← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 98

Sashe 85

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai kurum Zaliha take lokaci guda take furta "Umma Mairon da na gani yau bana tunanin Mairo ta ce, Umma Mairon da na gani yau ta banbanta da wancan, sannan ita wannan sunanta ya banbanta da wancan... Umma kaina ya d'aure gaba d'aya tunda nake a rayuwata ban tab'a ganin kamanni irin haka ba...." Ta k'arashe murya na tsananin rawa...

Shiru Umma tayi kana ta d'an dafata tace "Ba'a mamaki da ikon Allah, watak'ila kamanni kawai sukayi.. Allah babu abinda bazai iya yi ba...."

Jinjina kai Zaliha tayi still ta kasa daina kallon hoton Mairo had'ida tuno fuskar wancan matar ta foundation.... Kamannin yayi tsananin yawa.... Haka Zaliha ta kasance cikin tunani a wannan rana....

***

Shigowarsa garin kenan, daga can k'asar Bauchi garin Misau, sam baiyi zaton akwai mota bayarsa dake biyedashi ba.... Har ya iso wajen da babu mutane sosai baisan cewa ana biye dashi ba.... Kafin ya ankara sai gani yayi motar tasha gabansa.... Basuyi wata-wata ba suka isa motar nasa suka bud'e had'ida fincikosa lokaci guda suka sauk'e masa k'otar bindiga a k'eyarsa.... Lokaci guda Sabi'u ya fad'i wajen sumamme....

Take suka sungumesa suka jefa cikin mota....

Lokaci guda suka isa gaban Nasaar dake tsaye yana dubansu.... Jinjina kai yayi kana yace "Good, let's get going..." Take suka bar wajen cikin sauri, wasu daga ciki sukayi driving motar Sabi'u....

Bulama na hakince a parlor suka shigo da Sabi'u a hannu, Nasaar na gaba yayinda sauran muk'arabban nasa ke biye dashi.....

Dariya Bulama ya kece dashi had'i da mik'ewa yana dogara sandarsa, lokaci guda ya basu umarnin su shigar da Sabi'u d'akin da aka tanadar masa....

Bulama ya kuma duban Nasaar kana ya sakar masa murmushi "Nasaar keep on the good work..."

D'an murmusawa kurum Nasaar yayi kana yace "Zan koma gida Boss sabida kar Sabi'u ya farka ya ganni a nan...."

Bulama ya jinjina kai kana yace "Haka ne, kana iya tafiya, idan akwai wani abu zan nemeka...".

Nan ma jinjina kai kurum Nasaar yayi kafin ya fice cikin sauri....

***

"Nidai a ganina da kin sassautawa Siraj, ki barsa ya auri yarinyar nan tunda ya nuna yana k'aunarta..." Ayiya ta fad'i tana mai duban Ammah

"Ayshatu a koda yaushe nakan yi tunani hakki ne yake bibiyata kuma shine ke faruwa akan D'ana Siraj... Kina Siraj zai tab'a auruwa a duniyar nan tamu kuwa...?" Ta k'arashe tana mai duban Ayiyan...

Shiru Ayiya tayi tamkar bazatace komai ba sai kuma ta d'an muskuta tace "Ki daina irin wannan tunanin, ai Allah baya kama wani da laifin wani... Lokaci ne kawai, idan yayi sai kiga Sirajo yayi aure..."

Ammah ta jinjina kai kana tace "Har yau ina burin sake ganin Bintu mu rok'eta gafara...." Bata kai aya ba Ayiya ta mik'e tana mai fad'in "Mairo idan maganar Bintu zakiyi kinga tafiyata... FUKSA UKU bazasu sake kasancewa tare ba har abada.. Abubuwa da dama sun faru, bamu fatan su kuma faruwa.... Dan Allah kada ki kuma ambato Bintu, tinda mun riga mun aikata laifin.... Ko nace na taimaka maki wajen aikata laifin... Wllhi nayi d'an da na sani maras iyaka...."

Ammah ta goge hawayen da suka zubo mata kana tace "Munyi nadama gaba d'aya, kedai kawai mu ci gaba da rufa sirrinmu har tamu ta samemu..." Kuka sosai ya kufce mata, lokaci guda Ayiya ta k'arasa ta rungumeta, hawayen na sauk'a bisa k'uncinta itama...

***

Yau ma kaman jiya mafarki iri guda yayi da wancan matar da ya ganta cikin barcinsa.... Matan takan zo masa ne a matsayin matarsa. Lokaci guda yaji kansa na wani irin sarawa, sosai kansa ke masa ciwo.... Da k'arfin gaske ya kame kan nasa da duka hannayensa biyu...

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU🏮*

*56*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ko Sallan asuba bai iya fita ba sabida tsananin ciwon kai dake addabarsa, ji yake tamkar kwanyar tasa zata tarwatse, ji yake tamkar wasu abubuwa suna yawo cikin kwanyar tasa, saidai ya kasa tantance mai yake son tunowa, abubuwa ne da sam basu da dad'in tunani, abinda yafi buga masa kwanya shine k'onasa da ransa da aka tasamma yi, iyakacin abinda yake iya tunowa kenan saidai ko fuskar mutanen ya kasa tunowa, iyakacin abinda yake iya tunowa kenan sai kuma fuskar matar da ta addabesa cikin baccinsa da sunan matarsa....

Sosai abin ya dami illahirin gidan ganin ko sallah bai fita ba, mutumin da wataran karankataf gidan shike tasar dasu sai gashi yau shi bai fito ba, tabbas akwai abinda ke damunsa, misalin k'arfe takwas na safiya Mama Azumi ta damo masa kunun gyad'a mai kaurin gaske, nan ta tasashi gaba ya shanye kaman wani k'aramin yaro, had'in maganin ciwon kai mai tsanani ta masa, bayan ya samu ya sha maganin ne Baba Malam ya umarcesa da ya kwanta ya d'an sami bacci...

Kwanciyar kurum Ali yayi amma kansa ya kasa daina masa ciwo, wani irin sarawa kan nasa ke masa tamkar ana sauk'e masa guduma... Haka Hafiz ya saka d'an uwan nasa a gaba yana kallo tsananin tausayinsa ya cika zuciyarsa...

Idanuwarsa a lumshe kurum suke amma shi kad'ai yasan abinda yakeji.... A hankali ya bud'e idanunsa nasa ya sauk'esu kan Hafiz dake zaune gefen katifar tasa...

K'ok'arin mik'ewa yake Hafiz yayi saurin tallafa masa, ya jingina masa pillow ya d'an kishingid'a da kyau....

Sannu Hafiz yaci gaba da masa yana mai dubansa cikeda tausayawa...

"Yaya nikam nace bazamuje asibiti ba kuwa, kar mu biye na Mama kaga gwara mu tari ciwon kan da hanzari mu sani idan wani abin ne ma yayi causing...."

D'an murmusawa Ali yayi yana mai duban yatsun k'afafunsa da suke dogaye a mimmik'e kana ya d'an girgiza kai yace "Babu damuwa Hafiz maganin da Mama ta bani da alama ya karb'eni tinda gashi kan nawa ya soma daina min ciwon, kasan dama shi magani dace ne..."

Hafiz ya jinjina kai "Hakane Yaya amma zuwa asibitin nada muhimmanci, kaga dama Dr Sahal yace dole ka dinga ziyartan asibiti akai-akai sabida matsalar da kake fama da ita...."

Nan ma jinjina masa kai Ali yayi kana yace "Wato Hafiz wani abu ke damuna amma na rasa yanda zanyi na sanar da Baba Malam, kai bansan ta yanda zan soma sanar da kowa wannan zance ba...."

Gyara zama Hafiz yayi yana dubansa "Yaya ban gane ba... Meke damunka, wani abin ne ke damunka....?" Ya k'arashe cikeda kulawa...

"Hafiz wani mafarki nake yi mai firgitarwa had'ida ban tsoro da mamaki, sannan bayan wannan mafarkin sanda na farka na tuna abu guda about my past.... Shine bansan yaya zan soma sanar da Baba Malam ba...."

Ga mamakin Ali murna sosai ya gani kwance saman fuskar Hafiz harda hamdalah yake alamun godiyawa ubangijinsa...

K'uri ya masa kana yace "Ban gane kana murna ba alhali nace maka mafarki nake mai firgitarwa...."

"Yaya dole nayi murna tunda kace ka tuna abu guda gameda rayuwarka ta baya, sannan mafarkan da kake k'ila yanada alak'a da rayuwar taka ta baya...."

Shiru Ali yayi yana dubansa kafin ya jinjina kai yace "Haka ne Hafiz kace wani abu.. Amma wani hanzari ba gudu ba.... Gaskiya zuciyata tana raya min mummunar abu ne ya faru dani a rayuwata ta baya wanda sam bana fatan komawa cikinta, Hafiz nafi k'aunar kasancewa taredaku koda menene na baro a baya, zuciyata da tunanina suna fad'a min abu guda... Rayuwata ta baya anyi farautar ta ne, kuma wanda yayi farautar ta mutum ne mafi kusanci dani.... Shin Hafiz yaya zanji idan wani nawa ne silan shigata wannan tashin hankalin, shin zamata daku bai fiye min zama da wad'anda suke burin ganin bayata ba... Hafiz ba wai ina sanar dakai wannan bane don ina tsoron komawa rayuwata ta baya ko kuma don bazan iya tunk'aran wanda ya tasamma ganin bayata bane.... No, ina sanar dakai ne sabida banaso nayi rashin mutane irinku... Dukda ban saba da halayya da d'abi'un mutane sosai ba na tabbata ku d'in kunada zuciya mai kyau wacce ta wadata da alkhairai..." Ya k'arashe yana duban Hafiz d'in wanda tsananin taisayin Ali ya sanyasa zubda k'walla... Allah sarki ace iyakacin abinda zai iya tunawa kenan gameda rayuwarsa ta baya, mugun abu kawai ya iya tunawa ba tareda wasu alkhairai ba... Tabbas rayuwar Ali akwai ban tausayi da kuma Al'ajabi had'ida d'inbin jarabawa masu sauk'arwa bawa imani da tsoron mahaliccinsa... Kai d'an Adam ba komai bane idan ka d'auka kai komai ne, a yanzu Allah zai canza maka labarin rayuwarka kuma ya mantar dakai wancan rayuwar da kayi a baya, tabbas Allah shike samar da akwai daga babu.. Buwayarsa ya wuce gaban mamaki, ya kai d'an Adam mai yawan mantuwa da shagala idan kana tunanin idan an mutu babu wani rayuwa a gaba toh ka farka, tabbas akwai rayuwa bayan mutuwa, mahaliccinka zai tayar dakai bayan ya kashe ka..... Tunaninka kawai Allah zai shafe maka ka zamto tamkar sabon halitta... Ubangiji ka jarabcemu da jarabawan da zamu iya ci a rayuwa Ameen...

"Yaya a tunanina mu sanar da Baba halin da kake ciki ko akwai wani taimako da zai iya yi, tinda duk daren dad'ewa idan Allah yayi rayuwarka ta baya zata dawo maka dole zata dawo maka, shi bawa baya wuce k'addararsa a rayuwa...."

Jinjina kai Ali yayi kana yace "Shikenan Hafiz, da la'asar zaka min jagora na sameshi da maganar..."

Murmushi Hafiz ya saki don ba k'aramin dad'i yake ji ba idan ya bud'e idanu yaga yanada Yaya wanda zasuyi shawari tare ba sai lallai iyayensu sun sani ba, wannan wani ni'imace da ubangijinsa yasa yayi experiencing koda na d'an wani lokaci ne maras tsawo tunda a baya baida wannan gatan....

***

"Assalamu alaikum.... Sannu Umma, ina kwana...." Ma'ajura tace sanda take k'ok'arin duk'uwa, shigowarta gidan kenan ta tarar da Umma na firan dankali....

Amsa mata gaisuwar tata Umma tayi kana ta k'arada "Ma'ajura an fito, yaya su Umman naki...?"

"Eh Umma an fito... Lafiyansu lou tana ma gaisheki.... Umma fira ne kike, kawo na maki...." Ta k'arashe tana k'ok'arin amsar wuk'ar hannun Umma...

Murmushi kawai Umma take hankalin Ma'ajura na kuma birgeta... "Kinga kada ki b'ata jikinki, babu yawa ma ai na gama... Tashi abinki na yafeki...."

"Kai Umma wllhi Allah da kin bari na k'arasa maki...."
Chapter 85 · 0% Book details