Sashe 73
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida Lamid'o ya kwashi wasu mintoci yana duban Siraj kafin ya girgiza kai yace "Bansanta ba hasalima ban tab'a ganinta ba, sannan a duk lokacin da zatayi magana dani takanyi amfani da na'ura mai sauya muryar bil adama... Kub'uta daga hannunta da nayi kuma da taimakon mahaifina ne wanda baiyi wata guda da dawowa daga k'asar United States ba, a lokacin da ya dawo matar ta nemi contact dashi tayi demanding huge amount of money kafin ta basa ni....."
A birkice Ammah ta mik'e tana fad'in "Ko nawa ne take so wllhi zamu bata ta dawo mana da Nana K... Dan Allah ta buk'aci komai daga hannun mu koda k'arshen abinda muka mallaka kenan, idan zata dawo mana da Nana Khadija wllhi zamu bata...."
Mik'ewa Siraj yayi yana mai duban Lamid'on kana yace "Zan binciko matar ko a ina take kuma zan dawo da Nana K...."
Ai baikai aya ba Nana H ta cafe shi cikin jikinta tana girgiza kai take fad'in "Uncle dan Allah kar ka soma kaji irin had'arin da matar kedashi kaga yanda ta kashe Heedj sanda ya tasamma binciko Nana K... Uncle you can't afford to lose you... We love you so much...." Ta k'arashe tana mai kamo fuskarsa had'i da saita gajiyayyun idanunta cikin nasa....
Tallafo fuskarta shima yayi yana mai dubanta yake fad'in "Hafsat it is my obligation.... Hafsat dole na ne na nemo 'yar uwarku yanda ta shiga ta fita muddin tana raye sannan wannan mata bazamu barta haka nan ba dole ta biya duk wasu laifin da ta aikata, bansan meye wannan family suka mata ba amma jikina na bani ta jima tana hunting d'inmu bacin haka babu dalilin da zaisa ta sace Nana K tun tana k'arama... Kiyi hak'uri kinji sweetheart idan na mutu a hanyar nemo 'yar uwarku ki sani haka Allah ya hukunta amma bazan zauna doing nothing ba..."
Wani irin kuka Nana H ta fashe dashi tana k'ank'ame Siraj take fad'in "Uncle wllhi bazan tab'a barinka ka tafi ba, haba haba kai baka tausayi na, dududu ko wata biyu banyi da rasa mijina ba kace kaima zaka bisa wllhi idan ka tafi sai na kashe kaina... Wllhi kashe kaina nima zanyi....." Ta k'arashe cikin tsananin kuka mai tada hankalin mai saurare....
Da k'yar Siraj ya iya lallashin Nana H kafin Lamid'o yaci gaba da fad'in "Siraj na yarda da Nana H a wannan wajen... Ba haka zamu tunk'ari wannan Al'amari ba... Kaman yanda Ammah tace muji nawa take buk'ata a bata ta dawo mana da Nana K sai a bata tinda ni a nawa tunanin don tayi dukiya ta saci Nana K....."
Shiru Siraj ya d'anyi na wasu lokuta kwanyarsa naci gaba da buga domin kuwa k'iris ya rage kwanyar tasa ta daina aiki sabida abubuwa da suka cika....
A hankali ya zauna saman sofa yana mai tattare naman goshinsa kana ya d'ago yana dubansu d'aya bayan d'aya....
"Shikenan yanda kuka ce, Lamid'o zamu nemi contact da matar mu negotiating muji meye take nema sannan bayan mun kub'utar da Nana K sai mu gurfanar da ita gaban hukuma ta fuskanci shari'a..."
Lamid'o ya jinjina kai kana yace "Hakan yayi Siraj, Allah ya taimake mu ya wuce mana gaba..."
Gaba d'aya hardasu Ammah suka amsa da ameen, gaba d'aya jikin Ammah yayi sanyi ita kad'qi tasan kalan tunanin da take cikin kwanyarta...
Lamid'o da Siraj ne suka soma ficewa yayinda Nana A ta janyo 'yar uwarta Nana H suka haye sama tana mai ci gaba da bata baki da kuma k'arfafa mata gwiwan cewa sun kusa had'uwa da 'yar uwarsu a duniyar nan wacce sukayi zaton bazasu sake ganinta har abada ba... Kalaman Nana A haushi kurum suke bata, don dai kawai bataso mutane su soma zarginta da wani abin ne.. Ta k'osa Nana A ta fice mata a d'aki ta kira Nasaar taji wacce irin dolanci ya aikata a ranar data turasa sa kashe Ahidjo...
Ammah ma Ayiya ce ta rakata har d'aki ta bata maganinta, lokaci guda ta sauk'o parlor tana sauk'e ajiyan zuciya... Ita kad'ai zuciyarta ke bugu domin kuwa ita kad'ai tasan kalolin tunani da suka cika mata kwanya... A hankali ta lumshe idanunta sanda ta tuna abubuwa da dama da suka faru a can shekarun baya....
A farfajiyan gidan suka tsaya, Siraj ya dubi Lamid'o kana yace "Toh wai yaya zamuyi da case d'in wancan yaron kuma.....?"
"Wani yaro kenan....?" Lamid'o ya tambaya...
Saida ya kuma tattare naman goshinsa sabida kansa dake tsananin sara masa kana yace "Yaron nan tsohon saurayin marigayiya Zeenat wanda mukayi zaton ya mutu sama da shekaru hud'u...."
Gaban Lamid'o ya kuma bugawa kafin ya d'an saita kansa yace "Shima nemansa zamuyi mu basa ko nawa ya buk'ata ya b'ace daga rayuwarmu... Na tabbata fansa ya dawo dashi.."
Siraj yayi shiru tamkar mai nazari kana yace "Idan kuwa yak'i ya negotiating damu zai iya fad'ima duniya abinda muka tassama yi masa, na tabbata family na sukaji haka zan iya rasasu gaba d'aya musamman Nana A da Ammah... Sannan yanzu ne suke tsananin buk'atata yanzu da Nana K ta tabbata bata mutu ba tana raye....."
Jinjina kai Lamid'o yayi yana mai duba agogon hannunsa kana yace "Haka ne Siraj zan wuce ni sai kaji daga gareni..."
Bai sami zarafin amsa sa ba sai jinjina masa kai kurum da yayi,... Yana nan tsaye yana kallon Lamid'o har ya shige motarsa ya tada ya fice daga gidan... A dole Siraj ya komo cikin gidan don su tattauna a nitse kan maganar Junaid shida Nana A....
***
Lamid'o na fitowa daga gidan guard d'in dake kwance bayar motar tamkar babu mutum ya mik'e had'ida saka masa bakin bindiga saitin k'eyarsa...
Gajeren tsaki yayi kana yace "Zaka iya barina nayi tuk'i cikin kwanciyar hankali ko kuwa....?"
Murya a dake mutumin yace "Sorry Sir, but I'm just following an order..."
Bai kuma cewa komai ba har saida suka iso gidan Alh Bulama wanda take underground....
Guard d'in nan na biye da Lamid'o har suka shige cikin gidan, aiko yana zaune a parlor da alama dawowar Lamid'on yake jira....
Murmushi maras rahama ne kwance saman fuskar Bulama sanda ya umarci Lamid'o ya fito da abin d'aukan magana da aka mak'ala masa cikin jikinsa... Babu musu Lamid'o ya shiga b'alle boturan rigarsa....
Take wasu guards d'in guda biyu suka shiga cire sellotape d'in da aka manne wani k'aramin recorder cikin jikin nasa...
Bulama ya kece da dariya sanda ya soma playing conversation d'in...
Banda uwar harara babu abinda Lamid'o ke aika masa....
D'agowa yayi yana duban Lamid'o kana yace "Na yarda kayi hankali, ka kuma yi duk yanda na umarceka bakayi tunanin cin amanata ba, amma wanene wannan yaron da yazo d'aukan fansa akanku, zanso saninsa..."
Cikin sauri Lamid'o ya katsesa da fad'in "Babu ruwanka, Laushi's ne a gabanka, babu ruwanka da wannan issue d'in, nayi maka aikinka burinka ya cika sunce zasu bada komai in exchange for Nana K, I'm pretty sure har kampanin zasu iya mallaka maka amma wllhi kar ka tab'a lafiyar kowa cikinsu much less Nana A...." Ya k'arashe yana tsananin huci...
Murmusawa Bulama ya kumayi kana yace "Baka gama aikin ka ba sai ranar da nayi gaba da gaba da Hajiya Mairo sannan ne zaka san makomar ka, inmma na mallaka maka Freedom d'inka ko kuma kaci gaba da zama k'ark'ashin iko na... Ku shigar dashi d'aki sai na buk'aci ku fito dashi..." Ya k'arashe yana duban guards d'in nasa... Tuni suka aiwatar da umarnin uban gidansu...
Lamid'o kuwa ba tareda an rirrik'esa ko an turasa ba ya shige don yasan hak'uri k'alilan zai k'ara shirin da yake na kub'utar da kansa da kowa nasa daga hannun wannan azzalumi ya kammala....
Mik'ewa yayi yana dogara sandarsa har ya fice daga parlorn.... Shi kad'ai yake murmushi yana tunanin ya gama d'aure Bintu babu wanda zai yarda ba sace Nana Khadija tayi ba... Zata jima a gidan yari kafin ta fice da wannan dama kuwa zai samu Mairo ta zama mallakinsa bayan ya gama da iyalan Mas'ud Laishi gaba d'aya... Ya kuma kecewa da dariya duniyar tanai masa dad'i Al'amra suna tafiya yanda yake so...
***
*Damaturu*
Yau dai har sallan magrib saida ya fita, haka yayita kallon mutane sanda ya gansa a sallan Jam'i, gani yake kaman shid'in bai tab'a shiga taron mutane irin haka ba, sosai abin ya burgesa ya kuma samun nutsuwa cikin zuciyarsa da ganin girman mahaliccinsa ganin d'inbin jama'ar dake masa sujjadah, Allahu akbar k'alilan ma ka gani daga cikin bayin Allah wanda a kullum suke sanya goshinsu a k'asa sabida bautawa Rabbil Izzah....
A haraban masallacin ya had'u da Hafiz yana shirin burka babur ya samu ya tafi wajen karatunsu can gidan Ummarsa ko nace Yayarsa Mariya...
"Malam Hafiz yau bazamuyi karatu ba kenan..." Ali ya tambaya murmushi kwance saman fuskarsa..
"A'a Yaya zamuyi amma idan na dawo, kasan nace maka akwai gidan wata Ummata da nake koyar dasu tsakanin magrib zuwa bayan lisha, jiya ma da mukayi karatun dakai ban samu naje masu bane don babur d'in babu mai..."
Ali ya jinjina kai tamkar mai tunani kana yace "Badai gidansu Mairo zakaje ba...."
Hafiz ya jinjina kai cikeda mamakin yanda Ali ya kama sunan Mairo sosai a bakinsa kana yace "Eh can na nufa...."
Ga mamakin Hafiz murmushi ya gani saman fuskar Ali kana yace "Dama na fad'a maka ina son zuwa nai mata godiya, idan babu matsala zan iya maka rakiya..?"
Murmushin Hafiz ya fad'ad'a kana yace "Da zaka zama d'an rakiyana ai da naji dad'i Yaya, dama nakan rasa abokin fira, kaga yanzu tinda kaji sauk'i na samu abokin rakiya.. Ni ne da godiya Yaya....."
Ali ya murmusa kumatunsa suka lotsa kana yace barin shiga gida na sanar da Mama kar ta nemeni..."
Cikin sauri Hafiz ya sauk'o daga babur d'in yana fad'in "A'a Yaya Ali gani nan kuma ai sai na shiga na sanar da ita...."
Nan ma murmushi kurum Alin yayi kana ya dafo kafad'un Hafiz suka nufi cikin gidan gwanin ban sha'awa..
Aiko saida Mama tayi kashediwa Hafiz kan cewa ya tafi da Babanta Ali a hankali ya kula da hanya...
Ali na murmushi yake fad'in "Mama Insha Allah zamu kiyaye...."