Sashe 6
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da gudu suka k'araso suka rungumesa sunai masa waving.. Saida ya bisu da sunba had'i da addu'a kafin suka fice suna waving new Aunt d'insu Azeeza...
Har suka fice Azeeza murmushi take yayinda Barr ke faman binta da kallo...
Jikinta ne ya bata ana kallonta, aiko tana d'ago kai suka had'a idanu....
D'an sunne kanta tayi kana tace "Am... Am ina Yaya na....?"
Murmushi yayi yana jinjina yarintarta kana yace "Muna d'an magana dashi.... Idan bazaki damu ba ki k'arasa kitchen kiyi breakfast kafin mu gama koh...."
Jinjina masa kai tayi kana ta nufi kitchen d'in tana wasa da 'yan yatsunta... Har ta kai k'ofa ta jiyo muryarsa yana fad'in "Aunty Zee...." ta juyo tana dubansa cikeda mamaki ashe har yaji yanda Taheera ke kiranta...
Murmushi ya sakar mata kana yace "Thank you...."
Bata iya amsa sa ba sai sa kai da tayi ta shige kitchen d'in murmushi saman fuskarta....
***
Nana H ta kuma duban Nadiya a karo na biyu kana ta d'an sauk'e ajiyan zuciya tace "Nadiya ki sani jinki nake tamkar 'yar uwa ta jini a gareni, kuma na yarda dake hundred percent, nasan idan kinga abinda zai cutar dani bazaki bari na auka masa ba. Shin ke kin yarda dani kin yarda bazan cutar dake ba...?"
A hankali Nadiya ta jinjina kanta kana tace "Nana Hafsat wllhi na yarda dake d'ari bisa d'ari kuma nasan bazaki cutar dani ba..."
Nana H ta murmusa kana tace "Alhamdulillah da kika yarda dani..... Kuma insha Allah zaki sameni da rik'on amana...."
Nadiya ta murmusa cikeda jin dad'i....
Nana H ta kuma muskutawa kana tace "Nadiya nasan baku jima da dawowa garin nan ba, kuma nasan bakuyi k'wakk'waran bincike kan Siraj Laushi ba, koda shike koda kunyi bincike Uncle Siraj nada kyawawan d'abi'a tsakaninsa da Al'umma... Saidai abu guda tak da nake ji maki tsoro kuma mutane basa fad'i sabida gani da ake he's rich, handsome and famous.... and above all d'an babban gida.."
Nadiya ta kuma gyara zama had'i da ajiye fork d'in dake hannunta cikin plate tanai ma Nana H kallon ban fahimceki ba...
Nana H ta murmusa had'i da kuma lank'wasa k'afafu kana tace "Uncle Siraj Uncle d'ina ne wanda nafi k'auna fiyeda kowa a family na harma da 'yar uwata da muka zauna mahaifa guda..... Nadiya shin kinsan cewa duk macen data rab'i Uncle Siraj mutuwa take? Shin kinsan adadin matan da suka rasa rayuwansu ta dalilin soyayya da Uncle Siraj....? Kina so ki zama next victim.... Do you want to die at your young age....?"
Dukan tara-tara kawai k'irjin Nadiya keyi tana kallon Nana H cikeda tsoro da mamaki...
Babu alamun wasa a fuskarta taci gaba da fad'in "Nasan zakiji tsoro da mamaki toh ki sani wannan itace iyakacin gaskiyar, har yau babu wanda yasan dalilin da yasa 'yanmatan da Uncle ke nema suke mutuwa, na tabbata badon yanada dukiya ba da tunin an kullesa ko kuma an fatattakesa daga garin nan.... Amma idan baki yarda dani ba kina iya tambayan one of his friends mijina Ahidjo ko kuma Lamid'o da suke aiki company guda...." Tana kaiwa aya ta d'au coffee mug d'inta tana sipping lokaci guda take karantar Nadiya da ta koma tamkar mutum mutumi....
*SameenaAleeyou...📚*
[12/12, 6:45 PM] +234 810 044 6653: *FUSKA UKU*🏮
*05*
*©Sameena Aleeyou....✍🏽*
A hankali Barr ya durk'usa gaban wheelchair d'in Junaid yana dubansa cikeda tsananin tausayi, yana gani cikin idanunsa tsananin zalunci da aka masa, yasha gamuwa da masu case shigen na Junaid dukda baiji cikekken tarihinsa ba, amma tabbas yasan anyi masa zalunci mafi muni A DUNIYAR SA....
"Hannu yakai ya dafe na Junaid dake zube saman cinyoyinsa... Lokaci guda Junaid ya d'ago rinannun idanunsa yana duban Barr Nasaar.....
Barr yaci gaba da fad'in "Junaid let it out.. Kayi kuka domin zai rage maka zogi da rad'ad'i..."
Junaid ya murmusa wacce tafi kama da ta takaici kana yace "Barr yau shekaru hud'u kenan ina rayuwa cikin k'unci da burin d'aukan fansa, kuma banzo nan ba saida na shafe shekaru biyu ina karantar duk wani motsi nasu...." Shiru yayi ba tareda ya ci gaba da maganar ba....
Barr ya gyara tsugunonsa had'i da yima Junaid k'uri kana yace "Junaid su waye wad'annan mutane, sannan wacece suka kashe and meye dalilin kasancewarka saman wheelchair....?" Ya k'arashe fuskarsa cikeda alamun tambaya...
Sararin samaniya Junaid ya k'urama idanu kaman bazai kuma cewa komai ba domin har Barr yacire ran cewa Junaid bazai amsa masa tambayoyinsa ba....
A hankali ya saka hannunsa bayan kekensa ta d'an k'asa kad'an ya ciro wata 'yar kati kana ya shiga warwarewa....
Barr dai k'uri ya masa yana kallon ikon Allah har ya ida warware katin dake hannunsa sai sannan Barr ya lura cewa hoto ne a hannun Junaid wanda aka duk'unk'une waje guda....
A fuskar Barr ya manna hoton wanda da gani jikin news paper aka cire....
"Kasan wad'annan FUSKOKIN...?" Ya tambayi Barr sanda yake kuma ware hoton tarr idanun Barr...
Da mamaki Barr ya kuma gyara tsugunonsa yana kuma kallon hoton wanda da gani jikin news paper aka cire, k'irjinsa naci gaba da bugu.... Tabbas yasan mutanen dake cikin hoton kuma yasan exact ranan da aka d'auki hoton.... Hoton Boss d'insa ne da aminansa, lokaci guda yaji bakinsa ya masa nauyi ya kasa furta koda kalma guda.....
Ganin yanayinsa yasa Junaid kafesa sosai da idanu kana ya sauk'o da fuskarsa dab da na Barr yace "Ka sansu ne.....?"
Kallonsa kawai Barr keyi kafin yace "Kana nufin wad'annan sune FUSKA UKU da kake shirin d'aukan Fansa akansu....?"
Shiru Junaid yayi yana nazarinsa kana yace "Ka amsa min tambayata first.. Ka sansu ne.....?"
A hankali ya shiga jinjina kai k'irjinsa naci gaba da bugu.....
"K'warai na sansu sannan na san ranar da aka d'auki hoton,.... The photo was taken a ranar aurensa sa'ilin da 'yan jarida suka masa chaa domin jin ta bakinsa da aminansa irin farin cikin da suke ciki....." Shiru yayi ya kasa ci gaba da magana yayinda k'irjin Junaid taci gaba da tafarfasa....
Hannu yasa ya damk'o kwalan Barrister yana mai ci gaba da wani irin huci yake fad'in "Tell me everything.... I mean every.....thing u know about 'em......"
Barr ya d'ago yana duban Junaid yanda fatarsa ta koma ja gaba d'aya.... A hankali yake furta "Let me go....."
"No sai ka gaya min komai ko na fara daga kanka na murmuk'usheka a nan....." Junaid ya basa amsa yana kuma shak'e masa wuya....
"Ka sake min wuya sai na sami damar sanar dakai komai...." Cewar Barr dayaji damk'a sosai....
A hankali Junaid ya soma sakar masa wuya yana watsa masa wani irin mugun kallo had'i da huci
Saida Barr ya koma ya zauna gijif had'i da zubewa jikin garu yana kuma sosa wuyarsa kafin ya d'ago yana duban Junaid da babu alamun rahama a fuskarsa....
A hankali ya soma fad'in "Siraj..... Ahidjo.... Lamid'o....." Ya kuma duban Junaid dake faman ci gaba da tururi lokaci guda Junaid ya jinjina kai kana yace "The three Bastards... Tell me. ... who are you to them....?"
Barr ya jinjina kai yana duban Junaid kana ya soma fad'in
"Ni d'aya ne daga cikin Attorneys na Laushi Group, Companyn marigayi mahaifin Siraj wanda a yanzu haka Siraj yake running..... Kaji alak'ata dasu, sannan naji mamaki matuk'a da suka kasance sanadin K'uncinka sabida a iya sani na sunada alak'a mai kyau tsakaninsu da mutane...."
Murmushi Junaid yayi sabida har cikin ransa yaji dad'in samun wanda zaiyi linking d'insa da three devils d'innan cikin ruwan sanyi kafin ya turo kekensa ya k'araso dab da Barr yace "Haka suke a Fuska, amma a bad'ini sunfi kumurcin maciji guba... A yau zan sanar dakai da su waye kake aiki, da wasu irin azzalumai ka aminta har kake aiki k'ark'ashinsu...."
Barr ya kuma gyara zamansa dirshan a k'asa yana duban Junaid da tuni ya d'aga kai sama yana kallon sararin samaniya dai-dai sanda ya soma fad'in.....
****
*Misau*
Kasa tura k'yauren tayi sabida wani irin k'ugi da cikinta keyi, ba ta yunwa bace saidai koh ta tsoro domin yau karin kummalo maiji da lafiya Innah Balki ta bata....
Tsayuwa tayi tana kuma tsuru-tsuru da idanu tana tuna yau shikenan kashinta ya bushe batasan yanda zasu kwashe da Iya Gaje ba tasan yau rai kad'an zata rage mata.....
"Wayyo Allah na... Wayyo Allah ka ceceni kasa kar Iya ta jibgeni...." Tayi addu'ar a hankali idanunta na k'ok'arin ciko k'walla....
Har zata shiga gidan taja burki ta tsaya jin yanda Gaje take salle mahaifinta uwa ta sami yaronta, dama hakan take masa bashida fad'i a gidansa sai abinda Iya Gaje tace....
"Deejo dani take wasan nan, yau zata sanar dani gidan uwar wa taje ta kwana, shegiyar yarinya hatsabibiya ta iya bajewa d'akin saurayi tayi kwana amma batasan ta kawo min sisin kwabo ba sai anyi magana tace ita saliha batasan zancen ba koh....? Kai kuma sullutu gaula da anyi magana sai kace nice zan lalatata koh, toh yanzu sai ka sanar dani a gidan uwar na lalata maka d'iya....?" Ta k'arashe tana nuni da ludayi saman fuskar sa.... Kaman daga sama suka jiyo ana bugun k'yauren gidan, ko izinin shigowa ba'a basu ba suka tokari k'ofar suka shigo... Ba kowa bane illa Lado da muk'arrabansa... Yana hura taban wiwi yake fad'iwasu Muntala.. Ku shiga lungu da sak'o na gidan ku fito min da ita....."
Jikin Gaje ya d'auki kyarma ta nufi Lado tana fad'in "Lado mai asharalle wai lafiya... Ina Dijon ba'a wajenka ta kwana bane...."
Marin da Lado ya sauk'e mata ya sanyata had'iye kalamanta tana kururuwa....
Lado yaci gaba da fad'in "Ke har kin isa kici kud'ina a dad'in rai, saida mukayi dake kan cewa na jirata hanyar islamiyarsu ashe kinsan 'yar taki 'yar akuya ce baki bata irin tarbiyar da ya kamata ki bata ba, ga abokina nan Tanimu bayansa sai an masa d'auri sabida allon makarantar ta ta dinga rabza masa yanzu haka gashi nan d'ingishi yake, bata tsaya a nan ba ta dinga lailayamu cikin garin nan har saida ta cika mana yashin k'ofar kurmi cikin idanu muka kuma nemeta muka rasa kaman aljana ta b'ace... Toh wllhi kinji na rantse ko ki nemota ko na fanshe kud'ina akanki...." Lado ya k'arashe yana k'ok'arin cazgo kallabinta...