Sashe 22
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"How dare you Lamido, ni kake fadawa maganganu haka.... Just who the hell do you think you are...?" Ta murmusa kana taci gaba da fad'in "If I were you I wouldn't be so sure... You've no idea what I'm capable of..... You can't get rid of me so easily... Wllhi zan shayar dakai mamaki... Mu zuba dani da kai.." Tana kaiwa aya ta suri Jakarta ta fice fuuu tamkar zata tashi sama.....
Tana ficewa ya buga tsaki had'ida rufe k'ofar gidan gaba d'aya....
***
*Tambuwal*
Yanda take huci zai tabbatar maka cikin tsananin fushi take, Zaliha da Ummanta sai faman bawa Mairo baki suke amma tamkar da dutse suke, sunsan halin Mairo zata iya kwana a haka ba tareda ta furtawa kowa komai ba idan ranta ya b'aci irin haka.....
Aiko tana jiyo salesman Dadda ta mik'e ta shige uwar d'akin Umman Zaliha ta maida k'ofar ta rufe....
*SameenaAleeyou📚*
[12/28, 9:38 AM] +234 802 741 0766: *FUSKA UKU*🏮
*16*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Mik'ewa Zaliha tayi ta baiwa Ummanta da Dadda waje don su tattauna....
Umma ta gyara zamanta tana duban Daddah da gaba d'aya damuwa ya nuna saman fuskarta kana ta soma fad'in "Daddah dan Allah kada ku bar garin nan, kada ki k'untatawa d'iyarki, ta riga ta saba da garin da kuma mutanen dake ciki mai yasa kike son dasa damuwa cikin zuciyarta....? " Ta k'arashe damuwa k'arara a fuskarta
Girgiza kai kawai Daddah take tana duban Umman Zaliha lokaci guda take fad'in "Rabi bazaki gane bane duk abinda nakeyi duk gujema zaman garuruwa da nakeyi sabida kub'utar da d'iyata nakeyi, bamu tab'a jimawa a wani gari ba kaman yanda muka jima a nan, Rabi bazan zuba idanu inaji ina gani na rasa tilon d'iyata ba...."
Umman Zaliha ta sauk'e ajiyan zuciya kana ta matso kusan Dadda sosai ta kamo hannayenta kana ta soma fad'in "Daddah Mairo tana jin dad'in zamanta a nan tana jin dad'in sana'arta a nan, ina jiye maki tsoro kada ki rasata garin kareta da kikeyi, bazance ina son jin sirrinki ba amma ya kamata ki daina rufawa d'iyarki duk wani sirri, ki dinga fad'a mata abubuwa, abin yana damun Mairo sosai sanin cewa tsawon rayuwarta akwai abinda kike b'oye mata..... Dan...."
Ganin yanda Daddah ke watsa mata kallon daina wahalar da fatar bakinki ya sanyata had'iye zancenta don tasan Daddah yanzu sai ta tara mata jama'an unguwa abin fad'a bai mata kad'an koda shawarinka tazo nema idan ba'abi ra'ayinta ba toh kuwa zaman bazai k'are da kyau ba....
Mik'ewa tayi tana gyara d'aurin kwalinta had'i da d'aukan mayafi tana fad'in "Yo aikin banza aikin wofi, Mairo dai d'iyata ce kuma banga watsettsen da zai rabani da d'iyata ehe... Yo kuma duk matsugunin da naga dama nan zamu tsuguna ke baki isa ki hana ba... Banda shegen felek'e da firirita zaki wani kwantar da murya wai ke ga mai shawari koh... Toh shawarin yaci uwatai.." Ta k'arashe tana dukan k'ofan d'aki da iya k'arfinta tana kwad'anra kirawa Mairo uwa zata b'alle k'ofar.. ...
Zaliha da Ummanta tsaye sukayi suna kallon ikon Allah, baka isa ka kwab'i Daddah ba ta hayayyak'oka da bala'i , kan kace mai mak'ota sun soma taruwa.... Aiko nan Daddah ta bar bugun k'ofa ta dawo kansu da bala'i....
"Toh munafukan banza 'yan hana ruwa gudu, uwar me kuke kalla.... Zaku fice ko sai na k'araso wajen....!"
Aiko kan kace mai sun soma watsewa domin sanin kansu ne kad'an da aikin Daddah ne ta jibgi mutum idanma ka kai k'ara station ba saurarenka za'ayi ba domin rankatatab garin babu station d'in da Daddah da d'iyarta basu zaga ba sabida tsananin masifarsu da bala'in su...
Mutum d'aya ne tasan zai iya yima Mairo magana tayi hak'uri gashi baya nan yau kusan sati biyu, tabbas shi kad'aine mai iya sasanta Mairo da Daddah idan sunyi fad'arsu tasan yau kam zaiyi matuk'ar wuya Mairo ta saurareta, haka nan take idan ta hau dokin fushi bata k'aunar maganawa kowa, fushinta yakanyi wuyan sauk'a idan ba dukan mutum tayi ba wannan shine d'abi'ar Mairo ka taro fad'a da ita toh kuwa jikinka zai gaya maka koda kafi k'arfinta zaku dambatu yanda kasan 'yar wasan kokawa haka nan take, sanin bazata iya dambatuwa da Daddanta ba ya sanya take avoiding Daddah muddin sukayi fad'a irin haka...
Wannan shine d'abi'ar da Daddah ta tada d'iyarta Mairo bisa, tun tana k'arama tana makarantar primary take koyar da ita fighting back kan duk wanda ya takali fad'a da ita, Mairo bata kawo k'ara saidai a kawo k'ararta, ko cikin k'awaye Mairo ta shiga toh babu k'awar data isa juya Mairo saidai Mairo ta juyata, uwa uba Mairo tanada farin jini da saurin shiga zuciyar duk wanda ta rab'a ko ya rab'eta... Sam Daddah bata koya wa Mairo karb'an abin hannun kowa ba musamman samari wannan dalili ya sanya ta koyar da ita dogaro da kai tun kafin ta kawo yanda take a yanzu...
Juyin duniyar nan Mairo tak'i fitowa daga d'akin Umman Zaliha dole Daddah ta koma gida ba don taso ba, jigum tayi tana tunanin lamarin.....
Kaman daga sama taji sallaman sa, a zabure ta mik'e tana tunanin anya badai kunnuwanta bane suke mata k'arya sabida tsananin buk'atar dawowar nasa da take.... Sallaman data kuma ji ya tabbatar mata shid'in ne ya dawo...
Cikin sauri ta isa tanai masa lale ta bud'e k'ofar... Yauma sanye yake da kayansa ta bautan k'asa da alama sauk'arsa kenan don ta gansa da jakka.....
"Daddarmu barka da gida, da fatan na sameku lafiya...." Ya fad'i sanda ya zauna bisa turmi yana kwab'e takalminsa irinta 'yan bautan k'asa....
Daddah ta amsa masa da sakin fuska tana masa barka da dawowa, lokaci guda ta mik'e ta nufi kitchen don kawo masa abinci....
Jim kad'an ta fito da flask d'in tuwo da miya...
Saurayin da murnansa ya karb'i Flask d'in daga hannunta yana fad'in "Aiko dai wallah bazank'i ba don tunda muka taso bamu tsaya cin abinci ba nasan zan samu a gidan nan shiyasa ma na soma biyowa nan...." Ya k'arashe yana mai isa bakin famfo ya wanke hannayensa sai ci gaba da zuba yake ba tareda Daddah ta amsa sa ba... Kai k'arshe ya dawo ya soma yankan lomar tuwonsa Daddah bata amsa sa ba kaman yanda suka saba.... Hakan ya tabbatar masa akwai matsala sai sannan ya lura baiga 'yar bala'i Mairo ba... Waige-waige ya soma yaji gidan shiru babu Mairo babu k'awayenta 'yan sana'ar bead....
Karkato da dubansa yayi ga Daddah yana duba wacce ta had'e hannaye biyu ta zuba tagumi.....
Ajiye kwanon abincin yayi yana duban Daddah da kyau kana yace "Daddarmu lafiya banga yaranki ba.....?"
Sauk'e ajiyan zuciya tayi had'i da tab'e baki kana tace "Yo uwar gayya bata nan ina kuwa zaka gansu Nazeeru am..."
Saurayin da ta kirada Naziru murmushi yayi don yasan fad'a Daddah da Mairo sukayi kana yace "Amma dai lafiya koh...."
"Yo ina kuwa lafiya ai kaima tunda kaga haka kasan jiranka kurum nake ka ida cin abincin nan muje ka lallashota yanda ka saba ta dawo gida, kasan maganar ne kurum bata tsallakewa.... Maza ida tura tuwon...." Ta k'arashe tana tura masa ledar pure water....
Nazir yayi murmushi kana yace "Shine wai kika saka kanki a damuwa, toh wai idan mukayi auren haka zakike damuwa...." Yana maganar yana k'unshe dariyarsa...
K'iris ya rage bata kwad'a masa takalmin gefenta ba tana fad'in "Uwar aure zakuyi ba aure ba, idan kuma kunnani kake son sakeyi sai muji kasan sarai zan kwab'e mu daku dakai...."
Nazir ya had'iyi lomar tuwonsa dariya na neman k'warar dashi yake fad'in "Ai babban gangancin da mutum zaiyi shine ya nemi auren Mairo d'iyar Daddah, wllhi wllhi Daddah duk sona da mace mai kyau bazan iya sauk'e idanuna kan Mairo ba hasalima bana mata kallon mace, duk mace mai dokuwa da maza kam ai ta wuce mace......"
Bai kai aya ba ta katse sa da fad'in "Kar kuma ka zagar min d'iya ehe, yo da ace ban koya mata k'watan 'yanci ba ai da yanzu kun hure mata kunne da k'aryarku ta samari, maza ida ci ni da Allah muje dare nayi...."
Tsame hannunsa yayi cikin tuwon yana d'an darawa yake fad'in "Aima na k'oshi saidai a baiwa almajirai sauran....."
Kaman jira take nan ta tasa gaba suka fice.....
NAZIR matashin saurayi ne wanda yake bautan k'asa a garin, a lokacin dasu Daddah sukayi hijira daga garin Kazaure ta jihar Jigawa zuwa garin Tambuwal ta jihar Sokoto a lokacin Nazir ya taho garin Sokoto don yin bautar k'asa, a motar kasuwa suka had'u da Nazir yayinda taimako ya shiga tsakaninsu, sukayi rabo ta mutunci dukda ad'an zamansu a motar saida sukayi fad'a da mutane da dama cikin motar amma basuyida Nazir ba, wani ikon Allah sanda suka sauk'a unguwar da zasu zauna saiko suka had'u da Nazir shima gidan da ya kama d'an k'asa dasu kad'an ne... Nazir d'an asalin garin Jigawa ne, yakan je gida bayan sati bibbiyu yakai ziyara wani sa'in har tsaraba yakan yiwo wasu Daddah, haka kurum Allah ya had'a jininsu tun taimakonsu da yayi a mota, sam bai tab'a nuna interest d'insa kan Mairo ba saidaima ya taya Daddah yak'i da samaruka masu son Mairo tunda ya lura da abinda Daddar take so kenan, dad'ida k'arin yarda dashi da Daddah tayi har hoton matar da zai aura ya nuna masu sannan wani sa'in sukan gaisa da ita a waya, har sabo saida ta shiga tsakaninsu da budurwar Nazir, wani sa'in musamman take kira taji dramar Daddah da Mairo a cewarta dariya suke bata.... Lura da yanda Nazir ke tsananin son budurwarsa basu mintuna kad'an sai sunyi waya kaman su cinye juna ya kuma sa Daddah sakin jiki dashi, Allah sarki gashi ya kusan cika shekara guda d'insa ya kammala bautar k'asar sa tasan dole su rabu dashi nan bada jimawa ba, tabbas Nazir zai barsu da kewa.....
Agogon hannunsa ya duba sanda suka fito daga gidan, agogon ta nuna k'arfe 10:00pm duban Daddah yayi ita fa bilhakk'i da gaskiya gidan mutane ta nufa a daren nan....
Dubansa tayi ganin ya tsaya mata k'obarare kana tace "Miye ka tsaya min uwa dogari mu k'arasa mana...."