← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 98

Sashe 15

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daina fad'in haka 'yar Albarka babu komai cikin taron nan sai tarin alkhairi da izinin Rabbi, ki kasance mai kyakkyawan zato kinji... Ke d'in alkhairice ga 'yan uwanki masu fama da lalura irin taki... Maza kintsa kanki ki fito muje na tabbata isowarki kawai ake jira...." Tana ida fad'in haka ta sakar mata murmushi...

Murmushin ta maida mata dashi itama kana Ayiya ta soma ficewa lokaci guda driver ya fito ya bud'ewa Nana A bayan motar k'irar Camry....

K'afafunta wad'anda ke rufe cikin sauciki su suka soma fitowa daga cikin motar, a dai-dai lokacin Dattijuwa Ayiya ta k'araso ta tallafawa Nana Asma'u ta ida fitowa daga cikin motar....

Nana A ta d'aga kai sama tana duban ginin wanda a kullum take mafarkin kasancewar hakan sai gashi Allah ya cika mata burinta, lokaci guda ta saki murmushi had'ida hamdala kafin ta dubi Ayiya tace "Alhamdulillah Ayiya Allah ya cika min burina, burin da ya jima yake kwance cikin zuciyata, wanda nake kwana dashi kuma nake tashi dashi...."

Ayiya ta kuma kamo hannun Nana A kana tace "Haka ne 'Yar Albarka Allah shine abin godiya... Maza mu k'arasa na tabbata isowarki kawai ake jira...."

Nana A ta kuma sakin murmushi kafin suka nufi cincirindon mutanen, securities d'in Siraj sai taimaka masu suke faman yi.....

Daga yanda yake zaune cikin wheelchair d'insa yana hangosu,.... Fuskokin da bazai tab'a mancewa dasu ba sune suka sake bayyana gabansa, fuskokin da yake kwana yake tashi dasu FUSKA UKU wad'anda yake kwana yake tashi da burin ganin bayansu, idanunsa ya soma sauk'a kan Ahidjo wanda bai mance ba shine yaga bindiga rik'e a hannunsa, gashi nan da matarsa sai raha da farin ciki suke.... Lokaci guda idanunsa suka sake sauk'a kan Lamid'o mutumin da bazai tab'a mancewa ba shi ya soma tattaka k'afarsa da iya k'arfinsa mutumin da ya soma janyo sanadi na kasancewarsa cikin nakasa, gashi a yanzu ya kuma zama k'akk'arfa fiyeda yanda yake a baya, alamun kwamciyar hankali ya dad'a samunsa.... Lokaci guda idanunsa ya sake sauk'a kan mutumin da yafi tsana gaba d'aya a cikinsu, mutumin da yayi sanadiyan rabuwarsa da farin cikinsa ZEENATU mutumin da ya janyo masa fad'awa k'uncin da yake ciki a yau wanda baya tunanin zai tab'a gushewa daga cikin zuciyarsa, baya tunanin wannan ranar tana zuwa...

Gabaki d'ayansu Junaid yake bi da kallo abubuwan da suka faru a baya na dawo masa, lokaci guda yaji zuciyarsa na masa wani irin zafi, k'aran harbin da akayima Zeenatu ihunta da maganganun da sukayi cikin waya ba daina yawo a kwanyar Junaid da kunnuwarsa ba, gaba d'aya baisan mai ake gudanarwa a taron ba sai kafe FUSKA UKU da idanu da yayi, ji yake da yanada hali ya shak'esu d'aya bayan d'aya sun daina numfashi kaman yanda suka raba Zeenatu da rayuwarta.....

****

*Misau*

A guje yauma ta shigo gidan tana ihu tana kuka hannunta yayi jajazir alamun k'una,...

Innah na surfen wake tayi jifa da tab'arya a tamanin ta nufo Deejo tana sallalami tana tafe hannu ganin yanda hannun Deejo ya d'ura ruwa yayi jazir alamun k'una....

Kuka Deejo take tana fad'in "Innah dan Allah ki ceceni kada ta kasheni, wllhi tace kasheni zatayi muddin ban amso mata kud'in Lado mai gurmi ba.... Innah dan Allah ki b'oyeni kice mata na mutu ko zan huta... Innah kiji tausayina dan Allah...." Ta k'arashe tana kuma fashewa da wani sabon kuka...

Innah ta gyara d'aurin zaninta tana kuma tafe hannaye cikeda mamakin yanda Duniya ta lalace a yau, shin har yaushe za'a daina samun matsalan kishiyar uwa a k'asar hausa? Shin yaushene addini zai wadace mutane su gane cewa shi yaro na mutum guda bane? Shin har yaushe son zuciya da son abin duniya zai bar zukatan mutane A DUNIYAR MU? Yaushe za'a daina wulak'anta d'iyoyi mata a wannan rayuwa....? Yaushene mutane zasu fahimci shi d'a a hannun marik'insa walau iyaye walau akasin haka amanace....? Tirk'ashi tabbas d'an Adam nada babban k'alubale a gabansa.....

Innah na cikin wannan tunani ta jiyo k'ara.... Krarau! An banko k'ofa an shigo, ga tsananin mamakinta Gaje ce ta taso mijinta gaba tana surfa masa ruwan bala'i tana fad'in yayi iyakawa shegiyar d'iyarsa da wannan gidan da mutanen ciki....

Ai Deejo na jinsu tuni tayi cikin rumbu ta b'oye tsakankanin buhuhuna ita kanta Innah batasan yanda akayi Deejo ta b'ace a wajen ba kawai dai bud'e idanu tayi taga babu Deejo a wajen, iyaka dai tasan Deejo na cikin gidan bazata fice ba saidai ta nemi wajen b'uya sabida jiyo sautin Gaje da tayi.....

"Toh annamimiya shugaban munafukai na duniya maza a fito mana da d'iyarmu tinda ita Allah yayi bamu sallamatawa bariki ba.... Fito mana da ita ehe....." Gaje ta k'arashe tana shan d'amara uwa 'yar wasan tashe....

Tun daga waje Baffah ke jiyo hayaniyar Gaje, yau wani ikon Allah haka kurum yaji ya baro kasuwa ya dawo gida aiko sai ga abinda ya tadda, Gaje ta yanda shiga bata nan take fita ba, sai tsine-tsine da rantsuwa take tana fad'in Innah Balki ta fito masu da d'iyarsu....

Baffah ya d'anyi gyaran murya yana duban Innah Balki kana yace "Bilkisu kin tabbata Deejo bata shigo gidan nan ba...?"

"Malam wai kaima ka yarda da maganar wannan matar ne... Idan taga Deejon ta d'auketa mana... Neman tashin hankali kawai irin nata, yarinya ana azabatar da ita yo mai kuwa zai hanata gudu...."

Mahaifin Deejo kuka yake sosai yana fad'in Deejonsa bata gudu ba Deejo tana nan bazata gudu ba.....

Baffah ya girgiza kai cikeda tausayin Malam Ard'o mahaifin Deejo, dafa kafad'ansa yayi ya soma basa baki cikin harshen fillanci Gaje kuwa bata daina bala'i tana fad'in a fito masu da d'iyarsu ba... K'arshe bincike ta shiga yi a gidan tana lek'a lungu da sak'o, harta madafi saida Gaje ta lek'a bataga Deejo ba, wani ikon Allah, Allah bai bata basiran lek'a rumbu ba... Haka suka k'araci bincikensu babu Deejo...

Yanda Baffah yaga hankalin Innah bai wani tashi ba yasan tasan wani abu gameda b'atan Deejo.... Gaje fah bataji ba bata gani ba daga gidan kad'an kan Mijinta sukayi suka nufi gidan Mai Unguwa don bata yarda ba Innah Balki bace ta b'oye Deejoh.....

***

Cikin lumana da kwanciyar hankali taron ke gudana, bayan an saurari jawabai daga b'angarori da dama aka soma raba kyaututtuka wa duk wani mai nakasa da ya halarci taron, a lokacin ne hargowa ya kuma b'arkewa sosai... Ana tsaka da wannan hidima wayar Siraj ta soma ruri, lambar Nadiya shi ya gani b'aro-b'aro ana tana kiransa, baisan dalilin fad'uwar gaban da yaji ya sauk'a masa ba sanda yaga kiran nata, yau gaba d'aya ko waya da ita baiyi ba.... A hankali ya soma k'ok'arin barin wajen dan keb'ewa yana kutsa cikin jama'a... A dai-dai lokacin Nana H da Lamid'o suka kalli juna wanda su kad'ai suka san ma'anar kallon nasu... Cikin sauri Lamid'o ya takewa Siraj baya.....

Lamid'o na isowa yanda Siraj ke tsaye yana amsa wayar ai shima sai ya tsaya cak yana duban Siraj wanda ke faman salati babu k'akk'autawa...

Cikin sauri Lamid'o ya k'arasa yana tambayarsa "Siraj lafiya... Make faruwa waye ba lafia....?" Duka tambayoyin lokaci guda Lamid'o ke jerowa Siraj.....

Cikin sauri Siraj ya katse wayar yana fad'in "Maama I'll be right there.... Zanjeni asibitin yanzu, kin kwantar da hankalinki insha Allah Nadiya zata sami sauk'i, zanjeni yanzu....."

Yana ida wayar ya soma tafiya cikin sauri yanai ma Lamid'o bayani....

"Lamid'o I've to go... Nadiya tayi accident a hanyarta na zuwa taron nan, tana asibiti unconscious, mahaifiyarta ce ta kirani yanzun nan take sanar dani....."

Wani irin bugu k'irjin Lamid'o yayi yana mai girgiza kai yake salati yana jajanta yanda lamarin ya faru....

Nana H da isowarta wajen kenan taji suna batun.... Wani irin kuka ta saki tana kuka sosai take fad'in "Uncle mai ya sami Nadiya... Dan Allah mai ya sameta kada kucemin wani abu ne ya sami k'awata... We were together yesterday har tace min zata zo ta taron Nana A da akeyi yau.... Uncle ina Nadiya take.....?" Kuka yaci k'arfin Nana H.... Saurin rungumota Siraj yayi yana lallashi dukda shima k'arfin halin kawai yake...

A hankali yake shafa kan Nana H yana fad'in "Is OK baby.... Nadiya zata sami sauk'i insha Allah... Ki daina kuka kinji koh...." Jinjina masa kai kurum take ba tareda iya furta koda kalma ba....

Sanda Lamid'o ya sanar dasu Ammah abinda ke faruwa nan suka ce basuci ta zama ba dole su tafi duba Nadiya da halin da take ciki....

Sosai hankalin Nana A ma ya tashi taso ta bisu asibitin amma Siraj ya buk'aci ta zauna a ida taron itada Ayiya, hakan kuwa akayi, Gaba d'aya Lamid'o saiji yayi tashin hankalin da Asma'u ta shiga ya d'aga masa hankali, baison ganin hawayenta sam, gaba d'aya baisan mai yake ji gameda ita ba... Kusanta ya matso sosai had'i da kwantar da murya ya soma lallashi yana bata baki "Nana....." Ya kirawo sunanta a hankali.... D'ago idanu tayi tana dubansa kafin yaci gaba da fad'in "Everything will be alright OK.... Kin kwantar da hankalinki kinji...."

Cikin nuna damuwa sosai ta shiga jinjina masa kai tana goge hawayen idanunta take fad'in "Please keep us posted Uncle Lamid'o.."

Cikeda kulawa ya jinjina kai yana fad'in "I'll insha Allah ok.... Just take care of yourself ok...." Jinajina masa kai ta kuma kafin sukayi sallama da Ayiya cikin sauri yabi bayan su Siraj

Gaba d'aya suka d'unguma suka nufi asibiti cikin tashin hankali.....

Siraj yaso Ahidjo ya wuce da Nana H gida sabida yanda hankalinta ya tashi sosai amma ta doge tace itama asibitin zata, tana son ganin Nadiya tasan halin da take ciki... Sosai ta baiwa Ahidjo tausayi ganin yanda hankalinta ya tashi dukda a kwana biyun nan ya d'auke mata gaba d'aya amma yau sai ta basa tausayi, rungumeta yayi cikin jikinsa yana kuma lallashinta yana fad'i mata Nadiya zata sami sauk'i...

Idan ka kalli Siraj dole ya baka tausayi driving kawai yake amma kasan hankalinsa baya jikinsa, shi kansa tausayin kansa yake, Allah sarki Nadiya Allah sa kar itama ta mutu ta barsa, a hankali yasa hannunsa yana goge idanunsa da yaji suna k'ok'arin kawo ruwa... Lamid'o dake zaune gefensa a hankali ya sadda kansa cikin zuciyarsa yake ji tamkar tausayin Siraj na ratsa sa tako ina.....
Chapter 15 · 0% Book details