← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 98

Sashe 21

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Innah da ta kasa furta komai sai hawaye dake gangaro mata tafiya kawai take ta nufi yanda Ahidjo ke tsaye, hannayenta na rawa ta shiga shafa fuskarsa tana hawaye.... Shid'inma kallonta yake yana murmushi lokaci guda yake girgiza mata kai alamun ta daina kuka, a hankali yakai hannunsa fuskarta ya shiga share mata hawayen ta....

Ai Deejoh kam sai ta samu TV gyara tsayuwarta tayi da kyau rungume da takalmanta tana kallon ikon Allah, wannan D'an gayun kuma daga? Ta tambayi kanta....

Murya na rawa Innah take fad'in "Kaine da gaske, da gaske ka dawo garemu ne, ko kuwa wannan karanma sak'o kazo bamu kayi tafiyarka, dan Allah ka zauna damu kaji, kar ka kuma tafiya ka barmu kaji d'ana..." Ta k'arashe tana kuka sosai

Ahidjo ya kuma rik'o fuskar mahaifiyarsa yana share mata hawaye yake fad'in "Innah ba sak'o nazo baku ba, nazo ne sabida ku sabida na sake ganinku, sannan wannan zuwan nawa na maki alk'awarin ba kaman ko wanne bane zan kwana maki biyu Innah..."

Daga yanda Deejoh ke tsaye tana duban wadannan bayin Allah wanda takeji kaman ta masu kuka, kenan wannan D'angayun shine yaron Innah tilo da ya tafi bariki, Allah sarki Innar ta wani sabon tausayin Innah ya taso mata, cikin sauri ta nufi cikin gida don shiryawa D'angayu abinci tasan Innah zataji dad'in hakan...

Gaba d'aya Innah ta gaza sukuni Ahidjonta yazo gida, yau gaba d'aya mancewa da d'iyarta Deejoh tayi ko k'yafta idanu kan Ahidjo batayi, yo ita ko d'an kunyar nan ta fulani bata jisa ba koda shike k'ila don ta jima bata saka shi idanunta bane.... Suna zaune tsakar gida tana basa labarin Baffahn sa bai dawo ba da kuma irin fushin da yake dashi kaman daga sama suka jiyo k'auri daga kitchen wai Deejoh na girki.... Daga k'auri sai ihunta suka jiyo tana k'wallawa Innah kira, daga Ahidjo har Innah a d'ari suka nufi kitchen d'in salati da sallallami saman bakin Innah, sai sannan Innah ta tuna da Deejoh, tsaye suka ganta a kitchen d'in sai tsalle take ga wuta ya kama cikin tukunyar wanda zallan mangyad'a ce sai albasa ta d'ora bisa kurho d'in, Innah kame baki kawai tayi tana duban Deejoh tana tunanin yaushe ta soma girki a gidan... Ahidjo kuwa cikin sauri ya isa ya sauk'e tukunyar ya kashe wutan yana duban Deejoh wacce ya rad'a mata suna da Aljanar da yayi gamo da ita.... Toh wai shi a ina Innah ta samo wannan yarinya mai shegen tsoron tsiya da ihu, ya tsani hayaniya gashi ya tadda wannan creature d'in gidansu, anaya ma zai iya kwanakin da yace zaiyi da wannan yarinyar a gidan....? Muryar Innah ya katse masa tunanin sa sanda ta isa tana duba hannunsa tana tambayarsa bai k'one ba... Girgiza mata kai kurum Ahidjo yayi yana murmushi yake fad'in "Babu komai Innah babu abinda ya sameni...."

Kafin ya rufe baki Deejoh ta k'araso wajen a guje da ruwa cikin mod'a ga dukkan alamu daga randa ta d'ibo ruwan sabida sanyin da ruwan kedashi tamkar daga fridge aka ciro... Aiko tana isowa batayi wata-wata ba ta shek'awa Ahidjo a jikinsa gaba d'aya ita a dole zafin k'unan da yayi ya d'auke....

"Sannu D'angayu barin k'aro wani ruwan...." Ta kuma nufan k'ofa cikin sauri zata k'aro wani ruwan.... A d'ari Innah ta rik'ota tana fad'in "Ke Deejoh wai lafiyarki....."

Ahidjo dake faman binta da kallo da jik'ekk'en jikinsa sunan da yaji Innah ta kirata dashi ya maimaita cikin ransa _Deejoh_

Innah taci gaba da fad'in "Kanki guda Deejoh ya zaki jik'asa, jibi yanda kika masa daga sauk'ansa ,shin tarban da zakiyima Yayan naki kenan, ko so kike ya ce maki 'yar k'auye... Haba Deejoh...."

Banda rarraba idanu Deejoh bata komai, abinka da yarinta sai lokacin take jin kunyar abinda ta masa... Kai a k'asa tace "D'angayu kayi hak'auri.."

Innah baki sake tace "Ke banson sakarci Yaya zaki ce...."

Deejoh ta d'ago jagiranta da tun zuwan Ahidjo ya basa tsoro tana dubansa tace "Yaya D'angayu kayi hak'uri ciro rigar na shanya maka ita...." Ta nufishe tana jiran ya kwab'e rigar ya bata.... Innah ta dafe kai kurum tana jinjina shirirtar Deejoh...

Shiko Ahidjo yama kasa d'aga idanunsa daga dubanta wannan wata irin yarinya ce....

Muryar Baffah suka jiyo daga tsakar gida alamun ya dawo, a guje Deejoh ta kuma ficewa tana sannu da zuwa wa Baffah...

K'irjin Innah kuwa bugawa yayi tsoron yanda Baffah da Ahidjo zasu kaya, tasan mijin nata na tsananin fushi da d'an nasu....

Tuni Deejoh ta amshi bakkon da Baffah ya shigo dashi ta kai masa d'aki sai saka mata albarka yake murmushi kwance saman fuskar sa... A dai-dai sanda Innah da Ahidjo suka fito daga kitchen d'in Baffah ya hangesa, tilon d'ansa wanda ya sadaukar da komai nasa just to make him win, dukiyarsa da k'arfinsa a k'arshe ya watsa masa k'asa a idanunsa... Lokaci guda murmushi dake saman fuskar Baffah ya d'auke cak..... Ahidjo yana hango hakan fuskar mahaifinsa yayi saurin sadda nasa fuskar k'asa...

Innah ko gaba d'aya jikinta sai ya kuma yin sanyi, a hankali ta soma takowa ta nufo Baffah.... Zatayi magana Baffah ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu still idanunsa kan Ahidjo wanda ya sadda nasa fuskar k'asa...

Cikin dakekkiyar murya Baffah yace "Mai ya kawo ka gidana....?"

Shiru Ahidjo bai iya furta komai ba sai zafi da k'irjinsa ke masa yasan zai fuskanci hakan daga mahaifinsa, amma dole ya nemi gafaran mahaifinsa koda bazai gafarta masa ba.....

"Tambayarka nake...." Baffah ya kuma fad'i cikin dakekkiyar murya....

A hankali Ahidjo ya furta "Baffah kayi hak'uri...." Bai kai aya ba Baffah ya shige d'akinsa cikin sauri zuciyarsa na masa wani irin zafi......

Innah ta kai dubanta ga Ahidjo dake tsaye wajen tamkar wanda aka dasa kafin tayi saurin sa kai tabi bayan mijinta,... Deejoh kuwa gaba d'aya sai taji jikinta yayi sanyi bata tab'a ganin Baffah cikin yanayin ba kenan shi baya farin ciki da dawowar d'an nasu... Allah sarki, sosai suka bata tausayi, su Innah da Baffah mutane ne masu karamci wanda samun irinsu a wannan duniya tamu tai k'aranci, nasu jarabawan kenan kan tilon d'ansu D'angayu... Kasa fita tayi daga d'akin ta isa can k'urya ta zauna tana tunanin nata mahaifin wanda ke hannun azzalumar kishiyar mahaifiyarta, Allah sarki rayuwa....

***

Zaune yake a parlornsa tunanin abubuwa da dama sun kasa barin kwanyarsa, dafe kansa yayi yana duban kwalban barasa dake gabansa, maganganun Babansa ya shiga yawo a kwanyarsa, shida gidan mahaifinsa amma bashida ikon shiga, ya tirsasa masa abota da Siraj ya tirsasa masa kutsawa cikin familyn Siraj saida ya saba da Siraj yake jinsa kaman d'anuwa sannan ne mahaifinsa ke neman bijiro masa da abinda bazai tab'a yuwa ba, shifah cutar da Siraj da yakeyi ba'a son ransa bane toh yanzu kuma ta yaya zai soma dab'awa Siraj wuk'a a ciki, tabbas zai iya kashe kansa kenan, uwa uba yanzu da yake matuk'ar k'aunar d'iyar Yayan Siraj yanzu da yake neman yardar Siraj fiyeda lokutan baya ta yaya zai soma janyo abinda zai saka ma Siraj da family d'insa shakku akansa, shin waima meye dalilin mahaifinsa na neman ganin bayan ziri'ar Siraj, he needs to find out, dole yasan asalin dalilin mahaifinsa na ganin bayan zuri'ar Mas'ud Laushi.... Ya k'arashe tunanin yana kwankwad'ar barasar sa.... Knocking d'in da ya jiyo daga k'ofarsa ya sanyasa saurin mik'ewa yana neman wajen b'oye barasar domin ba kowa yasan yana sha ba idan ka cire Nana H....

Yana cikin dibi-dibin b'oye kwalbar giyar ta bud'e k'ofar parlorn ta shigo... Wani mugun tsaki ya buga yana watsa mata muguwar kallo....

Fashewa tayi da dariyar had'i da ajiye handbag d'inta saman hannun kujera ta nufi Lamid'o tana karairaya.... Saida ta iso har gabansa tana wani tottoshe hanci take fad'in "Oh what's this smell for... Gosh it's terrible.... Oh wait you seems very depressed meke faruwa darling...."

Lamid'o da tuni yazo wuya fincikota yayi da k'arfin gaske yana fad'in "What the hell brought you here,.... Didn't I tell you to stay away from me.... Stay out of my life, kar na sake ganin k'afafunki a gidana...."

Murmushin rainin hankali ta masa tana mai shafa fuskarsa take fad'in "Oh Darling seems you're tipsy don't worry I can take care of you OK...." Ta k'arashe tana wasa da yastun hannunta saman fuskar sa...

Hankad'eta gefe yayi ya shiga nunata da yatsa yana fad'in "Nana H ki fita daga rayuwata, kafin na zame maki bak'in kumarci a rayuwarki... I love Nana A and I want to marry her as soon as I proved to Siraj that I'm her Mr Right...."

Dariya ta kuma fashewa dashi tana nuna sa da yatsa take fad'in "Su Mr Right manya... Lallai you are fooling yourself, ai bari kaji na fad'a maka idan kana mafarki gwara ka farka, wllhi wllhi ina raye bazan tab'a bari ka rab'i 'yar uwata ba balle kayi tunanin aurenta.... You're just making a fool out of yourself, idan ka tak'ura zan fasa k'wai zan sanar da Heedj who you really are, zan sanar dashi kalan amanarsa dake ci, sannan kowa zai tsaneka ya juya maka baya including gurguwar masoyiyarka....... So darling ina shawartarka mu ci gaba daga yanda muka tsaya...." Ta k'arashe tana masa wasu salo...

Murmushi yake yana dubanta kana yace "Do you really think I'm scared of your threats...." Ya kuma murmusawa had'i da girgiza kai kana yaci gaba da fad'in " Kin b'ata wllhi, baki k'aramin komai ba sai k'arfin gwiwa, kedai kawai hassada kike Nana A ta auri wanda take so tunda ke wanda kike masifar k'auna babu aure tsakanin ku shiyasa kika zama trash mai kula ko wani irin shirgi... Wllhi Ahidjo bai dace dake ba sam and I'm hoping one day zai sami mace da ake kira mace ba irinki muna mata ba.... Wani abu ma sai randa kika rako Nana A d'akina don na tabbata kece zaki mata babbar k'awa na kashe maki idanu na maki godiya na kuma sallameki na janyo Matata....." Bai kai aya ba ta daka masa wani irin tsawa har b'ari jikinta keyi k'walla na neman ciko idanunta...

Lamid'o ya kuma murmusawa kana yace "Does it hurt....? Na tabbata yanzu zaki kwashi k'afarki ki fice daga gidan nan....."
Chapter 21 · 0% Book details