← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 98

Sashe 89

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin hawaye na gangaro mata ya sanaya jikin Siraj yin sanyi.... A hankali ya d'ago fuskarta yana duba, lokaci guda yake furta "Hey..... Why those tears, are you okay... Don't you wanna help me.... Didn't you say that you love me.... Am I asking for too much... Nana H com'on ban tab'a tambayarki wani alfarma irin haka ba... Idan ban aureta nan da sati uku ba wani daban za'a aura mata... Please do this for me... Kinji...." Ya k'arashe wasu hawayen na sauk'o masa wanda ba na komai bane illa tunanin idan ya mutu zai iya barin family d'insa cikin garari, Junaid da Lamid'o sune babban tashin hankalinsa...

Lokaci guda Nana H ta rungumeshi sosai cikin jikinta itama d'in hawayen ne ke sauk'a mata da gaske Siraj kuka wa mace yakeyi, da gaske ya makance akan Azeeza, bata tab'a ganin soyayya irin tasa ba, shin dama ana irin haka a gaske ba'a film ba, inama sabida ita Uncle ke kuka....

A hankali ta soma fad'in "I'll Uncle, I'll help you...." Tsananin kukan da take ya hanata ci gaba da magana

Shima d'in lumshe idanunsa yayi tausayinsu gaba d'aya ya cika zuciyarsa....

***

Daddah tana ficewa Mairo da Umma Marie suka d'auki hanyar gidan Baba Malam, saida suka bari Daddan ta d'an jima da fita kafin suma suka fice sabida kada su cimmata....

Ita kuwa Daddah tana isa gidansu Dakura ta tarar da saurayin Dakura TJ a k'ofar gidan saman motarsa ya d'aura k'afafu d'aya kan d'aya, dama tuni Dakura ta kirata ta sanar da ita yace yana hanya, kowa a layin tsoron TJ yake don yanzu zai maka cune da 'yan dabansa su maka lilis idan ka nemi shiga rayuwarsa, shiyasa ko Balaji mahaifin su Dakura ya rasa yanda zaiyi da TJ balle ya hanasa zuwa wajen d'iyarsa musamman yanzu da Dakura ta shiryu da taimakon Allah ta sanadin Daddah...

Kafin ta shige cikin gidan tayi tsaye tana k'are masa kallo yana zaune saman mota k'afafu d'aya kan d'aya karan sigari mak'ale a bakinsa sai busawa yake, uwa uba ga wata sark'a mak'ale a wuyarsa uwa matashin Kare.... TJ da yaga kallon da wannan tsohuwa ke masa yak'i k'arewa busa mata sigari yayi kana yace "Ke ya dai chuss, shiga gidan nan kice Dakura ta fito idan bazata iya fitowa ba kuma na shiga na fito da ita...." Ya k'arashe yana kuma feso mata hayak'in sigari ta hanci alamun ya shahara

Murmushi ta sakar masa a fili kana ta rusuna tace "An gama yallab'ai, badai Dakura ba zan kira maka ita yanzu..."

Ko kallo bata ishesa ba yaci gaba da pito yana busan hayak'insa...

Daddah tayi k'wafa cikin zuciyarta take furta "Ubanka zakaci...!"

Tana shiga gidan ta tarar da Dakura da Goni yana mata fad'an taje ta sallami wannan d'an iskan saurayin nata a k'ofar gidansu ta kuma sanar dashi ta tuba...

Caraf Daddah ta cab'i zancen da fad'in "A'a babban Yaya wannan ai aikin ka ne, kinga shiga ciki ki d'auko min almak'ashi cikin kayan sana'a.."

Tuni Goni ya soma gaida Daddah yana murmushi don sosai matar ke burgeshi, Falmata na jin muryar Daddah ta rarumo almak'ashin ta fito a guje....

"Daddarmu.... !!" Falmata tace sanda take rungume Daddar...

"Ke ni yi a hankali kada kijimin ciwo..." Daddah tace sanda take karb'an almak'ashin...

"Malam Goni muje koh...." Ta fad'i tana gyara zaman mayafinta. Sai ka rantse da Allah abin arziki zataje yi....

Falmata na rik'e da almak'ashin take fad'in "Muje Daddarmu nice orderly d'inki wllhi... Bana bari a bani labari ba...."

Har suka iso TJ baisan sun iso wajen ba sai surace da hayak'i yak'e...

Daddah ta dubi Goni tace "Malam Goni kayi zaman k'auye...?"

Goni yace "nakan je hutu dai da nake k'arami..."

Daddah ta jinjina kai tace "Toh ka tuna rik'on da aka wa buhun dawa idan aka ciro amfanin gona...?"

Goni yace "Da hannu bibbiyu ake damk'esa.."

Daddah tace "Alhamdulillahi... Kame min wannan Karen....."

TJ dai sai kallon ikon Allah yake wannan fah itace matar da ya aika kiran Dakura, kafin ya ankare saiji yayi Goni ya damk'e duka hannayensa biyu ta baya...

"A'a kai lafiya meye haka... Yaya dai..." TJ yace yana k'ok'arin k'watar kansa..

"Uwarka ne ba lafiya, har ni zaka kalla ka wulak'anta ka fesa min hayak'in sigari, toh kayi wa tsohuwarka mai kalwa ta bakin tasha... Malam Goni damk'e mani shi na masa askin yaran musulmai, Ke Falmata bani askar nan...." Ta k"arashe tana kwab'e mayafinta...

Falmata mai zatayi banda dariya, matasan lungun da TJ ke masu big time shiga babban yaro tuni suka ciro waya suka soma d'aukansu ana aski wa TJ sai ihu yake yana rok'on Daddah tayi hak'uri... Bata tsaya ba saida tayiwa TJ tal da cimbirarren sumarsa... Tana gamawa ta janyo sark'ar dake wuyarsa tana fad'in "Dan ubanka sai kayi min haushin kare na sakeka... Taci gaba da shak'e masa wuya da sarkar yana ihu yana bata hak'uri... Inaa Daddah kaman cewa ake ta k'ara, "badai kai ka mayar da kanka dabba ba Allah yayika mutum, imin haushin Kare nace..." Ta k'arashe tana kuma tura kansa cikin hammatarta, Falmata dariya harda zubewa k'asa, yara kuwa chaa sun cika lungun Babban yaro yasha damk'a

Haka dole TJ yayi haushin karen said baiyi shiri ba....

***

A farfajiyan foundation d'in Junaid ya hangeta ta nufi hanyar office d'inta, maimakon yaji haushinta sai wani sanyi da zuciyarsa tayi, duk wani damuwa dake cikin zuciyarsa sai ya nema ya rasa, wani irin nutsuwa zuciyarsa ta shiga samu a hankali, ya jima yana dybanta ba tareda ya iya koda motsawa ba....

Jikinta ne ya bata d'aya daga cikin su na wajen, Lamid'o ko kuwa Junaid, tanaji a jikinta akwai d'aya daga cikin su biyun a wajen....

A hankali ta juyo tana dubansa, ai kuwa idanu hud'u sukayi.... Lokaci guda ta d'auke idanunta daga duban nasa tasa kai zata shige saiji tayi ya ambaci sunanta "Asmah....!!"

Cak ta tsaya ba tareda ta juyo ba, hakan ya basa daman tura wheelchair d'insa ya isa gareta.... D'an kauda kanta gefe tayi alamun har lokacin tana fushi dashi...

"Asmah I'm...." Shiru yayi ya kasa ci gaba da magana domin kuwa hak'urin da yake shirin bata har cikin ransa da zuciyarsa ne ba wai to fool her kaman yanda ya saba ba, baisan yaya akayi hakan ta kasance dashi ba, bai san ya saba da ita har haka ba.... Ganin tana k'ok'arin sa kai ya kuma saurin shan gabanta idanunsa tar akanta yanda ta baiwa wani gefen mahimmanci sam idanunta basa dubansa...

Saida ya d'anyi k'ok'arin saita kansa kafin yaci gaba da fad'in "I'm sorry.... I'm sorry Asmah, please understand me, I.... I know I shouldn't have reacted that way.... Kiyi hak'uri kinji...."

Sai sannan ta d'an dubesa kafin ta k'ak'aro mirmushi wanda yafi kama da yak'e... "Babu komai, komai ya wuce..."

"Are you sure...?" Ya tambaya yana mai narkar da idanunsa wanda su sukafi komai kyau a fuskar sa...

Bata juran kallon k'wayar idanunsa, a hankali ta d'an sadda kanta k'asa kana ta jinjina masa kai alamun eh....

Murmushi Junaid ya saki had'ida matsowa kusanta, murya can k'asan mak'oshi ya furta "Thank you.... Thank you gorgeous...."

Yanayin da yayi maganar ya sanyata d'ago ido tana dubansa, suka d'an jima a hakan, itakam bata san mai takeji gameda shi ba, ta kasa tantance ko hakan soyayya ce musamman da yanzu maza suka fita cikin zuciyarta gaba d'aya... Shi kuwa Junaid a b'angarensa wani irin sanyi da dad'i yake ji can k'asar zuciyarsa tunda ya bata hak'uri kuma ta hak'ura, a 'yan kwanakin da yayi tana fushi dashi ba k'aramin jin jiki yayi ba..... Duk iya k'ok'arinsa ganin ya yakice hakan cikin zuciyarsa amma ya kasa..... A daidai wannan lokaci Lamid'o ya danno kai cikin foundation d'in, wani irin mummunar fad'uwan gaba yaji ganin Nana A da Junaid tsaye a farfajiyan wajen suna jifan juna da kallon soyayya, koda ba'a fad'a masa ba bazai tab'a mance fuskar Junaid ba bayan shekaru hud'u da suka rabu....

***

A tare Bulama da Sabi'u suka nufi cikin gidan Mas'ud Laushi... Alhaji Bulama yxa jima yana bin gidan da kallo yana tuna abubuwan da suka faru shekaru sama da arba'in... Tabbas yau zukata zasu tuna abubuwa a sa'ilin da sukayi idanu hud'u da fuskokin da suka jima basu gani ba....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*59*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

D'aya daga cikin securities masu tsaron gate ya k'araso yana kuma tambayarsu waye za'a sanar a ciki...

Bulama ya dubesa da kyau kana yace "Ka sanar dasu Detective ne mai binciken b'atar jikarsu Nana Khadijah...."

Shi kansa security d'in ya jima yana duban Bulama kafin Sabi'u ya gyara zaman suit d'in jikinsa kana yace "why are you still here? Ko bakaji abinda aka ce bane....?"

Cikin sauri Security d'in ya jinjina kai kafin ya nufi cikin gidan....

Sanda yajewasu Ammah da wannan batu ba Ammah kawai ba harta Ayiya saida ta tsinci kanta da fad'uwan gaba ba tareda sanin dalili ba....

Take Ammah ta basa izinin ya shigo da Detective d'in...

Jim kad'an security d'in ya dawo ya sanar dasu Bulama cewa an masu izinin shiga....

Ammah na zaune saman kujeran dake daga center wanda dama akanshi ta faye zama yayinda Ayiya ke zaune saman armchair daga gefe, su duka biyun sun zuba wa k'ofa idanu ga wani fad'uwar gaban dake addabansu ba tareda sun san dalili ba, gani suke tamkar Nana K ce zata shigo....

Sandarsa ya soma sakowa cikin parlorn kafin gangar jikinsa da fuskar sa suka ida shigowa....

Basu fahimce waye wannan tsohon ba wanda wani matashi ke biye dashi a baya ba har saida ya ida shigowa cikin parlorn sosai, k'irajensu suka yanke suka fad'i lokaci guda, a dai-dai lokacin da ya d'ago idanu yana dubansu ya sanyasu mik'ewa a tare su duka biyun daga Ammah har Ayiya....

***
Chapter 89 · 0% Book details