Sashe 32
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda yake babu bil adaman da ya tab'a tsugunawa ya gaidasa bayan 'yansanda 'yan uwansa masu sara masa....
Baice komai ba sai kallon da yake binta dashi, sosai yarinyar ta basa tausayi k'aramace sosai wacce ya kamata ace a dai-dai wannan lokaci tana class ne ba zaman aure ba...
"Kin gama sgiryawa...?" Ya tambaya yana dubanta
Jinjina masa kai kurum tayi ba tareda ta iya amsawa ba...
Ahidjo ya jinjina kansa yana dubanta yanda ta cukuikuye hijab d'in a k'irjinta don tunda ya shigo ta kasa k'arasa saka hijab d'in...
Taso basa dariya yanda take faman rarraba idanu amma ya d'an gimtse kana yace "Toh yaya yau bakiyi kwalliyar ba, ko baki son fitar ne...."
Idanunta a k'asa tana faman rarrabasu, da k'yar ta iya girgiza masa kai wanda bai fahimci amsar me take nufi ba....
Matsowa kusanta yayi tayi saurin d'ago idanu ta dubesa sai kuma ta maida dubanta wani gefen...
Nan ma murmushi yayi kana yace "Ina kayan kwalliyan naki...?"
Ta kuma dubansa cikeda mamakin yanda ya sauya gaba d'aya, kaman ba shine shekaran jiya ya kirata da mayya ba...
"Ni bazanyi kwalliya ba kuma ai Innah ce tace sai na raka ka, ai cewa kayi ni mayya ce..." Tayi maganar bakinta a ture
Yanda ta fad'i masa cikin zuciyarta kai tsaye ya birgesa...
D'an bakin nata yake kalla yanda ta turosa gaba kana ya gyara tsayuwarsa had'ida d'an sakin murmushi yace "Aw ashe dai fushi ake dani, shiyasa baza a min kwalliya ba, toh kiyi hak'uri kinji... Bani kayan kwalliyan naki...."
D'ago idanu tayi tana dubansa cikeda mamaki, saikace bashid'inba.... Lokaci guda ta mak'e kafad'a murya can k'asan mak'oshi tace "Dama bawa kai nayiba ba fah..."
"Toh a waye kikayi, samarukanki....?"
Nanma d'agowa tayi ta d'an dubesa sai kuma taji dariya, wai samarukanta ita inama taga samaruka...
"Banidasu...." Ta fad'i a tak'aice....
Ahidjo ya kuma murmusawa yana zira hannaye cikin aljihu kana yace "Hakan yafi... Muje dare yanayi...." Ya fad'i yana duba agogon dake d'aure hannunsa...
Kallo tabisa dashi har ya fice kafin ta d'an rintse idanunta, lokaci guda ta zira hijab d'in sanda taji muryar Innah na k'walla mata kira.....
Koda suka fito zasu tafi sayayyan Ahidjo shi ya bud'e mata k'ofa da kansa ya umarceta data shiga.... Gaje data nufo gidan tagajan magajan nan ta hangi kayan Al'ajabi wai Deejoh na shiga k'arfen nasara k'irar zamani.... K'iris ya rage bata d'ibi jiki ta fad'i ba....
***
Sauk'arsu kenan a birnin Damaturu, basu san yanda suka nufa ba, babu wanda suka sani a garin.......
Mairo batabi takan Daddah ba ta shiga k'ok'arin zak'ulo wayarta cikin jaka saidai wayam bataji wayar ba, Daddah na hankalce da ita saidai bata tambayeta abinda take nema ba....
"Kinga maza mik'e mu shiga gari har Allah yasa mu dace...." Daddah ta fad'i tana kuma gyara mayafinta had'i da janyo k'aton akwatinta...
Kallonta kawai Mairo take cikeda takaicin hali irin na Daddah, yanzu ina zasuje da wannan shirgin kayan nasu su ba kowa suka sani gari ba, ga yanayin garin ga kuma yanayi na rashin yarda da ake ciki.... Suna zaman zamansu a Tambuwal ta hura masu wuta...
Daddah kam tuni ta soma tafiya tana rarraba idanu tana kallon yanayin garin...
A kufule Mairo tace "Toh yanzu dan Allah Daddah fisabibillahi ina muka nufa.... Waye muka sani...?"
"Ke dallah banson felek'e da d'in can garuruwan da muka zauna waye muka sani duk ba daga baya muke sabawa ba...."
Mairo tayi k'wafa had'i da jinjina kai kana tace "Ai dai kinsan duk yawon da mukeyi arewa maso yamma muke yi bamu tab'a nufowa arewa maso gabas ba kindai san ana fama da matsalar tsaro tam! Wllhi aka ganmu da kayan nan za'a iya kamamu...."
Yab'e baki Daddah tayi kana tace "Yo a kamemun mana, uwar wa muke tsoro dallah wuce muje ni bansan Mairo ta da tsoron takife ba...." Tana ida fad'in haka ta janyo hannu Mairo suka sa kai...
****
Wani kanti mai kyau Ahidjo ya kaisu ya umarceta itama ta fito ta zab'i abinda take so, fir Deejoh tak'i yarda ta fito don gaba d'aya gani take kaman kowa a garin su yake kallo duk yanda suka wuce.... Da k'yar Ahidjo ya shawo kanta ta fito suka shiga Kantin, kaya sosai ya dinga jida yayinda Deejoh ke biye dashi uwa rak'uma da akala , itakam sam bata saki jiki da shi d'in ba....
Ahidjo ya d'an juyo suka had'a idanu lokaci guda ya sakar mata murmushi, dole ya jata sosai a jiki domin yasan itace kawai zata iya sanyawa iyayensa su amince ya tafi ba tareda sun masa baki ba..
Ahidjo ya umarce mai kanti da ya kawo masa kayan kwalliya, nan ya sai mata masu kyau ba irin wad'anda take amfani dasu ba....
Dangin kayan abinci kayan ciye ciye da na amfanin yau da kullum ya sai masu gaba d'aya gidan, Deejoh kam mamakin tulun kud'in da ya kashe tayitayi,...
Sanda zasu koma ma da kansa ya bud'e mata k'ofa, tayi k'ok'arin sakar masa murmushi....
Suna tafe a mota yake tambayarta ina ta tsaya a karatu?...
"Karatun Allo kawai nayi Iya Gaje ta hanani boko..."
D'an karkatowa yayi ya dubeta kana yace "Wacece Iya Gaje? "
"Mama ta ce...." ta basa amsa a tak'ice....
Bai kuma cewa komai ba sai maida hankalinsa ga tuk'i da yayi....
***
Unguwar dake kusa da tasha suka nufa saidai suna isowa mashigar unguwar suka had'u da wasu soji guda biyu masu tsaro, idan akwai abinda Daddah ke shayi a rayuwarta toh shakka babu Soja ne.....
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*23*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*SAMEENA ALEEYOU NOVELS Mi Familia😍 Allah shi bar so da k'auna fatan Alheri gareku gaba d'aya♥*
Suna k'arasowa wajen Daddah ta durk'usa tana gaidasu had'i da janyo hannun Mairo tanai mata alamu data gaisar da sojojin.... Tab'e baki kurum Mairo tayi had'i da karkata kallabinta don ko kallon arziki sojin basu samu daga gareta ba....
Daddah ta maido da dubanta ga sojojin tana fad'in "Yallab'ai kuyi hak'uri kunsan matafiyi da yunw....."
Bata kai aya ba guda d'ayan ya daka mata tsawa "Kee!! rufe mana baki, daga ina kuke da wannan lodin kayan...?"
Tsawan da ya darara mata saida ya sanyata zabura... Saurin washe baki tayi tana fad'in "Bak'ine mu Rankashidad'e... Yanzu sauk'armu garin...."
"Oya ku paka gefe we need to search your stuff...."
Daddah ta mik'e tana gyara d'aurin kwalinta take fad'in "Yallab'ai wai mai kace....?"
Sai sannan d'aya mai jan idanu uwa gauta yace "You no dey hear talk... Ka matsa gefe aka ce...!" Ya k'arashe cikin daka tsawa..
Cikin sauri Daddah ta janyo Mairo tana fad'in "Au toh toh.... Ai sai mu matsa gefen mai yayi zafi shiba wuta ba, aima ba sai kun tsaya d'aga jijiyan wuya ba...." Tsawan da d'ayan ya kuma daka mata ya sanayata had'iye zancen nata....
Gefe sojojin suka d'an matsa suna tattaunawa kafin suka kuma nufosu....
Daddah dai sai karanto ya Salamu ya Dafi take, karatun ta na allo ya shiga dawo mata, hardasu Alu ambaki duk saida ta karanto duk na neman tsari da wad'annan Sojojin....
D'aya wanda hausan yafi zama bakinsa yace "Ina kuka nufa da wad'annan kayan...?"
Izuwa lokacin Daddah ta soma k'uluwa da tambayoyin sojojin tinda tabisu a sannu....
Yab'e baki tayi kana tace "Nace maku bak'ine mu shigowarmu garin kenan..."
"Bak'i bakuda wajen zuwa....?" Ya tambaya yana ajiye zungureriyar bindigar dake rataye kafad'arsa a k'asa
Sojan nan bai ida d'agowa ba ya jiyo muryar Mairo tana fad'in "Cirani muka shigo....!" Yanda tayi maganan babu ko shakka balle tsoro a tattarre da ita... K'uri ya mata yana mamaki taunar chewing gum ma take... A duniya babu abinda Soja ya tsana kaman raini... Dole ya koyama wannan k'aramar marar kunyar hankali...
Kira ya doka wa d'an uwan nasa still idanunsa kafe kan Mairo yana kissama yanda zai keta mata haddi da k'arfin tsiya....
Nan ya umarce d'an uwan nasa da ya bincika kayan Daddah ya tabbata babu komai... Aiko Daddah tana ganin an janyo akwatinta ana k'ok'arin bud'ewa tayi wuf ta kame akwatinta don idan akwai abinda tafi tsana shine a bincika mata kayanta don ko Mairo tasan dokan Daddah bata son bincike sabida sirri da take yawan b'oyewa...
Soja na jan akwati Daddah na kuma rungumo akwatinta tana rantsuwan baza'a bud'e mata ba...
Shiko d'aya kan Mairo yayi ya janyota zai shige da ita d'an bukkan nasu...
Nan shima suka shiga kokawa da Mairo... Daddah ta hangi Mairo hannun Soja batasan sanda ta sunkuya had'i da danna bakinta saman hannun Sojan nan ba lokaci guda ta had'e hak'waranta ta gantsara masa wani irin gigitaccen cizo... Ai a d'ari ya saki akwatin yana yunk'urin janyo bindigar sa yaji sauk'an akwati gadon bayansa... Take a wajen ya zube yana tale gadon bayansa...
Daddah ta kuma rungumo akwatin tayi bukkan dataga d'ayan ya janyo Mairo... Aiko tana isa take sauk'e masa aka shima ya saki k'aran azaba... Cikin sauri ta taimakawa Mairo ta mik'e had'i da tsatta masa miyau kafin suka fito a guje kafin wad'annan Sojin su mik'e....
A guje suka kutsa cikin unguwar domin sunsan muddin sojin nan suka mik'e zasu harbesu da bindiga...
Wani k'aton shagon d'inki suka soma hangowa aiko nan suka shige ciki a guje suna neman d'auki....
Ganinsu haka kan kace mai 'yan shago an soma watsewa, daga mai haye taga sai mai kwanciya flat k'asar shago...
Mace d'aya ce bata gudu ba ta tsaya tana binsu Daddah da kallon mamaki yanda kasan wasu ribatattun yak'i....
***
Abin hawa Junaid ya tare ya hau ya nufi gida, Asma'u tsaye tana masa waving har ya wuce... Ta kuma duba agogon hannunta lokaci guda wayar Ayiya ya shigo mata, da murmushi ta d'aga wayar had'i da zolayan Ayiya...
"Kardai 'yar tsohuwa ta damu da rashin dawowata gida har yanzu....? " Ta fad'i tana fad'ad'a murmushinta...
"Yo ba dole na damu ba yau kin jima da yawa, yamma tayi fah... Inji dai lafiya...."
Nana A ta kuma murmusawa kana tace "Lafiya lou Ayiya mun tsaya mun duba wasu abubuwa ne nida Junaid, bai tafi ya barni ni kad'ai ba yanzu ma k'in tafiya yayi saida na shaida masa I'll be fine.... Junaid yanada mutunci sosai Ayiya,...."
Ayiya ta murmusa kana tace "Ni kaina naji ina son Junaid d'in nan tun kafin na gansa...."