Sashe 19
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin Siraj na kuks shar-shar Lamid'o ya rik'osa yasa su fahimtar Nadiya babu.... Wani irin k'ara mahaifiyarta ta saki had'i da zubewa k'asa... A guje Nana H ta k'araso ga Siraj suka rungume juna suna kuka sosai...
Nana A kuwa juyawa tayi ga Ayiya ta rungume tana kuka sosai itama...
Kallo Lamid'o yabi Nana A dashi wani irin al'amari yake ji gameda ita, bai tab'a jin hakan ga wata d'iya mace ba... Ji yake kaman ya k'arasa ya rungumeta cikin jikinsa sabida har cikin ransa yake jin zafin kukan nata... Shin mai ke shirin faruwa dashi? Shin son Nana A yake ko me.....? K'aran da wayarsa yayi ya sanyasa dawowa hayyacin sa....
Ganin mai kira ya sanyasa ficewa daga wajen domin amsa kiran....
***
*Misau*
Zaune suke gaba d'aya a fadar Mai Unguwan ana maida bayani... Mai Unguwa yaji komai kuma ya gamsu da komai domin ciwon dake jikin Deejo kawai ya isa shaida Gaje bata isa ta musa cewa bata musgunawa Deejoh ba..... Mai Unguwa iyaka yayi wa Gaje tsakaninta da Deejoh ya kuma tabbatar idan ya kuma jin tayiwa Deejoh wani abin toh gaban sarki zasu tafi....
Gaje kaman mutuniyar arziki sai jinjina kai take tana fad'in babu abinda zai kuma faruwa.....
Innah dai duban Gaje kawai take yanda take rantse-rantse bazata kuma musgunawa Deejoh ba tsoron kada akaita gaban sarki amma kam tasan wannan k'aryace Gaje bazata tab'a k'yale Deejoh ba...
Bayan Mai Unguwa ya sallami matan Malam Sanda mahaifin Ahidjo ya gyara zamansa kana ya soma fad'in "Allah gafarta dama wani hanzari ba gudu ba.... Wannan mata kaman yanda kowa ya sani a garin nan tafi k'arfin Malam Ard'o bashida cewa a gidansa sai abinda tace.... Kuma Allah gafarta yanda ta gama rantse rantsen nan a nan zaiyi wuya ta aiwatar da abinda tace zata aiwatar.... Allah gafarta idan Malam Ard'o zai amince zan nemawa d'ana Ahidjo auren Deejoh....."
Murmushin dake bisa fuskar Malam Ard'o ya kasa gushewa shikam hakan sai yafi masa sabida yasan d'iyarsa ta tsira muddin ta fita daga hannun Gaje... Muryar mai unguwa ne ya katsewa Malam Ard'o tunanin da yake.....
"Anya kuwa Malam Sanda, shin yaron nan naka bashine akace ka sallamasa wa bariki ba, shin baka tunanin wannan yaro naka bazai amince da auren da zaka masa ba.... Sannan idan akayiwa Deejoh haka ba tareda amincewarta ba kaman an shiga hakkinta....."
Malam Ard'o ne ya katse Mai Unguwa da fad'in "Allah shi taimakeka ni wllhi yafi min, Deejoh ta auri koma waye ta rabuda uk'uba na Gaje yafiye min wllhi,... Ni zanfi farin ciki ma Allah shi taimakeka...."
Gyara zama mai Unguwa yayi kana yace "Toh Alhamdulillahi tinda an sami fahimta daga b'angare biyun.... Kuyi duk wasu shirye-shirye da zakuyi ni nan zan saka rana...."
"Allah shi gafarta ban tari numfashinka ba amma da sadakin d'ana nake tafe idan babu damuwa ga Malam Mudi da Malam D'alha gaka nan cikon na uku kun isa shaidu, inaga a d'aura auren yanzu kawai yarinyar ta fita hannun azzalumar matar nan ta huta...."
Cikin sauri Malam Ard'o ya shiga jinjina kai yana fad'in "Wannan gaskiya ne, domin yau nasan Gaje kwana zatayi tana dukan Deejoh ta musamman da aka kawota k'ara, ni kaina nasan yau da k'yar zansha a hannunta...."
Cikeda tausayawa suke jinjina al'amarin gidan Malam Ard'o ... Mai Unguwa ya jinjina kai kana yace "Shikenan babu damuwa shaidu sun cika Malam Sanda ka gabatar da sadakin d'anka sharud'an aure ya cika...."
Cikin sauri Malam Sanda ya gyara zamansa had'i da zaro kud'ad'en da ya taho dasu daga kasuwa dama yau 'yan rance sun biyasa....
A k'ofar gidan Mai Unguwa aka d'aura auren Aliyu da Khadijah kan sadaki naira dubu ashirin lakadan ba ajalan ba.....
***
Gaba d'aya gidansu Nadiya suka nufa kan kace mai dangi da abokan arziki sun cika gidan, Allah sarki Nadiya shikenan an rufe nata chapter d'in ta zama tarihi cikin k'ank'anin lokaci, 'yan uwa muji tsoron Allah mu shuka khairan A DUNIYAR MU....
Yau dai Nana H harda su saka hijabi kaman ba ita ba, kana ganin zaman hijab d'in a jikinta kasan bata saba sakawa ba, yanda ta koma sukuku da ita zai tabbatar maka mutuwar ta shigeta....
Ahidjo da Lamid'o suna tareda Siraj wajen makokin maza yanda aka kafa manyan runfuna a farfajiyan gidan, gaban Ahidjo haka kurum ya dinga fad'uwa, gaba d'aya mutuwan Nadiya ya shiga jikkunansu, tunanin iyayensa ya shiga zarya a kwanyarsa, haka kurum yaji yana so yaje gida ya duba iyayensa da zaran an gama zaman ukun Nadiya....
***
Deejoh na zaune tsakar gida tana wanke-wanke wa Gaje dukda k'unan dake hannunta , Gaje na daga gefe tana 'yan wak'e wak'enta tana auna kalan cin uwar Deejoh da zatayi, kai yau a bulus zata kaitawa Lado suyi abinda sukaga dama da ita shida 'yan dabansa su Muntala, wllhi ko babu asi yau saita sallama masu 'yar banza shegiyar yarinya mai idanu uwa ta mujiya, baka hango komai a fuskar sai idanu da d'an k'aramin bakin munaduncin... Tayi k'wafa tana mai ci gaba da rigar geronta.... Kaman daga sama suka jiyo muryan mutane suna sallama, ganin Hajiya Uwa ce matar Mai Unguwa ya sanya Gaje mik'ewa tana washe baki had'ida goge ruwan hannunta jikin zani take fad'in "A'ah lale lale,.... Hajiya yau kece gidan namu, kai barka da zuwa.... Lale marhaban....." Ta k'arashe tana baza masu tabarma....
Deejoh kam baki sake ta bar wanke-wanken da take ta shiga bin su Hajiya Uwa da kallo... Tsawa Gaje ta daka mata tana fad'in "Toh mayya kin zuba masu ta mujiya salon suje su k'ware... Zaki tashi a wajen ko kuwa.....?"
Deejoh jiki har na rawa ta mik'e a wajen...
Su Hajiya Uwa suka bita da kallon tausayi.... Lokaci guda Hajiya Marka kishiyar Hajiya Uwa ta gyara zama tana duban Gaje tace "Aima ba zama mukazo yiba, amarya muka zo d'auka....."
Kaman daga sama Gaje taji batun, ajiye kwanun sha na ruwa data kawo masu tayi kana tace "Na'am Hajiya mai kika ce? Amarya amrya kuma a nan gidan.....? Kai k'ila dai mak'ota ne ba nan ba...."
Hajiya Uwa ta gyara murya tace "A'a ba nan bane gidan Malam Ard'o mahaifin Deejoh.....?"
Murya na rawa Gaje take jinjina kai tana fad'in "Iiii eh k'warai kuwa nan ne... Amma gidan nan babu amarya...."
Uwa ta murmusa kana tace "K'warai kuwa akwai amarya a gidan nan yanzu haka ita mukazo d'auka zamu tafi da ita...."
Gaje fah taga rainin hankalin nasu yayi yawa mik'ewa tsaye tayi tana gyara d'aurin zani take fad'in "Toh annamimai munafukai sa idinawa masu bacci da ido guda, ku tashi maza a tashi a bar min gida bana son munafuncin banza munafuncin wofi a gida uwar wa kukaga amaryar mutane da shegen munafunci da saka idanu a rayuwar wasu... Maza a tashi a fice min a gida ehe..."
Ta k'arashe tana cin d'amara uwa 'yar dambe..
Mik'ewa Marka tayi had'i da kwab'e mayafinta kana tace "Badai fad'a kikeso ba, toh bisimillah kinzo gidanta, dai-dai da kutirinki nake barin fad'a maki,.... Wllhi yanzu sai na lallasa maki duka a wajen nan...."
Hajiya Uwa ta mik'e tsaye ta rik'e 'yar uwarta tana fad'in "A'a Marka kar ki biyeta mu aiwatar da abinda mijin mu ya turo mu muyi gaba kinsan sanyi ya kad'a marassa lafiyan kwanya dole yayita motsawa ba laifinta bane...."
Haba nan fah Gaje ta kuma hawa.... "Yo har ni za'azo har cikin gidana ayimin bariki, wai ku ga masu zaman lafiya ko... Munafukai ai babu zaman lafiya tsakanin kishiyoyi sai na munafunci.... Ku fita kafin ranku ya b'aci, wayema zai auri Deejoh banda munafunci irin naku...."
"Billahillazi Yaya ki barni na watsarwa matar nan hak'wara, ta k'arashi rashin kunyarta akaina amma Allah koda wasa kada ta kuskura ta maki, banza kin zaci ko wace Mace jakace irinki, mai kishin jahilci da d'iyar cikinki..."
Gaje ta kuma hayayyak'a.... Deejoh dake mak'ale bayan k'ofa ta gama jin komai kukanta ya k'aru..... Innalillahi shikenan waye Baffanta ya aura mata, mai ya kawo matan Baba mai Unguwa gidansu...? Toh wai da gaske aure aka mata, aure da wane...? Kukanta ya tsananta saidai da ta tuna zata rabu da kurkukun Innah Gaje sai taji sanyi cikin zuciyarta, ko kuturu ne ko makaho ne ya fiye mata zama gaban Iya Gaje....
Marka bata kuma bin takan Gaje ba ta shige d'aki ta janyo Deejoh dake kuka sosai....
Shigowar Mai Unguwa da Malam Ard'o ya sanya Gaje shiga hankalinta....
Tabbas da gaske dai aure akayiwa Deejoh babu saninta, kururuwa ta dinga kurmawa tana fad'in Malam Ard'o ya cuceta don yaga ba ita ta haifi Deejoh ba shiyasa ya mata haka....
Kai tsaye gidan Mai Unguwa aka wuce da Deejoh dake kuka sosai, Kintsata Marka tayi ta dinga lallashinta tana sanar da ita ta kwantar da hankalinta mijinta ma ba mazaunin gari bane, kuma bazama ta gansa nan kusa ba balle hankalinta ya tashi, kawai dai anyi auren ne don a rabata da ukuban da take fuskanta na matar Uba... Da wannan batu na Innah Marka ya sanya hankalin Deejoh d'an kwanciya...
Da shike akwai k'awarta Haule 'yar islamiyarsu d'iyar Marka amaryar Mai Unguwa a gidan sai ta d'an sake sukayita hira da Haule....
Da yamma lis Marka da Uwa suka d'auki Deejoh suka kaita gidan Baffah Sanda, Deejoh kam sai mamaki take ganin ba'a kaita gidan wani miji ba sai gidan Innar ta k'ila dai dama babu wani auren da aka mata, an dai rabata ne da Innah Gaje... Allah sarki Deejoh ji tayi kaman an tsundumata a Aljannah gata gidan Innarta babu damuwan Gaje.....
***
Kallonta yayi cikin idanu kana ya girgiza kai "You know Nana H you're impossible.... How could you do that... Meyasa...."
Katse sa tayi da fad'in "Stop acting like you care... Kar ka manta na fad'a maka Uncle Siraj is mine... He's mine, ni kad'aina ... And who ever try to get in my way..... I'll get rid of him in every possible way I can ko shi waye...."
Matsowa dab da ita yayi had'i da kamo k'ugunta ya matseta sosai cikin jikinsa kana ya soma fad'in "Hafsat don't you dare hurt your sister.... Kar ki cutar da Nana A I beg of you..."