← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 98

Sashe 87

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gumi Sabi'u ya dinga yarfewa yana tuna cewa gidan matar Ahidjo za'a turasa bincike, babban abinda yafi d'aga masa hankali shine baisan binkicen mai zai kaisa gidan ba.... Babban damuwarsa shine Deejoh, baya fatan matar Heedj tasan yanada wata matar acan gida, za'a sami matsala komai ka iya faruwa musamman da yanzu yakeji Deejoh ce cikaton rayuwarsa.... Abincin da Sabi'u bai iya ci ba kenan sabida sabon tashin hankali da ya tsunduma ciki....

***

A daren ranar ma mafarkin abu guda ya sakeyi tareda wannan mata, ga tsananin ciwon kai da ya addabesa wanda har saida ya haifar masa da zuban jini ta hanci, ba Hafiz kawai ba harta su Mama saida ciwon kan nasa ya basu tsoro da mamaki wannan karan.... Hafiz da kansa ya tafi ya d'auko Dr Sahal don tunda Ali ya fad'i sumamme bai kuma sanin yanda kansa yake ba.....

Dr Sahal yayi wasu 'yan gwaje gwajensa kafin ya tabbatar masu sauk'i ne ke samunsa cikin yardar Allah, wannan ciwon kai mai tsanani da yake yawan yi ba komai bane illa tunaninsa dake yunk'urin dawowa kwanyarsa da k'arfin gaske.... Magunguna Dr Sahal ya rubuta masa kafin ya umarci Hafiz da ya biyosa ya amshi magungunan...

Baba Malam yayiwa Sahal godiya kafin ya masa rakiya har bakin zaure suna masu ci gaba da tattauna lamarin....

***

A jikin motar suka hangi Yaya Sufyan na gogeta, alamun su yake jira, suna k'arasowa Zaliha ta sadda kanta k'asa tana gaidashi, haka kurum bata iya jure kallonsa batasan dalili ba, sosai k'wayan idanunsa ke firgitata, wani sa'in takanji dama drop suke zuwa kawai su shiga itakam da ya fiye mata, da sakin fuska kuwa ya amsa kaman kullum kafin ya bud'e masu motar suka shige Ma'ajura gwanar surutu tana zuba masu zance, daga Sufyan har Zaliha babu mai amsata, shikam Sufyan tunda Zalihan tazo garin zuciyarsa ta gaza samun sukuni, da ita yake kwana sannan yake kuma tashi saidai bai san ta yanda zai soma sanar da ita abinda ke cikin zuciyarsa ba, yasan halin k'anwarsa Ma'ajura idan ta riga ta sani toh fah shikenan ta sami lagonsa....

A b'angaren Zaliha kuwa banda fuskar Nana A da Mairo bata hango komai cikin k'wayar idanunta, gaba d'aya wannan tunani ya sanyata ta zamto wata sukuku da ita, tana so ta tambayi Nana A kodai tanada wata 'yar uwa Mairo k'ila ta sanar da ita wani abu gameda Mairon idan har 'yar uwarta ce domin wannan kanni tasu tai yawa tamkar mutum guda ne.... Da wannan tunani Sufyan ya diresu k'ofar foundation d'in ya kuma sanar da Ma'ajura idan sun gama su masa waya zai zo shi ya d'aukesu... Sosai Ma'ajura tayi mamakin canzawan Yayan nata domin a baya sam baya yarda ya d'auko ita idan dai ya kawota sai gashi yau har cewa yake su nemesa da zaran sun gama, take zuciyarta ta shiga hasasho mata wani abin, bata dai furta ba sai murmushi da tayi had'ida yiwa Yaya Sufyan godiya ta janyo hannun Zaliha da sam zuciyarta bai wajen suka nufi cikin foundation d'in....

Suna tafe Ma'ajura tana son shan cikinta taji ko tanada saurayi amma Zaliha bata responding, gaba d'aya tayi nisa uwa wata duniyar.... Cak Ma'ajura ta tsaya tana k'are mata kallo kana tace "Wai nikam meke damunki ne Zulu gaba d'aya kin zama wata iri haka nan... Meke damunki don Allah...?" Ta k'arashe cikeda kulawa

Sauk'e ajiyan zuciya Zaliha tayi tana mai duban Ma'ajura kana tace "Ma'ajura wllhi wani abu ke matuk'ar damuna, bansan ta yanda zan soma maki bayani ba...."

Jin haka yasa Ma'ajura murmusawa had'i da d'aga mata gira sama kana tace "Umhum kice kema kin kamu da soyayyar tasa kaman yanda ya kamu da taki...." Tayi maganar cikeda zolaya

Kallon mamaki kurum Zaliha ta bita dashi kana tace "Ban gane ba shi wa....?"

Ma'ajura ta kuma d'an darawa kana tace "Ahaf ai naga kallon da kuke wa juna ko ma menene tayi tsami maji...."

Girgiza kai kurum Zaliha tayi kana tace "Ke kikaji wajan..." Lokaci guda tasa kai zata wuce Ma'ajuran tayi saurin rik'ota tana murmushi take fad'in "Haba matan Yaya yi hak'uri ki sanar dani...."

Zaliha ta kuma narka mata harara...

Ma'ajura ta kuma saurin kame bakinta kana tace "K'awata yi hak'uri dan Allah ki sanar dani abinda ke damunki...."

Cikeda fad'a Zaliha tace "Ai naga bakida niyyan jin abinda zan fad'a maki ne...."

Ma'ajura na k'ok'arin k'unshe dariyarta take fad'in "Yi hak'uri ki fad'a min, bazan sake ba...."

Zaliha ta kuma watsa mata harara had'ida yin k'wafa... Can saman wasu kujeru suka zauna kafin Zaliha ta ciro wayarta cikin jaka ta shiga shafawa...

Ma'ajura dai k'uri ta mata tana jiran taga mai zata nuna mata cikin wayar...

Saida ta kai dai-dai kan hoton Mairo kafin ta tsaya lokaci guda ta nuna fuskar wayar ga Ma'ajura...

K'uri Ma'ajura tayiwa hoton kana ta d'ago da mamaki tana duban Zaliha "Ina kika sami hoton Nana A,... Ke tsaya wannan ai Nana H ce, dama kin santa ne....?"

Zalihan ma k'uri tayiwa Ma'ajuran kana ta girgiza kai tace "Wannan ba Madam bace, ba kuma wacce kika ambata bace Nana H, wannan sunanta Mairo...."

Da tsananin mamaki Ma'jura ke duban Zaliha kana ta d'an murmusa irin ta raina mata hankalin nan kana tace "Kai haba Zaliha wllhi zan iya rantse maki cewa wannan Nana H ce... Ai ni bansan kinsanta ba, yaya akayi har kika sami hotonta wannan mai jin kan bala'in... Tab...."

Har lokacin Zaliha bata daina duban Ma'ajuran ba kana ta d'an girgiza kai tace "Wllhi wllhi ba ita bace, wannan sunanta Mairo aminiyata ce da muka rabu a Tambuwal, idan kina kokonto kiyi gaba zakiga hotunanmu tare, itace sanadin wannan sana'a tawa domin ita ta koya min...."

Izuwa lokacin tsoro da mamaki ya cika Ma'ajura, ai kuwa tana yin gaba hotunansu ne wasu a tare su biyu, iko sai Allah, wannan babu abinda ya rabata da Nana H da kuma Nana A, kamanninsu guda, saidai kurum wayewa da samun hutu da zasu gwada ma wannan.... Idan aka ajiye maka su duka uku bazama ka iya kama sunan guda ba, duka FUSKA UKUN zaka iya basu sunan mutum guda... Tirk'ashi wannan kamanni da yawa yake...

Ma'ajura ta d'ago tana duban Zaliha kana tace "Kika ce sunanta Mairo..."

Jinjina kai Zaliha tayi kana taci gaba da fad'in"Shiyasa kikaga tinda naga wannan matar Nana A na rasa nutsuwata, wllhi Ma'ajura harta maganarsu yana yanayi, ni ban tab'a ganin masu kamanni irin tasu ba.. Ma'jura ba don nasan Mairo tanada mahaifiyarta mai tsananin k'aunarta ba da sai nace wannan k'ila su 'yan uku ne ba 'yan biyu ba....."

Ma'ajura ta jinjina kai cikeda tsananin mamaki kana tace "Ko ni kin sakani a duhu Zaliha, wllhi wannan batada maraba da Nana A da kuma Nana H, musamman Nana H don wannan ma tanada tsananin hasken fata kaman ta Nana H fiyedata Nana A..... Wannan shine ikon Allah... Kuma kika ce kin santa kin san mahaifiyarta... Anya Zaliha kodai 'yan ukun ne aka rabasu ko maybe tun suna yara.... Kinsan fa a asibiti ma ana satan yara...."

Shiru kurum Zaliha tayi tana duban Ma'ajura kana tace "Gaskiya Daddah tana k'aunar Mairo fiyeda komai na rayuwarta, bana jin satar ta tayi...."

Ma'ajura dai shiru kurum tayi tana kuma duban hotunan Mairo kaman yanda Zaliha ta sanar da ita sunanta wacce batada maraba da tagwayen data sani.... Haka kurum jikinta ke bata akwai wani b'oyeyyen Al'amari.....

***

*Damaturu*

Tafe suke suna dawowa daga center, Daddah da Kaltume sunyi gaba Kaltume naci gaba da labarta mata yanda sukayi da tsohon saurayinta dake neman sakawa rayuwarta takunkumi...

"Wllhi Daddarmu ina fad'a maki baki gansa ba, sumarsa kaman zaren kwakwa, yanda kika san an shanya shinkafa wai shi gaye, ni baisan yanzu bayan Malam Hafiz ba bana ganin kowa a gabana, ga salihi d'an gaye mai ilimi mai zanyi da wancan mai cubirin gashin, Allah ya sawak'e min...."

Tunda ta soma magana Daddah bata amsata ba... Sai kad'a kai kurum take tana tunanin abinda zarayiwa TJ saurayin Dakura, don itakam bata fatan abinda zai hana soyayyar Dakura da Malam Hafiz...

"Kika ce da yaushe yake zuwa....?"

"Kafin mu tafi islamiya zaki gansa sai warin wiwi yake...."

Daddah ta kuma gyad'a kai kana tace "Ince Yayanki Goni yana gida....?"

Dakura ta jinjina kai kana tace "Ai kullum Yaya Goni yana gida idan dai baida wajen zuwa...."

Daddah ta kuma yin k'wafa tace "Shikenan Allah ya kaimu anjima, zanzo gidan naku...."

Cikeda jin dad'i Dakura ta amsa da "Yawwa Daddarmu dama wllhi har maganar turowa yake, gwara kizo ki taka masa birki..."

Daddah tace "Ai taka birki kad'an ne injin gaba d'aya zan cire masa... Kedai ki k'yaleni kawai dashi idan yazo kar ki fita nice nan zan fita..."

Su Mairo da Falmata suna saurarensu sai dariya suke, Falmata tana ganin Daddah bazata iya abinda take fad'i ba yayinda Mairo tayi k'us abinta don tasan halin Daddah abinda ba'a aiketa bama tanayi balle wanda aka bata katin gayyata ai sai yanda manta ya tsaya, ita dai dad'in da taji yau idan Daddah ta tafi gidansu Dakura ita kuma da Umma Marie zasu samu suje gidan Baba Malam maganar mafarkan da take yawan yi, a 'yan kwanakin sun k'aru....

***

Zuciyarsa ta gaza sukuni, so yake ya ganta koda bazai mata magana ba, baisan dalilin da yasa zuciyarsa ta damu da son ganinta har haka ba.... Cikin sauri ya fice daga gidan ya nemi Cab ya shige.....

***

Wayar na mak'ale kunnen Lamid'o yake ci gaba da fad'in "Thank you Sadiq, ba damuwa zamu sake waya, idan ka shiga garin ka kirani kawai...." Daga haka saurin katse wayar yayi kafin ya kuma d'aga kansa sama ya tabbata babu camera a wajen kana ya fice cikin sauri....

Allah sarki Lamid'o da ace kasan idon fakara kayi wannan shuka da bakayita ba.... Gaba d'aga Bulama ya gama ganinsa kuma ya gama jin duk wani conversation da yayi cikin wayar, wata k'wan wuta ne a parlorn wanda sam bazakayi tunanin akwai camera jikinta ba....
Chapter 87 · 0% Book details