← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 98

Sashe 65

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Sahal ya sanar dasu nan da sati biyu za'a iya sallamansa amma yanzu suna iya shiga su gansa domin ya sanar da majinyacin cewa sune mutanen da suka tsincesa suka kuma kawo sa asibiti...

***

Abu kaman wasa Deejoh bata farfad'o ba duk irin ruwan da aka yayyafa mata, cikin sauri Sabi'u ya mik'e yana fad'in "Baba asibiti ya kamata mu kaita, kar a kuma...."

Baffah cikin tsananin tashin hankali yake fad'in "D'an nan babur d'ina yau kwananta guda wajen gyara, asibiti ba nan kusa ba sai mun shiga gari...."

Sabi'u bai jira wata-wata ba ya sunkuci Deejoh da Innah ke rungume da ita tana fad'in kar ta tafi itama ta barta, hanyar waje Sabi'u ya nufa yana fad'in "Baba muje akwai motata a waje..."

Cikin tsananin tashin hankali Baffah ya rik'o Innah suka fice domin gaba d'aya itama taimakon take buk'ata

Suna isa health center aka karb'i Deejoh, Sabi'u ko zama baiyi ba saida ya tabbata likita ne ya amshe ta, gaba d'aya sai rawar k'afa yake yana nuna tsananin damuwarsa..

Daga can reception ya samawa su Baffah wajen zama yana mai ci gaba da basu baki yana sanar dasu Deejoh zata sami lafiya...

Baffah tallafo matarsa sosai yayi hawaye na gangaro masa yake ci gaba da fad'in "Aliyu na yafeka duniya da lahira, wllhi na yafeka, ka yafeni d'ana ni kaina nasan ban kyautawa rayuwarka ba koda ka kasance mai laifi... Kaico wannan rayuwa mai cikeda tarin dana sani...!" Kukansa ya k'aru

Innah ce ke k'ok'arin basa baki tana fad'in "Malam addu'a zamuyi ba dawo da abubuwan da suka wuce ba, amma Malam zuciyata ta kasa aminta Ahidjo ya rasu saidai kaman yanda kace ba'a wasa da mutuwa, amma nikam jikina yana bani d'ana na raye kuma idaniyata tana jin zata sake ganinsa. Na yafesa duniya da lahira, saidai idan har da gaske ya mutu wajen yak'i sun cutar damu da basu sanar damu da wuri ba.... Sun cutar damu cuta mafi muni...."

Sai lokacin Sabi'u dake satan kallonsu ya k'araso a hankali, daga gefe ya d'an durk'usa kai a k'asa ya soma fad'in "Baba kuyi hak'uri, wllhi ni tun lokacin da abun ya faru naso na sanar daku saidai marigayi bai sanar dani ainihin garinsa ba kawai dai ya sanar dani mahaifansa na raye kuma yanada iyali a gida wacce mahaifansa suka aura masa, tun bayan rasuwarsa nake neman garin da kuke sai kwanan Allah yasa na dace kuma ban huta ba har saida na iso na sanar daku, kuyi hak'uri da ace nasan garinku tuntuni da nazo na sanar daku... Kuyi hak'uri Baba tabbas da zafi ace d'anka ya rasu baka sani ba balle ka masa addu'a.."

Lokaci guda Baffah ya sami kansa da k'uncin irin abubuwan da yayiwa Ahidjo a baya, wannan itace rayuwar duniya, wannan itace misalin rayuwar duniya, tabbas duk sonka da ita duk k'ink'a da ita wata rana dole a wayi gari babu kai, hak'i ka zauna da kowa da alkhairi shine ribar zaman duniya, ina amfanin d'aukan gaba da d'an uwanka, ina amfanin rashin yafiya, hak'ika shi d'an Adam ajizi ne mai kuskure ne mahaliccinmu ma muna masa laifi kuma ya yafe mana, idan da ace babu yafiya tabbas da duniyar tuni an kifite... Mu zama masu yawan yafiya a tsakanin Al'umma....

Wasu hawaye masu d'umi suka zubo wa Baffah, inama zaiga Ahidjo a idanunsa a halin yanzu, da ya sanar dashi cewa ya yafesa duniya da lahira, Allah sarki saidai hakan bazai samu ba, Ahidjo ya tafi, ya tafi ya barsu tafiya ta har abada..... A hankali Baffah ya furta "Ubangiji ya sadaka da rahamarsa Aliyu....."

Lokaci guda Innah ta kuma kamo bakin mayafinta tana share idanunta da tuni suka mata wani irin nauyi, tabbas Allah shi ya halicci mutuwa a tsakanin bayinsa, kuma sai ya sanya wa zuciya dangana da mantuwa bacin haka batajin rashin tilon d'anta zai tab'a gushewa daga cikin zuciyarta, yau koda Aliyu na gabansu bazai wuce kwanakin da mahaliccinsa ya d'ibar masa ba, wannan itace rayuwar duniya ba komai bace face wata tafiya ce da mukeyi gaba d'aya wanda duk runtsi duk daren dad'ewa zamu isa destination guda d'aya wato kabarinka, Allah kasa muyi k'arshe mai kyau.... Ameen..!

Sabi'u sai ka rantse iyakacin gaskiyarsa kenan, gaba d'aya ya kasa zaune ya kasa tsaye jiran likita yake ya fito ya sanar dasu condition d'in Deejoh, haka nan tunda yayi tozali da Deejoh yaji bai tab'a son wata mace a duniya irinta ba, bazaiso Nana H tasan da matar Ahidjo ba balle tayi tunanin cutar da ita, yayi ma kansa sha'awar yarinya kuma yaci burin mallakanta da zaran ta gama takaban Ahidjo, kuma idan yayi haka shine ya rik'i amanar Ahidjo tinda yasan yanda Ahidjo ke son inganta rayuwar Deejoh, shi kad'ai ne zai iya bata rayuwa mai inganci a wannan k'ank'anin shekaru da take dashi.... Lokaci guda ya fuzar da iska had'i da gyara tsayuwarsa a dai-dai nan likita ya fito yana tambayar wad'anda suka kawo Deejoh...

Cikin sauri Sabi'u ya k'arasa yana fad'in "Dr ta farfad'o...."

Kallonsa da kyau likita yayi kana yace "Kaine ka kawo yarinyar nan...?"

Kafin ya sami zarafin amsawa Baffah da Innah suka k'araso suna fad'in "Mune iyayenta likita..."

Jinjina kai Dr yayi yana mai kai dubansa garesu kana yace "Kuna iya biyoni ofishi na...." Ya k'arashe yana mai tunk'aran ofishin nasa yayinda su Baffah suka take masa baya cikin sauri...

Badon Sabi'u yaso ba ya dakata daga waje yana addu'an Allah yasa lafiya take....

Likita ya dubi Innah da Baffah kana yace "Kune iyayenta...?"

Jinjina kai Baffah ya kumayi a karo na biyu kana yace "Mune iyayenta likita ka sanar damu meke faruwa da ita..." Cikeda k'arfin hali yayi maganar domin Innah kam ta gaza cewa komai har lokacin hawaye basu daina bin k'uncinta ba

Dr ya d'an gyara zamansa yana tunanin yanda iyayen wannan yarinya zasu d'auki batun da zai sanar dasu, amma sanar dasu d'in ya zama dole....

"Likita ka sanar damu idan ita d'inma mutuwar tayi..." Tayi maganar tsananin tashin hankali na kuma wanzuwa a fuskarta

Girgiza kai likita yayi kana yace "Bata mutu ba hasalima zuwa wannan lokacin ina tunanin ta farka... Amma yaya akayi kukayi sakaci da rayuwar d'iyarku haka, na tabbata d'iyarku bazata haura shekaru goma shabiyar ba.... Shin ku wasu irin iyaye ne masu sakaci... Da yawan iyaye son abin duniya kansa su kasa saka idanu a rayuwar d'iyoyinsu musamman 'yan mata irin haka wanda nasan shakka babu wasu a irin tallata tallacen nan suke had'uwa da tsautsayi irin wannan, sai kaga yara k'anana amma tuni an lalatasu iyayen basu sani ba, sam a kamanninku bakuyi kama da mutanen banza ba..."

Baffah ne ya dakatar dashi da fad'in "Kaga likita kar ka nemi kaci mana zarafi, da ace kasan tashin hankalin da muke ciki sam da baka zauna mana wad'annan maganganun ba.. Ka sanar damu yaya lafiyar d'iyarmu idan kuma bakayi ka bamu ita mu tafi..."

Girgiza kai Dr yayi kana yace "Ai kaga irin halin taku, toh abinda zan sanar daku a yanzu sai yafi jefaku cikin tashin hankali, ko kunsan cewa d'iyarku juna biyu ke gareta.... Toh idan baku sani ba Yarinyar ku tana d'auke da juna biyu na tsawon satittika biyar......"

Daga Innah har Baffah kallo sukabi likitan dashi kafin Innah ta furta "Juna biyu likita...." Dr ya jinjina kai..

Wani sabon tausayin Deejoh ne ya sauk'ar masu, ga kuma rashin Ahidjo, Allah sarki ashe rabo ne yasa aka masa wannan auren, tabbas wannan shi ake kira rabo....

Kukan Innah ya k'aru Baffah ma cikin k'arfin hali yake lallashinta...

Dr ya girgiza kai kurum kana yace "Ba kuka zakuyi ba abinda ya faru ya riga ya faru, yanzu abinda zakuyi shine kuyi k'ok'arin kamo wanda ya mata wannan aika-aika ku maka sa a kotu kuma kada kuyi yunk'urin kashe....."

Baikai aya ba Innah cikin tsananin fad'a hawaye basu daina fita daga idanunta ba ta katse sa da fad'in "Kada ka kuskura ka sheganta min jika, abinda ke cikin Deejoh D'ah ne na halak, da ubansa dukda zai rayu baisan mahaifinsa ba amma d'an sunnah ne kar ka sake cewa za'a kashe shi.. Insha Allahu sai ya rayu a doron k'asa...." Ta k'arashe cikin tsananin kuka tana nunawa Likitan yatsa...

Baki sake likita ke dubansu yayinda Baffah yaci gaba da fad'in "Bilkisu muyi hak'uri haka Allah ya k'addaro mana...."

Innah cikin kuka take ci gaba da fad'in "Malam Ahidjo ya tafi ashe ya bar mana ajiya jikin matarsa,..." Ta juyo tana watsa wa likitan mugun kallo take fad'in "Bazan bar wannan mutumin ya sheganta min jika mai cikakken asali ba, wanda k'ila ma ya fisa asali...."

Baffah yayi saurin rik'ota yana fad'in " Kiyi hak'uri Bilkisu.... Kiyiwa Aliyu addu'a shine kawai yake buk'ata daga garemu a halin yanzu..."

Sai sannan likitan ya gane meke faruwa, take nauyinsu Baffah ya kamasu, cikin sauri ya shiga basu baki yana fad'in baisan haka abin yake ba suyi masa hak'uri, lokaci guda ya buk'aci ya rakasu d'akin da Deejoh take, suna isa kuwa suka tadda ta farka amma bata daina kuka tana ambaton Yaya Ahidjonta ba...

Innah na hangota taji wasu sabbin hawaye suna ziyartan idanunta cikin sauri ta k'arasa ta rungumeta....

Cikin kuka Deejoh ke fad'in "Innah wllhi Allah k'arya ne wllhi Yaya Ahidjo yana nan da rai, yace kuma zaizo ya d'aukeni mu tafi... Innah ni nasan bai mutu ba... Kawai k'arya mutumin nan keyi... Baffah da Allah kar ku yarda dashi wllhi k'arya ne Yaya Ahidjo bai mutu ba..." Ta k'arashe cikin tsananin kuka tana mai kai dubanta ga Baffan wanda ke rakub'e daga gefe tausayin yarinyar da abinda ke cikinta ya hanasa tab'uka komai sai karaya da zuciyarsa ta kuma yi... .

Cikeda tausayawa Baffah ke dubanta kana yace "Khadija kiyi hak'uri mai rai duk mamaci ne, shi kuma Aliyu haka Allah ya k'addara irin mutuwar da zaiyi kenan bazamuga gawarsa ba balle mu sallata, kiyi hak'uri kiyi masa addu'a Ubangijinmu yafimu k'aunarsa ya d'aukesa daga garemu, kiyi hak'uri kinga a halin yanzu bakida ishesshen lafiya..."
Chapter 65 · 0% Book details