← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 98

Sashe 70

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maida dubansa ga wayar dake hannunsa yayi k'irjinsa na tsananin bugu, gaba d'aya ya kasa d'aga wayar sai duban screen d'in da yake yi cikin rashin yarda da abinda yake gani, sunan Lamid'o b'aro-b'aro, mutumin da ya b'ace sama da wata guda a halin yanzu.... Har wayar ta yanke Siraj bai daina kallon wayar ba, lokaci guda ya tuna da mutumin dake gabansa, cikin sauri ya d'aga kai saidai wani ikon Allah bai gansa ba, baiga wannan fuskar ba, fuskar da ya gaza tantancewa itace ko ba ita bace, kardai gizo abubuwa suka soma masa...

Cikin sauri Siraj ya nufi gate ba tareda ya sami zarafin magana wa securities ba... Ga tsananin mamakin sa babu mutumin nan, babu ko k'yallinsa, zuciyarsa taci gaba da bugawa, bai mutu ba.... Kai bashi bane, bashi bane mutumin da sukayi tarayya wajen ganin bayan rayuwarsa shida abokansa... Ya tabbata gizo abubuwa suka soma masa... Cikin sauri ya shiga shafa wayarsa yana ganin kiran Lamid'o na kuma shigowa... Jikinsa a mace ya d'aga wayar ba tareda ya iya furta koda kalma ba...

"Kana Company ko gida, ina zan sameka....?" Abinda Lamid'o kenan ya fad'i daga d'aya b'angaren....

Siraj ya zama lost gaba d'aya, wai meke faruwa ne...? Cikin sanyin murya yake fad'in "Lamid'o meke faruwa ne dan Allah... Ka sanar dani dan Allah....."

Katsesa Lamid'o yayi da fad'in "That's precisely why I called.... And if possible ka koma gida ka had'a 'yan gidanku gaba d'aya domin maganar ta shafesu suma..."

Jikin Siraj ya kuma yin sanyi... Girgiza kai yake cikin rashin gane ina kalaman na Lamid'o suka dosa kana yace "I don't get you, family na kuma.... Meye had'insu da b'acewar da kayi kuma...."

"Siraj kayi yanda nace domin babban Al'amari ke tafe dani...."

Jinjina masa kai yake tamkar yana ganinsa kafin yace "Shikenan, ina gida sai kazo....." Bai ko jira cewar Lamid'o ba ya katse kiran ya k'arasa saman wasu kujeru ya zauna yana tunanin yanda Al'amra suke tafiya masu, Fuskar da ya gani d'azu-d'azu a gabansa ta kasa b'ace masa, sannan zuciyarsa ta kasa aminta cewa shid'in ne... A hankali ya kifa kansa a wajen ga tunanin Azeeza na neman zautar dashi....

Kardai wannan shine Junaid... Yes Junaid, junaid sunansa, kardai shine saurayin da suka had'uda Nana A a foundation.... K'irjinsa tai wani irin bugawa... Tabbas sai yanzu abubuwa suka shiga dawo masa, yaron nan fansa yazo d'auka akansa tabbas bai mutu ba, wato yazo yayi amfani da Nana A ya d'auki fansar sa akansa.... Cikin sauri ya nufi cikin gidan kaman zai kifa da k'asa zuciyarsa na masa zogi....

"Nana A! Nana A!! Asma'uuuu....!!!" Ya k'arashe cikin tsananin d'aga murya...

Ba Nana A kurum ba gabaki d'aya d'okacin gidan a d'ari suka nufo downstairs yanda suka tarar da Siraj na faman huci, bai tab'a kasancewa irin hakan ba musamman kan nieces d'in nasa...

Jikin Nana A na rawa ta k'arasa garesa Ayiya na biye da ita tsoron kada ta kifa...

Baki har na rawa Nana A ke fad'in "Uncle... La... Lafiya.. Meke faruwa, wani abu ne ya faru....?"

Bai daina huci ba yake fad'in "Asma'u wanene Junaid, waye shi mai ya kawosa rayuwarki....?"

Gaba d'aya parlorn da mamaki suke dubansa, babu kaman Ayiya da Ammah,

"Tambayarki nake...!!!!" Ya kuma fad'i cikin daka tsawa...

Lokaci guda idanunta suka shiga fidda ruwa tana mai girgiza kai don batama san mai zata ce masa ba....

Ayiya kuwa juyawa kurum tayi tana watsa wa Nana H dake tsaye jikin staircase mugun kallo don tasan wannan bazai wuce aikin Nana H ba, ita dai tak'i jinin taga 'yar uwar cikin farin ciki, tasan bazai wuce d'aya daga cikin tuggunta ba....

Cikeda fad'a Ayiya ta maido da dubanta ga Siraj dake tsaye yana faman huci kana taci gaba da fad'in "Toh idan bai sota ba kaine zaka aureta ko me, kaji min tsiyan hali.. Ka wani zo kana kumfan baki... Toh Junaid shine mijinta yaron arziki kuma shi zata aura da yardar Allah ba mayaudari irin wancan gantalellen abokin naka ba...."

A hasale yake watsawa Ayiya mugun kallo kana yace "Idan ina magana da Asma'u ki daina saka min baki, ke baki san komai ba... Sannan duk duniyar nan ni ne mutumin da zai bada auren Asma'u kuma na gama magana bazata auri wannan yaron ba har abada...."

Kukan da Nana A ke rik'ewa ya kufce mata, cikin sauri ta fad'a jikin Ayiya tana mai fitar da sautin kukanta ...

Ammah da ranta ya gama b'aci dama bata huce da fushin da take da Siraj d'in ba ga wani tashin hankali ya kunno kai a hasale ta k'araso gaban Siraj dukda numfashinta dake seizing asthma d'inta naso ya tashi...

Cikin tsananin fad'a take fad'in "Siraj wai lafiyarka, ko shaye-shaye ne ka soma abinda bakayi a k'uruciya ba... Tun shekaran jiya ake d'aga hankalin kowa a gidan nan... What's gotten into you.... Meke damunka, don kai taka budurwar ta tafi tace bata sonka sai kace kowa ma bazaiyi aure ba, idan zakayi adalci wa Asma'u ince yanzu yanzun nan ko awa guda ba'ayiba ta ida kareka tana bin bayanka... Toh ka bud'e kunnuwarka da kyau kaji, idan a baya na zuba maka idanu ka banbance tsakanin Asma'u da Hafsat yanzu bazanyi ba, sanda Hafsat tace tana son marigayi abokin ka ince jikin ka har na rawa ka bada aurenta sai yanzu da Asma'u ta sami mijin aure zakace bazaka bada ita ba... Kai waye ya matsa maka, dukda lalura irin taka bamu tab'a fasa nema maka aure ba.... Toh bari kaji na fad'a maka.. Idan wannan yaro Junaid shine zai zamto farin cikin jikata then I'll give her my unconditional support.. Kai baka isa ka hana ba....."

Jikinsa ya d'anyi sanyi ganin yanda numfashin Ammahn ke fita da k'yar, dole ya bita a sannu sabida health condition d'inta... A hankali ya soma furta

"Ammah please understand me, bamuyi bincike kan yaron nan ba, haka kurum bazamu d'auki aure mu basa b....."

Katse sa tayi da fad'in "Banson jin komai, baki da baki muka jima muna hira dashi a nan, kuma da dabara na tambayesa komai gameda shi kuma ya sanar dani.... Nasan abinda nake Siraj, idan kai baka bada aurenta ba dangi basu k'are ba, wllhi kasa tsiya can Bulkacuwa zamu tafi a d'aura aure.."

Kansa a k'asa yayinda kukan Nana A ya sassauta, shiru ya d'an ratsa parlorn....

Dai dai nan Nana H ta k'arashi sauk'owarta daga bene tana mai tafe hannaye had'i da yin dariya mai d'an sauti kad'an take fad'in "Bravo Ammah, my Grandmother is now acting like the head of the family already.... Ammah kar ki hada soyayyata da Ahidjo da wannan gurgun saurayin Nana A d'in... Kar ki mance Ahidjo ya bani jini sanda nayi ciwo kaman zan mutu, sannan a lokacin bakuda abinda zaku biyasa dashi da ya wuce ku mallaka masa ni tinda ya nuna yana sona, idan ban mance ba da bai bani jininsa a wancan lokacin ba da zaiyi wuya idan baku rasani ba, so bakuda zab'i da ya wuce ku d'auki aurena ku baiwa Heedj dukda cewa baku san iyayensa ba baku tab'a ganinsu ba..."

Ta k'arashe tana mai k'arasawa kusan Siraj dake binta da kallon mamaki domin lamarin Nana H ya soma basa tsoro, duk duniya babu wanda take gani da gashin ido.... Hannayensa ta kamo had'i da saka fuskar tausayi kana ta soma fad'in "Uncle this isn't the first time da aka soma aure ba tareda sanin dangi ba a wannan gidan, idan baka mance ba anyi akaina da late DT Ahidjo, Uncle my Sister loves that crippled so much, dan Allah ka aura mata shi kaji Uncle, Nana A tana buk'atan aure ni na sani, kaga tayi k'ok'arin tsare kanta tsawon shekarunta, yanzu data sami mai k'aunarta tsakani da Allah ba irin Lamid'o ba ya kamata ka aura mata shi kafin hak'urinta da juriyarta su gaza ta soma bin maza...." Ta k'arashe tana wani juya idanu kana ta k'arada "Shawari ce..."

Gabaki d'aya parlorn babu wanda ya iya tofa mata yayinda Nana A ta bita da kallo idanunta na ci gaba da fitar da ruwa, tabbas bata san meye 'yar uwar tata ta d'auketa ba...

Siraj kam duk bayanin da zai masu yasan bazasu fahimcesa ba hasalima baiso k'wai ta fashe suji sirrinsa da ya jima yana b'oye masu... Cikin sauri ya fice daga parlorn kaman zai kifa da k'asa....

***

Waje ya kuma dawowa ya zauna saman wasu kujeru had'i da kwantar da kansa saman table d'in gabansa... Gaba d'aya ya tukwikuye kan nasa ya damk'e

Har bak'ar jeep d'in k'irar Prado ta ida shigowa haraban cikin gidan Siraj bai sani ba, tin daga cikin mota Lamid'o ke hangosa, tausayin Siraj ya rufe zuciyarsa, tsanar Bulama da bak'in ak'idarsa ta d'aukar fansa ya kuma cika zuciyar Lamid'o, dunuya a yau anyi watsi da hak'uri sai k'alilan Ubangiji ka sanyamu cikin k'alilan d'in...

K'arar rufe mota ne ya sanya Siraj d'ago da kansa daga kifen da yake...

Hango Lamid'o ya tuno masa abubuwa da dama, mutuwar Ahidjo da kuma yaudarar niece d'insa da yayi uwa uba bayyanar tsohon saurayin Zeenah da sukayi tunanin ya mace a baya....

Tsaf Lamid'o ya kula da kallon da Siraj ke masa, a b'angaren Siraj d'inma ya hango ramar da Lamid'on yayi saidai yayi haske fayau alamun bai fita, abinka da giant sai ramar ta masa kyau sosai, ba don tabon ciwo da Siraj ya hango a fuskarsa ba da tuni ya fincikosa ya kai masa naushi abinda yayiwa Nana Asma'u...

Muryar Lamid'o ya katse masa tunani nasa sanda ya k'araso wajen...

A d'an kaikaice Siraj ke dubansa kana ya girgiza kai yace "So you were kidnapped.... Ko kuma ka tsara abinka don kar kaji kunyar abinda ka aikata koh, you really have no shame, you know I don't wanna listen to your lies, sannan bansan dalilin da yasa na amince ka shigo gidan nan ba don duk gidan babu mai buk'atan sake ganinka after what you did...."

Shafa goshinsa Lamid'o yayi kana yace "Siraj you need to hear me out first, ka tsaya kaji da mai nazo..." Ya k'arashe yanayin fuskarsa na canzawa kafin ya k'arada "By the way, where's Nana A.. How's she.... I can't wait to see her..."
Chapter 70 · 0% Book details