← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 98

Sashe 42

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Siraj ya kuma murmusawa cikeda tausayinsu su duka biyun, haka tasu jarabawar tazo masu rashin abokan zama gashi shekarunsu yakai su mallaki abokan zama tuntuni, ga gata ga dukiya Allah ya hore masu, tabbas d'an Adam bai cika goma ba dole kowa a samu lapses a rayuwarsa....

"Kin tabbata zaki iya zuwa office yau? " Ya tambaya yana dubanta

Jinjina masa kai tayi kana tace "Zan iya Uncle, is better na fita d'in than na zauna a gida doing nothing, ...."

Ya kuma jinjina kai yana fad'in "Gaskiya ne fitar zai keeping d'in busy... Muje muyi breakfast koh...." Ya k'arashe yana mai taimaka mata wajen mik'ewa tsaye....

A tare suka sauka nufo downstairs, har cikin ranta dad'i taji yanda Uncle Siraj ya kwantar mata da hankali, tabbas ko mahaifinsu iyakacin kulawar da zai basu kenan....

***

Kallon Nasaar ta kumayi tana juya zoben d'an yatsanta lokaci guda take wani irin mayaudarin murmushi kana ta kuma kwanto da fuskarta dab nasa tace "Attorney nasan ka ganeni tsaf.... Kayi tunani kan maganar da na fad'a maka sai na jika...." Ta k'arashe tana wasa da d'an yatsanta saman fuskarsa....

Ko motsi mai kyau Nassar ya kasa sai bin Nana H da kallo da yake babu ko k'yafta idanu, ko pen d'in hannunsa ya kasa ijiyewa, har lokacin bai daina jin motsin yatsunta saman fuskar sa ba.....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*30*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cikin dabara Barde ya saka SIM card d'in tsakiyar abinci da wayar salula kana ya turawa Lamid'o ta k'asar k'ofa lokacin da ya kawo masa lunch....

Lamid'o yana bud'e abincin ya kuwa tcinci sim card ciki da wayar salula k'irar Nokia 3310 tsakiyar shinkafa.... Hannayensa har suna rawa sanda ya zak'ulo sim card d'in ya soma had'a wayar.....

Layin Nana A ya soma kira sanda ya had'a wayar domin da ita ya kwana ya tashi cikin zuciyarsa, soyayyarta a kullum ninkuwa yake a cikin zuciyarsa.... Saidai tunda ya soma kiranta bata d'aga ba, gashi dai wayar na ringing amma ba'a d'agawa.... Hankalin Lamid'o ya tashi sosai, yana tsananin buk'atar jin muryarta...

Nana A kuwa zaune suke itada Junaid yana bata baki gameda abinda Lamid'o ya mata sanda wayar Lamid'on ya shigo mata, nunawa Junaid fuskar wayar tayi yana kallon mai kira....

Cikin sigan kwantar da hankali Junaid yace "Ki d'aga wayar kiji mai zaice maki...."

Girgiza masa kai tayi kana tace "I don't want to hear any of his lies again.... Bazan d'aga ba, na goge shi a babin rayuwata,... He's already in the past..."

Kautar da fuska Junaid yayi had'i da sakin murmushi mai cikeda ma'anoni kana ya maido da dubansa ga Nana A lokaci guda fuskarsa ta canza tayi jazir abinda su Lamid'o suka masa shida farin cikinsa Zeenat ya dawo masa, jijiyoyin goshinsa sukayi rud'u-rud'u sanda ya soma fad'in "Da ace zanga wannan Lamid'on da sai yanda k'arfina ya k'are.... Sabida ya hurting d'inki Asmah.... It hurts me seeing you suffering like this...."

Kallonsa kurum Nana A take wasu sabbin k'walla na k'ok'arin ciko udanunta, ashe akwai mutanen da suka damu da damuwarta har irin haka bayan family d'inta, lokaci guda take jin al'amari mai girma gameda Junaid na ratsa ko wane k'ofa na zuciyarta, Junaid ya wuce aboki a gareta tabbas d'an uwa ne.... Murmushin k'arfin hali ta sakar masa kana tace "Kar ka damu Junaid, wllhi komai ya wuce a wajena, haka Ubangijina yaso ya jarabceni, shi bawa a koda yaushe rayuwarsa jarabawa ce walau jin dad'i yake ko ko akasin hakan, idan kayi tawakkali da kalan jarabawan da mahaliccinka ya d'auro maka toh sai ka samu dacewa da reward mai girma a gaba..." Ta k'arashe murmushi mai sanyi samar fuskarta....

Maganganun Nana A sun saka jikin Junaid yin sanyi for the first time da yaji zuciyarsa tana barazanar karaya da burin d'aukan fansa.... Ganin sanyayan kalaman Nana A na neman cin galaban akan dadd'en burinsa da ya rayu shekaru hud'u akansu yasa sa saurin tura wheelchair d'insa ba tareda ya kuma ce da ita komai ba ya fice daga office d'in nata...

Tissue paper ta zaro daga cikin kwali had'i da goge fuskarta tana mai bin bayan Junaid da kallo, tausayinsu su duka biyu na ratsa zuciyarta don tasan su d'in sun had'u da babban jarabawa a rayuwarsu.... Shigowar Aunty Larai ne ya sanyata saita kanta don bata so a gane halin da take ciki....

***

Cikin sauri ya shiga neman layin Nazir hannayensa har rawa suke.... Bugu biyu kuwa Nazir ya d'aga kaman jira yake...

"Ina ka shige tun jiya nake nemanka, ina tsammanin Bulama yana suspecting d'ina da bud'e maka sirrinsa don yanzu haka ce min yayi duk abinda nake na baro na taho Abuja, Lamid'o I hope ba fayyace masa komai kayi ba...." Cewar Nazir daga d'aya b'angaren

Shafe kansa Lamid'o yayi kana yace "Ince bakazo Abuja ba...?"

Nazir yace "Yaya za'ayi nazo bayan nasan babban laifin dana tafka masa dukda cewa kai d'ansa ne..."

"Yauwa Alhamdulillah, Nazir you better get lost sabida nayi imani Bulama ya kama ka bazai rage maka rai ba... And please koda ka sami wani information gameda Mairo kada ka sanar dashi, sabida a yanzu nasan wacece Mairo, nasan nufin Bulama akanta, don Allah kada kayi yasan yanda suka tafi...."

Nazir ya murmusa kana yace "Lamid'o kenan nasan abinda nake, yanzu haka ina airport ne, na yanki ticket already k'asar zan bari kafin ya cimma ni don I'm pretty sure his boys are after me.... And about Mairo or Khadijah na koma tashan motar ban bar wajen ba saida na sami wanda yasan garin da suka nufa a ranar, garin Damaturu ta jihar Yobe suka nufa a yanda na iske labarin, so probably suna can suna rayuwa.... Ina son Mairo da Daddah kaman 'yan uwana na jini, sannan na jima ina karesu daga sharrin Bulama ba tareda saninsu ba, tabbas nasan bak'in nufinsa akan Mairo kuma nasan idan yayi idanu hud'u da Daddah kasheta zaiyi shiyasa nake bibiyansu don na karesu daga sharrinsa... Dan Allah ka d'aura daga yanda na tsaya, kasan yanda zakayi ka kub'utar dasu daga sharrin Bulama.... Na barka lafia jirginmu zai tashi...." Daga haka katse kiran Nazir yayi yayinda Lamid'o yayi sakare da waya a hannu.... Shikam yama rasa sahun da zai jefa Bulama ciki.... Yanzu yaya za'ayi ya kare Mairo daga sharrin Bulama, bai kamata ya soma sanar da Siraj long lost niece d'insa is alive, sannan maiyasa ita wacce take rik'eda Nana K d'in bata nemi iyayenta ta maidata wajensu ba....? Kai wannan Al'amari akwai abin dubawa ciki, bai kamata ya soma sanar dasu Siraj kai tsaye ba dole su zargesa da wani mummunar abu tinda ba ce masu zaiyi mahaifinsa ne ya sace Nana K ba, dole Siraj yayi tunanin ya shigo jikinsa ne da mugun nufi wanda a yanzu sam babu hakan a zuciyarsa... Yanzu ya zaiyi waye zai samu ya kawo Nana K ga dankinta lami lafia kafin komai ya bayyana.... Lokaci guda tunanin Ahidjo ya fad'o masa... A hankali ya furta _"Heedj"_ kana yaci gaba da fad'in "Tabbas Heedj ne kawai zai min wannan babban alfarmar tinda Shi police officer ne sannan Nana K sister matarsa ce shima, yasan zaiyi iyaka k'ok'arinsa saidai zai sanar dashi this should be between them.... Da wannan tunani Lamid'o ya shiga dialing layin Ahidjo... Saidai duk kiran duniyar nan yayi wayar Ahidjo bai shiga.... A hankali ya fuzar da iska had'i da dafe kansa yana tunanin mafita...

***

*Misau*

Iya Gaje ce zaune tana faman tankad'en garin tuwo lokaci guda tana watsa bak'ar magana wa Malam Ard'o kan ya saida d'iyarsa Deejoh ya sallameta wa mayu 'yan shan jini.... Gashi tinda Deejoh ta auri bak'on bariki ko k'eyarta ba'a sake gani ba....

Duk wannan sababi da takewa Malam Ard'o k'ala bai ce mata ba, idan da sabo toh fah ya saba da halin Iya Gaje.....

Kaman daga sama suka jiyo dadd'an sauti mai cikeda kamala da k'warjini ana sallama....

Malam Ard'o ya mik'e yana fad'in "Gaje barin amsa sallama...."

Ai baikai aya ba ta katse sa da fad'in "Toh uban 'yan tsugudidi ni na aike ka ko me, daga jin wannan murya bak'in arziki ne, ni zan duba ko waye....." Ta k'arashe tana watsa masa bahagon duba kafin ta mik'a hannu saman katanga ta janyo wani mayafinta da yaji daud'a ta yafa a kafad'a ta nufi k'ofar tana 'yan wak'e wak'enta had'ida tambayan waye mai sallama....

Bud'e k'ofar da Gaje zatayi tayi idanu hud'u da Ahidjo wanda shakka babu taga bindiga a motarsa.... Ai a d'ari tayi wani irin juyi had'i da komawa cikin gida a guje tana rangad'awa Malam Ard'o kira tana fad'in "Malam ya biyo mu, wllhi ya biyomu ya karmu, nidai bazan tsaya ba na tabbata Deejoh ta sanar dashi komai...." Tana k'ok'arin cab'e garu take kururwan neman d'auki... Malam yayi kanta yana janyota daga saman garu....

Jin kururwar ya sanya Ahidjo kustowa cikin gidan shima...

Kowa yasan rashin mutuncin Gaje shiyasama da take kururwan neman d'aukinta babu wanda yakai mata d'auki..

Da k'yar Malam ya samu ya sauk'o da Gaje daga saman garu, dukda haka bata daina b'oyewa bayan Malam tana rok'on Ahidjo kar ya harbeta ba sharrin Deejoh ne...

Shikam yafi baiwa matar mai tab'in hankali, don bai tsamman wannan matar tanada sauran hankali ba....

Jiki har na rawa ta shige d'aki a guje had'i da kullo k'ofa....

Malam Ard'o girgiza kai kurum yayi kafin ya mik'awa Ahidjo hannu sukayi masabaha... Ga mamakin Malam Ard'o har k'asa matashin saurayin ya tsuguna yana gaidashi, ko ba'a ce masa ba zai iya shaida sirkinsa ne sabida ga kamannin Malam Sanda a tattaredashi...

Cikin sauri Malam Ard'o shima ya shiga k'ok'arin durk'usawa yana amsa gaisuwar Ahidjo... Lokaci guda ya umarci Ahidjo da ya mik'e ya isa saman shimfid'a... Cikeda rusnawa Ahidjo ya k'arasa saman shimfid'ar ya zauna.... Nan suka soma sabon gaisuwa da Mahaifin Deejoh kana ya masa bayanin ko shi waye...

Allah sarki, dad'i maras misaltuwa ne ya kama mahaifin Deejoh, shi kansa Ahidjon yaji dad'in yanda mahaifin Deejoh ya tarbesa, nan yake bayaniwa Malam Ard'o kan baisan dalilin da yasa matarsa take gudunsa ba tun ranar farko da suka soma had'uwa, nan dai Malam Ard'o yayita 'yan kame kamensa don shi kansa bai san mai zai ce ba....
Chapter 42 · 0% Book details