← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 98

Sashe 25

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zata kurma ihu ya zare mata manyan idanunsa yana fad'in "Kika ce fit sai na maki d'an karen duka a d'akin nan... Mayya kawai, mai na maki kike bibiyata, ke mayya ce....?"

Ya k'arashe yana kuma zare idanuwa....

I zuwa lokacin idanun Deejoh sunyi rau-rau banda karkarwa babu abinda jikinta keyi...

Ahidjo ya kuma matsowa kusa da ita ta matse jikin garu...

Murya a dake yaci gaba da fad'in "Kina jina idan naji kin sanar da Innah wani abu gameda maganar da kikaji inayi a waya sai na harbeki da bindiga. Ai kinsan bindiga koh...?"

Cikin sauri ta shiga jinjina kai hawaye na neman ciko idanunta...

Ahidjo ya kad'a kai kana yaci gaba da fad'in "Idan naji kincewa Innah zan tafi sai na harbeki da bindiga ta tana nan cikin mota, kuma saura naji bakinki... Has anyone ever told you how disgusting you are..?" Ya tambaya yana kuma matso da fuskarsa dab nata...

Yo ita yaushema ta fahimci abinda yake nufi, kallonsa kurum take da idanunta da tuni sunyi rau-rau....

"Stop staring at me mayya kawai..." Ya fad'i yana kuma watsa mata mugun kallo...

Ganin yanda ta razana sosai yasan ko kusa bazata sanar da Innah tafiya zaiyi ba... Murmusawa yayi kana yace "Daga yau sunanki Disgust kinji koh... Fad'a inji..."

Kasa fad'i tayi sai zazzare idanu da takeyi...

"Au bazaki fad'i ba...."

Ganin na k'ok'arin matsowa ya sanyata saurin fad'in kalman da ya umarceta ta fad'i dukda batada tabbacin cewa dai-dai ta fad'i..

Yanda ta furta kalmar sosai ta baiwa Ahidjo amma ya gimtse, kamo hannunta ya kuma yi yana fad'in "Zo ki fice min a d'aki , na sake ganin kinmin lab'e sai na fasa kanki da bindiga..."

Har sunzo k'ofa yaga tana share hawaye... Cak ya tsaya yana dubanta kana yace "Had'iye kukan nan ki kuma goge fuskarki, idan kikacewasu Baffah na maki wani abu kin san sauran...."

Ganin ta masa biris tak'i share hawayen ya sanyasa saka hannunsa ya shiga goge mata hawayen, aiko nan hannunsa ya b'aci da jan hodan Deejoh da kuma gazal d'inta.... Ahidjo ya kuma yin tsaki yana duban yanda ya b'ata farin hannunsa... Cikin sauri ya kuma finciko hannunta ya nufo da ita waje, saidai suna fitowa sukayi kicib'is da Innah ta nufo sashen nasa... Kan su ankare sallaman Gaje har cikin kunnuwansu, tanayi tana watsa k'afafu, yanda taga Innah tsaye sororo tana duban su Ahidjo da Deejoh wacce Ahidjon ke rik'e da hannunta ai sai Gaje ta saki salati da sallalami tana tafe hannaye take fad'in "Inyi abin yazo, ashe dai Deejoh har an tare d'akin miji... Yo wannan dank'areriyar motar da na gani k'ofar gida ashe ta mijin naki ne... Oh Deejoh an sami duniya an mance Ard'o, toh zuwa nayi na shaidawa mijin naki mune nan iyayenki ehe dole ko mai akaci a bamu..."

Tsaban shock da ya tsinci kansa ciki kasa sakin hannun Deejoh yayi, sai wani irin kallon mamaki da tuhuma da yake bin Innah dashi wacce itama tuni yanayinta ya kuma canzawa...

Deejoh kanta bata fahimci abinda ke wakana ba saidai tayi k'arfin halin fuzge hannunta daga rik'on da Ahidjo ya mata ta nufi Innah a guje....

*SameenaAleeyou📚*

*18*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kallon Innah ya kuma yi a karo na biyu idanunsa sunyi jajir sosai... A hankali ya soma fad'in "Innah is that really true... Innah da gaske ne aure kuka min without my knowledge...? Innah aure kuka min da gaske ki amsa min....?" Ya k'arashe yana zaro idanu waje wanda shi kansa baisan yana hakan ba...

Gaje dake tsaye gefe yab'e da baki tana kallon ikon Allah sallalami ta soma tana tafe hannaye.... "Oh yau naga duniya, haka kurum a lik'a wa mutum abunda baiji ba bai gani ba bai yaba ba.... Yo ina wannan had'edd'en saurayin ina Deejoh.. Nima dama nasan za'a rina haka.... Haba, haba ai wllhi wannan cutarka kawai akayi yaro mai kyau, wllhi wllhi kar ka yarda, kuma nan da kake ganin Deejoh k'aramar da ita babu kalan mazan da bata sani ba, duk lungu da sak'o da take zagawa talla sai ta mik'a kantawa maza, ni dama zuwa nayi naga kalan zaman da take a gidan sai gashi na tarar angon nata ya iso.... Ayyiriri dole nayi gud'a dukda babu hancin..." Ta k'arashe tana darawa...

Tunda ta soma magana Ahidjo ke dubanta, what's all this.... Meke shirin faruwa dashi, meye wannan....? Ko motsawa daga yanda yake ya kasa, dole ma ya tafi ya barsu ya sami k'wakk'waran dalilin da zai tafi abunsa, shine aka masa aure, auren ma a rasa da wanda za'a masa saida wannan yarinyar, haba haba... Ina zai kai wannan hallitar, ko don basu tab'a ganin kalan matarsa bane shiyasa zasuyi kuskuren lik'a masa wannan abar.... No no this is impossible, this can't be... Wllhi bazai d'auki wannan abun ba, ba dashi ba..... Lokaci guda ya juya ya barsu nan tsaye ya wuce d'akinsa...

Innah da idanunta suka ciko da k'walla kallon takaici kurum take aikawa Gaje ba tareda ta iya furta koda kalma ba, Gaje kuwa dariya ta fashe dashi had'i da tafe hannaye kana ta matso dab da Innah had'i da sassauta murya tana fad'in "Ai baki sani ba, insha Allahu sai ya dank'arawa Deejoh saki don a rayuwar Deejoh babu jin dad'i, wahala ce ta kamaceta kuma zata dawo nan gaba na taci gaba da bauta daga yanda ta tsaya, wllhi wllhi ina numfashi bazan tab'a barin Deejoh taji dad'in rayuwarta ba.... Bokana yafi naki na fad'a maki...."

Tana ida fad'in haka ta kuma murmusawa taja k'afaunta ta fice tana wak'enta dangin su Ayye cika dubaye. Wanda kasan da gayya kawai take.....

Sauk'e ajiyan zuciya Innah tayi had'i da goge hawayen da ya zubo mata, ta kalli k'ofar d'akinta wanda tunda aka soma maganar Deejoh ta shige ciki a guje tana kuka.... Ta kuma duban k'ofan d'akin Ahidjo wanda tuni ya rufe k'ofar shima, gaba d'aya Innah ta rasa da waye zata soma cikinsu, anya Gaje tanada zuciya cikin k'irjinta? Tabbas idan tanadashi yayi bak'ink'irin da mugunta da hassada ,k'yashi da sauran muggan abubuwa.... Ta Allah ba tata ba, da yardar Allah Ubangijinta zai shige mata gaba, lokaci guda Innah taji k'arfin tunk'aran yarantan, wajen Deejoh ta soma nufa ta hangeta tak'ure k'uryar d'aki tana kuka...

Ta yaya za'a ce D'angayu ne mijinta, ta yaya hakan zai kasance bayan tun had'uwansu kafin su san sud'in ma'arauta ne D'angayu ya tsaneta, ya kirata da sunaye marassa kyau ciki harda Mayya, toh inaga ance zasuyi zaman aure, ashe dai da gaske auren aka mata, ga maganganun da Iya Gaje ta ida fad'i akanta, Allah Sarki lallai maraici mugun ciwo ne ta tabbata da mahaifiyarta na raye k'ila da wasu abun baza'a mata ba.... Hannun Innah da taji saman kafad'unta ya katse mata tunanin lokaci guda ta d'ago kai tana goge hawayen da ya wanke mata fuska.....

***

*Tambuwal*

Shiru Nazir yayi yana duban Daddah k'irjinsa na bugawa, she's damn serious garin zasu bari..... D'an gyaran murya yayi kafin ya soma fad'in "Daddah gaskiya wannan karan bazanbi bayanki ba, ya kamata ku nitsu waje guda keda d'iyarki koda ba aurarta zakiyi ba, don nima bana goyon kiyi aurenta sai mahaifinta ya bayyana sabida gudun wulak'ancin mutane da kuma zarginsu, amma Daddah is high time ki sanar da Mairo wacece ita, sannan ki daina gujewa mutane ku nutsu waje guda, a yanda na sanki da taron fad'a ban zaci har akwai D'an Adam d'in da zai baki tsoro da shakku ba har ya sanyaki gujema gari wa gari...."

Tunda ya soma magana hanci d'age take dubansa, babu abinda yafi k'ona mata rai kaman cewa da yayi tsoron wani takeji, yo wani d'ancin k'aniya zataji tsoro, Mairo itace rayuwarta idan ta tsaya ta fuskanci matsalanta gaba da gaba tabbas dangin Mairo zasu rabata da ita, don dai Bulama ba tsoronsa take ji ba, duk randa sukayi gaba da gaba wllhi alwashi ta d'auka sai ta watsar masa da ragowar hak'waran gabansa koda zai mata d'aurin rai da rai....

Ganin Daddah ta masa shiru babu amsa yasan idan ya sake magana abun bazai masu da kyau ba.... A hankali ya mik'e had'i da d'an rusunawa kana yace "Daddah ni zan wuce, sai anjima...."

A dak'ile tace dashi "Mu jima da yawa...."

Nazir ya hangi k'ofar d'akin Mairo wanda tunda ya rakota cikin gidan ta k'ule uwar d'akin ta saka sakata... Ya d'iba mintoci tsaye a wajen kafin ya fice....

Daddah ta kuma jan tsaki had'i da tab'e baki kana ta soma fad'in "Shegen felek'e da firirta, ya wani soma min turancin iskancin banza saikace ni nace masa yawo wa gari wa gari na damuna, ba don kar naci masa mutunci ya daina shigo min na rasa mai shawo min kan Mairo ba da ya gane kurensa... Matsolon banza kawai..." Tana kaiwa aya ta mik'e ta nufi kitchen don girka wa Maironta abinda tafi so D'anwake.....

Nazir yana isa gida ya kunna wayarsa aiko take yaga sak'insa ya shigo, dama yasan za'a rina.... D'an dafe kansa yayi had'i da fuzar da iska.... Allah sa dai kar matan nan ta janyo masa rashi, dole ya shawo kanta cikin kwanakin nan.... Da wannan tunanin ya kunna laptop d'insa ya tarar wasu sak'on a email d'insa.....

***

*Abuja*

Suna gefe suna supervising ma'aikata lokaci guda sabo mai tsanani na kuma shiga tsakaninsu.... Aunty ce ta k'araso rik'eda crutches d'inta tana nuna masu wasu takardu had'ida neman shawarinsu kan sana'o'i da zasu k'ara a foundation d'in tunda gashi anyiwa sabbin shigowa register....

"Junaid mai ka gani...?"

Aunty Lami ta tambaya tana duban Junaid wanda ya d'anyi shiru kaman mai nazari.....

Jinjina kai yayi kana yace "Gaskiya ne Aunty Lami ya kamata a k'ara yawan sana'o'in tunda ci gaban foundation d'in ne...."

Asma'u tayi shiru tana nazari kana tace "Nima zanso hakan Aunty amma tunani na d'aya kar najewa Uncle da maganar yaga kaman karb'an kud'i kawai nake sonyi tunda dole a saya machines...."

Aunty Lami data kawo shawarin shiru ta d'anyi tana nazarin batun kana tace "Gaskiya ne Nana A, kuma dududu ba'a jima da bud'e Foundation d'in nan ba, mu bari idan mun saida abubuwan da ake kan had'awa da jarin sai mu k'aro wasu machines d'in ko yaya kuka gani....?" Ta k'arashe tana dubansu
Chapter 25 · 0% Book details