwa ta haye jikin wani k'ato ta rungumesa yana d'agata sama yanai mata wasa shi a dole ga kawunta koh... Toh kawu kayi hattara ibilis mak'iyinka da wannan dama da aka baka zai cutar dakai... Muyi hattara don Allah mu kiyayi rayuwa irinta yahudu da nasara sam ba wayewa bace ba kuma birgewa bace... Allah sa mu dace ya azirtamu da zuri'a d'ayyiba.. Ameen thumma Ameen...!*
*SameenaAleeyou📚*
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*47*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*K'awayen arziki har kullum kuna raina, Halee Mekeke, Aysha B. Abdullahi (Shaby) Allah shi bar k'auna ya haskaka maku rayuwanku fiddunya wal akhira😍🤝🏼*
Kwance take hancinta rufe da tafin hannunta, turaren Ahidjo ne ta fesa a hannun tana shak'a, tunda ta soma laulayi bata son k'amshin komai sai na wannan turare, idan ta manne a hannicinta bata tunanin kowa sai na mijinta wanda har yanzu bata amince ya mutu ba, babu yanda Innah batayi da ita ta daina amfani da turare sabida takaba da take ciki amma ta kasa, kullum turaren cikin k'amshinsa take, Baffah ma yayi nasihan yayi lallashin yayi fad'an har ya gaji, Deejoh dai ta dage Yaya Ahidjo bai mutu ba, koda Innah ta d'auke turaren kuka tayita yi wanda har saida ya haifar mata da zazzab'i ga lalurar da take fama dashi dama, ala dole suka k'yaleta,...
Hawayen da suka zubo mata ta goge sanda ta tuna zuwansa, tun farkon had'uwarsu da kuma yanda tasan cewa shine mijinta, ta yaya ma zata yarda ya rasu, ita kawai bataji a jikinta ya rasu ba, da ace taga gawarsa k'ila da zata iya yarda ya rasu amma haka kurum azo ace mata wai ya rasu ita sam bazata yarda ba, zatayi ta jiransa har Allah ya dawo mata dashi... Tin daga cikin d'akin ta soma jiyo hayaniyar Gaje tana fad'in a fito a raba gado a basu kason d'iyarsu kuma dole ta d'auki Deejoh ta koma wajenta....
Innah a fujajan ta fito daga kitchen tana duban Gaje cikeda tsananin mamaki, Deejoh da 'yan hanjin cikinta suka kad'a cikin sauri ta mik'e tana goge ragowar hawayen idanunta, dukda juwa dake d'an d'ibanta bai hanata fitowa a daddafe ba....
Gaje idanu a tsafe babu kunya balle tsoron Allah cikin dashesshiyar muryarta taci gaba da fad'in "Balki idan kin sallama wa bariki d'anki ni ban sallama dukiyarsa wa k'adangarun bariki ba ehe, banda sakarci da dolanci kun wani zauna a nan kun k'yale dukiyar wa matarsa ta bariki taci itada iyalanta ni kuma tawa d'iyan fah taci mene, yanda wancan take matarsa haka Deejoh take matarsa, kaso guda za'a basu domin yanda wancan zatayi takabansa haka Deejoh ma zatayi, ki fad'i min a banza zatayi takaba ko k'ak'a inyi... Ke Deejoh zo nan mu tafi wllhi baki takabansa sai an baki kason ki na gado...." Ta k'arashe tana k'ok'arin janyo Deejoh da kukanta ya k'aru....
Sai sannan Innah tayi hobb'asa ta fincike hannun Deejoh daga rik'on da Gaje tai mata, cikin tsananin b'acin rai take fad'in "Koda wasa kada ki kuskura ki kuma kai hannunki jikin Deejoh, anya kinada zuciya a k'irjinki Gaje wani irin bak'in zuciya ne wannan idanma kinada shi, shin ko tausayin Deejoh bakiji har kina bud'e baki kina maganar gado, sanar dani nawa ne kasonki a cik...." Bata kai aya ba Gaje ta shiga gud'a tana tafe hannaye take fad'in "Da aka aurar wa d'an naku Deejoh ai ba sayar masa akayi ba balle kice Deejoh ta shiga gado sai yanda kukayi da ita... Kuma na fad'i na sake fad'i idan kinga Deejoh tayi takaban sallamemmen bariki toh kuwa shakka babu an damk'a min gadon Deejoh ne ehe...." Ta k'arashe tana kuma kai damk'awa Deejoh dake k'ok'arin b'oyewa bayan Innah, cikin tsananin kuka Deejoh ke fad'in "Innah Gaje dan Allah kiyi hak'uri kar ki tafi dani, wllhi mijina bai mutu ba, dan Allah kiyi hak'uri Allah zai dawo...."
Baki Gaje ta kame tana salallami take fad'in "Inyi lallai Deejoh wato har kinsan dad'in miji kike fad'in bai mutu ba zai dawo koh, toh ki bud'e kunnuwanki da kyau kijini, ya mutu a yawon bariki bazaki sake ganinsa ba 'yancinki da hakkinki nake nema maki dana ce bazakiyi takabansa ba sai an baki kasonki na gado...."
Cikin kuka Deejoh ke fad'in "Nidai bani son gadon dan Allah ki k'yaleni, Innah dan Allah kar ki bari ta tafi dani..." Ta k'arashe cikin shesshek'a tana mai kuma kamo hannayen Innar...
Tsananin mamakin hali irin na Gaje ya hana Innah furta koda kalma sai kallon mamaki kurum da take binta dashi.... Bata ida mamaki ba saida taga Gaje ta kwab'e mayafinta tana kokawan sunkutan Deejoh... Innah ta soma kiciniyar hanata inaaa Gaje ingarmiya ce bata wasa ba...
Deejoh kuwa tsamin hammatan Gaje shi ya d'ago mata aman da take ji na taso mata tun shigowar Gajen..
Kokawar d'aga Deejohn take a dai-dai sanda amai yazo ma Deejoh gadan-gadan, aiko kan kace mai sai a fuskar Gaje.... Ihu ta saki tana shafa fuskarta tana jin tsantsi-tsantin aman... "Wayyo na shiga uku, Deejoh ki rasa yanda zakiyi amai sai fuskata dan ubanki, fuskar da ta raineki tun kina ficika ita zaki wanke da amai.. Mai hanani cin uwarki yau babu shi..." Ta k'arashe tana goge fuskar nata cikin gaggawa...
Innah kuwa fad'i take "Wllhi kika tab'a lafiyar Deejoh yau saidai ayi jini biri, yau ne zan nuna maki ba'a dandali kurum ake buga wasan shad'i ba a gida ma anayi..."
Deejoh dai tsugune tayi tana k'arasa sauran amai d'in dai-dai sanda Malam yayi sallama ya hangi Innah na kokawan hana Gaje d'aukan Deejoh...
"Subhanallahi, Bilkisu lafiya? Meke faruwa a gidan...? Ki saketa nace Bilki..." Ya k'arashe yana mai ida shigowa cikin gidan...
Sakinta Innah tayi tana mai ci gaba da huci take fad'in "Malam wannan matar mahaukaciya ce sai an mata na mahaukata tukuna a zauna lafiya da ita..."
Ganin Baffah ya shigo ya sanya Deejoh guduwa bayansa cikin sauri tana mai ci gaba da kukanta take fad'in "Baffah kace ma iya Gaje Yaya Ahidjo bai mutu ba zai dawo ya d'aukeni, Baffah kar ka bari ta tafi dani kaji dan Allah..."
Mamaki ya cika Baffah yama rasa meke faruwa har saida Gaje ta ci gaba da balbala ruwan bala'i kafin ya fahimci ina ta dosa....
Cikeda b'acin rai ya katseta da fad'in "A ina kika tab'a jin mace mai takaba ta baro d'akin mijinta muddin tanada masu kula da ita da kuma lafiyarta, babu yanda zaki d'auketa ki tafi da ita, kuma ki fice min a gida kafin na kira maki hukuma su rabamu tinda ke kin raina kowa...."
Gaje tayi shewa tana mai ci gaba da watsa bak'ak'en maganganu tana fad'in bazata bar Deejoh gidan ba sai an bada kasonta na gado.... Ana cikin wannan drama Sabi'u yayi sallama gidan don yanzu ya zamto tamkar d'an gida kullum k'afafunsa na Misau, aka kuwa yi sa'a yau d'in kakinsa ne a jikinsa....