Sashe 17
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Itama Innah mamaki ne ya cikata ganin Deejoh ta fito daga cikin rumbu, ashe nan ta shige ta b'oye, ita kanta Innah saida Deejoh taso bata dariya...
Baffah ya lura da yanda Deejoh ke rik'eda hannunta idanunta sunyi rau-rau
"Subhanallahi Deejoh mai ya sami hannun...?" Ya tambaya cikeda kulawa....
Nan Innah ma ta k'araso tana fad'in "Haka fah hannun nata da ciwo dama ta shigo, taho mu gani Deejoh... " Ta k'arashe tana fitowa daga d'akin....
Sosai hannun Deejoh ya k'one, abin tausayi idan ka gani, Innah kaman zatayi kuka sanda Deejoh ke basu labarin k'unar.... Oh Duniya abin tsoro, kasa ruwan zafi ka k'ona d'an mutum don bakai ka haifa ba, sai kace wani kaza....
Nan Baffah ya shiga had'a mata garin magani ya barbad'a mata a wajen k'unan dama Allah yasa ya iya ire-iren wad'annan magunguna na gargajiyan.... Innah ta zuba mata abinci paten dankalin hausa taci tayi nak sai bacci yayi gaba da ita.... Har d'aki Innah ta kaita ta kwantar saman gadonta mai rumfa... Zaune tayi gefenta had'ida k'ura mata idanu tausayinta na kuma ratsa ta, a haka ta dawo tsakar gidan ta tarar da Baffah na shirin komawa kasuwa, d'an zama gefensa tayi tana dubansa...
Dubanta shima yayi kana yace "Tayi bacci koh....?"
A hankali Innah ta jinjina kai... Kana ta muskuta tana mai fad'in
"Yanzu Malam haka zamu zuba idanu ana cutar da yarinyar nan... Malam anya bazaka duba maganata ta kwanaki ba....?"
Shiru Baffah yayi yana nazarin maganar nata kana ya sauk'e ajiyan zuciya yace "Shikenan babu damuwa anjima idan na taso daga kasuwa zan sami su Malam D'alha muyi maganar, idan yaso ko gidan Mai Unguwa ne sai muje, babu damuwa na fahimceki tabbas zaman yarinyar a hannun Gaje akwai cutarwa, kuma nasan da niyyan taimako kikayi hakan, babu komai Bilki na maki alk'awari wannan karan kam da yardar Allah Deejoh bazata koma gidan Gaje ba....." Ya k'arashe yana duban matar tasa wanda farin ciki da take ciki ya gaza b'uya.... Allah na gab da cika mata burinta...
***
Kallo d'aya yayiwa Nasaar ya watsar... Sandarsa da yake dogarawa ya kama sannan ya mik'e tsaye yana kuma duban Nasaar dake zaune gabansa kana yace "Nasaar na yarda dakai d'ari bisa d'ari kuma nasan bazaka failing d'ina ba....."
Dattijo d'an kimanin shekaru 70 a duniya ya fad'i yana duban Nasaar d'in...
*SameenaAleeyou📚*
[12/26, 12:44 AM] +234 810 044 6653: *FUSKA UKU*🏮
*14*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
K'uri ya mata babu ko k'yafta idanu yanda take kan faman murmushi, shid'inma murmushi ne kwance saman kyakkyawar fuskarsa...
Asma'u ta tsargu da kalan kallon da Junaid ke faman binta dashi.... D'an ware idanunta tayi kana tace "Ya dai...?"
Junaid ya kuma murmusawa had'i da girgiza kai kana yace "Has anyone ever told you that you are so beautiful... and especially when you smile....?" Ya k'arashe kannennun idanunsa akanta....
Murmusawa ta kuma yi had'i da rufe fuskarta da tafukan hannu tace "You so funny you know.... Now is your turn ka bani labarinka kafin su soma nemanmu a ciki...."
Junaid ya d'an gyara zamansa kana yace "Would it be OK if I start calling you Beautiful...?"
Kallonsa tayi yanda yayi maganar da iyaka gaskiyansa kana ta sadda kanta k'asa...
Ganin tayi shiru tamkar mai tunani ya sanyasa matso da kekensa kusanta sosai kana ya d'an sassauta murya
"Asmah...!"
Bata d'ago ta dubesa ba bata amsa sa ba, kwantar da murya ya kuma kaman mai son yin rad'a...
"Asmah I'm sorry idan bakiji dad'in maganata ba, and I promise bazan sake ba kinji, amma ko baki k'yaleni na kiraki da Beautiful a baki ba... In my heart zan ci gaba da kiranki Beautiful...."
Wani irin yanayi takeji wanda bata tab'a tsintar kanta ciki ba, jin muryarsa take yana ratsa duk wani sassa na jikinta, ji take tamkar a wata duniyar ta daban suke.....
Junaid na hankalce da ita, shikansa yasan plans dinsa suna tafiya yanda ya kamata.. D'an gyaran murya yayi kafin yaci gaba da fad'in "Asmah labarinki yayi shige da nawa, nima na rasa iyayena duka saidai ni banida wasu relatives a k'asar nan sabida iyayena ba 'yan k'asar nan bane, I was very young when my parents passed away... Ban san kowa nasu ba, koda na tafi k'asarsu ban san ta yanda zan soma neman danginsu ba.... I've no family... I'm all alone...." Ya k'arashe cikin siga na tsananin tausayawa...
Tunda ya soma magana take dubansa tausayinsa na ratsa b'argo da tsokarta....
Hannu tasa ta d'an goge hawayen da suka zubo mata kana tace "Allah sarki, labarinka yafi nawa abin tausayi sabida ni ko babu iyayena inada 'yan uwana wad'anda suke matuk'ar k'aunata.... Allah ya gafarta wa mahaifanmu baki d'aya, and insha Allah wata rana zaka sami danginka....." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta.... Junaid ya amsa mata da ameen yana mai hango fuskar Siraj a tattareda Asma'u, tabbas ji yake kaman ya shak'eta a wajen ya k'untatawa Siraj kaman yanda ya k'untata masa amma dole yabi komai a sannu muddin yana son cimma burinsa.....
***
Zaune yake a Office d'in nashi yayi k'uri ma hotonta cikin wayarsa, shi kansa ya soma tsoron kansa, ya soma yarda da batun Ayiya, toh ko dai da gaske aljanarce ta auresa, but how could that be possible... No..no baiso yasa ma ransa da gaske haka d'inne, zaici gaba da addu'a mahaifiyarsa tana tayasa, idanma wani abu ne ke faruwa da rayuwarshi koda a b'oyene Allah ya bayyanar masa... Saidai ya d'au alwashi ma kansa bazai kuma neman wata mace ba tsoron kada ya jefa rayuwarta cikin had'ari....
A hankali ya sauk'e ajiyan zuciya kana ya furta "Allah ya maki rahama Nadiya....."
K'aran da wayar talho d'in dake gefensa yayi ne ya sanyasa dawowa daga duniyar tunanin da ya tafi, a hankali ya d'aga wayar had'i da k'arawa a kunnensa...
"Yes Janet....." D'an dafe goshinsa yayi yana mai sauraron sakatariyan nasa kana yace "OK, send him in please....." Daga haka ajiye wayar yayi jim kad'an Nasaar ya shigo office d'in....
Cikin sauri Nasaar ya k'araso had'i da mik'awa Siraj hannu sukai masabaha lokaci guda suke gaisawa kana Siraj ya nunawa Nasaar kujera yana fad'in "Please seat Attorney...."
Nasaar ya zauna yanaima Siraj godiya.....
Gaisuwan ta'aziya Nasaar ya kuma yima Siraj da rashin da aka masa kafin ya sako masa wani zancen wanda ya shafi kasuwancin su....
Siraj ya d'auko wata jarida dake gefen table d'insa yana nunawa Nasaar yake fad'in "Naga an saka wad'anan estates d'in a kasuwa...."
Nasaar ya matso sosai yana kallon estates d'in kana yace "Yeah na gani nima a wasu jaridun...."
Siraj ya jinjina kai kana yace "I think I'm interested, get contact with the owner as soon as possible, and keep me posted.... Nayita neman wayan Lamid'o bai shiga amma tunda kazo shikenan....."
Nasaar ya jinjina kai kana yace "OK sir, right away..." Ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa had'ida sallama wa Siraj...
Har ya kai k'ofa Siraj ya kira sunansa, dawowa da baya Nasaar yayi yana sauraren Siraj d'in cikeda rusunawa....
Siraj yaci gaba da fad'in "About that girl.... Yarinyar da kake nema mata aiki, k'anwar matarka...."
Nasaar ya murmusa cikeda jin dad'i kana yace "Ai Sir tunda naga kwana biyun nan kaima baka zauna ba sannan ga rashi da aka maka shiyasa kawai na bar maganar zuwa wani lokacin..."
Siraj ya jinjina kai kana yace "Haka ne,.... Babu damuwa kana iya zuwa da ita gobe insha Allah...."
Nasaar da murmushin sa ya k'aru cikeda farin ciki yace "Really Sir..... Thank you Sir.... I'm forever grateful.... Na gode Sir...."
Murmushi kawai Siraj keyi kana yace "You've always been at good service to this company.... And this is the least I can do.... Besides kanada amana Nasaar so I'm quite sure duk wanda zaka kawo companyn nan mai amana irinka ne...."
Nasaar ya kuma masa godiya cikeda jin dad'in irin yarda da Siraj yayi dashi......
***
Lamid'o na shigowa gidan ya hangi Malam Sile zai tafi d'auko Nana A daga foundation... Cikin sauri ya fito daga motarsa ya nufi Malam Sile nan yake sanar dashi zai tafi d'auko Nana Asma'u ne lokacin tashinta yayi,
"Malam Sile ka barshi kawai ni zan d'aukota...." Cewar Lamid'o
Kallon mamaki Malam Sile ya bisa dashi kana yace "A'a rankashidad'e kar ka damu aiki na nake...."
Lamid'o ya murmusa kana yace "Kar ka damu ni na saka kaina...." Dai-dai lokacin Ayiya ta k'araso tana gyara mayafinta take fad'iwa Malam Sile ta fito.... Ganin Lamid'o wajen ya sanyata fad'ad'a murmushinta suka shiga gaisawa, nan Malam Sile ke sanar da ita buk'atar Lamid'o...
Ayiya ta dubi Lamido da murmushi tace "Anya kuwa Sarki zaka kula min da d'iyata har ka kawota gida...."
Lamido na murmushi yake jinjina kai kana yace "Insha Allah Ayiyarmu nayi alk'awarin kawo maki d'iyarki har gida sound and safe...."
Murmushi saman fuskarta take jinjina kai tana hango wani Al'amari idanun Sarki kaman yanda take kiran Lamido kana tace "Toh shikenan tunda kace haka, barin koma ciki na had'a maku sauk'a mai kyau kafin ku iso...."
Murmushi fal fuskar Lamido yake sunne kai yana fad'in "Yauwa Ayiyarmu... Idan na dawo akwai maganar da nakeso muyi...."
Ayiya ta amsa masa tana mai jinjina kai zuciyarta fari k'al hasashenta ya kusa tabbata....
Daga yanda take tsaye jikin window tana hangosu murmushi take har Lamid'o ya fice, cikin zuciyarta taci gaba da raya abubuwa da dama, lokaci guda ta sauk'e labulen ta shiga dialing layin mijinta taji ko ya sauk'a lafia.....
***
Suna haraban foundation d'in yana jira azo d'aukanta kafin ya tafi yayinda sauran ma'aikatam wajen keta masu sallama suna tafiya, idan ka gansu dole su baka sha'awa yanda suke cikin farin ciki,....
Nan suka hangi wata bak'ar Mercedes ta danno cikin foundation d'in.... Junaid ya dubeta da murmushi saman fuskar sa kana yace "Seems your driver is here.... Zanyi kewarki kafin gobe Asmah...."
Mamakin motar da ta gani ya hanata amsa maganar Junaid, da gaske motar Uncle Lamido take hangowa na shigowa cikin foundation d'in.... Junaid ya bita da kallo yanda take kallon motar.... A hankali shima ya maida dubansa ga motar, lokaci guda jijiyoyinsa jikinsa suka mimmik'e sake arba da yayi da d'aya daga cikin FUSKA UKU wad'anda yafi tsana fiyeda komai a rayuwarsa, Ji yake tamkar yayi tsalle ya shak'esa sanda ya hangesa ya nufosu murmushi saman fuskarsa....