← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 98

Sashe 34

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi kawai ta sakar masa ba tareda ta furta komai ba...

Idanunta a k'asa tace dashi "Dama gani nayi d'akin yayi k'ura shine... Shine na share..." Tayi maganar tana wasa da yatsun hannunta, lokaci guda tasa kai zata shige saidai kafin ta fice taji tattausan hannunsa ya kamo nata...

K'irjinta ya yanke lokaci guda, tayi saurin d'ago kai tana dubansa, wannan murmushin ne dai saman fuskar sa...

"Yaya zaki tafi bayan baki sanar dani abinda ya kawoki ba, ko kin mance ina waya kika shigo, ko yauma lab'e kike min kiji wayata da matata...."

Cikin sauri ta shiga girgiza masa kai kana tace "Wllhi Allah ba lab'el nake maka ba..." Tayi maganar kaman zata kurma ihu...

Ya d'an gimtse fuska kana yace "Toh mai ya kawo ki idan ba lab'el kikazoyi ba...."

Deejoh ta rasa mai zatace, wannan shine tsile, ita harga Allah tazo ganin yanayin da yake ciki ne domin sosai ya bata tausayi sanda ya fito daga sashen Baffah.. Toh ma mai zata soma fad'a masa, wani dalili ne ya kawota d'akinsa....

Ganin tayi shiru ta rasa abin fad'i ya sanya Ahidjo sakin murmushi kana yace "Kar ki damu nan ai d'akin mijinki ne ko kin shigo bakiyi laifi ba..."

D'akin mijinki da ya fad'i sai ya sanya jikinta yin sanyi, itakam wllhi harga Allah tama mance wai shid'in ne mijin da aka d'aura mata, tafi danganta gaskiyan labarin da tatsuniya sabida ko a mafarkanta D'angayu ya zarce irin mijin da take tunani, ina ita ina shi, wannan ko a 'yan gayun ma ba kowwacce bace ta dace dashi, wai ita Deejoh, Deejohn Iya Gaje itace wannan mutumin ya zamto mijinta, gashi har yana fad'i da bakinsa....

Bata ida tunanin nata ba taji ya kamo d'aya hannun nata ya mata masauk'i saman katifarsa yana fad'in "Zauna muyi magana"... Gefe da ita ya da ita ya zauna ta d'an matsa can k'arshen katifar a d'arare...

"Deejah ina so ki saki jikinki muyi magana... Ko kema baki son ganina ne kaman yanda Baffah baison ganina...?"

Da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a...

Ya jinjina kai had'i da furta "Good, kina jina ko....?"

Ta jinjina masa kai alamun eh...

Ahidjo ya kuma gyara zama kana ya soma fad'in "Kinga yanda Baffah ke fushi dani, kinga irin k'ok'arin da nakeyi wajen ganin na kyautata alak'ata dashi a matsayinsa na mahaifina.... Deejah duk duniyar nan ke kad'aice zaki taimaka min na sami soyayyar mahaifina da na rasa, ko baki so na sami albarkar sa...?"

A hankali ta furta "Ina so ka gyara alak'ar ka da mahaifanka.."

Ahidjo ya murmusa kana yace "Shiyasa nake so ki saki jiki sosai dani, ina so mu k'ulla shak'uwa tsakaninmu a matsayina na mijinki, idan Baffah ya lura da alak'a mai kyau dake tsanani na dake zai amince nayi na'am da zab'insu kuma hakan zaisa ya yafemin... Deejah inaso na tafi dake gidana Abuja na sakaki a makaranta kiyi karatu mai zurfi..."

Lokaci guda Deejoh ta shiga washe baki jin zata shiga makaranta, amma data tuna wai tafiya da ita zaiyi sai kuma taji murnan ta ragu....

Ahidjo na hankalce da ita yanda da fari ta soma murna daga baya kuma mood d'inta ya canza...

Kwanto da fuskarsa yayi kusan nata kana yace "Baki son karatun ne...?"

Da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a kana tace "Ina so sosai, babban burina kenan a rayuwata.... Amma ni banson binka nasan idan na tafi shikenan bazan sake ganin Babana ba kuma Innah da Baffah ai nima zasuyi fushi dani mutanen gari zasuce nima na gudu bariki...."

Kalamanta na k'arshe ya kusa sanyasa dariya wai zasuce ta gudu bariki... Gimtse dariyarsa yayi kana yace "Babu wanda zaice bariki kika gudu tunda mijinki kika bi, ko su Innah ma bazasu ce haka ba..... Ko baki son bin mijin naki ne....?"

Yanda yayi maganar ya bata dariya, saurin rufe fuskarta tayi tana murmusawa ba tareda tace komai ba...

Ledan sayyayan da ya mata fitansu d'azu ya janyo kana yace "Bud'e fuskarki..."

Kaman bazata bud'e ba sai kuma ta sauk'e hannayen nata a hankali idanunta a k'asa sabida sabuwar kunyarsa da ya shigeta.....

Mik'a mata ledar yayi kana yace "Wannan naki ne..."

Tabi ledar da kallo kana ta dubesa....

"Karb'i mana..." Ya sake fad'i yana dubanta..

A hankali ta girgiza masa kai kana tace "A'a na gode...."

Ahidjo ya d'an d'aure fuska kana yace "Mai yasa bazaki karb'a ba...?"

Idanun Deejoh a k'asa tace dashi "Ai Baffah zaiyi fad'a idan na karb'a..."

Murmusawa ya d'anyi yana mai dubanta yace "Waye yace maki Baffah zaiyi fad'a, kin tab'a ganin miji yayiwa mata kyauta tak'i karb'a.... I'm your husband Deejah... You're my responsibility, kar ki sake k'in karb'an wani abu daga wajena kinji... Idan su Baffah sunk'i karb'an kyautata ke ya zama maki dole ki karb'a kinji koh... Oya gashi amsa...." Ya k'arashe yana mik'a mata...

Hannu tasa ta karb'a had'ida d'an durk'usawa kana tace "Na gode Allah k'ara bud'i...."

Godiya da addu'ar data masa ya sanyasa binta da kallo wani abu na tsargar masa cikin zuciyarsa, har cikin ransa dad'i yaji donshi tunda yake kyauta dukda shid'in ba gwanin kyauta bane bai tab'a yin kyauta aka gode masa irinta yau ba... Ashe kayi kyauta ayi maka godiya akwai dad'i shikam bai tab'a sani ba sai yau... Har Deejoh ta fice daga d'akin bai daina binta da kallo ba....

****

*Abuja*

"A gaskiya Yaya Junaid kurum naji ban yarda da niece d'in nan tasa ba, gaskiya ni ina zarginta cikin FUSKA UKU in fact kawai ni jikina na bani itace FUSKA UKU, inaso na shiga jikinta sosai domin akwai abubuwa da dama da nake son sani gameda ita.."

Junaid da ya k'urama waje guda idanu d'ago rinannun idanunsa yayi yana dubanta kafin yace "Ba wannan na aikeki ba, you know nothing Azeeza.... Abinda na umarceki kawai zaki min... Rayuwar Siraj nace ki shiga... Kin fahimta..." Ya k'arashe yana bud'e mata idanu....

Jinjina masa kai kurum tayi kana tace "Shikenan Yaya zanyi yanda kace..."

Jinjina mata kai shima yayi kana yace "Good, Umma Marie ta kira baki nan zan kirata yanzu na had'aku..."

Azeeza harda d'an tsallen murnarta take cewa "Da gaske Yaya, dan Allah kira min ita... I miss her so terribly...."

***

*Damaturu*

Zaune take da bak'in nata wad'anda ta masu masauk'i a yammacin ranar, ganin kiran Junaid na shigo mata ya sanyata saurin mik'ewa tana fad'in bari ta amsa kira...

Jinjina mata kai kurum Daddah tayi tana mai ci gaba da kai lomar tuwo... Ta dubi Mairo data kafa goran Fanta a baki tana kwankwad'a ta d'an yafaci cinyar Mairo tana mai k'asa-k'asa da murya tace "Kinga Mata 'yar aljanna bata sanmu ba ta bamu masauk'i ta karrama mu.. Allah dai ya biyata...."

"Ameen.." Mairo ta amsa dashi lokaci guda ta tintsire da dariya....

Daddah ta bita da kallon tuhuma kana tace "Yo mai kuma nayi...?"

Mairo ta d'an tsagaita dariyarta kana tace "Wllhi Daddah Sojojin nan kawai nake tunani... Wato ranar da matar nan tasan kalan mutanen da ta baiwa masauk'i inaga ranar zata sallame mu...."

Yab'e da baki kurum Daddah ke dubaunta kana tace "Allah bazai amshi bakin ki ba, ni daga yau na zama salihatu kuma ai. ...Ke fita wannan bazan kuma ba balle nayi arangama da Sojin nan..."

Mairo ta murmusa tana maida kallabinta gefen goshinta domin idan da sabo yabi jikinta kana tace "Toh Allah sa Daddah ta, Allah sa daga garin nan bama kuma hijira ba...."

Daddah bata amsata ba sai kai lomar tuwonta take.....

Dai-dai nan Umma Marie ta k'araso tana fad'in "Ayya kuyi hak'uri na barku ku kad'ai..."

"A'a wllhi ai babu komai, Allah dai ya biyaki da Aljannah Mariya, samun irinki wannan zamani namu sai anji jiki...." Daddah ta fad'i tana kuma karyar lomar tuwo...

Murmushi kawai Umma Marie take tana jin k'aunarsu har cikin ranta lokaci guda suka ci gaba da fira garin da suka baro...

***

Tana jin k'aran bell tasan shine ya iso, cikin sauri ta mik'e tana kuma sauk'e wuyar rigarta ta isa k'ofan tana bud'ewa saiji tayi ya mak'ure wuyarta da iya k'arfinsa ya had'eta da garu yana fad'in "What the heck did you do Nana A... Where's she... Tell me, What did you do to her....?"

K'ok'arin k'wace wuyarta take amma ta kasa, sosai Lamid'o ya shak'eta... Duk iyaka k'ok'arinta ta kasa k'watan kanta sai faman k'ak'ari take tana shure-shure...

Har cikin ransa yake ji kaman ya gama da shegiya kowa ya huta, domin Nana H ta wuce annoba a cewarsa

Flower vase dake gefenta tayi k'ok'arin rarumowa don k'watar kanta.... Aiko Allah ya bata sa'a ta d'auko vase d'in nan lokaci guda ta sauk'ewa Lamid'o akai...

K'ara ya saki had'i da zubewa gefe.... Nana H ta samu ta mik'e tana watsa masa mugun kallo lokaci guda ta shiga sosa wuyarta yanda ya shak'eta....

Ta jima tana zube gefe itama tana sosa wuyarta had'i da yin tari kafin ta zamto dai-dai... Sai sannan ta hangi Lamid'o ko motsi baiyi ga jini a k'asar wuyarsa... Dafe kanta tayi cikeda tashin hankali ta shiga fad'in "Oh no no what have you done Nana H...."

Kaman zautacciya take shiga jijjiga Lamid'o shiru kakeji baya mosti... K'aran da wayar Lamid'on yayi ya kuma razanata... Cikin sauri ta ciro wayar daga aljihunsa tana kallo... Lamba ce kawai babu suna...

Hannunta na rawa ta d'aga wayar had'i da k'arawa a kunnenta ba tareda tace komai ba....

Daga d'aya b'angaren Malam Ayuba yace "Rankashi dad'e na zuba masa maganin cikin shayinsa kuma na tabbata yasha, na cika nawa aikin rankashidad'e saura naka...."

Wani irin bugu k'irjin Nana H yayi... Lokaci guda ta katse kiran tana tunanin waye Lamid'o ke yunk'urin kashewa....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*25*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 34 · 0% Book details