Sashe 78
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin haushi da takaici ta kuma basa, bai daina huci ba yake ci gaba da fad'in "Fine, na fahimceki Nana A, kuma sai yanzu na yarda da batun 'yar uwarki Nana H da tace min baku auren talaka Uncle d'inku bazai tab'a bari ba.... Na fahimci matsayina a wajen ki, zan tafi, zan tafi na fice daga rayuwarki completely, amma ki sani ban tab'a soyayya da wata mace ba saike kuma bazan sakeyi ba har abada....." Daga haka juyawa yayi ya fice cikin sauri kaman zai d'age wheelchair d'in nasa sama....
Dirshan ta zauna saman kujera had'ida kifa kanta tana kuka sosai...
Aunty Lami da bata jima da shigowa ba taga ficewar Junaid cikin wani irin yanayi da bata tab'a ganinsa ciki ba, hakan yasata saurin nufan ofishin Nana A don ta lura daga nan ya fito..
***
*Damaturu*
Tafe suke kan babur d'in nasu, babu mai cewa komai cikinsu domin kuwa sun tapka rashin sa'a a lokacin da suka isa gidan Umma Marie suka tarar babu kowa wani mak'oci ke sanar dasu ai sun tafi wajen sana'arsu kuma basu dawowa sai can yamma, sam basuji dad'in hakan ba musamman Ali wanda tun baiyi idanu hud'u da Mairo ba yake jin babban Al'amari a tattare da ita, ji yake wani abu na fizgarsa musamman idan ya tuna jininta ke yawo cikin jijiyoyinsa, a koda yaushe idan aka ambaci sunan Mairo yakan tsinci kansa uwa wata duniya na tunani wanda shi kansa bai isa yace ga tunanin tak'amaimen abinda yake ba, can k'asar zuciyarsa baida burin da ya wuce ya sanya Mairo cikin idanunsa... A hankali ya saki murmushi kafin ya furta "Mairo...!"
Hafiz dake tuk'in Babur d'in saida gabansa ya yanke ya fad'i, mai yasa zuciyarsa ta soma raya masa wani abu gameda Ali, shifa ya soma shakku irin yanda Ali ke matuk'utar son ya sanya Mairo cikin idanunsa, anya kuwa bazai fito fili ya sanar da Ali k'udirinsa akan Mairo ba, toh amma baijin kunyarsa zai barsa ya fito fili ya fayyace abinda ke zuciyarsa gameda Mairo uwa uba idan ya tuna Daddah da kalan masifanta sai yaji jikinsa yayi sanyi gaba d'aya, a wani b'angare na zuciyarsa tausayin kansa yake don ko kad'an Mairo batasan yana wannan aiki ba.... Saurin maida hankalinsa ga tuk'i yayi ganin tunanin na neman zautar dashi, cikin Ali da Hafiz kowa da kalan tunanin da yake har suka isa gida, tabbas su duka biyu sun aukawa tunanin mace guda wacce ko d'aya batasan sunayi ba....
***
*Abuja*
Lamid'o yana fita apartment d'insa ya wuce, yanda ya tarar da abubuwa na ban mamaki, tabbas akwai wanda ya shirya masa gadar zare a cikin wannan gidan kuma yabi kai ya auka..... Rik'e yake da kwalban whiskey da ya tsinta a parlorn nasa wasu tunanin suna yawo cikin kwanyarsa, ya jima yana bin parlorn da kallo kafin ya sinkayo muryar guard d'insa yana fad'in "Sir ya kamata mu fice a nan sabida Boss baisan zamu zo wajen nan ba idan ya sani zan iya rasa rayuwata kuma time d'in da ya d'ibar maka a waje ya kusa cikawa...."
Dubansa Lamid'o yayi da straight face kana ya jinjina kai yace "I won't get you into trouble JD kar ka damu... So may I use the restroom....?"
Jinjina kai JD yayi kana yace "I hope so don kasan Boss yana da idanu everywhere, don't take too long otherwise nidakai duka mu shiga trouble...."
Jinjina kai Lamid'o ya kumayi kafin ya nufi bedroom d'insa... A nan ne gabansa yayi wani irin bugu, inners d'in mace ya gani zube saman gadonsa had'ida wasu shirgin da ba Nana A ba koma wacece ta gani dole ta k'yamacesa...
Huci kurum yake zufa na kuma tsartsafo masa, cikin sauri ya fad'a bathroom d'in kafin ya cire takalmin k'afarsa guda, tsakiyar takalmin d'an tsagu ne lokaci guda ya zaro wata wayar salula daga ciki........
*SameenaAleeyou...📚**FUSKA UKU*🏮
*53*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Yana ciro wayar ya d'aga k'asan takalminsa yanda wasu lambobi ke rubuce lokaci guda ya shiga lodasu cikin wayar ko ba'a fad'i maka ba recharge card ne ya rubuta a wajen ya shigar cikin wayar tasa, take ya soma dialing wata layi,... Shiru shiru ba'a d'aga ba,... Desperately yake furta "Pick up... Pick up... C'mon..." Lokaci guda aka d'aga wayar,....
Magana sukayi na shud'ewar wasu dak'ik'ai wanda sam ko nima ban iya saurarowa ba, saidai daga bisani naji yana furta "Don't fail me please.... Sai ka jini, kar ka damu da kirana duk sanda na sami chance ni zan kiraka no one should know nida kai muna communicating.... I've to hang up... Kawai yanda na sanar dakai d'in..."
Jiyo k'aran footsteps d'in guard d'insa ya sanyasa saurin katse wayar lokaci guda ya cire SIM card d'in ya tura cikin ramin takalminsa kafin ya jefa wayar cikin toilet seat had'i da flushing d'inta....
Aiko yana fitowa daga bathroom d'in sukayi idanu hud'u da JD....
K'uri yayiwa Lamid'o yana karantarsa kana yace "What are you planning...?"
Kallon ban fahimceka ba Lamid'o ya masa kana ya murmusa da gefen bakinsa yace "I just used the bathroom ko shima za'a hanani ne...?"
Girgiza kai JD yayi kana yace "I hope you don't get us into trouble..."
Lamid'o dai bai furta masa komai ba saima k'ok'arin daidaita belt d'in wandonsa da yake lokaci guda yake furta "If you don't believe me, you can go ahead and search me...."
JD ya kuma dubansa kafin ya kai masa wata damk'a ya janyo wuyarsa yana furta "Let's get out of here...."
Haka ya janyo Lamid'o kaman wani rago ya jefasa cikin mota kafin suka d'auki hanya...
***
"Kana nufin babu hali naga Azeeza....?" Ya kuma tambaya a karo na biyu yana mai duban Nasaar d'in...
Wani irin takaici da haushin Siraj ya kuma shak'ure masa mak'oshi... Shafe goshinsa ya d'anyi yana k'ok'arin shanye takaicin Siraj d'in kana ya d'ago fuska yana mai dubansa yake fad'in "Siraj this is the condition, Akwai Uncle d'inta guda d'aya da yayi saura yana can garin Bama ta jihar Borno, ashe wajen shi ta gudu so shi kuma yana maganar aurar da ita ma koma waye, duk wanda yayi ra'ayi, shine ya kirani yana sanar dani zai mata aure in three weeks time, so ni kuma nasan yanda kake k'aunar Azeeza shine na nemi alfarma wajensa a matsayina na wanda ya rik'e Azeeza ya kuma bata kulawa na d'an gajeren lokaci da ya bani damar ragamar aurar da Azeeza a nan Abuja idan lokacin yayi da mijin da ya zab'a mata d'in, kaga ni kuma sai nayi amfani da wannan damar na aura maka Azeeza, so kaji plan d'in yanda ya kasance...."
Siraj gaba d'aya murmushin dake bisa fuskarsa ta kasa gushewa, ta yaya zai soma godiyawa Nasaar, yayi masa hallaci iri-iri a rayuwa, yayi masa abubuwan da sam bazai iya biyansa ba dukda cewa yana aiki k'ark'ashin company d'insu, Nasaar ya cika aboki na k'warai... Baisan sanda yayi hugging Nasaar d'in ba yanai masa godiya...
Shiko Nasaar wani irin zogi zuciyarsa ke masa, ya k'ware wajen tsara kalamai a matsayinsa na lawya shiyasa sam bai shan wahala wajen manipulating mutane....
Daga nan kai tsaye gida Siraj ya wuce da zummar sanar da Family d'insa batun saka auren nasa wanda ya kasance cikin gaggawa, ya sani Azeeza tana k'aunarsa can k'asar zuciyarsa ke raya masa wani abin ke damunta, Da dai ya bari a aura mata wani can wanda bata so gwara ya amince da auren nata koda bada saninta bane ya tabbata daga baya al'amra zasu daidaita cikin yardar Allah....
A b'angaren Nasaar kuwa kiran Mai gidansa Bulama ne ya shigo masa, take ya sanar dashi yana son ganinsa can gidan da suka saba had'uwa.....
Zaune yayi a parlorn yana jiran sauk'owan Bulama, mintoci kad'an ya sauk'o downstairs kaman kullum rik'eda sandarsa da yake dogarawa....
Yana isowa Nasaar ya mik'e ya isa garesa had'ida mik'a masa hannu, cikeda risinawa yake gaidashi...
Bulama ya amsa cikeda izza da isa kaman dai yanda yake a d'abi'arsa....
"Nasaar na kiraka ne kan maganar Junaid...." Ya fad'i cikin muryarsa da tsufa da girma ya kama sosai...
Jinjina kai Nasaar yayi yana mai ci gaba da dubansa yake fad'in "Alright Alhaji ina saurarenka...."
Bulama ya kuma jinjina kai kana yaci gaba da fad'in "Inaso ka samo min wancan police d'in da Junaid yayi amfani dashi wajen ganin bayan Ahidjo, ina son ganinsa cikin gaggawa sabida idan babu shi aikinmu bazai kammala ba...."
K'uri Nasaar yayi Bulama had'ida sauk'e ajiyan zuciya kana ya shiga jinjina kai yana fad'in "An gama Alhaji, zan nemo Sabi'u a duk yanda ya shiga ya fita...."
Bulama ya kuma jinjina kai murmushi kwance saman fuskarsa kana yace "Na yarda dakai d'ari bisa d'ari Nasaar, banada haufi akanka..."
K'ak'aro murmushi Nasaar yayi kana ya masa godiya lokaci guda yake k'ok'arin mik'ewa domin barin gidan, gaba d'aya Nasaar bashi a hayyacinsa sabida tunanin Azeeza dake neman zautar dashi, ga wani sabon aikin da Bulama ya b'ullo masa dashi, dole yanzu yasan yanda zaiyi ya cimma Sabi'u ko a ina yake kafin Bulama ya ankare da abinda yake shirin aikatawa, babban dad'in da yaji shine rashin tambayarsa inasu Hammad suke don ko shakka babu da ace ya tambayesa da bai san mai zai sanar dashi ba, sauri-sauri ya fice daga gidan kana ganinsa basai ance maka damuwa da d'imauta sun taru sun masa yawa ba.... Tabbas duk wanda ke aikata ba dai-dai ba bai tab'a samun nutsuwa da kwanciyar hankali saidai shi ya kasa fahimtar hakan....
***
A b'angaren Nana A sam bata iya ci gaba da zama a foundation d'in ba, dukda babu yanda Aunty Lami batayi ba domin ta sanar da ita mai ke faruwa, tana ficewa Cab ta shige abinda bata tab'a yi ba don bazata iya jiran Malam Sile yazo d'aukanta ba...