Sashe 50
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwiwoyinta ne sukayi wani irin sanyi sanda ta tura k'ofar d'akin taga babu shi.. Babban abinda yafi d'aga mata hankali shine bata ga kayansa ba... Take wasu irin hawaye suka shiga zarya a idanunta.... Da gaske ya tafi, da gaske Yayanta ya tafi... Kuka sosai take sanda ta nufi waje k'ofar gida ta hangi k'asar bishiyar da yake paka motarsa babu motar..... Bata san sanda ta tsuguna a wajen ba ta shiga rusa kuka mai dalili....
Baffah da Innah da sukayi jigum-jigum a k'ofar Baffan, don tunda zai fita sallan asuba yaga bai ga motarsa ba sannan bai gansa a sahu a masallaci ba yasan akwai wani abun, koda ya dawo gida ma saida ya duba d'akinsa ya tarar baya nan... Tun daga nan yasan Ahidjo tafiya yayi....
Jiyo kukan Deejoh da Innah tayi ya sakata kamo bakin zaninta wani sabon kuka na taso mata....
Baffah baice komai ba sai girgiza kai da yayi tausayin Deejoh na shiga cikin zuciyarsa, shi dama yasan za'a rina, don mai hali baya canza hali, Aliyu bazai canza halinsa ba, tabbas yayi kuskuren aura masa Deejoh....
***
Zaune yake a office yana duba takardun Estates d'in da ya saya recently a Jabi, wayarsa ya ciro cikin suit pocket d'insa kafin ya shiga neman layin Nasaar....
Nasaar dake zaune office d'insa idanunsa sunyi jazir ya k'urama waje guda idanu ba sai ance maka tunanin wani babban abin yake ba, lokaci zuwa lokaci yake huci shi kad'ansa yana murza pen d'in dake hannunsa da iyaka k'arfinsa, tsanin matse pen d'in da yake har saida pen d'in ta fashe a hannun sa lokaci guda yaji masa ciwo a hannunsa, sai sannan ya kula da wayarsa dake faman ruri.... D'an matse hannunsa mai d'igan jini yayi kafin ya d'aga wayarsa nasa, ganin Siraj ne mai kira ya dad'a bak'anta ran Nasaar, kaman bazai d'aga ba don kira na uku kenan....
A hankali ya furta "Imbecile..." Kafin ya d'aga wayar...
Daga d'aya b'angaren Siraj ya sanar dashi yana nemansa ba tareda ya kawo komai cikin zuciyarsa ba...
Azeeza na zaune gaban table d'inta tana wasu 'yan danne-dannenta cikin computer Nasaar yazo wucewa zai shige office d'in Siraj....
Cak ya tsaya yana duban Azeeza idanunsa sun kad'a sunyi jazir, shi kad'ai yasan irin k'unan da zuciyarsa ke masa, musamman idan ya tuna jiya hotel ya gansu itada Siraj.. Jikinta ne ya bata ana kallonta aiko tana d'ago kai sukayi idanu hud'u, fuskar nan nasa tamkar bai tab'a dariya ba.... Gaban Azeeza ya yanke ya fad'i, takai dubanta ga hannunsa dake d'aure da tissure paper da alama ciwo yaji, k'irjinta ya kuma bugawa, tama kasa cewa komai gaba d'aya, bata tab'a ganin Nasaar cikin irin wannan yanayi ba.... Ta yunk'ura zata mik'e cikeda kulawa, saidai kafin ta k'arasa mik'ewa Nasaar ya shige office d'in Siraj....
Ganin Nasaar ne ya shigo yasa Siraj mik'ewa yana kuma bubbud'e documents d'in dake hannunsa yake fad'in "Nasaar are you sure takardun nan sun cika, banso daga baya azo ana samun matsala kaga ba k'aramin kud'i aka zuba....." Aya yayima kalamansa jin sam Nasaar d'in bai tareda shi...
D'ago idanu Siraj yayi yana dubansa kafin yace "Lafiya? Is everything alright....?"
Bai kai aya ba Nasaar ya katsesa da fad'in "Nothing is alright Siraj...."
Ajiye takardun hannunsa yayi yana duban Nasaar d'in cikeda mamaki kana ya d'an girgiza kai yace "Sorry ban gane ba... Mai kake nufi, badai kan Estates d'in bane koh...." Ya k'arashe yana duban Nasaar d'in dake faman huci tamkar mai shirin kai masa naushi...
Nasaar yaci gaba da fad'in "Siraj, don't you try that with Azeeza....." Cikeda gargad'i yayi maganar....
"Wait what did you say... What do you mean Nasaar, meye kake fad'i....?" Cewar Siraj dake duban Nasaar d'in cikeda mamaki....
Matsowa Nasaar yayi dab da Siraj yana bud'e idanunsa yake ci gaba da fad'in "Nasan ka san abinda nake nufi Siraj, don't try it with Azeeza...."
Girgiza kai Siraj yayi lokaci guda fuskarsa ta sauya kafin ya soma fad'in "I've no idea what you're talking about, yes I admit I love your sister in-law, amma bansan mai kake nufi da kar nayi trying da Azeeza ba... What the hell was that...?"
Murmusawa Nasaar yayi da gefen bakinsa kana yace "Come on Mr President, you know I know you well, and I know all of your secrets cos I'm your lawyer,...."
Cikin sauri Siraj dake faman huci ya katse Nasaar da fad'in "You shut up already! get out of here... Get the hell out of my office, now!!!" Ya k'arashe yana nuni da k'ofa wa Nasaar....
Girgiza kai Nasaar yayi had'i da murmushi da gefen bakinsa kana yace "You can't boss me when it comes to our little secret you know.... So tell me itama abinda kayi da sauran matan kake shirin yi da ita,...?" Ya kuma murmusawa kafin yaci gaba da fad'in "You've always been a womanizer, ko k'arya ne...? Kowa na ganinka sallah sallah while on the contrary kai ba mutumin da ake zato bane.... Duk 'yan matan da kake nema kafin ka kai ga aurensu kake lalata masu rayuwa, bansan mai ya kashe sauran but zaka k'aryata akan Zeenat...? Zaka k'aryata cewa baka aikata hakan da Zeenat ba, nida kai munsan Zeenat committed suicide because she never loved you and you forced her tayi zina dakai kafin aurenku, you even threatened her idan bata amince ba zaka kashe saurayinta da take so take mafarkin aura.... A dalilin haka ta kashe kanta ko ba haka bane..."
Girgiza kai Siraj yake kana yace "No Nasaar Zeenatu was murdered, bata kashe kanta ba.... Tsohon saurayinta ya kasheta...."
Murmushi Nasaar ya kumayi kana yace "Siraj kenan, meyasa ka dage tsohon saurayinta shi ya kasheta, sabida baka so ka rayu with the guiltiness ya ringa eating d'inka alive.... Sabida kai da abokan ka kunyi tarayya wajen murk'ushe rayuwar tsohon saurayin Zeenat wanda bashida laifin komai.... Sannan da mahaifin Zeenat ya shigar da k'ara ni ne lauyan da na tsaya tsayi da fata har aka kori shari'ar akayi watsi da ita aka kuma rufe maganar harta family d'inka basu san da zancen ba.... Siraj ni ne nan na rufe sirrin FUSKA UKU ya rufu babu wanda ya kuma ji har rana mai kaman ta yau... Zeenat ta rasa rayuwarta because of you Siraj, sannan kaida abokan ka kuka kashe JUNAID tsohon saurayin Zeenat...."
Siraj dake zuban hawaye sabida laifuka da dama da ya aikata a baya cikin sauri ya rik'o hannun Nasaar kana ya soma fad'in "Nasaar you know I've changed completely and wllhi ni ba Siraj d'in da ka sani a baya bane... I love Azeeza with my heart, kuma itama wllhi tana sona.... Nasaar dan Allah kar ka zama sanadiyan rasa farin cikin da nake shirin samu....."
Fincike hannunsa Nasaar yayi kana yace "No Siraj, ai laifukan daka aikata zaiyi wuya Ubangijinka ya barka ka sami farin ciki a wannan rayuwar taka, har sai ka biya laifukan da kayi a baya, shin banza Allah yake d'auke rayuwar duk 'yan matan da kake nema.... Idan baka sani ba ka sani, hakkin Zeenat da Junaid sune suke binka.... Siraj I'm sorry bazan iya baka Azeeza ba, baka auren Azeeza sanin ko kai waye tamkar cin amana ne, na sani mu dukanmu masu laifi ne... Bazan iya ba sabida kai ba tsarkakke bane....." Ya k'arashe cikin tsananin rawar murya idanunsa sunyi rau-rau tsananin soyayyar Azeeza na fizgarsa, b'angare na zuciyarsa yana tuna Bulama shi ya tsunduma sa cikin rayuwar Siraj...
Cikin sauri ya fice daga office d'in yana mai k'ok'arin saita kansa....
Gijif Siraj ya zauna cikin kujeransa numfashinsa na fita da k'yar, dafe kansa ya kumayi wasu hawaye na kuma zubo masa, Nasaar ya d'aga masa mik'in da ya kasa warkewa cikin zuciyarsa....
***
Da k'arfin gaske Junaid ya bugi wheelchair d'insa yana wani irin huci yake fad'in "Sabi'u why... Yaya akayi hakan ta kasance, saida ka tabbatarmin baza'a sami failure ba gashin an samu.... Na rasa chance d'ina..."
Shafa kansa Sabi'u yayi kana yace "Junaid, wllhi canza hanya yayi, duk a tunani na ta Jos zaibi ashe ta Kano yabi.... Amma kar ka damu friend idan ya tsallake wannan bazai tsallake gaba ba I promise you....."
Huci kawai Junaid keyi kafin ya kashe wayar ba tareda ya kuma furta koda kalma ba.... Shi kad'ai yake faman tururi yana hura hanci, idan ka tsaya gefensa zaka iya jiyo turirin da yakeyi.... Da k'arfin gaske yayi jifa da wayar yana furta "Damn it...! You damn imbecile da hannuna ya kamata na kashe ka..... Kayi escaping wannan amma gaba I promise you bazaka sha ba.... I'll face you man to man even if I'm on this damn chair...." Ya k'arashe yana duban kujeran nasa da hannayensa...
Nana A da Aunty Larai dake tafe suna zaga foundation d'in suka jiyo kaman sauti daga office d'in Junaid...
Nana A ta dubi Aunty Larai tace "Kina ji kuwa....?" Ta k'arashe tana nuni da office d'in Junaid...
Cikin sauri Aunty Larai ta jinjina kai kana tace "Naji Asma'u, sauri muje mu duba shi...."
"Yeah sure, let's go....!" Nana A ta fad'i cikin sauri sanda suka nufi office d'in Junaid.....
Junaid yana jiyo sautin takalmansu yayi saurin saita kansa tamkar yana aiki.... K'wank'awasa k'ofar sukayi suna masu neman izinin shiga.... Take yayi saurin tura kekensa ya k'arasa ya d'au tarwatsttsen wayarsa ya had'a kafin ya basu izinin shigowa...
Kallon kallo Aunty Larai da Nana A suka shiga yima juna ganin lafiya suka tadda Junaid...
Da sakin fuskarsa suka gaisa, kafin Aunty Larai ta fice ganin babu abinda ke faruwa...
Nana A kuwa k'uri ta masa tana karantarsa bayan Aunty Larai ta fice...
D'an dubanta yayi had'i da d'aura murmushi saman fuskarsa kafin yace "Are you alright Gorgeous.... Akwai wani abu ne.....?"
D'an girgiza kai tayi had'i da tab'e baki kana tace "I know you're not well, I can see it from your eyes... Meke faruwa...?"
Kauda fuska Junaid yayi fuskar Kawunta Siraj na masa gizo cikin idanunsa, a kullum idan ya kalli Nana A fuskar Siraj yake gani k'arara a tattareda ita sai yaji tamkar ya murk'usheta ko tsananin hatred d'in da yake cinsa ciki zai ragu.... Girgiza mata kai yayi kafin a hankali ya furta "Babu komai Asmah, I'm.... Just fine..."