← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 98

Sashe 66

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai take tana duban Baffah take fad'in "Baffah kaima ka yarda.. Baffah fah Allah wllhi wllhi k'arya ne, idan gaskiya ne ai da sun kawo mana gawarsa, nidai Allah Baffah nasan mijina na raye, zai dawo kaman yanda ya min alk'awari..." Ta k'arashe tana mai fad'awa jikin Innah...

Innah ma kasa juriyar tayi dole ta rungume Deejoh sukayita kukan su mai tsananin ban tausayi...

Sabi'u dake rakub'e daga bakin k'ofa sai binsu data mujiya yake, idanunsa kan Deejoh dake kuka wanda yake ji kaman ya rungumeta ya bata kafad'unsa tayi kuka bisa....

Likita ya sanar dasu tana buk'atan hutu sabida jaririn cikin dake jikinta sannan idan son samu a daina barinta tana shiga damuwa sabida kada yayi affecting cikin... Sabi'u shi yayi komai na asibitin ya kuma maidasu gida cikin motar sa, sosai Baffah yayita masa godiya yana tambayarsa yaushe zai tafi..

Sabi'u ya d'an gyara tsugunonsa kana yace "Baba dama zanso mu tafi can Abuja taredaku sabida ayi maganar rabon gadon Aliyu tinda nada wata iyali acan... Amma duba da yanayi na rashin lafiya da iyalinsa na nan gida ke ciki sai nakega bai kamata ta tunk'ari wancan matar tasa ba sabida mace ce mai tsananin kishi, a gaskiya Baba ina tsoron zata iya yiwa Deejoh wani abin musamman duba da yanda auren ya kasance bata san da ita ba...."

Bai kai aya ba Baffah ya girgiza kai kana yace "Allah shi yace a raba gado koma nace ya riga ya raba abundantly amma bacin haka sai na ce maka mu bamu buk'atan wani abu ya had'amu da wad'ancan mutanen balle har mu kuma jefa Deejoh da abinda ke cikinta cikin had'ari, mu wllhi dukiya sam bata gabanmu, mu mutane ne masu wadatan zuci, Alhamdulillahi... Sannan a halin yanzu babu zancen rabon gado sai an jira Khadijatu ta haife abinda ke cikinta an gani mace ne ko kuwa namiji ne kaman yanda shari'a ya tanadar... A bar wannan maganar a halin yanzu domin kuwa sam babu shi...."

Sabi'u da zufa ta shiga k'eto masa jinjina kai na dole ya shiga yi don bai zaci Deejoh ciki ne da ita ba.. Cab aiko plan d'insa zai ruguje shi da yake son aurenta nan da wata hud'u da zaran ta gama iddar ta, yanzu sai ya jira nan da watanni tara kenan bayan ta haife abinda ke cikinta, baijin zai iya jira dole yasan yanda zai zama rid of abinda ke cikin Deejoh ya samu ya aureta nan kusa....

Gyaran murya yayi sabida wata miyau data tokare masa mak'oshi kana yace "Ga... Gaskiya ne Baffah yanda kace haka ne... Allah ya sauk'eta lafiya, ni kuma zan sanar dasu a can d'in.. Kar ka damu Baffah insha Allah Khadija da d'an dake cikinta bazasuyi maraici ba nayi alk'awari.."

Jinjina kai kurum Baffah yayi kana yace "A gaskiya babu abinda zamu ce maka saidai Allah ya biyaka da alkhairi tabbas ka cika aboki na gari da har ka nememu ka sanar damu, Allah ya saka maka da alkhairi..."

Sabi'u ya murmusa kai a k'asa kana yace "Baba abinda nayi dole na ne nayi gobe zan wuce insha Allah kuma zan dinga zuwa akai akai ina dubaku..."

Baffah ya jinjina kai ya kuma masa godiya kafin sukayi sallama... Sabi'u shi da kansa ya koma fadar mai Unguwa ya sanar dasu abinda ke faruwa, take labari ya ratsa gari tuni aka soma tururuwan zuwa gaisuwa gidan Malam Sanda.... Wannan kenan....

***

*Abuja*

"Tell me what did you do to him...." Lamid'o ya kuma tambaya idanunsa suna fitar da wasu irin hawaye masu zafi...

Dariya Bulama ya fashe dashi a karo na uku kana yace "I managed to get rid of him completely, I told you so duk wanda yayi yunk'urin exposing Nana K I'll get rid of him..... "

Girgiza kai Lamid'o yake yana mai furta "No no no... No, this can't be happening..."

Baikai aya ba Bulama ya katsesa da fad'in "But is already happened... Abu guda ne banyi ba shine ban bisne maka shi cikin d'akin nan ba kaman yanda na bisne maka Nazir ba....." Ya k'arashe yana nuni da kabarin Nazir dake can gefen d'akin....

Lamid'o kasa furta komai yayi sai durk'usawa da yayi saman gwiwoyinsa wani irin kuka mai sauti na fita masa....

Murmusawa Bualama ya kumayi kana yaci gaba da fad'in "Now you know what I'm capable of doing akan biyan buk'ata ta... Lokaci yayi da zan mallaka maka freedom d'inka muddin kabi shard'ana, idan ka sab'a guda d'aya wannan gurguwar itace zata zama next victim d'ina... Idan ka kuma yin tunanin cin amanata kaman yanda kayi a baya wllhi zan zo maka ta yanda baka tab'a zato ba balle tsammani, na kashe Nazir na bisneshi a d'akin ka kana kwana tareda shi duk don sabida na hukunta ka ne sannan na kashe abokin ka Ahidjo shima domin na hukunta ka.... Lamid'o kar ka mance I own you, sai yanda naso nayi da kai, yanzu na tabbata ka yarda zanyi abinda bazaka tab'a tsammani ba.. So idan ka fita daga nan zakayi duk abinda nace ko ka wayi gari babu ko d'aya daga cikin su....."

D'ago jajayen idanunsa yayi da suka ci tsananin azaba yana huci yake duban Bulama kafin ya soma fad'in ".....*FUSKA UKU*🏮

*46*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tofar da jinin bakinsa Lamid'o yayi kafin yaci gaba da fad'in "You're nothing but a coward, ka kasa fuskantar Siraj da Family d'insa, ka b'oye a bayan fage kana cutar dasu.... Meyasa bazaka tink'aresu kai tsaye ba... Why meyasa...?" Ya k'arashe jajayen idanunsa suna fitar da wani irin ruwa masu d'umin gaske...

Murmushi Alh Bulama yayi had'i da tafe hannayensa kana yaci gaba da fad'in "Wannan shine dalilin da yasa nazo muyi magana da kai, to be my accomplice again, and this time around if you try something foolish..." Yayi wata murmushi kafin yaci gaba da fad'in "You know exactly what I'm capable of doing.... Lamid'o nasan akwai tambayoyi da dama da kake so na amsa maka sannan idan kayi yunk'urin cin amanata kaman yanda kayi daga fari bazaka tab'a samun amsoshinka ba, sannan abubuwa bazasu tab'a daidaita ba, and lastly kar ka mance I've eyes everywhere, I'll be watching you....."

Fuzar da iska Lamid'o yayi yana tunanin nakasa masa rayuwa da Bulama yayi, ciki harda kisan amininsa Ahidjo, a hankali ya d'ago yana duban Bulama kana yace "Bazan kuma barinka ka cutar da wani wanda nake so ba, I'll do whatever you asked me to do.... Na amince zan kuma maka aiki kaman yanda ka buk'ata..."

Alh Bulama ya kuma murmusawa kana yace "Yanzu ka tabbatar min cewa kai d'in d'an halak ne.... Za'a fito dakai yanzu kayi wanka ka canza kaya, akwai likita da zai treating wounds d'insa zamu fita tare...." Daga haka bai jira cewar Lamid'o ba yayi ficewarsa yana alamu wa guards d'in da su kwance kacan dake d'aure da hannayen Lamid'o....

***

Mik'ewa Nasaar yayi yana mai watsawa Siraj mugun kallo sanda yaci gaba da fad'in "You know Siraj, this is all your fault, nayi nadaman samarwa Azeeza aiki a kampaninka, yanzu ta tafi and the worse part of it shine bansan yanda ta nufa ba, yanzu mai zance wa danginta randa suka nemeta, mai zan sanar da tsirarun danginta da sukayi saura..... Tell me mai zan sanar dasu Siraj....!!" Ya k'arashe cikin tsananin d'aga tsawa had'ida buga table...

Shafa kansa kurum Siraj yayi kana iya hango tsan-tsan ramar da yayi sanda yaci gaba da fad'in "Nasaar Azeeza is my life, she is my life.... Zan tafi Maiduguri ko can ta koma...." Baikai aya ba Nasaar ya katsesa da fad'in "Don't even start Siraj, idan ka tafi Maiduguri ya tabbata bata can mai kake tunanin danginta zasumin, na sayar masu da d'iya ko mai? Mai kake tunani Siraj...."

Shima Siraj d'in huci yake sanda yaci gaba da fad'in "So kake na zauna doing nothing bamu san yanda Azeeza take ba, bamu san mai zai sameta ba... What exactly is wrong with you Nasaar.... You know what, you can not stop me, bazan huta ba har sai na sami Azeeza cikin k'oshin lafiya...."

Cikin sauri ya fice daga gidan tamkar zai tashi sama...

Hankalin Nasaar idan yayi dubu ya tashi, yanzu idan Siraj ya tsananta bincike fah, yana iya gano ahirinsu, tabbas basuda zab'i da ya wuce su bud'e Azeeza....

Kallon kallo suka shiga yima juna shida Junaid kafin Junaid yace "Naji komai kuma idan wancan imbecile d'in ya tsananta bincike tabbas yana iya gano wani abu, ka bar min komai a hannu na Azeeza dole tabi umarni na if not zan sanar da ita bazata sake ganin Siraj ba har abada sabida zan kashe shi kaman yanda muka kashe abokinsa....."

Fuzar da iska Nasaar yayi kana yace "Allah sa ta saurareka...."

***

*Damaturu*

Zaune yake gaban Baba Malam k'afafunsa gaba d'aya a mik'e sarb'al sabida har yanzu bai gama recovering ba amma sosai ake samun ci gaba....

"ALI bansan yaya zamu samu iyayenka ba ko wani naka amma komawarka ga danginka zai fiye maka zama a nan k'ila suna can suna nemanka ko a zatonsu baka a raye..."

Mutumin da Baba Malam ya kira da Ali sauk'e ajiyan zuciya yayi kana yace "Baba banida dangi sai ku, bansan kowa ba a wannan rayuwar sai ku, bansan wasu iyaye ba face ku, banida 'yan uwa ko dangi sai ku.. Baba bansan dalili ba dukda bansan ko ni wanene a baya ba ina ji a jikina zamana daku yafi wanda nayi a baya, sabuwar rayuwata ta fiye min wanda nayi a baya, dukda cewa bansan yaya rayuwatar ta kasance a baya ba...."

Baba Malam ya sauk'e ajiyan zuciya had'ida d'anyin jigum kana yaci gaba da fad'in "Bansan meyasa kakeji wannan rayuwar ta fiye maka wanda kayi a baya ba amma ina mai tabbatar maka zamu ci gaba da rik'eka bisa gaskiya da amana tamkar mu muka haifeka har lokacin da Allah zaisa tunaninka ya dawo ka fahimci ko kai wanene...."

Ali ya d'an murmusa kana yace "Ni ba kowa bane face Ali d'an gidan Baba Malam kuma d'an uwa ga Hafizu.... Amma Baba a ina na samo wannan suna Ali....?" Yayi tambayar idanunsa kan Baba Malam..
Chapter 66 · 0% Book details