Sashe 74
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda suka zo fita daga gida saida Hafiz yayiwa Ali tunin addu'an fita daga gida da ya koya masa.. Aiko tiryan-tiryan ya karanto da alama kwanyarsa na saurin d'aukan abubuwa....
****
Zaune suke gaba d'ayansu a parlor suna jiran isowar Malamin nasu Mairo na tisa masu karatun da Malam Hafiz yace zai karb'a a daren yau d'in... Dakura sai k'ok'ari take taga ta iya domin kuwa zataso ta birge Malam Hafiz da k'wazonta... Daddah kuwa da k'yar aka kama aya biyu sai tik'i-tik'i ake, amma da alama ta soma son karatun itama, saidai fah tana jiyo sautin shirin nan da ake nunawa a gidan talabijin na Arewa24 mai taken Dad'in Kowa zata mik'e shikenan an gama karatun koda kuwa a gaban Malam Hafiz ne magana ne babu wanda ya isa yayi ta wanke mutum tass koma tayi zuciya tace ta gama karatun... Shiko Malam Hafiz tsananin kunyar Daddah yake amma bata ganewa, yo ita ina ruwanta ma shi yasan yana wani kunya, tsaf zata tsayar masa ya nemi tak'urawa rayuwarta....
Jiyo sallaman sallaman Hafiz da sukayi ya sanyasu dasa aya wa karatun nasu....
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*50*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Da rawar jikinta takai shimfid'ar tasu da suke zama bisa, ta kuma dawowa ta amshe kujeran Malam daga hannun Mairo ta kai masa... Duk wannan rawar k'afa da Dakura keyi Daddah na hankalce da ita, ita dama burinta Malam Hafiz ya fahimci yanada matsayi sosai cikin zuciyar Dakura domin bata fatan ya sauk'e idanunsa kan d'iyarta Mairo, don ta kula tsaf da take-taken nasa, muddin hasashenta ya tabbata toh kuwa shafawa zasuyi suji sun bar garin....
A haka yauma sukayi karatun su kaman kullum Malam Hafiz yau saida yasha mamakin yanda Daddah ta kawo masa ayoyi har guda biyar babu gargada, ga kuma Dakura ma tas ta kawo nata babu wani gargada... Hakan sosai ya masa dad'i shi kad'ai yakan saci kallon Mairo yayi murmushi domin yasan wannan aikinta ne... Bayan sun ida karatun ne Hafiz ya buk'aci Mairo da ta tsaya su d'anyi wata magana... Aiko tun kan yakai aya Daddah ta taka masa birki da fad'in "A'a a'a kuyita a gabana, ko menene naji da kunnuwana ehe...."
Mairo ta wurgawa Daddah wani kallo cikeda takaici... Aiko Daddah kam ko ajikinta taci gaba da fad'in "Eh toh gwara na sanar dashi gaskiyar lamari idanma cewa zaiyi yana sonki Dakura ta jima da fad'awa kogin k'aunarsa.. Aike kinsan da hakan idan ba kuma amanar k'awarki kike son ci ba...."
Daga Hafiz har Mairo baki sake suke duban Daddah....
"Mai ya kawo maganar cin amana kuma a nan... Daddah bakifa san maganar da zai fad'a min ba.. Kuma maiyasa zakiyi wa Dakura haka bazaki bari....." Daddah ce ta kuma katseta da fad'in "Yo kar na fad'i gaskiya... Kema kinsan bakina bayya shiru... Hafizu bawan Allah kaga kayi hak'uri amma ai gaskiya na fad'i, bai dace ka nemi Mairo ba bayan Dakura yarinyar nan tana mutuwar k'aunarka, kaga duk lemun kwalban da kakan sha ma gidan nan ita da kanta take sayo maka ai kaga bai kamata kak'ita ba.. A dai duba lamarin Malam Hafizu...." Ta k'arashe tana gyara mayafinta murmushi mai bayyana hak'wara saman fuskarta... Daddah kenan Daddah case ba ruwanta ta fad'i ya maka dad'i ko kar ya maka duk kai kaji wajen...
Malam Hafiz da jikinsa yayi sanyi sosai d'an gyara tsayuwarsa yayi kana yace "A'a Daddah dama ba wannan maganar zan mata ba... Aiko bak'on nan d'an uwana da kwanaki Mairo ta basa jini shine yace na rakosa yayi godiya domin ko ranar da kukaje sab'ani kukayi.... Yanzu haka yana waje yana jira dama cewa nayi ya jirani daga waje har mu kammala karatun..."
D'an murmusawa Daddah ta kumayi kana tace "Aiko dama bai damu ba domin kuwa Mairo dan Allah ta bashi jini.... Kuje kawai abinku basai yayi godiya ba..." Ta k'arashe tana goge hak'waranta da karan dalbajiya...
Tsananin mamaki ya hana Mairo furta koda kalma, ta sani Daddah nada k'arfin iko akanta amma bata sani ba ta soma jin akwai ranar da zata iya bijirewa umarninta muddin taci gaba da irin wannan hali...
Malam Hafiz ya d'an risina kana yace "Kiyi hak'uri Daddah shikenan zan fahimtar dashi..." Daga haka sallama ya masu ya nufi hanyar fita.... Mairo dake faman huci tana duban Daddah saurin takewa Malam Hafiz baya tayi ba tareda ta furtawa Daddah koda kalma ba...
Daddah ta hangame baki tana duban ikon Allah, duk kiran da take rangad'awa Mairo bata tsaya ba saida ta fice har bakin zaure yanda babur d'in Malam Hafiz ke pake....
"Malam dan Allah kayi hak'uri..." Ya sinkayo muryar Mairo daga bayansa tana fad'i...
Juyowa Hafiz yayi murmushi kwance saman fuskar sa kana yace "Babu komai Maryam... Da kinbi umarnin mahaifiyarki kin koma gida domin su iyaye bijirewa umarninsu babban had'ari ne, ko kin mance hadisin manzo sallallahu alaihu wa sallama wanda muka karanta jiya akan wanda yafi cancanta kayi kyakkyawan zama dashi... Mahaifiya tanada daraja har guda uku kafin mahaifi.. Ai kin tuna hadisin ko.. Sannan a Alqur'ani mai girma idan Allah yace a bauta masa shi kad'ai yakance iyaye kuma a kyautata masu.. Iyaye babban jigo ne a rayuwarmu wanda sab'a masu ka iya jefa mutum cikin hasara mai girma..."
Jinjina kai Mairo tayi cikeda rusunawa kana tace "Toh Malam insha Allah zan kiyaye., dama so nake na baka hak'uri dan banji dad'in abinda tai maka ba...."
Hafiz ya d'an murmusa kana yace "Haba Maryam idan da sabo ai na saba da halin Daddah ki daina damun kanki kinji koh.... Yauwa mu k'arasa Yaya na Ali ya maki godiya tinda kin fito...."
Fuskarta d'aukeda murmushi tace "Kai haba Malam saikace nayi wani abin, ba sai ya min godiya ba, ni fah dan Allah nayi, Allah ya k'ara masa lafiya...."
Malam Hafiz ya murmusa shauk'in k'aunarta na kuma d'ibansa saidai tunowa da maganganun Daddah ya sanyasa fad'uwar gaba, don shi harga Allah bai tab'a jin soyayyar Dakura cikin zuciyarsa ba hasalima tsakanin itada Falmata bazai iya banbancesu ba don shi ko iya kallon fuskokin d'aliban nasa bai iyawa tsananin kunya irin tasa.....
"Kinga ki sanarwa Umma Marie zamu zo gobe da safe insha Allah , hakan ma zaifi..."
Sam bata son jayyaya da Malamin nata, d'an murmushi ta kuma saki kana tace "Shikenan Malam zan sanar da ita, Allah shi bamu alkhairi." Daga haka juyawa tayi ta shige cikin gidan, yayinda Hafiz ya bita da kallo zuciyarsa na bugu... Wani irin soyayya yakewa Mairo wacce bai tab'a yin irinta ba tsawon rayuwarsa, Mairo ta had'a duk wasu qualities da yake so wajen d'iya mace.. A hankali ya lumshe idanunsa ya kuma bud'e su kafin ya k'arasa ma'jiyan babur d'in nasu
"Malam Hafiz yaya na ganka kai kad'ai... Ina Mairo....?"
Yanda Yaya Ali ya kama sunan Mairo saikace ya santa ko ya tab'a ganinta...
Hafiz dai murmushi kurum yake don yau d'in ya d'anyi dogon zance da Mairo, duban Yaya Ali yayi kana yace "Mairama baiwar Allah, cewa tayi basai ka mata godiya ba tsakani da Allah tayi..."
Cikin sauri Ali ya mik'e daga saman babur d'in kana yace "Amma Hafiz kasan yanda nake son ganinta, ko babu komai jininta ne a jikina yake aiki yanzu haka.... Ni a wajena ta cancanci godiya...."
K'uri Hafiz ya masa zuciyarsa na maimaita masa kalman _Jininta ne cikin jikina yake gudu_.... Baisan daliliba amma kalaman sun masa wani iri... K'ak'aro murmushi yayi kana yace "Tuba nake Yaya kar ka damu nace ta sanar dasu Umma gobe ido na ganin ido sai muzo mu gaidasu gaba d'aya...."
Ga tsananin mamakin Hafiz wani irin ajiyan zuciya yaji Yaya Ali ya sauk'e kana yace "Shikenan Allah ya kaimu goben ai yau da gobe duk d'aya ne....."
Hafiz ya amsa da ameen kafin ya tada masu Babur d'insu suka d'au hanyar gida...
***
*Abuja*
Mik'ewa tsaye Nasaar yayi yana mai duban Junaid d'in kana yace "So finally kayi ido hud'u da Siraj Laushi...."
Jinjina kai Junaid yayi a karo na biyu kana yace "And I'm pretty sure yana nemana yanzu haka.... Nasaar banida wani zab'i da ya wuce na bud'e Azeeza su ci gaba da soyayya da Siraj tinda ta zama weak point d'insa, kaga a ranar aurensu sai na masa abinda na tanadar masa, Siraj must not know Azeeza k'anwata ce ba, kai kuma zaka ci gaba acting as her only guardian.... In short zaka basa auren Azeeza cikin gaggawa..."
K'uri Nasaar yayiwa Junaid zuciyarsa naci gaba da bugawa, mai yake nufi, ta yaya zai iya baiwa Siraj auren Azeeza ba tareda zuciyarsa ta buga ba... Lallai kuwa a ranar auren daga Siraj har Junaid zasu nemi Azeeza su rasa, lokaci guda kuma plan d'in Junaid d'in ta masa dad'i don ta haka ne kurum zai iya mallakan Azeeza ba tareda d'ayansu ya sha gabansa ba.... Yaransa kuma bazai d'aukosu daga can gidan da yakaisu ake kula dasu ba sai bayan ya d'aurawa kansa aure da Azeeza idan yaso daga baya yaje ya d'aukosu Bulama kansa nemansa zaiyi ya rasa don kuwa barin k'asar zasuyi gaba d'aya...
"Baka ce komai ba...." Muryar Junaid ya kuma katse sa..
Cikin sauri ya saita kansa kana yace "Wannan shawari naka tai dai-dai Junaid, haka ne kurum zaisa ka d'auki fansar ka cikin sauk'i akan Siraj... Yanzu sai kasan yanda zaka shawo mana kan Azeeza ta amince...."
Junaid ya jinjina kai kana yace "Kar ka damu da wannan kai kam kurum kayi aikin da na saka ka, Azeeza won't be a problem nasan yanda zanyi da ita...." Daga haka bai jira cewar Nasaar d'in ba yaci gaba da gungura wheelchair d'insa lokaci guda wayar Nana A ke shigo masa..
Kallo Nasaar ya bisa dashi yana mai shafa hab'arsa shid'inma lokaci guda wayar Nana H ke shigo masa....
***
*Misau*
Duk firan da suke tana daga d'aki tana saurarensu, Kwad'ayin kifin bakin kwalta ne wanda jiya Baffah ya kawo mata ya addabeta, shi kawai take son ci har cikin ranta... Mik'ewa tayi ta fito waje yanda ta tadda Baffah da Innar... Sosai suke kula da ita musamman yanzu da take d'aukeda laluri....