Sashe 93
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaliha da tuni zuciyarta ta kai k'ololuwa wajen tafasa, a fusace ta katse Nana H da fad'in "Kada ki sake jifarmu da mummunar kalma irin haka, dukda cewa mud'in talakawa ne amma munfi k'arfin aikata abubuwan da kika zargemu akai...." Ma'ajura nata k'ok'arin tab'a Zaliha alamun tayi shiru inaa Zaliha saima fuzge jikinta da tayi ta dubi Ma'ajura tana fad'in "Ki k'yaleni nayi magana, wllhi sam ba d'abi'ata bace na tsaya ana ci min mutunci... Kar Allah sa ta yarda mana sai me.... Idan har bayyanar Mairo ba alhari bane a gareku ina rok'on Allah kada ya bayyana maku ita, domin wllhi wannan zasu kwashi 'yan kallo ne kawai da Mairo muddin ta kawo mata rainin hankali...."
Ta k'arashe Ma'ajura na k'ok'arin janyeta don su fice daga office d'in... Saidai ambato Mairo da tayi ya kuma tabbatar masu cewa tabbas Nana K d'in ce, tinda irin sunan da Lamid'o ya ambata kenan...
Kafin su fice Nana A tabi bayansu cikin sauri yayinda k'irjin Nana H yaci gaba da tafarfasa, wai ita wannan k'azama kucakar ta ida gayawa magana... Lallai kuwa batasan da wacce take ba.... Cikin sauri itama ta take masu baya...
****
Sosai ya rik'eta yana mai ci gaba da fad'in "Deejoh... Ashe zaki nemeni, Deejoh nayi kewarki sosai, Deejoh ki sanar dani wanene ni dan Allah.... Wllhi iyakacin abinda nake iya tunawa kenan inada mata kuma matar kece, kullum sai na ganki cikin baccina Deejoh.... Deejoh nid'in wanene....?" Ya k'arashe hawaye na gangarowa daga udanunsa...
Tsananin mamaki da tausayi ya hanasu Malam katab'us, harta Umma Marie mamaki ya hanata motsawa, ita kanta Mairon ko mosti k'wakk'wara ta kasa sai kallon ikon Allah da takeyi, a ina wannan mutumin ya santa, ita ko mai irin kamanninsa bata tab'a gani ba gashi yana ambaton ta da matarsa, ya rad'a mata wani suna wanda ko mai irinta bata tab'a sani ba saidai mai shigenta..... Hafiz dake gefe k'wallan da yake rik'ewane suka shiga zubo masa, shikenan ta faru ta k'are, ya tabbata hakan ka iya zama sanadiyan k'ulla soyayya tsakanin Yayansa Ali da Mairo, mai yasa yayi nauyin baki, mai yasa bai sanar da ita tuntuni ba, mai yasa bai sanar da Yayansa Ali tuntuni ba, toh koma ya sanar dashi ai ba sanin Mairo yayi ba, yauce ranar farko da suka had'u kuma ta kasance haka, tabbas a 'yan kwanakin Ali yana yawan yin mafarki da wata mace, toh kodai Mairo yake gani cikin baccinsa... Innalillahi wa Inna'ilaihi raji'un... Kalmar da Hafiz ya iya furtawa kenan.... Muryar Ali ya kuma katse masa tunanin nasa sanda yaci gaba da fad'in
"Deejoh... Talk to me please, ki min magana, kin daina sona ne,.... Yaya akayi kika sameni... Ki sanar dani asalin sunana da kuma yanda na fito kinji Deejoh...." Har lokacin hawaye basu daina zarya saman fuskarsa ba.... Ga tsananin mamakin mutanen dake wajen hawaye suka hango cikin idanun Mairo, sosai wannan bawan Allah ya bata tausayi, itakam ko d'aya batasan maganar da yake ba bata fahimci komai ba....
Baba Malam ne yayi k'ok'arin k'arasowa kusansu ya soma janye Ali daga rik'on da yayiwa Mairo "Ali saketa wannan ba matarka bace...."
Bai saketan ba saima k'ara rik'ota da yayi ya damk'e mata hannaye sosai tamkar mai tsoron kada a rabasu.. "Baba wllhi itace, wllhi Matata ce, Baba itace kullum nake gani cikin baccina, itace kullum take zuwa min... Sannan a zahiri ma na tuna fuskarta... Baba wannan matata ce Deejoh.... Deejoh dan Allah kada ki sake tafiya ki barni kinji...." Ya k'arashe yana kallon fuskar Mairo wanda tuni hawaye ya wanke....
K'ok'arin k'watan hannayenta ta shigayi amma ta kasa, gaba d'aya kowa yayi iyaka k'ok'arinsa ya raba Mairo da Ali abu yaci tura... Innalillahi kawai suke ambata, abin nasa ya koma tamkar tab'in hankali, suna murna ya farka k'ila ya farka da tunaninsa saiga akasin haka, Allah kenan buwayarsa ya wuce tunanin bawa, idan zai gudanar da al'amransa baya shawartan kowa, kuma dole duk yanda ya turo maka k'addara ka amsa hannu bibbiyu...
Ganin Ali bazai saki Mairo ba yasa Baba Malam umartan Hafiz da maza ya kira Dr Sahal...
***
Har saida suka kai bakin gate Nana A ta cimmasu, saurin tare gabansu tayi hawaye bai daina zubo mata ba take ci gaba da fad'in "Ma'ajura dan Allah ku sanar dani yanda 'yar uwata take... Wllhi na yarda daku, na yarda d'ari bisa d'ari...." Ta k'arashe tana had'e hannayenta biyu waje guda alamun rok'o...
Shiko Junaid tinda yaga fitowarta daga office tana biye da wasu 'yan mata ga kuma Nana H a bayansu ya sanyasa fitowa daga nashi office d'in shima....
Ganin irin hawaye da Nana A keyi tana rok'onsu ya sanya jikin Ma'ajura yin sanyi, sosai zuciyarta ta karaya da ganin irin kukan da Nana A keyi, tabbas sun jima ba tareda 'yar uwar tasu ba....
Da k'yar Ma'ajura ta shawo kan Zaliha dake faman fizga kan ita tafiya zatayi babu abinda zata tsaya tayi a wajen nan....
"Ma'am shikenan tinda kin amince damu kuma kin yarda bazamu maki k'arya ba.... Zaliha da kike gani aminiyar wacce muke zargi cikon ta ukunku ce...."
Nana A tayi saurin kai dubanta ga Zaliha wacce ke faman huci tana watsawa Nana H muguwar kallo, wannan da take rainon madara da k'wai ta tabbata da a lokutan baya ne sanda take tareda aminyarta Mairo wannan kallon banza bazata masu ba.... Bata ida tunanin nata ba taji hannayen Nana A saman nata, cikin murya irinta mai kama da wanda ke kuka taci gaba da fad'in "Zaliha take me to her please... Take me to my sister... I want to see her... Please take me to her....!" Ta k'arashe tana jijjiga hannayen Zaliha....
Ma'ajura ta d'an kamo hannayen Nana A kana tace "Ma'am a halin yanzu Zaliha bata tareda Mairo... Amma sunyi zaman gari guda...." Muryar Nana H ce y katse ta...
"Wani proof kuke dashi da zai tabbatar mana cewa 'yar uwarmu ce kuke magana akai....?"
"Ba lallai ki amince ba sabida ba dake dama muke magana ba... Da wacce tasan darajan d'an Adam muke bake ba.... Kuma idan sai mun nuna maki wani abu ki amince kar Allah yasa ki amince domin dama ba amincewar taki muke nema ba...."
Tunda Zaliha ta soma magana Nana H ke dubanta, she really had no clue who she was messing with..... Murmushi tayi a karon farko ba tareda ta furta ba....
Nana A tayi saurin rik'e hannayen Nana H tana mai k'ak'aro murmushi take duban Zaliha lokaci guda take furta "no no kar ki damu basai kin nuna mana komai ba, mun yarda, babban burinmu shine ki sanar damu yanda zamu sameta....."
"Ma'am babu damuwa zamu nuna maku proof...." Ta k'arashe tana k'ok'arin ciro wayar Zaliha cikin jaka..
Cikin sauri Zaliha ta soma rik'e jakarta tana mai duban Ma'ajuran take fad'in "Meye haka Ma'ajura, ki sakar min jakka ai dai kinji abinda suka ce, kuma sanin kanki ne ni a halin yanzu banma san yanda zan sami Mairo ba...."
Ko saurarenta Ma'ajura bata tsaya yi ba tayi k'ok'arin ciro wayar, itadai kawai damuwarta Nana H ta yarda ba k'arya suke ba...
Duk iya k'ok'arin k'wace wayarta da Zaliha keyi Ma'ajura ta hana har saida tayi nasaran shiga gallery ta nemo folder d'in da hotnan Mairo ke ciki... Lokaci guda ta hasko hoton Mairo b'aro-b'aro take ta shiga nuna masu a fuskokinsu....
Tsananin shock ya kama Nana A da Nana H, tabbas Nana K ce, cikon ta ukun su, koda akazo cirosu cikin mahaifiyarsu Nana A aka soma cirowa sannan Nana H sai kuma wacce aka cirota daga k'arshe Nana K wacce take a matsayin autarsu.... Fuska irin tasu ce ta bayyana, hawayen Nana A ya k'aru, jikinta yasha bata 'yar uwarta na raye kuma wataran Allah zai had'asu ...Allah sarki ashe da gaske Nana K na raye tana nan a raye..... Hannayenta na rawa ta amshe wayar daga hannun Ma'ajura tana mai ci gaba da zuban hawaye ta k'urama wayar idanu tana mai shafa screen d'in, lokaci guda murmushi ya cika fuskarta dukda hawaye dake kwaranya mata.... "Itace... Wllhi itace, Nana K ce.... Our baby sis.... She's alive.... She's not dead, Nana K is alive... Our sister is alive Nana H, kin ganta....." Ta k'arashe tana nunawa Nana H da tuni tayi mutuwar tsaye screen d'in wayar, wani irin farin ciki ne ya wanzu saman fuskar Nana A yayinda Nana H ta kasa koda motsawa sai kallon hoton Mairo da take wanda kyakkyawar fuskarta ya bayyana jikin screen d'in wayar..... Bata amshi wayar ba sai yatsina fuska da tayi tana kallon Nana A dake faman murna da kuma hawaye kana tace "No no hold the phone, kinsan ban iya rik'e irin wad'an nan wayoyin ba sai ya Jimin ciwo... Rik'e daga hannunki ma ina iya kallo.... K'warai Nana K ce, your beloved sister Nana A, she's alive.... Tana raye..." Ta kuma d'ago idanu tana duban su Zaliha dake faman binta da kallon mamaki abin kaman bai dameta ba... Lokaci guda take fad'in "So how can we find her..... Ku sanar damu....."
Zaliha dake faman d'aga gira sai sannan ta gyara tsayuwarta
"Kaman na sanar daku bansan yanda za'a sameta ba....."
Ma'ajura ta d'an dubi Zaliha kana tace "Zulu kiyi hak'uri ki duba lamarin, wannan taimako ne...."
Kallon Ma'ajura kurum tayi kana tace "Kema kinsan iyakacin gaskiyata kenan.... Mairo da Daddah hijira suke wa gari wa gari, wa yasan yawan garuruwan da suka canza bayan barinsu Tambuwal....."
Nana A kam duk wannan zance da ake bama saurarensu take ba kallon hotunan Nana K kurum take tana kuma shafa screen d'in, gani take tamkar ta ganta a gabanta, ta girma itama kaman su kuma ga dukkan alamu budurwa ce mai cikeda farin ciki....
"Ki karb'a min wayata ni zan tafi....." Zaliha ta fad'i tana faman waige-waige don gani take tamkar Daddah na hangota abinda take....
Har saida Ma'ajura ta amshi wayar hannun Nana A kafin hankalinta ya dawo garesu....
Cikin sauri Nana A ta soma fad'in "Nana H call Uncle, ki kirasa ki sanar dashi idan yaso sai a soma bincike tun yanzu.... Zaliha don Allah ki tura min hoton Nana K nakai gida wasu Ammah...."