← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 98

Sashe 88

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Bulama ya saki kana ya furta "Thank you for always being honest with me my dear boy, ka kyauta min...." Ya kuma sakin wata murmushi kafin ya furta "SADIQ...!!!" Lokaci guda ya danna wata intercom a gefensa take guard d'insa guda ya shigo... Duba d'aya ya masa kafin yace "Sunansa Sadiq, inaso ka cimmasa a yau d'in nan, I'm pretty sure ya isa garin Damaturu, kada ka bari ya cimma Bintu da d'iyarta, da fatan ka fahimceni...."

Cikin sauri guard d'in ya jinjina kai kana yace "An gama Boss...."

Lokaci guda Bulama ya mik'e yayi shirinsa tsaf cikin babbar riga da hula, a dai-dai lokacin da aka fito da Sabi'u yasha suit na alfarma, kallo d'aya Bulama ya masa ya saki murmushi kana yace "Ina fatan kana sane da aikin da zakayi..."

Sabi'u ya jinjina kai cikeda risinawa kana yace "Yes Sir...!"

Bulama ya jinjina kai kana yace "Good...." Lokaci guda suka fice daga gidan a tare.....

***

Lamid'o na isowa gidan sashen Siraj ya wuce yanda ya samesa so miserable, gaba d'aya gidan babu wanda yasan Siraj na cikin gidan, duk a tunaninsu ya tafi wani waje ne, don a baya hakan yake yi musamman idan suka sami sab'ani da Ammah, yakan kashe wayarsa su nemesa su rasa sa sai bayan wasu kwanaki ya dawo, ko kuma idan Nana H ta matsa masa, toh yanzu ita kanta bata goyon bayansa tunda taji aure yake son yi, ko takansa bata bi ba, tafi so ta gama da Azeeza kafin ta nemo Uncle d'inta a lokacin babu damuwar Azeeza a tattareda ita...

Dafe kansa Lamid'o ya kuma yi kana yace "Siraj we need to do this... Rayuwar Nana A na cikin had'ari idan bamu samo wannan jerk d'in ba... Who knows mai zai je ya mata... Siraj don Allah ka tashi mu fita nemansa...."

K'uri kawai Siraj ya masa da jemmemen fuskar sa wanda damuwa ya cikasa sosai kana yace "Lamid'o I know you can do this, don Allah ka rik'e min amanar 'yan uwana, jikina na bani I don't have much time left.... Na sani zuciyata tana gab da daina aiki.... Abubuwan da na aikata a baya suke bibiyata, na zalunci mutane da dama... Na tauye hakkin mutane da dama... Lamid'o kana tunanin ubangiji zai barni haka unpunished ne...? Com'on Lamid'o, meye saura a wannan rayuwar tawa... Wllhi babu.... I wish duk wad'anda na zaluncesu sun yafe min.... Don Allah take care of my family... Promise me you will...." Ya k'arashe cikin tsananin rawar murya.....

Jikin Lamid'o yayi sanyi sosai da jin kalaman Siraj... Lokaci guda ya shiga girgiza kai.....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*58*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Girgiza kai Lamid'o yaci gaba da yi yana mai duban abokin nasa cikeda tausayawa "Siraj don't say that please, ya kake magana haka... You need to be strong.... For your family... For yourself, Siraj think about this, idan muka zauna doing nothing mai kake tunanin zai faru, kana tunanin rayuwar family d'inka baya cikin had'ari.... Siraj..."

Katse sa Siraj yayi ta hanyar d'aga masa hannu "Lamid'o I give up on life, I don't wanna live anymore.... Komai nasa a gaba bana ganin nasara saidai akasin haka.... My life is a complete mess, I caused so much to my family.... Lamid'o wllhi nayi nadaman duk wasu abubuwan da nayi a baya...."

"Siraj don Allah ka daina fad'in haka, mu dukanmu masu laifi ne, kuma ka mance Allah yace mu rok'esa gafara zai yafe mana..."

Wani irin kallon rainin hankali kawai Siraj ke watsawa Lamid'o kafin ya mik'e da k'yar yana nuna masa k'ofa yake fad'in "Get out... Get the hell out of here I said....!!" Ya k'arashe jijiyoyin goshinsa suna mik'ewa...

Shafa kansa Lamid'o ya d'anyi kana yace "No you must hear me out Siraj, you're ruining..."

"Cut it out...!!" Siraj ya katse sa da fad'in haka kafin yaci gaba da nuna Lamid'o da d'an yatsa yana mai ci gaba da fad'in "It was your idea.... You ruined our lives... Soyayyar da nake wa Zeenah bai kai na aikata abinda na aikata, bai kai na tilasta mata aurena ba.... Kar ka mance har nayi giving up ka dinga zigani sabida akwai kud'i a hannu na duk abinda nake so zan iya samu.... Lamid'o kai kazo da shawarin idan mahaifinta bai amince da auren ba mu karya masa tattalin arzikin sa kuma, na biyeka a haka, mahaifin Zeenat ya bani aurenta... Lamid'o I've no idea what really happened that night... Wllhi ban sani ba, bazance kai baka sani ba amma wllhi wllhi nayi imani Heedj ma bai sani ba... Sanda muka iso gidan domin siyan bakin amarya mai muka tarar..? Gawar Zeenah muka tarar hannun Junaid, bamu sani ba ko shine ya kasheta ko ba shi bane... Amma mai kace, take kace shine, muka masa lilis kazo da shawarin mu kashe sa.... A tunaninmu ya mutu, muka d'auke shi muka jefarshi a daji.... Mahaifin Zeenat yazo yana shari'a damu, Lamid'o kaine ka soma bani shawarin na d'auko lawya ya kare mana k'aryarmu don asirinmu ya rufu, quite alright na san bamu kasheta ba amma sanda mahaifin Zeenat yayi filing complaint yayi harda na kisan Junaid, aka rufe maganar nan har rana mai kaman ta yau... Sai gashi yanzu abu ya zamo mana sabo.. Junaid bai mutu ba... Yana shirin d'aukan revenge dinsa harda 'yan uwana... What else mai kake so nayi.. Wani gurb'ataccen shawari zaka kuma bani.... Meyasa ka shigo rayuwata, mai yasa kayi ruining d'ina... Wllhi sai yanzu na gane duk wasu abubuwan da suke faruwa dani ba komai bane illa amfani da shawarwarinka da dinga yi babu hangen nesa... And now ka b'ullo da zancen kana son niece d'ita, kuma kana sanar damu wai Nana K na raye... Just tell me what the hell are you up to this time around.. Tell me, ka sanar dani mai kake shiryawa....?"

Tunda ya soma magana idanun Lamid'o suka kad'a sukayi jazir, sabida duk abubuwan da Siraj ya fad'i gaskiya ne, da fari ya shigo rayuwarsa ne da bad intentions kuma duk aikin mahaifinsa ne... Ta yaya zai sanar da Siraj ba sonshi bane, ta yaya zai sanar da Siraj cewa zuciyarsa ta jima da gyaruwa.... Bai ankare ba sai jin hannun Siraj yayi ya damk'o hannunsa da iyaka k'arfinsa... Lokaci guda ya shiga jansa bai tsaya dashi ko ina ba sai bakin k'ofa...

Siraj yaci gaba da fad'in "Kaine sanadin mutuwar Heedj, k'arya kakeyi babu wata Nana K dake raye, so kake kayi ruining d'ina da Family na shiyasa ka tura Heedj ka kashesa sabida kawai na auren Nana H... Lamido I don't know you anymore, bansan da waye nake tare ba, aboki ne ko kuwa bak'in kumurci ne.... Koma kai waye, I want you out of my life, I don't wanna see you ever again... Get out...!!" Ya k'arashe yana mai masa nuni da k'ofa cikin wata irin dakakkiyar murya...

Jinjina kai Lamid'o yayi kana yace "Bazan tab'a bari wani ya cutar da Nana A ba koda kuwa 'yar uwarta ce da suka fito duniya tare.. I'll protect her with my life, and you Siraj please forgive me, I know I had been a bad influence to you... Ka yafe min... Sannan zan tafi, zan tafi na tsare Asma'u kuma insha Allah zan kawo Khadijah gidan nan, sannan komai zai fito fili.... Excuse me....!" Yana ida fad'in haka yayi focewarsa cikin sauri zuciyarsa na masa wani irin ciwo....

Daga yanda take lab'e tana ganin ficewar Lamid'o cikin tsananin tashin hankali ta saki murmushi kafin ta tura k'ofan sashen Siraj ta shige, yanda ta hangosa saida ta razana, gaba d'aya ya fice a hayyacinsa yayi bak'i ya rame kaman ba Uncle love d'inta ba... Cikin sauri ta k'arasa ta fad'a jikinsa cikeda tashin hankali take fad'in "Uncle my goodness, Uncle ka ganka kuwa, Uncle ka saurarawa kanka please..." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya tamkar zata kurma ihu....

D'an d'agata yayi daga jikinsa kana yace "Kar ki damu I'll be fine...."

Bata amsa sa ba sai kallon da tabi parlorn penthouse d'in nasa dashi, da alama dangin crackers dasu cornflakes kawai yake ciki.... Hankali tashe ta mik'e tana fad'in "Uncle you can't go on like this, you'll fall sick, dubi fah baka cin komai.... Haba Uncle.... So kake nima na daina cin abinci, duk munyi zaton wani wajen ka tafi ashe kana cikin gidan nan...." Ta mik'e tsaye tana fad'in "I'll cook something for you myself...."

Saurin rik'ota yayi yana mai girgiza mata kai yake fad'in "Don't.... Banso Ammah tasan ina gidan nan sweetheart...." Ya k'arashe yana mai lank'washe wuya hannayen Nana H na cikin nasa yana murza yatsun nata a hankali, gaba d'aya sai taji ya tsundumata cikin wani irin yanayi, shiko Siraj sam bai kawo irin tunanin nata cikin zuciyarsa ba hasalima alfarmarta yake so ya nema...

"Sweetheart can you do me a favor...?" Ya tambaya yana mai dubanta

Da k'yar ta iya jinjina masa kai kana tace "What's that...?"

"You know I love Azeeza, I love her so much, that I couldn't imagine life without her....."

Kallonsa kawai Nana H keyi don sam bata kawo abinda zai tambayeta ba kenan, taso ace tambayarta yayi ta mallaka masa kanta ba tareda sanin su Ammah ba sai taji batun tsinanniyan yarinyar nan yake mata, take idanunta suka ciko da k'walla har yau Siraj ya kasa gane wane irin soyayya take masa... Muryarsa ta jiyo yana ci gaba da fad'in "Nana H taimako zaki min har na mallaki Azeeza ba tareda sanin Ammah ba, idan yaso bayan na aureta a b'oye komai ya lafa sai mu sanar da Ammah... Please sweetheart do this for me...."

Kallonsa kurum take yanda ya zama wani lusari akan mace macen ma wai ba ita ba.... Bata jin duk duniya akwai mai yiwa Siraj irin soyayyar da take masa, amma baya gani, har mijinta ta salwantar duk akan Siraj amma Siraj shine ke kuka kan wata mace daban, macen ma da ba k'aunarsa take ba kaman yanda yake k'aunarta....
Chapter 88 · 0% Book details