Sashe 2
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafin ta soma magana Sule ya tari numfashinta da fad'in "Wllhi wllhi Ayiya ba laifina bane, kindaiga yanda Nana Hafsat ta fice a gidan nan cikin fushi da b'acin rai, ni kuma wllhi magiyan da Nana Asma'u tayita min shiyasa na kaita..."
Baikai aya ba ta katsesa da fad'in "Ka kaita a muzanta ta a wulak'anta ta a fad'a mata kalamai marassa dad'in ji koh... Kadai san Hafsatu ba mutunci bane da ita wulak'anci sam bai mata wahala, ni kuma ina numfashi k'aryan mutum ya muzanta 'yar albarka ko ya wulak'anta ta... Kai billahillazi sai mu tafi har kotun Buhari da duk mahaluk'in da ya hana 'yar Albarka rawan gaban hantsi...."
Sule dai dubanta yake cikeda mamaki yanda yaga bilhakk'i laifinsa kawai Ayiya take gani sam bataga laifin Asma'u ba.....
"Ayiya bafa ni na kar zomon ba rataya aka bani....."
"Kai tafi can rufe min baki, da wani abin ya sameta yau da ka gane kurenka...."
Ta wuce fuuu tana ci gaba da sababi....
Nana A ta bita da kallon mamaki yanda sam fad'a bai mata wuya musamman idan akanta ne.... Ko tankata batayi ba ta janyo hannunta suka nufi cikin gidan..
Sum-sum Nana A ta take mata baya...
A parlor suka tarar da Ammah ta rapka uban tagumi, don duk ranar da Siraj da Nana H suka b'ata sam gidan haka zai zamto babu walwala domin gaba d'aya basu gane kan Siraj har sai ya shirya da niece d'in tasa wacce yake matuk'ar k'aunarta da kuma jida ita....
****
Bakin zaninta ta kamo tana kuma goge hawayen da suka mak'ale cikin idanunta take ci gaba da fad'n
"JUNAID ka tabbata zaku iya zama ku biyu rak, ka tabbata komawa wancan gari mai bak'in tarihi shine jin dad'inku..... Junaid I'm afraid... Ina tsoron kada su sake ganinka don na tabbata a iya tunaninsu ka mutu tuntuni...."
Matashi ne wanda a k'iyasce bazai gaza shekaru 32 ba zaune saman wheelchair aka kirada JUNAID, dukda cewa a ido k'afafunsa lafiya lau suke saidai a zahiri ko motsasu bai iya yi, yau kusan shekaru hud'u kenan da faruwan Al'amarin....
Cikin tsanaki ya soma tura tayan keken guragun nasa har ya iso gaban middle aged woman d'in da ke ci gaba da matsan k'walla...
Cikin muryarsa wanda yake tamkar ana hura sarewa ya soma magana...
"Umma Marie thank you for everything.... Thank you for taking care of us.. Nida Azeeza, na gode da jinyata da kikayi, na tabbata banida abinda zan biyaki dashi... Kuma na gode da b'oyeni da kikayi a lokacin da ake farautar rayuwata.... Umma Marie I don't have a choice than to face those three..... Nayi alk'awarin d'aid'aita FUSKA UKUN nan ta ko wani irin yanayi, kiyi hak'uri Umma Marie dole ce tasa nayi hakan..."
Cikin rawar murya Umma Marie tace "Toh Junaid baka tsoron ka jefa rayuwar Azeeza cikin had'ari, meyasa bazaka tafi kai kad'ai ba ka barmin Azeeza, kar wani abin ya taso kai kuma ba k'afafu gareka ba....."
Murmusawa yayi had'i da sunkuyar da kai ya k'urama k'afafunsa idanu kafin ya d'ago ya dubi Umma Marie yace "Kar ki damu Umma I can protect her and provide for her... Bazan tab'a bari wani abu ya sameta ba, ki kwantar da hankalinki kinji....."
Jigum tayi tana dubansa kafin tace "Shikenan, Allah ya tsareku gaba d'aya, amma Junaid muddin naji wani mummunar labari gamedaku zan baro Yobe na taddaku a can Abujan...."
Murmusawa ya kumayi kana yace "Umman mu kar ki damu, na rigada na shirya, kawai taimako guda da zaki sake min shine ki shawo kan Azeeza ta yarda ta biyoni, and please kar ki sanar da ita komai gameda k'udirina..."
*SameenaAleeyou...📚**FUSKA UKU*🏮
*02*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
_*Tambuwal* _Sokoto_
Zaune suke baje-baje a tsakar gidan ko wacce hannunta rik'eda kananan beads irin wanda ake had'a sark'a na amare dasu....
Budurwa ta tsakiyar mai kimanin shekaru 24 itace ke fama zira na hannunta tana yi tana taunar chewing gum ga d'aurinta a gaban goshi irin wanda hausawa ke cema ture kaga bala'i, itako wacce ke zaune daga k'arshen tabarman sai faman 'yan wak'e-wak'enta take tana had'a nata 'yankunnen
Wata dattijiwar mace ce wacce bazata gaza shekaru 58 ba ta fito hannunta rik'e da langa tana duban 'yanmatan wanda yanzu sun k'ware sosai a sana'ar tasu, har cikin ranta take jin dad'in yanda suka rik'i sana'arsu babu ruwansu da abin hannun saurayi, shiyasa take matuk'ar son k'awancen d'iyarta da Zaliha don ya fiye mata k'awance da yaran lungun nasu don duk bawai tayi na'am da tarbiyarsu bace....
Sai sannan 'yan matan suka lura da ita, har suna had'e baki wajen cewa "Dadda barkada fitowa...."
Fuskarta d'aukeda murmushi tace "Sannunku da k'ok'ari 'ya'yana Allah dai ya dafa maku...."
Gaba d'aya suka murmusa itako mai taunar chewing gum d'in harda wani yin k'araras dashi kana tace "Ameen Daddata abin alfaharita, da kud'in beads zan kaiki Makka na sai maki hak'orin gwal...."
Nan fah Dadda ta washe baki tace "Allahumma ameen d'iyata...."
Ana cikin haka wani almajiri yayi sallama ya soma gaida Dadda da tuni ta gimtse fuska don tasan yaron bazai wuce aike yazo ba.... Aiko kaman jira yaron yake nan ya soma fad'in "Wai ana sallama da MAIRO a waje...."
Ai bai ida maganar ba Dadda ta dasa butar ta a k'asa kana tace "Jekace bazatazo ba dan uwarka...."
Yaro kuwa jin haka ya fice a guje har yana cin karo da k'yaure...
Dadda taci gaba da sababi tana fad'in "Inyi ai kaji irinta, dagaji sune irin samari masu lalata yaran mutane, toh dan ubanka bazata zo ba, salon ya matseta a lungu koh... Ni d'iyata sai na darje mata miji kafin na aura mata ehe, babu shegen da zai wanko b'aragurbin k'afafunsa ya nemi auren d'iyata na basa....."
Bata ida magana ba sai ganin saurayin sukayi har cikin gidan, don tsaf yana jiyo zage-zage da masifar da Dadda ke faman yi...
Saurayin nan yana shigowa 'yan matan nan suka bar abinda suke suka mik'e tsaitsaye babu shiri suna kallon ikon Allah...
Dadda na ganinsa ta shiga gyara bakin zaninta tana fad'in "Toh jarabebbe d'an naci, ni dama nasan kaine fitinannen da bazaka d'auke idanu kan d'iyata ba... Toh duk maitanka haka zaka ganta ka barta dan uwarka, shege d'an bakin uwa...."
Batakai aya ba saurayin ya shek'e da dariya kana yace "Gwara ni ko uwata ta min baki inada uba, shegiyar 'yar taki da kike b'oyeta uwa gwal ki sanar damu ubanta, aikin banza aikin wofi ashema yawon garuruwa da kuke ba haka kurum bane, idan ba tsoro ba ki sanar da d'iyar taki ubanta mana ko kuma ki sanar da ita ga garinta mahaifarta...." Yayi wata murmushi kafin yaci gaba da fad'in "Bakuda gari yawon duniya kawai kuke, ki jik'a 'yar taki ki sha babu abinda zamuyi da shegiya maras asali, kuma kinji na rantse idan baku bar mana gari ba sai mun kwance maki zani a kasuwa....."
Baikai aya ba yaji sauk'ar lafiyayyar mari a k'uncinsa...
Shaye da mamaki yake rik'e da fuskarsa yana duban wacce ta maresa gata a gabansa baifi yayi wurgi da ita ba...
"MAIRO ni kika mara....?"
"An mareka d'in maras mutunci wanda baisan darajan tsofaffinsa ba, kaji na rantse maka idan baka fice a gidan nan ba sai mu lallasa maka na jaki...."
Ta k'arashe tana kwance d'aurin kwalinta had'i da shan d'amara dashi...
A tamanin d'aya budurwar ta fad'a kitchen ta rarumo wuk'a ta shiga wasawa yayinda Mairo ta sunkuya ta wawuso k'afafunsa ji kake timmm ta kadasa k'asa babu ko gizau a tattareda ita.. Fad'i take "Zaliha yi maza ki kawo wuk'ar kafin ya tashi...."
Jin haka yasa Saurayin kukan kura zai tashi don bai zaci Mario nada k'arfi har haka ba, saidai kafin ya mik'e Dadda ta zaune akansa tana fad'in "Dan uwarka koma babu yanda zakaje..."
Ai tuni ya bud'e murya ya soma neman d'auki... Basu k'yalesa ba saida suka masa lilis, bai t'aba yarda da hausan da akace b'aro a hannun mata ba sai yau, shikam ya shaida dukda ba sata ya shiga ba...
Saurayin nan yana ficewa a guje Dadda tasha jinin jikinta don tasan yau an d'agowa Mairo gyambon dake zuciyarta, akasarin garuruwan da suka baro wannan dalili shikesa su baro, sannan wannan na d'aya daga cikin da yasa Mairo batada tak'amemmen manemi, da zaran sunji batada asali sai su gudu ko iyauensu suk'i yarda, idan ma baka gudu don rashin asalinta ba zaka gudu don bala'in uwarta Dadda....
Dadda zatayi magana Mairo ta d'ago mata hannu alamun dakatarwa, ta kuwa cika tayi fam sabida b'acin rai, cikin tsananin fushi ta wuce uwar d'aki ta kulle, don duk masifa irinta Dadda tana tsoron masifa da fushin Mairo...
****
*LAUSHI GROUP*
Tafe suke cikin tampatsetsen kamfanin wanda ya tsaru iyaka tsaruwa, yaji landscaping....
Matasa ne wanda a k'iyasce bazasu gaza shekaru 35 zuwa 36 ba, sannan da gani zasu iya kasancewa sa'anni ko kuma subawa juna ratan shekara d'aya zuwa biyu...
Wanda yake daga tsakiya shi ne yafisu haske gaba d'aya sannan sanye yake cikin business suit d'insa wanda ya amshi jikinsa sosai ya dad'a fito da kyaun halittarsa...
Shi kuwa d'ayan wanda yake daga b'arin dama sanye yake cikin kaki irinta Nigerian police force, shima kakin ta 'yansanda ta amshesa sosai saidai shi baida haske kaman na mai sanye da suit d'in amma kallo guda zaka masa ka fahimci tsan-tsan bafillace ne ga sumarsa da suke a nannad'e irinta fulben usul...
Shi kuwa d'aya na b'angaren hagu sanye yake cikin wata lallausar yadi ruwan toka d'inkin half jampa, shi yafisu duhu gaba d'aya saidai Allah ya masa kyaun jiki da cikan zati, wanda hakan yasa yakeda gizo sosai a idanun jama'a...
A wata 'yar k'aramar rumfa ta shak'atawa suka zauna suna ci gaba da tattaunawarsu lokaci guda wata mace sanye da farin uniform ta ajiye k'aramar tray a gabansu wanda ke d'auke da cups basai ance maka Champaign bane cikin cups d'in.....
Saida ya sipping Champaign d'in kafin ya kuma duban saurayin dake sanye cikin business suit yace "You've been an ass.... Ka sani ko?"