← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 98

Sashe 44

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba d'aya Ahidjo ji yayi jikinsa ya masa sanyi sosai, bai tab'a tsammanin shak'uwarsu da Deejoh yakai haka ba.... Kasa furta mata komai yayi sai bin kyalkyawar fuskarta da hawaye ya wanke yake da kallo.... Zuciyarsa ta masa rauni sosai, ji yake kaman bazai iya tafiya ya bar Deejoh ba.... Shin ta yaya zai sanar da ita wani tafiya zaiyi mai tarin had'ari.... Wani b'angare na zuciyarsa can k'asa ji yake kaman idan ya tafi bazai dawo ba.... Lokaci guda ya janyota cikin jikinsa ya matseta sosai kaman mai tsoron kada a rabasu.... Yana jin kukanta har cikin k'irjinsa,....

"Dee I'll come back for you kinji.... Idan na dawo wannan karan zan d'aukeki mu tafi koda su Baffah bazasu amince ba.... You're my wife Dee, Shari'a ta yarjemin koda su Baffah basu yarjemin ba kinji koh....."

Kasa cewa komai tayi sai hawayenta da suka k'aru, girgiza masa kai kurum take tana fad'in kada ya tafi ya barta cikin kuka....

Rungumota ya kumayi cikin jikinsa yana girgiza mata kai alamun ta daina kuka, lokaci guda yasa harahensa ya shiga lashe hawayen dake bisa fuskarta idanunsa a lumshe shima..... Daga nan al'amra suka soma canzawa tsakaninsu..... A wannan daren Ahidjo ya mance amaryar tasa k'aramar yarinya ce mai k'aramin shekaru.... A wannan dare Ahidjo ya maida Deejonsa cikakkiyar mace cikin lumana da tsananin nuna shauk'i dukda cewa su duka biyun sun wahala sosai....

Nitsuwa ya samu wanda ya jima bai sameta ba.... Tana kwance cikin jikinsa tana kukan da bai fita... Gani take ta tapka babban sab'on da Allah bazai tab'a yafe mata ba... Ita harga Allah batasan wannan itace rayuwar aure ba....

Shi kansa baiso hakan ta kasance ba amma babu yanda ya iya don ya kasa controlling kansa, ba a haka yaso yazowa Deejoh ba, shi kansa yasan ya apka mata da wuri, rayuwa mai cikeda jin dad'i ya tanadar masu saidai kana naka ne Allah na nasa, Na Allah shine dai-dai, tuni Allah ya k'addara faruwan hakan, tunawa da yayi Deejoh halal d'insa ne sai yaji hankalinsa ya kwanta ya sami nutsuwa sosai cikin zuciyarsa....

Lallashinta yaci gaba da yi yana sanar da ita halacin abinda suka aikata, da kuma matsayin mata da miji a addinance... Sosai yake fayyace mata komai yana sanar da ita wasu ilimi da bata sani ba...

Tsananin kunyarsa ya hanata koda motsa d'an yatsanta ne, jin abinda sukayi ba haram bane sai ya sa hankalinta kwanciya, ta daina kukan sai ajiyan zuciya da take sauk'ewa...

Albarka Ahidjo yaci gaba da saka mata had'i da masu addu'o'in samun zuri'a d'ayyiba...

Gaban Deejoh ne yayi masifar fad'uwa sanda ta tuna yanda suke... Ta zabura zata mik'e taji azaban zafi ta k'asanta... Lokaci guda ta saki k'ara, saurin rik'ota yayi yana tambayarta mai take so..... Ai sabon kuka Deejoh ta fashe masa dashi tana nuna masa d'akin da suke ciki....

Sai sannan Ahidjoh ya fahimci d'akin Innah suke ciki, bazai tab'a son wani ya tadda halin da suke ciki ba shida iyalinsa..... Cikin sauri ya fice ya nufi kitchen yana k'ok'arin dafa ruwan d'umi, saidai kunna risho d'inma ya zame masa aiki.... A haka Innah ta jiyo karauniyarsa a kitchen, mamaki ya cikata ganinsa da tukunya yana k'ok'arin d'aura ruwa....

"Babana lafia dai koh...?" Innah ta tambaya tana dubansa, baima san ta shigo kitchen d'inba sai lokacin... 'Yan kame kame Ahidjo ya soma ya rasa mai zai ce mata gaba d'aya... Karb'an tukunyar tayi tana fad'in "Ai da ka kira Deejoh ta dafa maka ruwan .. Wai ina ta shiga ne ma....?" Ta k'arashe tana k'ok'arin d'aura tukunyar bisa madafi...

Shafa k'eyarsa ya shigayi warily ba tareda ya furta komai ba don baisan mai zaicewa Innah ba, a hankali ya zame ya koma d'akin cikin sauri, ya soma kintsa wajen don wannan wani sirri ne nasu da ko mahaifansu bai kamata su gani ba, kaman yanda take a baya a Al'adan fulani....

Yana k'ok'arin taimakawa Deejoh ta mik'e suka jiyo sallaman Innah... Deejoh taji wasu sabbin hawaye suna gangaro mata, kallo d'aya Innah ta masu ta gane wani abu ya faru...

Shafa kansa ya kumayi murya na sark'ewa yake sanar da Innah cewa Deejoh ce bataji dad'i ba...

Innah da tuni ta gane meke wakana jinjina masa kai kurum tayi zuciyarta na mata wani irin dad'i kana tace "Jeka zan kula da ita...."

Ya kuma shafa k'eyarsa yana satan kallon Deejoh dake faman hawaye murya can k'asa yace "Toh.... toh Innah..."

Sihirtaccen annuri ne kwance saman fuskar Innah, fatanta Allah ya azirta yaran nata da zuri'a d'ayyiba.. A haka ta k'arasa ta kamo Deejoh tanai mata sannu har suka fice daga d'akin...

Innah da kanta ta had'a wa Deejohnta ruwan d'umi ta kimtsa ta, daga bisani ta umarce Deejohn da tayi wankan tsarki irin wanda ta koya mata kwanakin baya lokacin data soma al'ada, dashike Deejoh batafi wata guda da soma Al'ada ba kafin zuwan Ahidjo.... Niya kawai Innah ta umarceta ta banbanta amma wankan iri guda ne....

Wajajen k'arfe goma da rabi na dare k'afafu sun soma d'aukewa garin ya soma yin shiru babu shaguna sosai a bud'e sai ka fice bakin babban kwalta....

K'aton super market dake gefen gidan mai yajesa yayo ma Deejoh sayayya, duk abinda ya d'aga sai yaga zataso, dangin kayan mak'ulashe da sauransu...

Yana tafe a mota shi kad'ai yana sakin murmushin nishad'i, wani irin nutsuwa ya tsinci kansa ciki saikace ango mai auren fari....

Yana shigowa gidan ya iske Innah da Baffah basuyi bacci ba suna zaune parandar Baffahn tamkar shi suke jira... Gabansa ya yanke ya fad'i lokaci guda.....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*32*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

_God Bless Momma's_

Gabaki d'aya kasa shiga gidan yayi, ji yayi kaman an d'aure k'afafunsa, tamkar ya juya haka yaji saidai kafin ya ida wad'annan tunani nasa ya jiyo muryar Innah tana fad'in "Babana shigo mana ya ka tsaya daga wajen...."

Da k'yar Ahidjo ya iya saita kansa kana ya soma takowa wata sallaman saman harshensa, gani yake tamkar Baffah zai masa d'add'aya....

Daga can gefe ya d'an zauna wacce tafi kama da durk'uso yana mai gaida iyayen nasa.... Innah dai sai wani sabon faran-faran take masa yayinda Baffah ya amsa babu yabo babu fallasa kaman kullum.... D'an sayayyan da yayo masu ya k'arasa ya aje gefen Innah yana mai fad'in "Innah ga wannan babu yawa...."

"Kai madalla, toh Allah yayi albarka... Ka shiga ka duba Deejohn ne....?"

D'an shafa kansa yayi kana yace "Dam yanzu.... Zan shiga ..." Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye....

Har ya soma tafiya ya jiyo muryar Baffah ya ambaci sunansa cikin dakekkiyar murya... "Aliyu"

"Na'am Baffah....!" Ya amsa cikeda rusunawa, lokaci guda ya dawo mazauninsa ya kuma zama

Saida aka shafe kusan mintuna uku masu kyau Baffah baice komai ba, ba Ahidjo bane kawai ya damu da shirun Baffah harta Innah saida ta tsinci kanta cikin fad'uwar gaba da shirun mijin nata....

Bayan shud'ewan dak'ik'an Baffah yaci gaba da fad'in "Aliyu, ban aura maka Deejoh don kaci zarafinta ko ka wulak'anta ta, ko kayi mata wani abu mai kama da haka ba...."

Maganganun Baffah sun saka k'irjin Ahidjo bugawa, innalillahi mai Baffah yake nufi, ba dai magana yake akan abinda ya faru tsakaninsa da Deejoh daren yau ba.... Muryar Baffah ya katse masa tunaninsa yanda yaci gaba da fad'in "Deejoh amanace a hannunmu kuma kaima amana ce a hannunka... Aliyu sam Deejoh bata kamace ka ba..."

Ahidjo ya d'ago idanu yana duban Baffah, Innah ma Baffan take duba...

Baffah yaci gaba da fad'in "K'warai Deejoh bata kamace ka ba, sabida ita yarinyace mai biyayya kai kuma D'ah ne maras biyayya,.." Sai sannan Innah tayi saurin katsesa da fad'in "Haba Malam, ya zaka dinga fad'in kalamai irin wad'annan akansa, baka gudun kalamanka suyi tasiri akansa....!"

Wani kallo kurum Baffah ya mata ta kasa ci gaba da maganganun nata amma kam zuciyarta bata daina mata zafi ba...

Baffah yaci gaba da fad'in "Kana saurare na.... Wllhi idan ka wulak'anta Deejoh bazan tab'a yafe maka ba..."

Cikin sauri Ahidjo ya kuma d'ago kai yana duban Baffah kafin ya shiga girgiza kai yana mai fad'in "Haka bazata kasance ba insha Allah... Nasan na tapka kurakurai a baya amma insha Allah bazan sake tapka irin kuskuren dana tapka a baya ba.... Baffah koda ace bana son Deejoh ta zama wani b'angare na rayuwata a yanzu kuma the last thing da zanyi a rayuwata shine na wulak'anta ta.... Insha Allah bazaka sameni da wannan kuskuren ba na maka alk'awari..."

Tausayin Ahidjo sosai ya kama Innah mai yasa mijinta bazai dinga kyakkyawan zato wa tilon d'ansu ba, meyasa yana mik'a wuyarsa ga shiriya mahaifin na pushing d'insa.... Tabbas wasu iyayen suke janyo wa yaransu fad'awa wata irin rayuwa, bazata gushe ba tana addu'an samun sauk'i da shiriya D'anta....

Har Ahidjo ya bar wajen Innah bata daina jimami da takaicin irin kakkausar harshe da mijinta ke amfani dashi kan d'an nasu ba....

Shiko Ahidjo gaba d'aya sanyi jikinsa ya masa musamman da ya lek'a d'akin Innah ya hangi Deejoh k'udundune a gado hawaye na sauk'owa daga idanunta, A hankali ya k'arasa shigowa d'akin had'i da zama gefe da ita, yana jin sanda sautin kukanta ya k'aru.... Zuciyarsa naci gaba da masa rauni... Baisan sanda ya kwanto ya rungumeta ta baya ba had'i da lumshe idanunsa....

Itama lumshe idanun nata tayi sabbin hawaye suna gangaro mata....

Sun d'an jima a haka kafin ya mirgino da ita suna fuskantar juna, lokaci guda Deejoh ta lumshe idanunta bata yarda sun had'a idanu ba...

K'uri yayiwa fuskarta wanda siraran hawaye suke kwance bisa.... Murya can k'asan mak'oshi tamkar mai rad'a yace "Are you still crying...?"

Jin bata amsa sa ba yakai 'yan yatsunsa saman fuskar nata yana bin hawayen yana shafasu a hankali yake fad'in "Dee kuka kike har yanzu.... Kiyi hak'uri kinji...." Ya k'arashe shima tamkar mai shirin kukan...

Fuskarta ta juyar d'aya b'angaren sabon kuka na zuwa mata tace "Ni ka k'yaleni......"

Ahidjo kuwa kwantar da kansa yayi a bayanta hannayensa na kewaye da ita gaba d'aya kana yace "Dee bazan iya k'yaleki ba, ke d'in b'angrene daga jikina..."

Kukanta ne ya sassauta kana tace "Da gaske....?"

Yanda tayi tambayar cikeda yarinta yasa Ahidjo dad'a rungumota jikinsa had'i da murmusawa kana yace "Sosai ma ko bakisan daga ribs d'ina aka cireki ba...."
Chapter 44 · 0% Book details