← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 98

Sashe 7

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A d'ari Gaje tayi bayan Malam Ard'o mahaifin Deejo tana kururuwa take fad'in "Malam ka agajeni kada su min fyad'e... Malam zasu tona mana asiri.... Wayyo Deejo kin cuceni babu abinda zai hanani yankaki cikin gidan nan....." Tsam ta d'ale bayan Malam Ard'o dukda ta fisa a tsaye da kuma jiki sai kururwa take....

Dai-dai lokacin Malam Sada da mai d'akinsa Innah Balki suka shigo had'i da wasu 'yan unguwa Deejo kuwa na mak'ale da Innah Balki....

Mamaki ya cika mutane jin abinda Gaje tayi akan marainiyar 'yar mijinta Deejo... Lallai duniya abin tsoro, gashi ta shanye mijin nata gaba d'aya bai iya um balle um-um....

Innah Balki kam batasan sanda k'walla suka shiga zarya a idanunta ba sam batayi zaton rashin imanin Gaje yakai nan ba, Malam Sanda kuwa sai faman girgiza kai yake cikeda mamakin yanda wasu mutanen basu san girman amanan d'a a wajensu ba.... Tabbas barin Deejo hannun wannan azzalumar mata babban had'ari ne gwara yasan yanda zaiyi ko gaban Mai gari suje idan abu ya gagara su dangana gaban sarki a canzawa Deejo uwar rik'o koda wajen dangin mahaifiyarta ne a maidata tunda yasan bazata rasa ba....

Da k'yar aka samu aka fatattaki su Lado a gidan, Gaje ta baje a k'asa kallabi a hannu tana maida numfashi, tabbas yau taga tashin hankali....

Innah Balki ta girgiza kai cikeda takaici kana tace "Toh Gaje shidai kukan kurciya jawabi ne amma fah mai hankali ne ke fahimta, kuma ki sani Deejo bata kwana d'akin ko wani gardi ba sai d'akina, gashi k'ulleliyar da kike shirin yi mata ya tasamma juyewa kanki, toh wllhi kiji tsoron Allah, dan ke Allah bai baki ba bawai ya k'iki bane sannan fad'owar Deejo hannunki alamun Allah ya baki kenan koda ba ke kika haifa ba, shin godiyar da zakiyiwa mahallicinki kenan.... Ki sake tunani Gaje ki kuma gyara halayanki tun kafin lokaci ya k'ure maki... Kuma bazan gushe ba ina sanar dake shidai d'a na kowa ne ba'a musguna masa sabida son zuciya bakisan waye zaki mora ba nan gaba, bakisan mai Allah ya ajiye tattareda wannan 'yar marainiyar Allahn ba...."
Tunda ta fara magana Gaje ke watsa mata mugun kallo.... Mik'ewa tayi had'ida shan d'amara da kallabinta kana tace "Toh kanwa uwar gami... Sai ki dake ni kawai nasan kin haifeni, banda felek'e kin wani sakani gaba uwa 'yarki kina silleni sabida makirci da munafunci irin taki... Toh sai ki gaya min idan kina kawo kwabo cikin kud'in tufatar da Deejo koko ci da ita.... Wllhi wllhi kinji na rantse ki fita daga hidiman gidana...." Ta k'arashe tana finciko hannun Deejo take fad'in "Saketa tinda ba 'yarki bace, yo ke wa ya kaiki asara kin haifawa bariki tuk'ek'en saurayi... Ahayyye abin kunya na tattare dake wllhi gwamma ni dama ban haifa ba ke kuwa kin haifa wa karuwai ya tafi ya barki...." Ihun da Deejo ta saki tana k'ok'arin k'wace hannunta daga rik'on da Gaje tai mata ya sanya Gaje dasa aya tana kuma janyo Deejo take fad'in "Nan ne gidan ubanki dan uwarki babu yanda zakije, nan ne dolenki...."

Deejo ihu take tana tsalle take fad'in "Nidai wllhi gidan Innah zan koma, ni wllhi bana son nan gidan...."

Gwab'e mata baki Gaje tayi tana fad'in "Uwarkice baki so bamu ba shegiya annoba...."

Innah Balki ta yunk'ura zata janyo Deejo Malam Sada ya rik'eta had'i da girgiza mata kai...

"Malam kagafa abinda take mata... Malam wllhi ina son Deejo...." Innah ta k'arashe cikin kuka...

Malam Sanda durk'usawa yayi gaban Malam Ard'o kana ya soma fad'in "Malam Ard'o zan rok'i alfarmanka guda d'aya.... Dan Allah kayimin ita..."

Malam Ard'o da tuni k'walla sun gama ciko idanunsa kallon Malam Sanda kawai yayi had'i da jinjina masa kai....

Malam Sanda ya d'an sami k'warin gwiwa kana yace "Dan Allah ka min izini na tafi da Deejo gidana, ba ina nufin ka bani ita ba, a'a ina nufin rik'onta ya dawo hannu na da iyalina..."

Ai bai kai aya ba Gaje ta malmalo ashariya ta watsa cikin azama ta hankad'a Deejo d'aki wacce ke faman ihu da bori.... Gaje bata fasa fad'in "Toh tsinannu munafukai annamimai baza'a baku ba kuce neman 'ya'ya kuke kota halin k'ak'a toh kace a baka auren Deejon mana kaga tinda da jini a jikinta zata haifo maka abinda matarka ta kasa baka... Kadai ga yarinya mai jini a jika kana so a baka ka dinga bin dare ko... Toh baza'a bayar....." Bata kai aya ba Innah dake faman huci ta d'aga hannu zata kwad'a mata mari Baffah ya rik'e hannun cikin sauri.... Tabbas ya yarda yanda kunya yabi toh fah Gaje bata bisa ba, dole abin abun a lallama....

"Ahayye da ka barta ta mareni yau datasan ta d'abo Gaje mai jigidan masifa da bala'i... Ku fice mana a gida kafin ranku gaba d'aya ya b'aci...."

Ta k'arashe tana hankad'e Innah Balki dake kuka shar-shar don tana jiyo sautin kukan Deejo tana fad'in "Innah dan Allah kar ki tafi ki barni... Baffah dan Allah ku d'aukeni daga gidan nan.. Innah ta dan Allah ki d'aukeni...."

Cikin sauri Malam Sanda da zauciyarsa ta karye gaba d'aya ya janyo matarsa suka fice daga gidan.... Suna jiyo Gaje yanda taci gaba da ashariya tana surfa masifa wa mijinta....

Har suka isa gida Innah bata daina kuka ba tana fad'in "Malam yanzu haka zamu barta, yanzu babu abinda zamuyi.. Malam kace min wani abu dan Allah...." Ta k'arashe cikin kuka sosai...

Baffah ya sauk'e ajiyan zuciya kana yace "Balkisu kiyi hak'uri insha Allah zamu kub'utar da Deejo daga makircin kishiyar uwarta bi iznillahi, kuma babu abinda zai cutar da ita, ki bani zuwa d'an wani lokaci...."

Jinjina masa kai kurum tayi hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta....

***

Junaid yaci gaba da fad'in "Kamar yanda na fad'a maka asalinmu 'yan k'asar Cameroon ne, mahaifanmu gaba d'ayansu 'yan asalin k'asar Cameroon ne birnin Yawundi.... Iyayenmu mu biyu suka haifa tak daga ni sai k'anwata Azeeza, a lokacin da muka dawo k'asar Nigeria inada kimanin shekaru 8 a lokacin Azeeza bata wuce shekara d'aya tak ba, kaga akwai ratan kusan shekaru bakwai tsakaninmu.... Lokacin da muka dawo nan k'asar Nigeria mahaifina sai ya samu aiki da wata k'aramar Company a nan birnin Abuja, ya fara aiki gadan-gadan babu kama k'afan yaro... Abinka da k'aramin ma'aikaci wanda kuma tsananin matsi yasa ya baro k'asarsa ta ainihi sai mukaji rayuwar ta mana dad'i, dai-dai gwargwado munajin dad'i muna samun duk abinda mukeso wanda baifi k'arfin mahaifinmu ba...."

Sauk'e ajiyan zuciya yayi had'i da sakin murmushi sabida tunowa da yayi da mahaifansa kana yaci gaba da fad'in "A companyn da mahaifina yake aiki, shi mutumin wanda mahaifina ke aiki a k'ark'ashinsa ya kasance yanada wata d'iya ZEENATU... Zeenatu zan girme mata da shekara biyu zuwa uku, toh a lokacin makaranta d'aya mahaifinta ya sakamu, komai tare yake mana, Shak'uwa mai tsanani ya shiga tsakanina da Zeenatu wanda ta kasance ko dawowa mukayi daga makaranta toh idan banje gidansu ba ita zatzo namu...." Murmushinsa ya k'aru wanda har takai ya kasa ci gaba da baiwa Barr labari...

Barr kuwa ya k'agu yaji ci gaban labarin...

"Umhum ina jinka mai ya sanyaka dariya haka....?"

Junaid ya kuma murmusawa kumatunsa suka lotse kana yaci gaba da fad'in "Kawai na tuna idan Momma mahaifiyata ta had'amu abinci plate guda ne toh sai anyi fad'a kafin a ida cin abincin, kuma da zaran anyi fad'an toh za'a shirya bayan an gama cin abincin... Barr na k'are maka nida Zeenatu rakiyar kura muke ma junanmu tamkar bazamu rabu ba... A haka rayuwa taci gaba da tafiya mana, har zuwa lokacin dasu Zeenatu suka bar inguwarmu amma bata daina zuwa yanda nake ba nima kuma ban daina zuwa yanda take ba, aminci tsakanin iyayenmu ya k'ara k'ulluwa, har takaiga sun k'ulla alk'awarin aure a tsakanin mu dukda cewa mu a lokacin bamu fahimci soyayya muke ba, a lokacin shekaruna bazasu wuce sha tara zuwa ashirin ba, Azeeza kuwa bata wuce Sha biyu ba.."

Shiru ya d'anyi idanunsa suka cika da ruwa....

A hankali yaci gaba da fad'in

"Wata rana mahaifanmu sun tafi ziyara k'asar Cameroon suka barmu ni da k'anwata hannun Mai taimakawa mahaifiyata da aikace-aikace na cikin gida mai suna Umma Marie... Iyayenmu sunso tafiya damu saidai lokacin muna tsaka da makaranta dagani har k'anwata....."

Hawaye suka soma zubowa daga idanunsa sanda yaci gaba da fad'in "Dawowar da basuyiba ta har abada, kallo na k'arshe da muka masu sanda muka rakasu airport.... A hanyarsu ta dawowa Nigeria sukayi had'arin jirgin sama wanda ko d'aya a cikinsu babu wanda ya rayu......" Kukan Junaid ya tsananta... Lokaci guda Barr yasa hannu yana k'ok'arin maida nasa k'wallan...

Bai tak'urawa Junaid yaci gaba da basa labari ba har saida Junaid d'in yayi kuka mai isarsa had'i da addu'o'i wa mahaifansa Barr na amsawa da ameen kafin ya daidaita kansa yaci gaba da fad'in

"Mun rasa mahaifanmu a wannnan lokacin, daga ni har Azeeza rasa mai k'arfin zuciya akayi cikinmu har saida Baba Datti mahaifin Zeenatu yayita nusar dani nine babba dole na koyi hak'uri ko don k'anwata Azeeza, haka Umma Marie wacce ta zamto tamkar uwa a garemu taci gaba da bamu baki.... A haka har abin ya soma barin jikinmu kullum Zeenatu tana gidanmu tana d'ebe mana kewa.... A lokacin ina jami'a Baba Datti ya buk'aci na soma aiki da DATTI INVESTMENT Companyn sa tinda yaga kalan k'wazona da himma na, sannan sunyi zama na amana da mahaifina marigayi Alhussain..... A haka na soma aiki da Datti Investment na maye gurbin mahaifina, ina karatuna ina aiki na soyayyarmu da Zeenatu na k'aruwa, kowa yasan muna soyayya I zuwa lokacin..... Wata rana Companyn mu ta soma samin barazanar fad'awa matsalan kariyar arziki wato bankruptcy, a lokacin Zeenat ta soma aiki itama da Comapanyn sai ya zamana mun hutar da Baba Datti nida Zeenat mune akan Compnayn muketa k'ok'arin shawo matsalar da muke k'ok'arin aukawa ciki... Kwatsam ana haka cikin k'ok'arin tallata hannun jari na kampaninmu da mukeyi Zeenatu ta had'u da SIRAJ LAUSHI President na LAUSHI GROUP.......

*SameenaAleeyou...📚*
[12/13, 5:14 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮

*06*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 7 · 0% Book details