← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 98

Sashe 86

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'ajura badai surutu ba, ta yanda suka banbanta da k'awarta Zaliha kenan, ita dai barta da fad'a amma sam bata da yawan magana shiyasa ma tasu tazo dai-dai da Mairo don kana masu abu basu tsayawa cacan baki saidai kaji a jikinka.....

A dole Umma ta hana Ma'ajura karb'an firan nata....

"Ki shiga ciki ki sameta ina tunanin ko shiryawa batayi ba, fad'a na mata yanzun nan, wai cewa tayi ta fasa aikin...."

Da mamaki Ma'ajura ke duban Umma kafin tace "Ta fasa aikin...? Barin shiga na sameta Umma...." Ta k'arashe tana mai shigewa d'akin Zalihan...

Zaune ta sameta gaban sark'artar ta bead ta zuba masa idanu had'ida yin tagumi hannu bibbiyu....

D'aka mata dundu Ma'ajura tayi kana tace "Wllhi idan kin isa sunana ba Ma'ajura ba... Kaji min 'yar rainin hankali, a d'auke ki aikin bugu d'aya kice bakiso, toh zaman me zakiyi a gida, naga dai ko kin zauna a gidan ma ba taya Umma da komai kike ba... Dan Allah kada ma mu soma wannan wasan tashi ki shirya Yaya Sufyan na jiranmu...."

Harara kurum Zaliha ke watsa mata kana ta kauda kai gefe "Ke nace maki na fasa aikin, ki daina b'atawa kanki lokaci ki tashi ki tafi ko ana dolene...."

"Wllhi ni kuma nace baki isa ba, ki tashi kawai tun kafin Umma ta jiyo mu...."

Wata tsukan Zaliha ta kuma bugawa kana tace "Toh sannu uwata, ke wai an taba aikin dole, naga dai ra'ayina ne da fari yasa naji ina sha'awa yanzu kuma banayi...."

K'uri Ma'ajura ta mata don taga abun nata babu alamun wasa ciki... Gyara zamanta tayi had'i da cire mayafinta kana tace "Wllhi kinji na rantse idan kika ajiye aikin nan nima zan ajiye nawa dukda jimawan da nayi a wajen kuwa... Idan wani abu ne aka maki sai ki sanar dani tunda duk abinda ya shafeki nima ya shafeni...."

"Nifa na fad'a maki babu abinda aka min kawai bazanyi bane, ki tashi kitafi abinki.... Kina b'atawa Yaya Sufyan lokaci...." Ta k'arashe tana mai tattare bead d'inta had'ida zubawa cikin drawer...

"Wllh saidai ya gaji da jira ya tafi, amma wllhi kinji na rantse bazanje babu ke ba.... ke wani irin zurfin ciki ne dake tun jiya na lura wani abu na damunki amma kin kasa sanar dani.... Idan kuma ni ce na maki wani abin sai ki sanar dani ai ba wai kiyi fushi ba..."

Sosai ta baiwa Zaliha dariya.. "Ke d'in zakimin laifi nayi fushi kawai ai saidai kiji sauk'an bulalu..." Gaba d'aya suka saka dariya kafin Ma'ajura tace "Kice da uwar mazga nake tafe...."

Murmushin Zaliha ma tayi tana tuno Maironta, wanda itace ta koya mata jibgan mutane, tayi kewan Daddah da Mairo bila adadi... D'an duban Ma'ajura tayi ganin da gaske ba tafiyan zatayi ba kafin ta mik'e ta soma shiri tana fad'in "Ya na iya tinda kin nace...."

Murmushi Ma'ajura ta kuma saki kana tace "Haka nan nake idan naso abu, naci ne dani, d'inkin nan ma da kika gani wllhi da naci na koyeta...."

Jefa mata pillow Zaliha tayi tana mai fad'in "Kyaji dashi dai uwar surutu...."

Sauri sauri ta shirya sukayi sallama wa Umma kafin suka fice....

Tinda suka isa foundation d'in take raba idanun ina zata hango matar nan mai fuskar Mairo.... Yau d'in ma Ma'ajura na hankalce da ita, zama tayi gefenta tana tambayarta wai meke damunta da foundation d'in ne...

Zaliha ta d'an dubeta kana tace "Me kuwa zai dameni iyakaci dai nasan na zama ma'aikaciya a wajen.... Yawwa wai ni matar nan bata zo ba....?"

Ma'ajura ta dubeta kana tace "Wata mata kenan, wai kina nufin Aunty Lami, a wajenta zamu amshi Key din store nasan ta kusa isowa.."

Zaliha ta girgiza kai alamun a'a... "Matar nan ta jiya wacce kika ce min kaman itace mai wajen nan...."

"Aww wai Nana A kike nufi...."

Kallonta Zaliha tayi kana tace "Sunanta kenan Nana A... ?"

Ma'ajura ta jinjina kai "Eh Nana Asma'u sunanta, Nana A d'in ya samo asali ne daga gidansu, su d'in twins ne akwai 'yar uwarta Nana Hafsat, ita kuma Nana H ake kiranta.... Idan kin gansu kanninsu guda da Nana A babu abinda ya rabasu saidai yanayin shiga da kuma d'abi'a, ni har gidansu wani sa'in Aunty Lami na aikana ko kuma idan ita Nana A d'in tayi mantuwa takan aikeni, a nan nasan 'yar uwar tata amma kam tana da d'agawa da jin kai, sam halinsu baizo d'aya da Nana A ba...."

Cikin sauri Zaliha ta katseta da fad'in "Kina nufin ita wannan d'in 'yar biyu ce, akwai wata daban mai irin fuskarta...?"

Jinjina kai Ma'ajura tayi "K'warai kuwa, idanma kika gansu sai ki rantse mutum guda ne, kawai dai ita wancan Nana H d'in tafita hasken fata ne kuma nasan bazai wuce k'ari da man kanti da take ba sabida tsananin gayunta...."

Shiru Zaliha tayi domin kwanyarta ta kuma sukurkucewa idan hakane wannan tanada mai kama da ita tamkar an tsaga kara tabbas itama wancan d'in zatayi kama da Mairo.... Toh amma babu abinda ya had'a Mairo da wad'annan..... Muryar Nana A data jiyo suna gaisawa da securities ya sanyata saurin d'ago kai tana dubanta yayinda Ma'ajura ta tafi tarbanta...

Harta muryarta irinta Mairo ce saidai ta wannan tafi ta Mairo sanyi, yanda muryar Mairo keda zak'i da fad'a haka na wannan keda zak'i da sanyi, sai sannan kuma ta lura wannan tana d'ingishi ba kaman Mairo da take a mik'e ba, wannan shine ikon Allah, Allah d'aya gari bambam, sosai taji tana k'aunar taga wancan Nana H d'in da Ma'ajura ta fad'i, tana so taga yanayin kamanninta da Mairon itama.....

Har suka k'araso wajen Zaliha bata daina bin Nana A da kallo ba tana mai tsananin mamaki, har saida Ma'ajura ta d'an tab'ata kafin tayi k'ok'arin saita kanta, gaisawa sukayi da Nana A d'in, ta kuwa amsa mata da sakin fuska harda tambayarta yaya taji aiki dasu, ya mata dad'i ko akwai wani matsala...

Fuska fal murmushi Zaliha tace "A'a babu komai babu wata matsala...."

Nana A ta jinjina kai murmushinta mai sanyi bai bar saman fuskarta ba... Saida ta d'anyi gaba kad'an kafin ta kirasu tace suzo su rakata ta d'an zaga taga maike wakana....

Aiko cikin sauri Ma'jura ta janyo hannun Zaliha suka take mata baya, yanda Nana A ke treating employees d'inta tamkar family babu ruwanta da differences na rayuwa da sukedashi kowa yayi mata wannan shaidan, kasancewar babu Junaid ne yasa ta kirawosu su rakata... Ai kuwa sosai ta sake dasu sai tambayansu shawarwari take sosai abin ya masu dad'i musamman Ma'ajura da takeji tamkar Nana A ta zamto k'awarsu ce, ita kuwa Zaliha harta wasu d'abi'u na Nana A sai take hango yanayinsu ga Maironta., Wasu d'abi'un iri guda data Mairo... A haka sukayita zaga foundation d'in gwanin ban sha'awa...

****

Mask Nasaar ya saka ya rufe fuskar sa dashi kafin ya tunk'ari d'akin da aka kulle Sabi'u, yana yashe a wajen yana rawan d'ari don tuni suka kwab'e masa riga dagashi sai singlet..

Sabi'u yaga tashin hankaliuraran, irin horo da ukuban da yake yima wasu shi ake masa yau, kawai bud'e idanu yayi ya tsince kansa cikin cell, iyakacin abinda yake tunawa shine jiya a hanyarsa ta dawowa daga Misau ya had'u da wasu mutane 'yan bindiga sun kuma kwad'a masa wani abu mai nauyi a k'eyarsa, bai kuma sanin komai ba sai farkawa da yayi ya gansa a wata fankon d'aki wanda babu komai sai siminti....

Baki na rawa sabida tsananin yunwa da galabaita yake fad'in "Su waye ku, mai kuke nema daga gareni.... Mai na maku don Allah....."

Nasaar da fuskarsa ke rufe cikin Masks matsowa kusan Sabi'u yayi yana wata iriyan murmushi mai sauti "Inspector ya kake....? I know you must be hungry, ku kawo masa abincin" Ya fad'i yana mai zama kujeran gefen Sabi'un...

Kallonsa kurum Sabi'un keyi ba tareda ya furta komai ba, ji yayi kaman yasan mai irin muryar saidai bazai iya tuna a yanda ya sani ba....

"Me kake nema daga wajena... Who are you...? Ya kuma tambaya yana mai duban Nasaar d'in

Murmushi Nasaar ya kumayi kana yace "Ni ne mutumin da yasan sirrinka, nasan baka mance da abokinka Detective Ahidjo ba wanda kayi ajalinsa a garin Damaturu....."

Ai tun kafin yakai aya 'ya'yan hanjin Sabi'u suka shiga kad'awa, shikenan tasa tazo k'arahe muddin aka sani a ma'aikatansa hukuncinsa kisa ne.... Baki na rawa yake fad'in "Dan Allah wanene kai, ka sanar dani Dan Allah...." Ya k'arashe jiki na tsananin rawa...

Murmusawa Nasaar ya kuma yi kana yace "Relax, just get a hold of yourself, abu ne mai sauk'i if you cooperate with us.... I'm pretty sure bazaka so wannan sirri naka ya bayyana ba dukda na sani ka kashe DT Ahidjo ne domin ka cikawa abokinka burinsa na d'aukan fansa...."

Izuwa lokacin rawan da jikin Sabi'u keyi tayi yawa, daga ji wannan ya masa farar sani, bazaiso ya mutu yanzu da yake burin mallakan Deejoh ba, zaiyi komai domin ya kub'uta ya kuma d'auke Deejoh su gudu...

"Mai kake nema a wajena, ka sanar dani, wllhi zanyi maka shi ko menene..." Ya k'arashe yana had'e hannayensa biyu waje guda alamun rok'o...

Nasaar ya fashe da dariya don bai tab'a cin karo da matsoracin d'an sanda ba irin Sabi'u...

"Aiki zaka min, zaka zamto tamkar private investigator da nayi hiring... Daga lokaci mai kaman ta yanzu I own you, your freedom belongs to me, muddin kanaso wancan sirrin naka ya rufu......"

Da tsananin mamaki Sabi'u ke duban mutumin da ya rufe fuskar tasa cikin mask "Ban gane ba Rankashidad'e, kana nufin sai abinda ka sakani ko ka haneni zanyi, Yallab'ai inada mata da iyali sannan akwai iyalan marigayi da nake kula dasu... Kayi min rai wajen aikina zasu zargeni...."

Tsawa Nasaar ya daka masa wanda ya hanasa ci gaba da magana, lokaci guda Nasaar ya mik'e yana mai ci gaba da fad'in "Don't think you can fool me, idan kana tak'aman kai D'ansanda ne ni kuma Lawya ne, kasan a fannin tsara kalamai da zance saidai na koya maka... Ku basa abinci yaci, gobe zaka soma aiki a matsayin private investigator a gidan Mas'ud Laushi....."

Jin an ambaci gidan Mas'ud Laushi ba k'aramin fad'uwar gaba ya kuma haifarwa Sabi'u sabuwar fad'uwar gaba....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*57*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 86 · 0% Book details