Sashe 35
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta jima rik'eda wayar a hannunta tana tunanin waye Lamid'o ke k'ok'arin rabasa da rayuwarsa... Toh kodai Uncle Siraj yake yunk'urin kashewa tunda gashi itama yayi yunk'urin kasheta, tabbas Uncle Siraj baya goyon bayan relationship d'insa da Nana A itama kuma bata goyon baya, in fact gaba d'aya gidansu su biyu ne basu goyi bayan abin ba wato shine yace bari kawai ya kashesu ya huta.... Lokaci guda jikinta yaci gaba da k'yarma Uncle Siraj d'inta... No no ina bazai mutu ba.... Jiki na rawa ta rarumo wayarta hannayenta har suna wani irin karkarwa ta shiga dialing layin Siraj....
Sau uku tana kira gashi dai wayar tana ringing amma ba'a d'agawa... Ji tayi tamkar an sauk'e mata guduma a k'irjinta... Cikin muryar kuka take fad'in "No no my Uncle love is alive... I know he's alive... He won't leave me... Yana raye bazai tab'a barina ba I'm sure of it....."
Duk sunbatun da take Lamid'o dake faman nishi da k'yar yana kallonta, murmushi ya saki a hankali dukda jin jiki da yakeyi... Lokaci guda wayar Lamid'o ta sake ruri... Nana H ta kuma zabura tamkar zautacciya... Ta yunk'ura zata d'auka saiji tayi Lamid'o ya janyota da iya k'arfinsa yana k'ok'arin k'watar wayar yake fad'in "Give me that.... Idan kika d'aga wayar nan sai na fasa maki kai wllhi...."
Bata saki wayar ba take fad'in "How dare you... You traitor , bayan duk abinda ya maka is that how you repay him akan kawai yace bazai baka auren 'yarsa ba... You should be ashamed of yourself Lamido.... Na rantse da Allah wani abu ya sami Uncle Siraj kaima zaka mutu....!" Ta k'arashe tana wani irin huci...
Murmushi Lamid'o yake bayan ya k'waci wayarsa da k'arfin gaske, yana shafa k'eyarsa yanda jini ya d'an zuba ya kuma damk'ota da iya k'arfinsa lokaci guda annurin fuskarsa ya d'auke cak.... Cikin wani irin huci yake fad'in "Wannan shine abinda na tanadar ga duk wanda yace zai hanani samun farin cikina Nana A.... And let me remind you this young lady... You're messing with the wrong person..." Yana ida fad'in haka yayi jifa da ita jikin kujera ya fice cikin sauri yana kuma dialing layin Malam Ayuba...
Da k'yar Nana H ta isa ga wayarta ta janyo ta kuma dialing layin Siraj... Tana kira kuwa ya d'aga wannan karan... Wani irin nannauyan ajiyan zuciya ta sauk'e kana tace "Uncle kana ina ne..? Are you sure you're fine... Where are you please....?" Yanda tayi maganar cikeda damuwa bai baiwa Siraj mamaki ba tinda yasan ta saba masa hakan amma wannan karan jin muryar nata cikin wani irin yanayi ya d'an sanyasa damuwa... Murya cikeda kulawa yace
"Sweetheart lafiya... Meke faruwa... Gani a hanyar gida.. Hope all is well...?"
Sauk'e ajiyan zuciya tayi kana tace "No babu komai Uncle, kasan kana huld'a da mutane da dama so you need to be very very careful, kasan mutane nowadays ba abin yarda bane..."
Murmushi Siraj yayi kana yace "Kar ki damu sweetheart zan kula da kaina sosai insha Allah I promise you, so ki kwantar da hankalinki koh...."
Cikeda jin dad'i ta amsa masa kana ta hanging up wayar.... Zama tayi cikin kujera had'i da cunk'ushe sumarta waje guda... Duniyar tai mata zafi batasan da waye zata soma ba, bata san ta yanda zata b'ullowa lamarin ba... Ga Lamid'o ga wancan shegiyar sakatariyar Siraj d'in wacce ke neman zame mata alak'ak'ai.. Koda shike wannan yarinyar mai sauk'i ce.... Lokaci guda ta saki murmushi tana hango fuskar Azeeza cikin idanunta mai zubin taliya a cewarta.....
***
Yana isa gidan suka keb'e da Malam Ayuba... Malam Ayuba yace "Yallab'ai tuntuni na saka masa maganin a shayi kuma na tabbata yasha.."
Lamid'o ya jinjina kai cikin ransa yace idan kuwa yasha he probably fell asleep by now.... Lokaci guda ya dubi Malam Ayuba kana yace "Na gode Malam Ayuba kana iya tafiya..."
Malam Ayuba ya kuma masa godiya kafin ya fice...
Kai tsaye sashen mahaifin nasa ya nufa, aiko kishingid'e ya taddasa jikin kujera Television na faman aiki.... Cikin sand'a ya isa yanda keys d'in d'akinsa yana neman Key d'in domin kuwa yasan halin mahaifinsa sam bai barin d'akinsa a bud'e kuma baka isa ka shiga masa d'aki saidai shi ya umarceka, babu mai shiga sai masu gyara masa kuma suma a gabansa suke gyaran, shi kansa Lamid'o rabonsa da shiga d'akin idan bai manta ba tun yana matashi d'an shatakwas, mahaifinsa bai yarda da kowa ba.....
Cikin sand'a ya d'auki keys d'in ya isa k'ofar d'akin ya soma gwadawa, cikin sa'a a gwaji na uku k'ofar ta bud'e saida ya sauk'e ajiyan zuciya had'ida yin hamdala kafin ya shiga d'akin....
Cikin sauri ya nufi drawers ya soma bincike....
Abinda ya basa mamaki hoton su Nana H tun suna yara ya soma zak'ulowa, FUSKA UKU jikin hoton kamannin su iri guda... Guda d'aya daga cikin 'yanukun an zana mata jan marker....
Sosai Lamid'o ya tsaya yana duban hoton.... Bai gama mamaki ba saida ya d'ago wasu hotunan wanda akasari na iyalan gidansu Siraj ne hardama wad'anda bai sansu ba wanda shakka babu yasan bazai wuce Yayan Siraj marigayi bane da matarsa... Kan Lamid'o ya kuma d'aurewa, domin kuwa sunan mahaifiyarsu Siraj kenan Mairo... Toh kodai itace... Kai bazai yuwu ita bace tinda a wayar yaji ana cewa Mairo sun gudu.... "Toh wacece Mairo...?" Ya tambayi kansa a hankali.... Cikin sauri yaci gaba da bincika duk wasu takardu dake wajen... Baiga komai ba bai fahimci komai ba, saiko hotunan family d'in Siraj da ya gani kala daban daban, wanda yasan mahaifinsa ya jima yana bibiyan wannan family... Toh amma su waye suka gudu har hankalin mahaifinsa ya tashi haka.... Lokaci guda ya mik'e had'i da fuzar da iska don bai sami abinda yake nema ba, mugun kallo kurum ya watsa wa mahaifin nasa sanda ya fito lokaci guda ya tuna guy d'in da ya kira mahafin nasa tunda ya d'auki number sa zaiyi yanda zaiyi ya sanar dashi mai mahaifinsa ke k'ullawa ko nawa zai kashe....
Cikin sauri ya fice daga gidan ya nufi gidansa ya shirya tsaf don zuwa ganin farin cikinsa Nana A....
Wani kulawa da soyayya Lamid'o ya dinga nunawa Nana Asma'u wanda ba kad'an ya tab'a zuciyar Nana H ba, haka aka watse aka bar masu parlorn don su samu su fahimci juna.... Siraj na mik'ewa Nana H tabi bayansa tana mai watsawa Lamid'o harara... Murmushi kurum Lamid'o keyi yana aika mata da wasu kallo da ita kad'ai tasan ma'anoninsu...
***
*Misau*
Tsaye yake jikin motar sa waya manne kunnensa daga d'aya b'angaren Sabi'u abokin aikin nasa da suke wayar tare yace
"DT amma kanaga zamanka a Misau bazai kawo mana matsala a binkicen da mukeyi ba, we really need you here...." Ya k'arashe murya cikeda damuwa...
D'an shafe goshinsa Ahidjo yayi kana yace "Sabi'u ni kaina na sani ya kamata na dawo, kasan abu da iyaye kuma babu wanda yasan Misau nazo sai kai kad'ai ko matata bata sani ba.... Yanzu abinda nake so da kai ku sake komawa ku bincike guy d'in sosai nasan anything next week zan dawo insha Allah... Just keep on the good work..."
Sabi'u ya d'an shafi k'eyarsa kana yace "Shikenan Detective Allah ya nuna mana, agaida mutan gida...."
Ahidjo ya amsa masa kana sukayi sallama ya katse kiran, zama dirshan yayi cikin motar nasa yana tunanin ya kamata ya koma kafin abubuwa su rincab'e masa a office...
Gaje kuwa tun da ta hangesa ta soma sauri uwa zataci da k'asa, sai faman wage baki take.... Tana isowa ta soma magana cikin dashesshiyar muryarta wanda da k'yar yake fita...
"Salama alaikum, salama alaikum.... Bakin bariki..."
Karkatowa kurum yayi yana binta da kallon mamaki wai bak'in bariki....
Kafin ya sami zarafin magana Gaje taci gaba da fad'in "Baka gane ni ba koh.... Toh nice dai uwar goyon matarka Deejoh wacce ta cinye uwarta ta kuma kama kurwan ubanta dake kwance yana jinya, nima don kurwata tafi k'arfinta ne shiyasa bata kama ba.... Yanzu maganar da nake maka ni ce nan mai biyan hayan gidan ubanta ga bashin kud'in magani ya mana katutu... Tinda na rasa Deejoh na rasa 'yar talla shine nazo......!!" Aya ta saka wa maganganun nata ganin bindiga a gaban motarsa a ijiye cikin motar tasa..... Gaje ta kuma ware idanu tabbas bindiga take gani ra'il ainu ba cikin shirin wasan kwaikwayo ba.... Waige-waige ta soma tana neman ta wani hanya zata arce... Ba komai ya fad'o mata rai ba sai tunanin k'ila d'an fashi ne ko d'an shan jini bacin haka mai ya had'asa da bindiga....
A tamanin ta tattare zaninta ta rik'e a hannu ai kafin ya sami zarafin magana ta arce a guje.... Ahidjo ya bita da kallon mamaki yana tunanin k'ila tab'in hankali takedashi domin maganganunta ma gaba d'aya baiyi kama dana masu hankali ba... Girgiza kai kurum yayi yana mamakin yanda Deejoh ta zauna da wannan mata... Lokaci guda yaji yana son sanin komai gameda Deejoh, cikin gida ya shige ya kuma samu Innah ce kawai zaune a tsakar gidan....
Innah ta fad'ad'a murmushinta tana fad'in "Baba wuro an shigo...."
Murmushi kwance saman fuskarsa ya zauna daga can gefen tabarman yana gaida Innah.... ta kuwa amsa masa da sakin fuska... Nan ya shiga d'an waige waige yana neman ta yanda zaiga Deejoh... Tsaf Innah na hankalce dashi...
"Ahidjo lafiya dai koh.... Naga sai dube dube kake..?"
"Lafiya lou Innah, kawai dai naga ke kad'ai kike zaune banga Deejoh ba...."
Innah ta d'an murmusa cikeda jin dad'i kana tace "Deejoh na ciki na bita karatunta na allo kada su gudu mata tunda kaga yanzu ba zuwa take ba.."
Ahidjo ya jinjina kai had'i da gyara zama kana yace "Innah ni dama akwai abinda nake son tambayarki gameda Deejoh...."
Gyara zama Innah tayi tana dubansa cikeda kulawa tace "ina jinka..."
"Innah wai dan Allah mai yasa akayiwa Deejoh aure a 'yan shekarunta... Sannan wacece ita, mai yasa matar nan tace min ita uwar goyonta ce sannan da na tambayi Deejoh cemin tayi mahaifiyarta ce... Innah menene gaskiyar Al'amarin... Ina son sani a matsayina na mijinta..."
Innah ta murmusa had'ida kalmashe k'afafunta kana tace "Allah sarki Deejoh, ashe ce maka tayi Gaje mahaifiyarta ce..."
Ahidjo ya jinjina kansa alamun eh...