Sashe 80
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaliha murna kaman mai gashi dama Abbanta ya amince mata zata iya faran aikin idan dai an d'auketa, haka suka sanya abincin da Ummah ta zuba masu gaba har ya gama hucewarsa basu sami zarafin ci ba sai faman zuba labari suke Ma'ajura na sanar da ita yanyin foundation d'in nasu da kuma working hours da dai sauransu, Ummah dai tayi maganar su bar surutu suci abinci har ta gaji k'arshe dai murmushi kawai tayi tana mai jin dad'in yanda suka sake da juna tamkar wasu 'yan uwa, cikin ranta take saka masu albarka had'ida fatan nasara a sana'ar tasu....
***
Misalin k'arfe takwas na dare Siraj ya tadda Ammah a d'aki tana mai sallame sallar lisha, saman stool ya zauna yana jiranta ta ida lazimi, mintoci kad'an suka shud'e kafin Ammah ta maido da dubanta ga Siraj wanda ya k'urama waje guda idanu sihirtaccen murmushi kwance saman fuskar sa....
Murmushin itama take tana mai dubansa domin ba k'aramin dad'i takeji ba taga iyalan nata cikin farin ciki....
"Babana an shigo, wannan murmushin naka ince dai lafia...." Ta fad'i tana linke abin sallarta had'ida aje cazbahan bisa....
Siraj ya tattaro hankalinsa ya maidosu ga Ammah kana yace "Eh Ammah lafiya lou, dama wata magana ce ke tafe dani..."
Aifa nan Ammah ta fad'ad'a murmushinta don a zatonta labari mai dad'i aka samu gameda Nana K...
"Toh ina saurarenka Allah sa ka sanar dani Khadija zata dawo gidan nan ne gobe gobe...."
Jikin Siraj ya d'anyi sanyi da jin kalaman Ammah... D'an sosa k'eyarsa yayi had'ida gyara zama yayinda Ammahn ke lura da canzawan yanayinsa...
"Ina saurarenka Sirajo sanar dani meke faruwa,...." Ta kuma fad'i wannan karan damuwa ya d'an nuna itama a fuskarta, bata fatan Siraj ya sanar da ita an sami kuskure ba da gaske bane Nana K na raye...
D'an sosa k'eyarsa ya kumayi kana yace "La.. Lafiya Ammah, maganar Nana K kuma sai gobe mukayi zamu kuma had'uwa da Lamid'on kinsan ya fini sanin case d'in dole na nemi taimakon sa..."
Ammah ta jinjina kai tace "Ai babu damuwa yau da goben duka d'aya ne, toh akwai wani abu ne.....?" Ta k'arashe tana dubansa
Saida ya kuma muskutawa kana ya soma fad'in "Ammah dama... Dama kan maganar Azeeza ce, an sanya mana aure nan da sati uku....."
Ai baikai aya ba ta katse sa da fad'in "Rufe min baki, sabida bakada hankali yarinyar data gudu a sabida bata k'aunarka taje can uwa duniya ta gama tambad'ewarta shine za'a lik'a maka da aka rasa yanda za'ayi da ita... Wannan ta gujeka kafin aure toh mai kuma kake tunanin zatayi bayan auren... Kana jina kar na kuma jin kayi maganar wannan yarinyar a nan gidan, a baya na tausaya mata dashike bansan mummunar halinta ba, amma yanzu kam dana sani ina numfashi bazan bari ka auri wannan yarinyar ba kaji na fad'a maka...." Ta k'arashe tana mai hura hanci..
Tunda ta soma magana kan Siraj a k'asa yake, zuciyarsa na masa wani irin zafi, yayi tunanin ya sami Azeeza bazata kuma kubce masa ba sai ga wani babban tashin hankalin dake shirin kunno masa daga wajen Ammah wacce a baya bai tab'a rasa support d'inta ba a duk abinda yasa gaba...
A galabaice ya d'ago yana duban Ammah kana yace "Ammah don Allah kar ki hanani samun farin ciki ..."
Bata bari yakai aya ba ta kuma katsesa da fad'in "Ka min shiru nace maka, idan kaje ka auri wannan yarinyar wllhi kaji na rantse maka bada yawuna ba, waya sani ma ko 'yar lek'en asiri ce, from nowhere ta shigo rayuwarka tashi guda ta zautar dakai, wama yasan uwar me ta saka maka kaci, kaji na rantse bazaka auri yarinyar nan da goyon bayana ba..."
Nana H da tunda tazo wucewa ta jiyo hargowar Ammah tuni ta mak'ala kunnenta jikin k'ofar, banda bugu babu abinda k'irjinta ke mata, Uncle ke maganar auren Azeeza, toh ina alk'awarinsu da Nasaar, lallai Nasaar Zaire amsa mata, kambala'i kenan k'arya yake mata kokuwa me...? K'irjinta yaci gaba da mata zafi, lokaci guda ta fasa sauk'a k'asan ta koma d'akinta ta d'au wayarta ta shiga dialing layin Nasaar hannayenta har rawa suke sabida tsananin b'acin rai, wani kayan takaicin shine wayar Nasaar d'in a kashe take, ta kira yafi abinda yafi baya shiga, tamkar tayi jifa da wayar salular haka taji, lokaci guda ta tura masa sak'o kan su had'u gobe duk yanda za'ayi...
Haka ta zauna saman gadonta tana mai faman ci gaba da huci, duniyar tai mata zafi, tana murna Azeeza ta fice daga rayuwar Uncle sai gashi tana shirin dawowa, inaa bazata tab'a bari hakan ta kasance ba koda wasa....
***
Baisan ta yanda zai soma tuntub'ar Junaid lambar Sabi'u ba don ko kad'an baiso yayi suspecting d'insa wani abu, dabara ta fad'o masa lokaci guda ya saki murmushi da gefen bakinsa kafin ya mik'e ya fice daga parlorn, duk runtsi duk tsiya dole a yau d'in nan ya saci lambar Sabi'u ya soma aiki wa Mai gidansa Bulama muddin yana son kansa da lafiya....
***
A can Damaturu kuwa tinda ya kwanta yake mafarki da wata mata, a mafarkin nasa matar tana a matsayin matarsa ce, kyakkyawa ce sosai kuma mu'amala ta aure suke cikin baccin nasa, tinda ya farka yake jin jikinsa babu k'wari, ya jima zaune yana tunanin wannan mafarki ga kyakkyawar fuskar matar ya kasa b'acewa daga idanunsa, a hankali ya saka tafukan hannayensa ya shafe fuskarsa, agogon bango dake manne a d'akin ya d'aga kai ya kalla ya nuna k'arfe biyu da rabi na sulisin dare asubahi tanada saura, a hankali ya karanto addu'an da Baba Malam ya koyar dashi kafin ya mik'e ya d'auki tocilansa ya nufi makewayi, tsarkake jikinsa yayi ya kuma d'auro alwala kana ya dawo d'akinsa ya shiga jera nafilfili, ya jima yana sallolinsa har wajajen k'arfe uku da rabi kafin ya kuma kishingid'a wani bacci ya kuma satarsa, har saida ya kusan makara asubahi, bugun k'ofar da Hafiz ke masa ya farkar dashi, cikin sauri ya gabatar da alwala kana suka jera suka tafi masallaci tareda Hafiz d'in kaman yanda suka saba, dama kullum Alin ke tada Hafiz sai gashi yau Hafiz d'in ne ya tada shi, Baba Malam kam kasancewarsa Liman yakan rigasu isa masallacin saidai su jera su dawo gida tare bayan sun gaggaisa da mutanen unguwa a masallacin idan an ida sallah...
Yau gaba d'aya tinda suka jero suna tafiya Baba Malam ya fahimci wani abu na damun Ali, saidai yayi shiru bai tambayesa ba, shi kuwa Alin mafarkin nasa sosai ya damesa musamman da fuskar matar ya kasa b'acewa daga idanunsa, yanaso ya tambayi Baba Malam saidai nauyi da kunya bazai barsa ya masa irin wannan tambaya ba, a haka suka isa Gida suka yada zango a zaure suka shiga k'arin karatu kaman yanda suka saba duk sanda suka dawo daga sallan asuba....
***
K'arfe bakwai na safiya tayiwa Ma'ajura a gidansu Zaliha, tuni Zalihar ma ta shirya Ma'ajuran kawai take jira, tsaban zumud'i ko karyawa sun kasa tsayawa suyi wai zasuyi latti, babu yanda Ummah batayi ba kan su tsaya su saka wani abu cikinsu amma sunk'i, tuni suka fice bakin hanya yanda Yaya Safiyanu yayan Ma'ajura ke jiransu....
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU🏮*
*54*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Har wajajen k'arfe 7:30am bata tashi ta shirya ba sakamakon daren jiya gaba d'aya kusan ta yisa idanunta biyu sabida abubuwan da suka faru a jiya d'in tsakanin manemanta guda biyu wato Lamid'o da kuma Junaid.... Ayiya sosai ta sha mamakin rashin ganin sauk'owar Nana A, ta sani sosai Nana A ke mutunta lokaci, idan tasan tanada abinyi toh tun kafin lokacin zata tashi tayi shirinta lalurar dake jikinta sam bai hanata yin wasu abubuwan....
Da sallama Ayiya ta shigo d'akin yanda ta hangi Nana A d'in har lokacin kwance take cikin gadonta, zama tayi gefenta fuskarta fal murmushi, tinda take a rayuwarta Yaro guda ta haifa kuma ta rasa shi tun yana k'arami, bayan wannan yaro nata data nuna masa tsan-tsan so da k'auna babu kaman Nana A, ji take tamkar ita ta haifeta tsananin soyayyar da take mata, bata tasheta ba saima gyara mata kwanciyarta da tayi sannan ta fice had'i da rufe mata k'ofan...
A can Foundation kuwa su Zulaiha tuni sun isa suna jiran isowar Nana A amma shiru bata iso ba, a dole Ma'ajura ta tafi bakin aikinta ta k'yale Zulaiha nan reception tana zaman jira, taimakon TV dake aiki a reception d'in yasa ya d'an d'ebe mata kewa, tun tana k'irga mintoci har dai ta koma k'irga awanni, nan ta soma tunanin anya kuwa matar nan zata zo, can jimawa Ma'ajura ta k'ataso wajen itama d'in izuwa lokacin rashin zuwan Nana A d'in ya dameta..
"Ma'ajura anya kuwa madam d'in nan taku zatazo, anya kodai na tafi ne gobe na dawo kinga da nayita zaman kurum a nan gwara na koma gida na taya Umma da wani aikin..." Zulaiha tace damuwa fal fuskarta
Zama gefenta Ma'ajura tayi tana mai duba agogon Gucci dake d'aure left hand d'inta kana tace "Kai Zulu dan Allah ki k'ara hak'uri nima dai rashin zuwan nata ya soma damuna amma nasan anything 11 zata iso insha Allah.."
D'an sauk'e ajiyan zuciya Zulaiha tayi ga wani fad'uwar gaba da ya addabeta tinda ta shigo foundation d'in....
"Shikenan babu matsala idan kince Haskell, Allah sa ta k'araso wllhi na k'agu tayi ta zo ban sani ba amma gabana sai fad'uwa yake tinda na shigo wajen nan..."
Murmusawa Ma'ajura tayi kana tace "It's natural, you're nervous kar ki damu zakiji dad'in aiki da foundation d'in nan insha Allah, oya tashi muje kiga yanda muke gudanar da ayyukanmu...." Ta k'arashe tana mai janyo hannun Zalihan....
***
Cikin shirinta na fita ta sauk'o parlorn, fuskar nan tasha kwalliya uwa mai zuwa gidan biki, doguwar riga ce jikinta wanda yasha tsagu, gaba d'aya sharab'arta a bud'e suke, wata 'yar k'aramar mayafi ta saka a kafad'arta wanda da gani kasan a dole ta saka shi, ga wani uwar d'auri datasha tamkar dai mai shirin yin beauty pageant, sai watsa k'amshi take tana faman kad'a d'an makullin motar ta....