← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 98

Sashe 60

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka take fad'in "Babu ruwanka dani koma mutuwa nayi, you've no idea how much I hate you..." Ta k'arashe tana kuka sosai..

Koda suka iso gida ma da kansa ya sureta ya jefata a d'aki suka kulleta shida Junaid...

Kuka Azeeza take daga cikin d'akin tana rok'on Yayanta Junaid ya bud'eta...

Cikin b'acin rai yake fad'in "This is the consequences of your actions Azeeza, a cikin d'akin nan zaki zauna har sai na gama d'aukan fansata kan Siraj, na tabbata rashinki zai jefasa cikin musiba da k'unci yanzu zai d'and'ani zafin ka rasa masoyi kafin ya bak'unci lahira...

Cikin Kuka Azeeza take fad'in "Yaya Junaid don't hurt him please, I beg you kar ka cutar dashi, hurt me instead, dan Allah kar ka cutar da Siraj...."

Duk kalaman da take a kunnen Nasaar ji yake kaman yaje ya shak'e Siraj Azeeza ta daina tunaninsa... Cikin sauri ya fice daga parlorn don bazai iya ci gaba da sauraron kukan da take akan Siraj ba....

Haka suka kulle Azeeza saidai su dinga mik'a mata abinci babu fita

A haka aka kuma kwashe sati biyu, a dai-dai wannan lokaci Sabi'u yayi shirin tunk'aran iyayen Ahidjo domin ya sanar dasu mutuwar d'ansu....

Gidan Mai unguwa Sabi'u ya soma zuwa ya kuma sanar da abinda ya kawosa cewa sak'o yazo badawa ga mahaifan Aliyu, Mai Unguwa ya buk'aci a kirawo Malam Sanda saidai Sabi'u ya nuna yafiso idan da hali a kaisa can gidan Malam Sandan ya fad'i masu sak'om domin kaman hakan zaifi...

Mai Unguwa ya jinjina kai kana ya kirawo d'aya daga cikin 'yan fadansa yace suyiwa bak'om rakiya zuwa gidan Malam Sanda...

Tafiyace mai d'an rata kad'an dashike gidan ba'a cikin gari yake ba kafin suka isa....

Sank'ira yayi sallama k'ofar gidan Malam Sanda, baki na biyu aka amsa daga ciki kafin Malam Sanda ya fito suna gaisawa da Sankira... Nan Sankira yake masa nuni da bak'on da yazo nemansa daga can birnin tarayya

Malam Sanda ya maido da dubansa ga Sabi'u kafin ya mik'a masa hannu sukayi masabaha, cikeda rusunawa Sabi'u ke gaida Malam Sanda kafin Sankira ya masu sallama yace ya barsu lafiya...

Malam Sanda ya dubi Sabi'u kana yace "Toh bawan Allah gashi ban wayeka ba, lafiya dai koh...?"

Sabi'u ya d'an gyara tsayuwarsa kana yace "Toh wato Baba wani Al'amari ke tafe dani, kuma akan D'anka Ahidjo ne, amma idan bazaka damu ba zanso mu shiga daga ciki sai na sanar dakai komai gaban sauran iyalan naka domin Ahidjo ya sanar dani yanada iyali a nan gida..."

Baffah ya jinjina kai kana yace "Haka ne, amma abinda ban gane ba shine wani sak'o ne zai baka dashi bazai iya zuwa ba, wato abin nasa har ya kai ya daina zuwa saidai yayo aike, toh idanma wani abin ya baka ka kawo mana ka maida masa kayansa don dagani har iyalaina bamuda buk'ata...."

Shiru Sabi'u yayi yana duban Malam sanda had'i da karantarsa kana ya d'anyi gyaran murya yace "Baba wato wannan Al'amari da zan sanar daku Al'amari ne mai girma, kayi hak'uri mu shiga daga ciki, ka zauna kaima domin sak'o na magana zan sanar daku ba ta dukiya ko na wani abu makamancin haka ba... Dan Allah Baba..." Ya k'arashe cikin k'ank'an dakai...

Shiru tamkar Malam Sanda bazaice komai ba sai kuma yace "Shikenan mu shiga daga ciki...

Baffah da kansa yayiwa Sabi'u shimfid'a kafin ya kirawo Innah, ganin Baffah da bak'o matashi ya sanya jikin Innah yin sanyi don ba kowa ya fad'o mata ba face tilon d'anta, gaisawa Innah sukayi da Sabi'u kafin Baffah ya buk'aci ta kirawo Deejoh su taho tare...

Nan Innah ke sanar da Baffan Deejohn bataji dad'i ba tun safe zazzab'i ya rufeta, bata gane jikin ba....

Baffah yace "Subhanallah yaya baki sanar dani ba...?".

Naga zazzab'in ya d'an sauk'a ne shiyasa ban sanar dakai ba amma yanzu haka ma bacci take..."

Baffah ya jinjina kai kana yace "Ki zauna toh wannan bawan Allah sak'o yaron nan ya basa ya kawo mana..."

Jin haka yasa k'irjin Innah bugawa da k'arfin gaske domin kuwa tabbas tasan Ahidjo Baffah ke nufi, lokaci guda ta nemi waje ta zauna k'irjinta naci gaba da bugu, don haka kurum ta tsinci kanta da tsoron jin sak'on da za'a isar masun

***

*A garin Damaturu*

Yau yake cika sati biyu cif a asibitin, a hankali ya soma motsa d'an yatsansa, yana mai k'ok'arin bud'e idanunsa da suka masa nauyi tamkar an d'aura masa manyan duwatsu, da kad'an kad'an idanun nasa suka bud'e gaba d'aya... Nurse dake k'ok'arin d'aura drip mamakine ya cikata taga abinda batayi zato ba.... A guje ta fice kiran Dr Sahal hakan yayi dai-dai da shigowarsu Baba Malam da kuma Hafiz, ganin Nurse d'in ta fito daga d'akin a guje ya sanyasu nufan d'akin cikin sauri...

*Toh fah mai karatu wasan zai soma... Just stay tuned guys*

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*43*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Saita kansa ya d'anyi had'i da k'ak'aro murmushin k'arfin hali kana yace "K'araso mana...."

Azeeza da tayi tsaye a wajen tamkar wacce ruwa ya shanye da k'yar ta iya jan k'afafunta ta soma tafiya tamkar kazar da k'wai ya fashema....

Kujeran dake gaban table d'insa ya nuna mata kana yace "Zauna...."

Babu musu ta zauna kaman yanda ya umarta d'in.... K'irjinta sai wani irin bugu yake tamkar zai fito waje, k'warjinin Siraj gaba d'aya ya cika wajen., sunan Allah kurum take ambata cikin zuciyarta don batasan da wanne zata soma ba....

K'uri Siraj ya mata yana karantar ta ganin yanayin nata, tamkar ba Azeezar da ya sani mai tsiwa da confidence ba.... Yanayin nata sosai ya d'aga masa hankali domin kuwa damuwa ya hango k'arara saman fuskar sa....

"Azeeza lafiya, meke faruwa...?" Ya tambaya cikeda kulawa bai janye idanunsa daga dubanta ba

Banda murza 'yan yatsun hannunta babu abinda take, da k'yar ta d'an iya k'ok'arin saita kanta kana tace "Sir.... Dama.... Dama.....!" Shiru tayi ta kasa ci gaba da magana sabida girman abinda take shirin fad'in

Siraj ya matsar da fuskar computer d'in dake gabansa yana dubanta sosai kana yace "Ina saurarenki wani abu ne ya faru, ko wani abin aka maki a nan, fad'a min ko wanene...." Ya k'arashe cikin d'an d'aga murya wannan karan...

Muskutawa ta kumayi kukan da take mak'alewa lokaci guda ya shiga zuwa bakinta....

Cikin sauri Siraj ya shiga girgiza kai yana fad'in "Oh no no please Azeeza, if there's one thing I hate in this life shine naga mace na kuka, please ki daina kukan nan kinji...." Ya k'arashe murya cikeda kulawa....

Bata daina kukan ba saima k'aruwa da yayi, Siraj ya mata k'uri kawai don baisan yaya zaiyi ya lallasheta tayi shiru ba.... Hannayensa yake k'ok'arin kaiwa saman nata, har saida yakai hannayensa kusan nata kaman wanda ya tuna wani abu sai kuma ya fasa rik'o hannayen nata, wani irin zogi kukan nata ke masa can k'asar zuciyarsa, Azeeza kuwa kaman cewa ake ta k'ara....

Dafe kansa kurum yayi had'ida tattare naman goshinsa lokaci guda ya d'an matso da fuskar sa kusan nata....

A hankali ya soma furta "Azeeza... Zeeza look up, ki kalleni please....!"

Yayi maganar cikin tsananin sanyin murya.... Cak kukan nata ya tsaya, lokaci guda ta d'ago idanu tana dubansa, chocolate face d'inta ya zamto very pale, fuskar Siraj dab nata ta gani, k'wayan idanuwansu ne suka had'e waje guda.... Su duka d'in basu san suna kallon juna haka ba.... Lokaci guda Azeeza tayi saurin sadda nata idanun k'asa k'irjinta naci gaba da bugu cikin sauri, sai faman shan zuciya da take alamun taci kuka...

K'ok'arin saita kansa shima yayi had'ida d'an yin gyaran murya kana ya soma fad'in "Azeeza ever since I met you, I become allergic to your tears...."

Kallonsa tayi da kod'add'un idanunta...

Siraj ya jinjina kai sihirtaccen murmushi saman fuskarsa kafin yaci gaba da fad'in "Yeah, idan na ganki kina kuka toh shakka babu I'll fall sick.... Dan Allah kar ki sake kuka irin haka kinji idan ba so kike nayi ciwo ba...." Ya k'arashe idanunsa a kanta....

Lokaci guda ta d'anyi murmushi sabida harga Allah ya bata dariya da yace he's allergic to her tears....

Ganin tayi murmushi yasa Siraj jin dad'i shid'inma murmushi saman fuskarsa kafin yaci gaba da fad'in "Ina saurarenki, ki kwantar da hankalinki ki fad'a min meke faruwa...."

K'irjin Azeeza ya kuma bugawa but she has to do this batada wani zab'i muddin tana son kub'utar da Siraj....

A hankali ta soma fad'in "Sir there's something you need to know......!" Batakai aya ba wayan salulan Siraj ta soma ringing, ganin Nasaar ne mai kira ya sanyasa d'agawa had'ida d'an d'aga mata yatsa yana fad'in "Excuse me I've to take this..." Don yasan it must be something about business

"Yes Nasaar ina jinka...... Whattt....!!?" Ya fad'i yana mai mik'ewa tsaye..... Lokaci guda Azeeza ma ta mik'e tana mai ci gaba da dubansa ga k'irjinta dake wani irin bugu don ita kam sam bata k'aunar tarayyan Nasaar da Siraj tinda tasan cin dunduniyarsa yake da sunan taimakawa Yayanta wajen d'aukan fansa....

Girgiza kai kurum Siraj yake yana karanto innalillahi kafin yace "Nasaar kar ka bar wajen ka kira duk wani kampani na kashe gobara daka sani, gani nan tafe..." Daga haka katse wayar yayi cikin sauri ya nufi ma'ajiyan suit d'insa ya d'auka yana k'ok'arin saka suit d'in Azeeza ke tambayarsa meke faruwa, damuwar dake bisa fuskarta sosai ya k'aru....

Yana mai daidaita zaman suit d'in jikinsa yake fad'in "Wllhi Estates d'in da bamu jima da saya bane wuta ya kamasu, yanzu haka fire service sunata iya k'ok'arinsu wutan tak'i cinyewa, Allah yasa babu kowa cikin gidajen.... Zan tafi yanzu, and please office d'ina na hannunki don bansan yaushe zan dawo ba..." Daga haka ficewa yayi cikin sauri wani wayar na shigo masa....

Komawa kurum Azeeza tayi ta zauna cikin kujera had'ida dafe kanta, itakam anya zata iya zama tanaji tana gani ana cutar da Siraj, gaskiya bazata iya ba, gwara ta tattara ta koma Damaturu k'ila can tafi samun kwanciyar hankali....

Kafin ta bar office d'in saida ta tattara masa duk wasu takardunsa dake bisa table tayi ta maidasu cikin folder a gefe, gaba d'aya Azeeza wani iri take jinta, zuciyarta ta cika da damuwa sosai.. Daga office gida ta wuce straight....
Chapter 60 · 0% Book details